iyakarka asibitocen jahar, banda haka babu inda zaka iya zuwa a cikin Kano." Jamil yace.
"Yanzu na gama cewa su Iman su shirya anjima muje yawo shine suke min wani irin kallo ko basu yarda dani bane captain?" Haneef ya kallesu yana murmushi kafin ya maida idonsa kan Jamila yace.
"Haba! ba dai tsoro ba Dr, zata yiyu suna tsoran faɗan Mamah ne ko Iman?" Da sauri ta gyada masa kai alamar eh.
"Toh sai ka shirya muje harda kai tunda ni ne ba'a lamuncewa fita dasu ba." Haneef yai murmushi.
"Ni babu inda zanje, sai dai ku tafi da Areef. Kuma ba wai maganar ba'a yarda da kai bane. Mamah duk bata son irin wannan yawon, kasan iyayen mu sunfi bawa yara mata kulawa ta musamman fiye da namiji, wanda hakan yana da kyau tunda mace dole sai da sa ido akan ta."
"Haka ne gaskiya, kuma wannan tarbiya ce yana da kyau." Jamil yai maganar yana nuna gaskiyar maganar da abokin nasa ya yi.
"Karfe huɗu zamu fita kunga lokacin Mamah ta dawo, ku kuma sannan kunyi wanka sai muje."
Ganin Yaya Haneef yana dariya yasa su amsawa cike da murna banda Hanan wacce a lokacin take jin wani irin ciwon mara yana nuƙurkusarta. Areef ya fito daga cikin ɗakin shi fuskar nan a daure ya ƙarasa tare da gaishe da Haneef ya juya ya gaida Jamil a tsaitsaye sannan ya nufi kitchen.
*DA YAMMA*
Ƙarfe huɗu da rabi.
Mamah ta kalli yaran nata kowace tasha kyau sai ta samu kanta da yin murmushi wanda ita ta barwa kanta sanin kona menene. Daman tunda ta dawo daga wajan aiki suka sanar mata da fitar su bayan sun tabbatar mata da cewa Yaya Haneef ya amince da fitar hakan yasa bata wani ce baza su ba.
"Saura kuje kuyi ta rawar kai musamman ma ke Iman da Ikram, nasan bani da matsala da Hanan ku biyun nan wallahi kar inji kar in gani." Mamah ta faɗa cike da gargadi.
"Kai Mamah mu ɗin?" Iman ta faɗa cikin shagwaɓa.
"Kina zaton ban san halin kowa ba a cikin ku?"
"Kin sani mana." Cewar Ikram.
"Suna ina ne kun barmu a bakin gate kamar wasu samarin ku?" Haneef ya faɗa yana shigowa ɗakin.
"Woww babban Yaya harda kai zamuje?"
"Eh! Gani nayi babu abinda zanyi idan na zauna a gidan."
"Wallahi kayi kyau Yaya Captain, kai matarka ta caɓa."
Yayi dariya yana ƙarasawa wajan madubi. Kallon kansa ya shiga yi yana gyara belt ɗin jikinsa. Mamah ta kura masa ido tana murmushi tace.
"Ina yaga budurwar ma bare ayi tunanin mata, ina jin dai ni zan zaɓo masa da kai na."
Haneef ya juya tare da janyo stool ɗin madubi ya zauna yana cewa.
"Wallahi kuwa Mamah, dan kinsan bani da wacce nake so."
"Kai Yaya duk girman ka?" Iman tai maganar cikin mamaki tana zaro mayafinta daga drower.
"Wallahi kuwa. Ina naga matan ma bare na zaba? Kullum muna cikin jirgi akan ruwa."
"Aikuwa Yaya wallahi akwai wata ƙawata Jannat Allah ya zuba mata kaunar nevy, ko da ita za'a yi ne?"
Cewar Iman jikinta har rawa yake dan murnar zata zabawa Yayan su mata.
"Ke rufewa mutane baki zabiya. Kuzo ku wuce dan kar kuyi dare." Mamah ta faɗa tana dakatar da Iman.
Fita suka yi dukan su shima Haneef ya yiwa Mamah sallama yabi bayan su. A crv suka fita, Haneef ne mai tuki yana tambayar su inda zasu fara zuwa.
AREEF Shima ya fito cikin shirinsa sanye da riga da wando jeans, ya yi matuƙar kyau, suka hadu da Mamah a bakin ƙofa.
"Za'a fita kenan?" Ta tambayesa.
"Eh Mamah."
"Toh a dawo lafiya." Ya ce.
"Allah yasa."
Yana fita kiran Feenah ya shigo ya daga bayan ya tsaya daga ƙofar fita waje.
"Baby please ba zaka zo bane?."
"Zan zo mana, so nake na biya gurin Aslam na karbi mashin ɗin sa." Ya faɗa zuciyar shi na tsananta bugawa.
Baya son zuwa gurin da take saboda baya son tana yawan bijiro masa da dabi'un da basu dace dasu ba. Amman me? Zuciyar shi tana ƙawata masa alaƙar dake tsakaninshi da ita, yana kuma gudun karta zo gidan su nemansa, dan haka bashi da wani ƙwarin gwiwar ƙin zuwa gare ta.
A hankali yake tafiya har ya ƙarasa majalisar da Aslam yake zama, mukullin mashin ɗin ya karɓa ya nufi guest house ɗin Feenah wacce har zuwa wannan lokacin iyayenta basu san tana zuwa can ba.
Har cikin gidan ya shiga da mashin ɗin, suka gaisa da mai gadin sannan ya nufi ciki kai tsaye.
Tunda ya doshi ƙofar shiga cikin falon yaji wani irin fitinannan ƙamshi yana shiga cikin ƙofofin hancinsa. Jikinsa ya fara wani irin yammhhh...yammhh yana kuma buɗe hanci yana shaƙar sanyayyen turarukan da aka sanya, idanunsa sai yawo suke suna son hango masa ta inda zata fito. Ganin har ya gama baza idanu be ga fitowarta ba yasa shi samun guri ya zauna a falon.
Duk wani motsinsa yana kan idanuwanta har ya zauna. Ta kallesa ta cikin labule tare da sakin wani ƙayataccen murmushi, zuciyar ta na kuma narkewa da sabuwar ƙaunarsa. Cikin ranta tana ganin 'wai me yasa yake ganin kansa a matsayin ɗan ƙaramin yaro da har yake tunanin idan ya kai maganar auren su gurin iyayensa ba zasu yarda ya yi ba? Ta kuma kai kallonta jikinsa tana ƙare masa wani shu'umin kallo.
A hankali ta juya ciki ta kuma shafa wata arninyar khumra mai masifar ƙamshi da ta siya a gurin ceo ta yerwa incense & more. Kallon kanta tayi a cikin madubi tana bazarbaza gashi ta dauki jan baki ta shafa akan leɓanta, murmushi ta saki mai ban sha'awa da burgewa ta juya zuwa falo tana wata shegiyar tafiya. Idanunsa ya sarƙe a na juna Areef yai saurin kawar da kansa zuciyar shi na tsananin harbawa.
"Shine sai yanzu ko Baby?"
"Banyi sauri ba kenan?"
"Ni dai Allah nagaka daɗe baka ƙaraso ba, amman ina tunanin dan na ƙagu da son sanya ka cikin idona ne shi yasa naga dadewar."
Tana magana tana zama kusa dashi, da sauri ya ɗan janye jikinsa daga yadda yaji sun gogar ƙafaɗa junan su. Ya ɗan yi murmushi kaɗan tare da cewa.
"Gani nazo."
Ta kama hannunsa tana kallon fuskarsa, ya kasa kwacewa ji yake tamkar yana tsoranta ta yadda yake ji baya iya tsawatar mata akan abinda baya so tana yi masa.
"Bani da kuɗi Baby, kuma ina son zan ɗinka ankon nan dana ƙarbo. Tunda na dawo gidan mu su Daddy da Mommy suka dena yi min komai, ban da abinci da suke bani ko kuɗin auduga basa bani."
Danƙari anzo daidai wajan da yake ƙi wato tambayar kuɗi, waya bashi ballantana yace zai ɗauka? Ɗari biyu da ashirin ne a aljihunsa yake ta ajiya. Ya shafa kyakkyawar fuskarsa yana tunanin abinda zai gaya mata ta yadda ba zai bada kansa a gurinta ba.
"Baby kayi shiru. Kaga karka damu zuciyarka idan baka dasu."
"A'a kash (cash) ne babu sai dai ko nayi miki taransfa." Ya faɗa cikin dakiya da nuna rashin damuwa.
Wani farin ciki ya mamaye Feenah da sauri ta faɗa jikinsa ta rungume shi gagam, ji take tamkar ta shige cikin jikinsa saboda tsanani so. Shi kuwa rintsa ido ya yi yana cizon leɓe saboda kuɗin cikin bakin nasa, Abba ne ya turo yace ya ciro ya kaiwa Hajiya wato kakarsu, wacce mahaifiyar Abban ce, ta kirashi akan tana son kuɗi zatayi amfani dasu a ranar.
"Baby kayi kyau wallahi, Allah yasa dai da ka taho babu shegiyar yarinyar da ta ganka?" Tana magana hannunta yana kan maɓullayen rigarsa.
"Nida na taho akan mashin me zai haɗa ni da wasu ƴan mata?" Ya faɗa yana kallon yadda gashin kanta ke kalli yasha gyara.
"Akwai Mayu wallahi, kai kana tafiyarka hankali kwance, su kuma suna binka da kallo kamar zasu kwace ka."
"Ni ban hadu da kowa ba, zuciyarki ce kawai ke gaya miki haka."
Ya faɗa zuciyar shi na bashi umarnin shafa mata gashi, babu zato bare tsammani yaji saukar bakinta a nashi. Jikinsa ya mutu matuka hakan yasa ya kasa hanata har shima ya fara bada gudunmawa wajan tallafo fuskarta izuwa kan tashi. Suna ciki basu san da zuwan sa, yana daga bakin gate suna magana da mai gadi.
"Malam barka da yamma."
"Yauwa barka Alhaji."
"Tambaya nake ko nan gidan waye?"
"Ikon Allah, lafiya dai ko Alhaji?"
"Lafiya sumul malam kawai ina son na sani ne."
Mai gadin ya yi shiru yana ƙare masa kallo, a zahiri bai yi masa kama da mugu ba, bai kuma yi masa kalar ƴan damfara ba, hasalima mutum ne nagartacce da mutunci a ido. Dan haka mai gadin ya kalli gidan tare da kallan mutumin yace.
"Wannan gidan hutawa ne, kuma na wani yaro ne. Baya ƙasar nan amman ya bawa matarshi da suka rabu, dama da kuma ikon shiga. Toh yanzu haka dai itace a ciki sai kuma wani wanda shi kadai ta bani umarnin bari ya shiga ciki."
Gaban shi ne yai wani irin bugu, ya rintsa ido yana karanto addu'o'in da suke zuwa cikin zuciyar shi.
"Malam ka barni na shiga dan na tabbar da komeye. Idan kuma ba zaka bari na shiga ba Toh dole zan shigo da ƴan sanda, idan suka zo kuma harda kai zan sa a kama idan har zargina ya gama tabbata."
Jin anyi maganar ƴan sanda yasa mai gadin jujjuya kai tare da cewa.
"Duk bata kai nan ba Alhaji, Amman kai min alfarmar shiga na sanar da ita zuwan naka." Da sauri ya dakatar dashi ganin har ya mike zai shige.
"Ina son abin ne a sirrince gudun musu da kuma karyatawa. Kayi zamanka anan ni zan shiga ciki."
Babu yadda mai gadi ya iya, tunda yaji batun ƴan sanda yaji tsoro dan baya son yin abinda zai taɓa mutuncinsa. Sai dai ya kasa zama jikinsa sai rawa yake yi yana kuma leka cikin gidan.
Feenah ce ke tura Areef kan kujera, ƙoƙarin kwantar dashi take yana ɗan kakkaucewa har dai ta samu nasarar faɗawa jikinsa. A dai dai lokacin aka buɗe ƙofar tare da yaye labulan dake ƙofar. Hasken da suka gani ne yasa Feenah kallon bakin ƙofar, Areef ma da sauri ya tashi zaune duk suka zaro idanuwa ganin wanda ke tsaye ransa a matuƙar ɓace...... ✍️
_________________________
_Ohohooooo hooooo! 🤸♀? masu karatu, anan dole aka bani damar tsayawa da baku ɗanɗanon labarin ZO GARENI. Wai shin waye zai zo? 😂 me zai faru tsakanin Iman da Dr Jamil? Feenah da Areefullah? 😰 Wannan labarin na daban ne, tsarin na burgewa ne, darasin na musamman ne. ZO GARENI, yana cikin tafiyar Top 10 da Qungiyar Haske suka zaɓo muku, guda bakwai ne labaran duk akan naira ɗari biyar kacal. Ina wadanda suka biya? 😂 kuzo Muje kuji yadda za'a kafta._
_😳KIN SIYE SU 'YAR UWA?, KINA DA TANADINKI AHANNU?, KINA SO?, ZAKI KI KOYA?, SHIN KE CIKAKKIYAR MACECE? IDAN AMSARKI ITACE *EHHH..😅* 'YAR UWA INA YIMAKI SAMBARKA, I DAN KUMA AMSAR ITACE *A'A😥* TO MAZA KI HANZARTA KIYI REGISTER DA👇_
*TOP 10, TAKUN HASKE, BATCH A, INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI, 1- *ZO GARENI* NA HAJJACE, 2- *IBTISAM* NA AYUSHA MOH'D, 3- *WASU MAZAN* NA BILLY S FARI, 4- *AZAAD JUNAID* NA JEEDDAH ALIYU, 5- *WATA SOYAYYAR* NA OUM HANAN, 6- *NI DA RAHEEMAH* NA ASMY B ALIYU, 7- *KUKAN ZUCI* NA SLIMZY,💃💃💃KAI KAI KAI....!😱TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N500 KACAL, GA KUMA SHIRE-SHIRE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU DA KUKA ZABEMU, 1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍 DAGA CHIEF DEEJARH BARVER, 2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI HA'DA MAGUNGUNAN NI'IMA DANA KARIYA DAGA CUTAR INFECTION DA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA DAGA MAMAN KHADIJA, 3-SHIRIN KOYOR DA TSAFTA, GYARAN JIKI, GYARAN GIDA, SAMUN WARAKA DAGA MATSALTSALUN JINI DA SAURANSU DOMIN ZAMOWA FITILAR GIDANKI DAGA UMMI A'ISHA*
_WOHOHOOO DUKA FA AKAN NAIRARKI 'DARI BIYAR KACAL ZAKI MALLAKA. REGISTER A *TOP 10, TAKUN HASKE BATCH A* SAI KIGA KIN ZAMA QASAITATTAR MACE, ISASHSHIYA KUMA ZINARIYA AWAJEN MIJINKI!_
_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N500)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK AISHA M. SALIS
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼
+447894142004
_IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA WANNAN LAMBAR_👇🏼
07043079282
SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼
07065283730
_GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU 550F TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_
+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.
MUN GODE.
*HAJJA CE 👈.*
2/4/22, 11:20 - Buhainat: *ZGN*✍️
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*11*
Jikin Areef yayi mugun sanyi, banda bugawa da harbawa babu abinda zuciyar keyi saboda yasan yau kam ƙaryarsa ta ƙare. Yana tsaye ya rasa abin yi saboda ruɗewa hakan yasa biji lokacin da Alhajin ya ƙaraso kusa dashi ba. Cikin rashin sani yaji an ɗauke kyakkyawar fuskarshi da wani lafiyayyan mari. Feenah ta kalle shi a gigice tana dafe kunci tamkar ita aka yiwa marin, baki na rawa tace.
"Daddy mai yasa?"
"Ubanki ne, nace Ubanki ne yasa munafukar yarinya kawai." Ya kuma juyawa gurin Areef da ko motsin kirki bayayi saboda gigicewa.
"Kai! Ashe daman kai ne matsiyaci azzalumin da yake hure min kunnan yarinya? Kai wane irin shaiɗanine da har kayi sanadin fitowarta daga gidan mijinta? Kasan Allah? Wallahi idan na sake ganinka da ita sai na lahira ya fika jin daɗi. Kuma yanzu ma ba kyaleka zanyi ba sai nasa anyi maka shegen duka."
Yayi maganar yana shaƙo wuyan Areef, ganin yadda ake jan wuyan rigar Areef ne yasa Feenah kuma yunƙurawa ta nufe su, gaban su ta tsaya ta tokare hanyar fita tana kuka kamar ranta zai fita tana cewa.
"Abba ka kyaleshi dan Allah, wallahi Abba shine rayuwata, ina son shi."
Kau! Itama Alhaji Nura ya sauke mata yatsunsa biyar a fuskarta. Amman ko gezau ba tayi ba, babban burinta shine ya saki Areef da idanunsa suke a rufe tamkar wanda ya makance.
"Idan kika kuma saka min baki sai na illataki. Daman tunda aka ce min a cikin ƴaƴana marar kunyar ciki tana zuwa wani gida na musamman ita da wani yaro nasan cewa kece. Kuma idan baki wasa ba Nafisa sai naci mutuncinki yadda duniya ba zatai miki daɗi ba, mutuniyar banza mutuniyar wofi. Matsa ki bani guri ko na illataki."
Ya faɗa tare da saka hannun da ya wanka mata mari ya bangaje ta gefe guda. Ya kuma janyo wuyan Areef suka fito zuwa compound yana ta ƙoƙarin fito dashi waje. Gaba ɗaya idanunta a rufe suke ta kasa tsayawa tayi tunanin ɓarnar da mahaifinta ya kamata zasu aikata. Babu ko ɗankwali a kanta bare mayafi ta rugo a guje ta ƙanƙame Areef wanda Alhaji Nura yake ta son fitowa daga guest house ɗin.
Ya saki baki tare da ware idanu ganin yadda Feenah ta bawa yaron wata kyakkyawar runguma. Duk sai ya rasa abin yi saboda tsabar mamaki da al'ajabi.
"Koki sake shi ko na kuma wankeki da mara." Cewar Alhaji Nura cikin fushi.
"Dokarni Daddy, ka dokeni indai zaka rabu dashi. Wallahi Daddy shine rayuwata dan Allah dan Annabi ka rabu dashi ya tafi."
Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarsa ta fara rikicewa ganin yadda Feenah ke kuka tana riƙo Areef kan kar a fitar dashi waje. Sai kawai itama yasa ɗaya hannun ya damƙota ya nufi waje dasu gaba ɗaya. Mai gadi ya kasa cewa komai sai ido da yake binsu dashi har suka fito, Alhaji Nura ya danna su a motar shi. Duk wannan masifar Feenah na maƙale jikin Areef yayin da shi kuma baya ko motsin kirki bare ya ƙwaci kansa.
"Zakuci ubanku wallahi tallahi, kai kuma yau sai ka gaya min waye ubanka a jihar Kano."
Ya buga mota tare da janta da ƙarfin tsiya yabar unguwar. Ko a cikin motar masifa da bala'i kawai Alhaji Nura keyi. Yayin da Feenah keta kuka, shi kam Areef baya cewa komai. Abinda kawai ya sani shine yau duk wata ƙarya tashi ta ƙare babu abinda zai iya kare kanshi dashi a wajan iyayensa musamman ma da yaga sun doshi folisteshen. Alhaji Nura na ƙoƙarin yin fakin yana cewa.
"Sai nayi maganinka mutumin banza mutumin wofi. Haba shi yasa naga taurin kan yarinyar nan yayi yawa ashe ka daɗe da toshe mata baki wajan koya mata ƙazantacciyar rayuwa. Toh daga yau ko ba ƴa taba yaran wasu ma ba zaka kuma kallo ba bare kasa hannunka a jikin su."
Ya rufe murfin da karfi tare da buɗe ɓangaren da suke ya fisgo Areef. Haushin Areef ɗin yake sosai, gani yake tamkar shi ya hurewa ƴarsa kunne musamman da yanzu ya gansu cikin wannan halin. Kotakan Feenah bebiba haka yaja Areef suka nufi cikin folisteshe, ta kuwa biyo bayan su da gudu har lokacin kuka take tana ihu kamar wacce ake yankar naman jikinta.
"Zakici ubanki Nafisa, daman nasan zaki biyo ne shi yasa ban tsaya kamoki ba marar kunya."
Daidai lokacin da ya hankaɗa Areef kusa da kantar da folisawan ke tsaitsayawa. Ɗaya daga cikin folis ɗin ne yake kallon Alhaji Nura tare da tambayarshi abinda ya kawo shi.
"Ranku ya daɗe ku daure ku haɗani da DPO dan Allah, saboda wannan kes ɗin yana buƙatar a kula dashi sosai." Cewar alhaji Nura yana gyara hular kansa.
"DPO baya nan, Amman zaka iya gaya mana abinda ya kawoka kawai."
"Wannan yaron na kawo, ko da dai ba zan kirashi da yaro ba tunda yasan yadda zai yi ya sarrafa mace yadda yaga dama."
"Dan Allah Alhaji ka tafi kai tsaye ka sanar damu laifin da ka kawo, duk wannan bayanin naka zamu same shi idan mun fara bincike."
Ɗan sandan ya faɗa yana sake kallon Feenah wacce duk ta kiɗime gurin da masifaffan ƙamshin jikinta.
"Ranka ya daɗe mun yiwa yarinyarmu aure, amman saboda huduba da kuma shaiɗanci irin na yaron can sai da yasa ta kaso auran. Tun shekaran jiya ake sanar dani ana ganin ƴata Nafisa a wani guest house ita da shi, ban dauki maganar ba saboda ina cikin fushi da ita. Yau kam da aka kuma sanar dani dawowata daga gurin aiki ko gida ban shiga ba na nufi inda aka gaya min. Wallahi tallahi yallaɓai da wannan idanun nawa naga yaron nan akanta. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah ne kadai yasan tun lokacin da ya ɓata min yarinya, dan wallahi gaba ɗaya yarinyar nan bata jin magana."
Alhaji Nura ya gama bayani ɗansandan yayi rubuce-rubuce a cikin wani littafi. Can ya ɗago yana kallon Areef tare da tambayar sa.
"Kai ya sunanka?" Yai mishi banza tamkar besan da shi ake ba.
"Bakaji ana tambayarka?" Nan ma yai shiru tamkar wani bebe.
"Bafa ƙaramin marar