Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   33 / 54

96K to 99K   out of 159.5K words

jaje kennan, idan kuwa maman malan ta yarda ta kai magariba to fa tabas zata ga malan a bayanta ya je nemanta

Sai da ta rakata har tsakar gida, kiri.kiri mai dakin tsakiya ta yi dariya a bayane sannan ta ce" wani lamarin sai a gidan mu, yaro ya je bariki ya dawo a ci gaba da ririta shi ana kara tura shi wani barikin

Ikon Allah ko kallonta Hafsat bata yi ba bale ta nuna ta ji me ta ce ko ta tankata, wannan abin shi ke kara basu haushi dan irin ta tanka mutun din nan irin na da a yi ta masifa har yayansu su kai mata duka su ce ta yiwa masu rashin kunya basa samu, du inda ta je din nan ya kware su dan magana ba irin wada basa yaba mata aman sai ta zama tamkar dutse ta ki motsi ta ki nuna ta ji bare har a yi fitinar da zata fitar da malan ! A haka basa tunanin zasu ci galaba a burin sakawa uban ya tsaneta harma ya koreta, wau shi malan karfin imani da daukan kadara ko? Yarinya ta je yawon ta zubar ta dawo masa aman ba wanda ya ji inda ya yi mata fada da daga murya ma bale a yi tunanin duka da kora, aa sau nasiha da nuna soyaya!

Tsaki ta ja masu mai karfi sannan ta ja gefe ta tsaya tana kallonsu tana son jin me za.a cewa Hafsat

Mama ta kali Hafsar fuska a hade ta ce" *ANMIH,* ki tabata magariba ta yi maki a gida in sha Allah, Allah ya tsare ki da dukan sharin abin shari, Allah ya kare ki ya shirye ki

A hankali Hafsat ta amsata da amen Mamana, sannan ta juya ta sa kai ta fice tana dariya cikin ranta, sarai ta gane nufin matar babanta so take ta tankata a dawo kada mata rashin mutuncin, bata san Kutkale da horon zama Bodyguard ya horeta zama kurma sannan makauniya gaban du wani abinda ta yi niya, sai ta yi niya zata tanka koma menene, idan ta ki ba zata tanka komai ba walahi!


A hankali take tafia da pos fara kal a hannunta har ta isa bakin titi
Tana tsayar da taxi ta fada masa Butik din da zai kaita sannan ta shiga gidan gaba ta daura belt ya ja suka kama hanya

Kanta ta sada dan irin yanda fuska da yawa ke binta da kallo irin kugun kallon nan mai sakawa a fadi,
Ta san kallonta suke dan su gane wai ita ce ko ba ita ba?

A haka mai taxin ya tsaya ta cire kudinsa ta bashi ya bata canji a cikin kudin da Malan ya bata

Sai da ta daga kanta ta karanta tankamemen rubutun dake jikin Boutik din kafin ta zagaya a hankali ta je hanyar shigar

Matar dake tsaye da abin caje mutun ce ta cajeta sannan ta shiga
Sai da ta yi tafia mai dan tsayi kafin ta tura madubin wajen ta shige
Zuwa ta yi wajen accenseur ta shiga domin inda zara yi siyayar dole shi zai kaita ki ta yi ta hawan matatakala har sai ta hau hawa tara!

Tana fitowa a nitse ta taka ta je wajen da ake siyar da liptom din, lipton din malan kennan, wanda yake anfani da shi

Gidan Lipton din kansa abin kallo ne, kwaya daya ne ta siyo aka saka mata a jakar Butik din, sannan ta fita ta nufi ainafin aiken da akai mata wato siyen shada gizner ta babar sallar dake karasowa tata da kuma ta yayarta wace yayar tata ce da kanta ta kawo mata kudin kan ta je ta siyo masu ta kai masu wajen mai dinkinta

Tana shiga wajen mai tsaron wajen wani bature ne jajajir da shi da gilas dinsa na karin ganni yana zaune da jaridarsa a hannunsa yana karantawa da ganninsa saurayi ne mai jinni a jika hutu ya kwonta masa

Wajen shadojin ta je tana dubawa cikin nutsuwa ba tare fa ta yi kwaramniya ko ta tsaya a cito mata ba

Tun fa ta shigo yake kallonta, dan da yawa wasun idan suka shigo sai su wani zarto wajensa su shiga tambayarsa inda zasu je su dauko abinda suka zo nema bayan ga komai a ajiye idan ka zo zaka kala ne a katon screnn din kana dudubawa har ka samu wace ta yi maka sai ka nuna a ciro maka ka biya kudin ka juya abinka aman sai an yi ta basu wahala

Mai ruwan maroon mai manyan zane ta tafi da ita, dan haka sai kawai ta danna daidai ita sannan ta juya ta je wajen biyan ta ciro kudin a pos dinta ta mika ta tsaya tana jira mai gidan nasu ya bata canjinya ta juya abinta

Canjin ya taso sa kansa ya miko mata yana kallonta, da yannayin gimshewa ya miko mata makekiyar wayarsa ba tare da ya yi wani dogon magana ba ya ce" No

Wayar ta kala, sannan ta bi hannayen nasa da kallo masu dauke da gashin jiki sosai kalar fatarsa dan ba bakake bane gashin a haka har ta kai fuskarsa dake dauke da dan karanmin saje dan siriri
Sai da ta wana idannuwanta tana kallon yanda yake wani tsarewa yana wani kamewa abinsa
A hankali ta yarfe shi da idannuwan nata da suka dauki bakin kwali suka kara fitowa radau da su sannan ta buda labanta cikin wani yannayi na shegantakar da ta koya wajen Abdul a wani irin hankali ta ce" *Baka da saje da gemu*

Tana gama fada ta karbi jakar kayan ta juta da canjinta tana sakawa cikin pos dinta

Idannuwansa ya firfitar da matsanancin mamaki sannan ya kali madubin wajen da ya zagaye ko.ina,
Na farko a rayuwarsa an fizga shi, wai bashi da saje, saje kuma a me?
Ina ba zai barta ta tafi haka ba bayan ta zama ta farko da ta ki shi fan saje

Juyawa ya yi wajen yaran nasa ya ga du sun kawar da dubansu a kansa wato suna kallon du abinda ya faru?

Juyawa ya yi ya shiga bin bayanta a hankali jar suka fito bakin inda zata dauki taxi

Shi dai bai gane taxi ne zata dauka ba sai da ya ga ta tsayar da daya yace ba can ya nufa ba mamaki ya kara kashe shi,
Bama ta da motar kanta? Aman ta iya dizga namiji kamarsa? Ko dai dan ya biyota ne? Aa, ko dai tana da aure? Ko kuma mata take so?

Shi daya ya yiwa kansa tambayoyin da sun kai biyar aman ba amsa dan haka yake tsaye yana magana ko zata saurare shi har ta amsa kiran wayar da ajau ta yi mata inda ta fadi sunnan Boutik din fa take sannan ta ci gaba da neman taxi domin lokacin saukar aikin yama ya yi taxi na wahala sosai bare anguwar yan gayu taxi na wahala sosai.......




>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 1??


Cikin yannayin rashin tsoro da kyama take duban keayar idannuwan Muhammad dake dan langi sakamakon kwayoyin da ya hadiya ta shiga mayar da zancen duka kaf da ta gano wajen bincikenta, da irin sato tan da suka yi shi da sojansa mai bashi goyon baya, da komai da komai

Sai da ta ja numfashi ta kai dubanta wajen BS da har jikinda bari yake tsabar firgita da ikon Allahn nan, ya ga lamari da yawa, ya ga gaba da yawa, aman bai taba gannin ci amana irin wannan ba

Idannuwanta cike da hawaye ta ce" wannan da kake gani, wanda ba zan iya kiransa da madaukakin sunna irin MUHAMMAD ba, domin ya kasance azalumi, mai izgili da rashin tsoron Allah, wannan aljanin mutumen wanda ban ga sunnan da ya dace da shi a musulunce ba!

Ta kuma rinyse idannuwanta sannan ta ce" *shi ne mai kashe kashen nan baki daya ban cire maka ko daya ba, kuma yana yi ne dan vengeance*

Sai da BS ya dafe gaban kirjinsa dan luguden kidan da yake masa,

Dubansa ya kai wajen algungumin a daidai lokacin da ya daga hannunsa ya nuna Hafsat ya ce" karya ne!


Gindin bindigarsa ya saka ya daki keyarsa hakan ya katse masa fitsarar da ya dauko a bakinsa ya silale wajen a sume

Da kallo ya bi shi sannan ya bada umarnin a nufi asibiti da Abdul da Hafsat
Shi kuwa ya dadaure Muhammad dauri irin na huhun goro sannan ya shiga bincike da harhada du abubuwan da zasu isa cikaken shaida haka kuma ya tabo ikon garin wa.inda bai isa ya aiwatarwa da Muhammad wani abu ba sai abinda aka yanke masa a kotu

A lokacin da aka saka masa ankwa bayan sun dankara masa wata gigitaciyar allura mai taba kwakwaluwa aminin Abdul mai sunna Ahmad ya yi tsai yana kallon motar da aka shigar da shi baima san inda kansa yake ba,
Tabas shima ya girgiza, sai dai da wuri ya kwabi kansa a lokacin da ya tuna cewa Muhammad fa mutun ne, dan adam ba, dukan abubuwan da ya ringa yi ke dawo masa a idannuwansa,
Sai da ya kalli BS dake kokarin tayar da mota dan bin bayan su Abdul sannan shima ya buda motar da shiga wace ke dauke da gagan sojoji wa.inda ba alamar sun taba sannin wani abu mai sunna dariya a rayuwarsu sannan ya gyada kai a ransa ya ayyana........shara.ar Muhammad ya dace a barwa Allah, bai ga hukuncin da za.a yiwa wannan bawa a nan cikin duniya ba, bai ga irin abinda za.a iya yiwa wannan bawa ba a huce ko a rama irin abubuwan da ya shuka, tabas zasu tura shi kasarsa a hukuntashi a can, ya tabata kisa ne ta hanya mafi muni ya je can kuma ya fuskanci wanda ya halice shi!



A asibiti kuwa tun a hanya BS ya samu ya kirayi number Malan, domin tun ranar da Abdul ya je BS ya gane akoy fahimta tsakanin datijon da Abdul, a irin yanda Abdul ya zame kasa ya duka ya gaishe shi wanda hakan shi ne gannin farko da ya yi ya mutunta mutun

Bayanin da ya yiwa malan ya saka shi jin zufa ta keto masa, cikin nutsuwa ya nuna masa cewa da zai samu jirgi a lokacin tabas da ya zo da kansa domin kuwa dole Abdul na bukatar mutun a kusa da shi

BS na jin haka ya ce da shi ya kasance cikin shiri koda yaushe ana iya zuwa daukansa in sha Allah za.a kawo shi

BS ma karasawa ya tarar likitoci na kan Abdul , famansu shi ne su dawo da numfashinsa da bugawar zuciyarsa daidai,

Hafsat kuwa na zaune saman kujera an saka mata magana a fuskarta an gyara mata an yi an yi ta kwonta ta huta aman ta kasa tana zaune ta saka wata riga baka mai dogon hannu aman bata canza wandon jikinta ba ta faure kanta da dan kwali baki ta yi zuru da ita tana kallon waje daya, a kasan zuciyarta kuwa sai adu.a take kan Allah ya sa ya yi hakuri ya dauki komai da sauki

Sun dauki kusan awa kafin a fitar da shi a kai shi dakin hutu sai a lokacin ta mike ta koma dakin da ya dace a kwontar da ita ta shiga bayi ta yi wani irin wanka sannan ta fito ta dauki wani wandon da rigar baka da hijab da Hasana ta kawo mata ta saka ta kabarta sallah a nitse

Ta jima tana ramuwar salolin dake kanta, ta dauki lokaci tana sallah kafin ta salamce ta shiga adu.a da godiya ga Allah

Jaka kawai ta tsinci kanta da yi masa adu.a mai nauyin gaske, ta jima tana rokon Allah ya taimaketa ya ji kanta duda baya barin wani dan wani ya ji dadi ita kam bata tunanin zata ci gaba da walwala idan bai mike ya samu kansa ba

Tana ta jero adu.o.in ta ji wata kamilaliyar murya, nitsatsiyar murya, muryar da ta kasance mai yi mata nasiha da lalaba ta, muryar dake tsananin girmamata ta hanyar kiranta *UWATA* muryar da ta kasance daya daga cikin adu.o.inta na Allah ya nuna mata ranar da zata kara jin muryar a duniya

Kasa kunne ta yi tana mai jin zuciyarya na bugawa a lokacin da ta ji BS ya yi magana sai kuma ta ji muryar ta ce" Allahu ya tashi kafadar bawan Allah, ya bashi lada da juriyar wannan jarabawa, domin Abdallah mutumen kirki ne

Wata irin mikewa ta yi ta doshi kofar, sai dai me, Hasana ce ta riko hannunta da karfin gaske ta ce" ki koma ki zauna H, kar ki jazawa kanki kin san kina cikin mission ne

Wani kallo ta yiwa hannunta da ta riketa da shi sannan ta ce" ki cika ni

Hasana ta saketa ta ce" zaki lalata aikin ne

Hafsat bata ce da ita komai ba ta buda dakin da saurin gaske ta fita

Tsayuwa ta yi ta shaki kamshin turaransa, bai canza shi ba shi dai ne har yanzu,

Da sauri ta shiga raraba ido tana neman inda zata gan shi, ina zata ga hasken idanniyarta,

Kyalkyalin tazbaha da ta gani a daidai kofar dakin da aka saka Abdul ya sakata nufar wajen har tana hardewa , muryarta ta buda ta ce" *ABANA*

Da sauri ya saki kofar da ya buda da jiyar shiga domin likita ya ce ana iya shiga Abdul ya farka ya juyo inda ya ji muryar

Ita ce tsaye gabansa
A hankali ya furta" Alhamdulilah.... *UWATA*

AI kuwa Hafsat ta fashe da kuka sannan ta arta a guje , tana zuwa ba wata wata ta fada jikin mahaifinta ta kankame hannunsa tana wani irin kuka , bata wani damu da tunawa ya hana su fadawa jikinsa ba, ko jikin wani namijin haka kawai ba, shi kansa sai da ya ji kwala ta cika idannuwansa sannan ya yi mamakin yanda mamansa ta girma a dan lokacin nan fuskarta ta nuna alamun ta nutsu.

A hankali ya cirata a jikinsa yana kallonta ya ce" ya isa haka ko Uwata?

Tana haki da komai ta ce" Aba, ba guduwa na yi ba Abana, Abana ka min auren da du wanda ka zaba min na maka alkawarin da zauna da shi koda kuwa yankan naman jikina yake, Abana ka yafe min, ina mamana? Abana ka san inda aka kai ni? Ka san me aka min? Abana gidan yarin *KUTKALE* aka kai ni a matsayin wace ta yi laifi na zama budurwar dan ta.ada, Abana daga nan aka kai ni .....

*UWATA* ya fada cikin nutsuwa yana kallonta,

Hannunsa ya saka ya share hawayenta sannan ya ce" Abdallah ya je ya fada min,

Shiru ta yi tana kallonsa, sai a lokacin mamaki ya kamata na jin wai Abdallah ya je wajen mahaifinya ya fada masa wannan maganar,
Ikon Allah, sai yanzu tunanin me ya zo yi asibitin ya dirar mata,

Dubanta ta kai cikin dakin marar lafiar nan ta hango Abdul kuri su yake kallo
Gabanta ne ta ji ya yanke ya fadi lokaci daya kuma ta damki hannun mahaifinta a hankali ta ce" Abana, ya farka

Malan ya kai dubansa wajen Abdul din, ya ga gaba daya hankalinsa a kansu dan haka ya ja hannunta da niyar shiga da ita, sai dai ga mamakinsa hannun ne ya fara rawa ta kasa motsawa harma ta iya furta cewa" Aba

Tsayawa ya kuma yi da mamaki ya kalli yannayinta, a hankali ya cika hannun nata sannan ya juya ya shiga dakin , sai dai ya kasa rufe kofar dan du ji yake idan ya rufe ba zai bude ya kuma ganninta a wajen ba

BS ne ya zo ya yi mata magana fuskarsa a tamke hakan ya sakata bin bayansa suka je suka tsaya nesa da dakin, bai ce da ita komai ba sai dai shirun da ya yi shima yana kallon waje daya kamar yanda ya ga hankalinta ya raja.a dakin da mahaifinta da kuma Abdul ke ciki

Tun da malan ya shiga ya nemi waje ya zauna, ba abinda yake karantawa Abdul sai girman hakuri mahinmancinsa da sakamakon da ake samu mai kyau idan an yi shi,
Jarabawar da ya shiga mai girma da duhu ya ringa bashi baki da musalai da kuma ribar da zai samu idan ya yi hakuri da ita a hakan,

Shiru ya yi yana kallon yanda Abdul ke kallon kasa bai ce da shi komai ba
Ci gaba ya yi da bashi baki, da nuna masa kar ya dauki maganar cewa zai dauki fansa shima, hakan ba zai kai shi ga ci ba, ba zai samu wata nasara ba

Abdul ya dago idannuwansa da suka yi jajajir da mugun nauyin da sukai masa ya sauke a kan malan
Sai da ya hadiyi yawu mai daci da kuma yauki a hankali ya ce" ba komai *ABA, ALLAH YA JIKAN DU WA.INDA SUKA MUTU*
Sai da ya ji zuciyarsa ta girgiza, ba komai fa yace? Tabas yana iya karbar abin aman ba komai din na lokaci daya ya bashi mamaki, ko dan yana cikin hali na rashin dadin yannayi shi sai ya ce kamar yau baya cikin yan magana ma,

Ajiyar zuciya ya sauke ya mike da niyar fita, sai dai

33 / 54