Kutkale Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Sajida Niger Category :  Love

Chapter   14 / 54

39K to 42K   out of 159.5K words

aminta ya yi masa voice cewar yana cikin duhu mai tsanani, yana son adu.ar da zai lazumta ko Allah ya warware masa haske a duhu
Shi ne ya ringa taimaka masa da adu.o.i da shawarwari, a wadinnan lokutan har ya bashi kadan daga cikin labarin rayuwarsa ya boye masa wasu, ya dai shaida masa ana harin rayuwarsa ne,
Cikin muryar datako ya ce" Abdul Jabar kana ji? Ba wanda ya isa ya saka , ko ya hana sai Allah, tabas Allahn da ya ankarar da kai cewa ana harin rayuwarka, shi ke tsare ka, ina so ka farga cewa da ya yi niyar baiwa mai bin sahunka sa.a a kanka da tuni mai faruwa da kai ta faru,
Mai runfar na sama yana kallo Abdul,
Kuma wannan magana da ka ce an fada maka cewa makashinka na tare da kai, kar ya baka damar zargin kowa, wannan ma kuskure ne, ka dai ci gaba da adu.ar in sha Allahu Allah zai kawar da mai son kawar da kai da kansa

Kansa yake gyadawa har ya gama sauraron muryar datijon mai magana cikin nutsuwa, wanda ke amsa kiransa bayan bai taba haduwa da shi ba, bai san ko shi waye ba, bai san ko mai niyar cutar da shi bane ko na kirki ne? Wato su dai malamanmu Allah ya saka masu da alkhairi, suna aikin Allah tare da dogaro da shi da zuciya daya da imanin du abinda ya same su daga shi ne,
Ajiye wayar ya yi yana lankwasa yatsutsansa,

Ya yi mata magana kan kar ta saka kanta a wannan lamari, lale zai ji dadi idan ta bi maganarsa, shi ya sa bai mata maganar da wata hayaniya ba , ya bita a laluma ya kwatanta mata wannan sako daga cikin ransa yake

Wani digon tsaki ya ja ya mike ya shiga cire kayansa dan kara shiga ya yi wanka ya je bangaren bakuwarsa mai rawar kai, wace ya dasawa hajia=? ?, a fili ya ce" Hafsat, bakya jin magana! Mai taurin kai kawai! Uwar gardama,=?D?, mai kyauna=? ?


Hafsat na fita a dakin Abdul zuwa ta yi ta dauki abubuwan aikinta ta fito cikin tafiar basarwa irin tana cikin aikinta ne na kare lafiar Abdul ta nufi garden ,

Tana zuwa wajen abin shilawar wajen ta je cikin sando ta makala abin hannunta sannan ta bar wajen ta kuma dauki hanyar dakin Furaira

Tana zuwa sojan dake kofar tsaye ya hanata shiga, ya ce oga ya hana kowa shiga

Bakinta ta yatsina ta juya tana kallon yannayin wajen da fatan abinda ta wurga a lokacin da ta daga hannunta da niyar shafa gashinta ya makalu a labulen dakin,

Bangaren su Abdul ta koma cikin nutsuwa take takunta ta nufi dakin Ni.ima

Tana zuwa ta shige dan a nan ba wanda zai hanata shiga

Tana shiga ta tarar da Ni.ima na zaune gaban madubin dakinta ta dira kanta saman table din madubin hannunta rike da tamfatsetsiyar wayarta

Bata ji shigowar mutun ba hakan ya sa bata motsa ba, wannan ya baiwa Hafsat damar aiwatar da du abinda ya kaita dakin sannan ta juya ta fice ba tare da ta san ta shigo dakinta bama ta lula duniyar tunanin damuwar dake damunta

Haka Hafsat ta kara sadadawa ta shige dakin Muhammad domin sojojin dake gadin kofarsa sunna tsakar gida sai zagaye suke tun da aka yi harbin nan,

Sadadawa ta yi ta shige dakin, abinda ya kaita ta aiwayar ta zo fita kennan ya fito daga bayi daidai kuma Abdul ya shigo dakin

Da mamaki Abdul ya kaleta, inda Muhammad ya ce" aa, yau harda yar rakiyar taka kake tafe har cikin dakin nawa?

Abdul ya tsurawa hafsat ido, ita kuwa ta sada kanta kasa ta raba shi ta fice a dakin hakan ya baiwa Abdul damar shigewa ciki yana mai jin ransa na suya,
Me ta zo yi dakin nan? Me ya kawota? Ba dai abinda ya hanata ne take kokarin daura aniyar yi ba?

Haka ya je suka tatauna da amininsa, dan uwansa kafin ya mike ya zarce dakin Furaira

Gaba daya hirar da ya yi da matar bai fahimci komai ba sai tsabar bariki dake dawainiya da ita,
Karara ya fahimci cewa abin duniya ya rufe mata ido, kuma shi ke janye da ragamar rayuwarta
Dan haka ya biyewa sallon kidanta suka doka gangar iya iyawarta ya bari bangarenta bayan ya nuna mata kudi akoysu, wanfa hakan ya sakata kara share waje ta baza tabarmarta



Kwonci tashi, har an kara sati biyu cikin wannan hali,
A cikin gidan Abdul, an ci gaba da fuskantar hatsaririka kala kala,
Du wani wanda ke gidan ya koyi sannin mahinmancin lumfashinsa, irin hare haren da aka ringa kawowa ya saka kowa ya gane cewa rai ba karamin abu mai daraja bane da Allah ya arawa bawa wanda yake iya karbarsa a kowani lokaci, hakan ya saka musulman ciki suka kara mayar da kansa wa Allah, christocinma suka kara rike adinnin su,

Har yanzu Furaira na gidan, wanda take son fitarsa ido rufe aman cikin ikon allah Allah hakan ya gagara ta rasa dalilin da ya sa du irin iya barikinta da wayonta ta kasa samo kalaman da zasu saka shi barinta tafiarta dan kuwa tana son fita a gidan

Hafsat na nan har ta fada ina nufin ta rame tsabar irin yanda ta sakawa kanta damuwar wani a ranta, dan kuwa ta zama tamkar fatalwa wajen iya leken asiri da daukan rahiranni tana hadawa a cikin kundin bincikenta dan samun amsa gamsashiya wa hasashen da take wanda ke nukurkusarta ita kanta yana bata tsoro, dan kuwa amsar da take hangowa bata tunanin idan ta fito fili za.a wanye lafia

A tsakiyar daren talata, a wannan rana ce Hafsat ta saurari wayar da ta firgitata,
A wannan rana ne ta fito da niyar zuwa dakin Abdul a talatainin dare,
A wannan rana ne aka wayi gari ba Hafsat ba labarinta,

A lokacin da BS ya shiga dakinta gannin har karfe tara da rabi ta fice bata fito ba bayan hakan ba sabonta bane yana shiga ya tarar ba computenta, ba wayarta, ba du wani abin aikinta an kwashe babu ita babu alamunta,
Hakan ya saka kansa sarawa ya fito da gudu yana harhada du wani ma.aikacinsa suka rarabu suka shiga nemanta ilahirin gidan

A haka ya je dakin Abdul da ya gama ganawa da Ni.ima ya shiga a firgice yana mai tambayar a yau ko ya ga Hafsat?

Abdul dake zaune saman salaua ya dago a hankali tare da rintse ido dan irin yanda gabansa ya yanke ta fadi ya kali BS ba tare da ya yi masa tambaya ba, yana jiran karin bayani

BS ya ce" mun nemeta bata nan, wannan batan ba irin wanda ta saba ficewa bane domin ba kayanta a dakinta

Wata irin mikewa Abdul ya yi tsaye, lokaci guda kuma ya dafe kujerar dake kusa da shi domin wani irin jiri ne ya ji ya zo ya rufe idannuwansa,


Da wani irin ihu ya ce" ina take? Ina ta shiga?

A hankali kuma ya shiga rage muryarsa yana magana tamkar wanda ya zauce cewa" sai da na hana ki, sai da na hana ki, kin gano ne? Kin gono ko waye? Kin gano an ganki kafin ki fada ne? Ina kike? Kina ina? Ki zo gare ni?????








...........saura kirisssssss


>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 3??



Yannayin shigarsa , ba zai tabatar maka da shi din ko wanene ba koda kuwa ka saba gannin jalabiyoyi masu tsada,
A yau , ranar da aka daura aurensa, suka dauki hanyar zuwa dauko mutanen da zasu kasance masu basu tsaro, cikin tawagarsu, da mutanen Muhammad amininsa, da mutanen Elhaj, da auntynsa da amaryar tasa kanta wace ta sha abaya sai walwali take goshin amare na kara haskata, sai shi,
Jalabiya mai shigen milk ce ya saka,
Bai wani gyara kasumbar da ya ajiye ba, tana nan yanda take, saima kara cajeta da ya yi ya dora hirami saman kansa,
Sai takalmi da ya zura mai shige da silifas inda Muhammad ya sha farar shada ta karbe shi sai annuri yake bazawa tamkar shi ne angon,
Dubansa ya yi a lokacin da ya gama shirin ya ce da shi" daurin aurenka ne zamu je fa Abdul?

Abdul ya dage girarsa guda yana dubansa sannan ya ce" na *Shida* ba, ina cike da zumudin ku gama jana a kasa ku bani macen ta sakar min mara!

Kansa kawai ya girgiza, domin kuwa lamarij na abdul tamkar wanda akaiwa asirin da mace? Baya iya boye bukatuwarsa da harkar mace ko a gaban waye, wannan abin ba da shi aka haife shi ba, domin ya san shi ba yau ba, sun yi karatu tare sun yi yawo tar, wannan lamari ya same shi ne daga baya, yana mai binsa da kyakyawar adu.a......yana mai cike da tausayin Ni.ima da ya fahimci irin yanda take rawar kai da murnar samunsa a matsayin miji, bai san yaya zata iya da tashin hankalin jarabar mijin nata ba bale idan suka daga baki daya suka kara yin nesa da iyayenta, wato suka juya saudiya


GN ne da kansa ya laya Bodyguard din da yake ji da su maza da matan biyu rak dake iya tafia, domin kuwa biyun suna asibiti wannan rigimar sai da ta kaisu da shan matsiyacin dukan da aka kwontar da su!

Da kansa Elhajin ya bi layin mazan dake tsatsaye, cikin sannin aikinsa da irin kwazonsu ya zakulo maza biyu da BS cikon na ukun domin kuwa har shi ya nemi da a laya duda irin tsadar aikinsa,

A haka ya dawo wajen yan matan, dayar ta fi Hafsat tsayi, da yannayin alamun karfi, Hafsat a yannayin jikinta ba zaka taba tunaninma wai zata saka kafa a wajen nan,
Dan haka ya juyo wajen GN ya maida shi gefe cikin yannayin damuwa ya ce" GN, wannan yarinyar ba zata iya aikinmu ba, ana son yarinya daya da namiji daya su baiwa Ni.ima tsaro, yarinya daya da maza biyu kuwa su baiwa mijinta tsaro ne, dayar da alamun karfi a tatare da ita, aman wannan bana jin zata wani iya wanu abu,

GN cikin yannayin son a yarda da maganarsa ya ce" na yarda da formation din yarinyar, na matukar yarda da ta tsaya saman kaina a lokacin da ba bace cikin jeji, in sha Allah kwakwaluwarta mai ja ce,

Yar gidan waye?

Sai da gaban GN ya fadi, domin Elhaj na daya daga cikin wa.inda suka so bashi wahala sosai kan a fitar da ita a sakata wannan aikin,
Aman ya ya iya, ya fada masa gaskiyar ita ce wace aka fitar daga *KUTKALE*

kana nufin, matar dan ta.adan zaka bamu a matsayin wace zamu je da ita da yarda ta baiwa iyalina tsaro?,

GN ya sada kansa, domin mai gidansa ne, bashi da bakin wani daga murya ko wani abin,
A tausashe ya ce" *a bakin raina*

Sosai abin ya bashi mamaki, a bakin ransa fa ya ce? Idan ta aikata wani abin a kama shi , idan ta kashe a kashe shi? Ya yarda ya daukarwa kansa wannan baban hatsarin a kan dan adam mai iya canzawa saboda kudi? Ko wani ra.ayi nasa mai girma ko marar girma?

Kansa ya jinjina kafin ya kai hannunsa ya daki kafadar GN ya ce" zamu yo signed kan ran ka! Aman kuma ba ita zata baiwa Ni.ima tsaro ba, sai dai ta hadu da baban yaronka su baiwa Oga Abdul Jabar tsaro! Ka ga a wajen namijin mun dauki wanda ya kware mun hada da Abdul, a wajen macen mun dauki wace ta kware mun hada da Ni.ima,

Murmushi GN ya yi a fili mai cike da ma.anoni, kafin su tatara su je a yi du abinda za.a yi, a tarkata su su dauki hanya , suna zuwa cikin gari suka dauki jirgi suka juya inda suka bar Aunty da mijinta,

Suna dira baban gidansa suka zarce,

Kowa na neman hutu banda masu tsaron su, da kuma shi kansa uban tafian,

A lokacin da ya ga Hafsat tsaye a bayansa matsayin wace du inda ya kutsa ta kutsa sai da ya rike kugu ya dafe habarsa ya kare mata kallo tun daga kafarta hat kanta sannan ya yi kwafa a ransa ya ayyana....yanzu wannan ai almubazaranci da sakani a uku ne, toh mana, maimakun na yi ta raina kadai sai na hada da ta jaririyar nan, idan ba son banza irin na iyayenta ba, ya zasu dauketa su kaita irin wannan aikin da sai mazan wajen sun gama kwakule masu yaya sannan a koya masu abubuwa irin na karti, su juye su dawo bawa karti tsaro? Wai yanzu wannan yar jaririyar ce zata kare wani abu ya same ni, ni wannan uban da ni, da na yi imanin da na yi aure da wuri da na zubawa matar cikin yan hudu irinta?

Haka ya juya ya shige inda Hafsat ta sha mamakin ashe wannan bakin mutumen mai sifar samudawan ne za.a baiwa tsaron? Ita walahi du ji take wancen balaraben mai sifar yayan gatan ne za.a baiwa tsaron, domin sam ba.a basu fuskar wata tambaya ko wani cikaken bayani a kan wannan aikin ba, dan kuwa Oga ne da kansa a tsaye a wajen wanda ita saima a ranar ta fara ganninsa da sannin matsayinsa a Niger.

Biye take da shi a lokacin da ya fito daga dakinsa, inda BS ya bita da kallo, ya so ace shi aka baiwa wannan aikin mai hatsari na ko menene sai ta fara duba zai iya anfani da shi, ko zai ci kai koma menene, ya so ace shi ne da wannan abin ba dan komai ba sai dan a yannayin aikin, wannan mutumen na cikin hadari sosai, wanda sai an yi da gaske, an baza ido, an baza komai kafin idan da rabo a samu galaba....

Kansa ya sada ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya ja dayan suka ci gaba da bincikar gidan lungu lungu da kayan aikinsu......

Shi dai bai ce da ita ta koma, ko ta tsaya ba, har suka karaso kofar dakin Ni.ima, wanda suka tarar da Bodyguards dinta tsaye bayin Allah kowanne a kame waje guda,
Sai da ya tsaya ya kara kama tsatso, wanda yake kamar sabonsa ne, ya kare masu kallo,
Murmushi ya yi a fili, shi walahi an kawo masa nishadi, yo nishadi mana, wanna lamari kamar gunkina? Ba um bare umum, du sun kame suna jiran uwar gidansu, shi ko a million goma a wuni ba zai iya irin wannan aikin ba!

Bude masa namijin ya yi ya shiga, sai dai ga mamakinsa, yarinyar dake biye da shi itama ta shigo,

Tsayuwa ya yi ya juyo ya dubeta, sannan ya kai dubansa wajen Ni.ima da ta mike da sauri daga ringeshen da ta yi cikin riga da wandonta na barci ,

Sai da ya ciro harshen sa , ya lashi lebensa na kasa sannan ya kara dubansu a tare,

Wani murmushin yan duniya ya yi, ya rike tsatsonsa ya dubeta da kyau kafin ya ragewa idannuwansa girma su dawo kalar baci ya ce" ni dai a sanina mace daya aka daura min aure da ita a yau, kuma wajenta na zo dan ta kama wannan abin ta rage masa nauyi (=?-?ni dai wannan labari a hargitse yake dan sakin magangannun ciki),
Da hannunsa ya nuna inda yake nufin a ragewa nauyi, wanda hakan ya saka su a tare rintse ido daga Hafsat din har Ni.imar, dan kuwa ba warda ta yi tunanin, ko a tsuman ranta cewa abinda zai aikata kennan,
Ci gaba ya yi da magana bayan ya wani rausayar da kai ya ce" zuwa na yi na kwonta da matata, ko yar biyu za.a yi?

Ya fada yana mai fitarwa da Hafsat gaba daya idannuwansa, sai kuma ya ja wani yaji yaji ya ce" ko a zina ba kyai hada biyu, bale yanzu na bar zina, kin ga ki dan fita na gama sai ki maida ni daki ko?

Hafsat kam, yau ta ga ubanta a rashin kunya, yau ta ga ikom Allah, da hasken gari ba wai dare ya yi ba, kiri kiri, ra.aine da ra.aine, kunne da kunne, ya dubi tsabar idannuwanta, da na wace a tunaninta a yau aka daura aurensu, ya gangantsaro wadinnan gantsara gantsaran magangannun?

Sai da ta lumshe idannuwanta ta hadiye wani yawu makwat, sannan ta daga kafafuwanta ta shiga kara saka kanta cikin dakin tana mai nufar.......


Comment plz=?O?

>???=???>???=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>???=???>???


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA

14 / 54