na gani ne shi yasa yake bani mamaki. Kai yanzu kasan cewar har yanzu da mijinta amman kuke irin wannan hirar da ita? Idan ita bata da ilimin isilama kaima naka da su Mamah sukai kokari wajen ganin ka samu ɓarewa yayi? Kaji tsoran Allah ka guji abinda zai sakaka cikin fushin ubangiji."
"Insha Allahu zan kiyaye, kuma kici gaba da yi min addu'a kinji."
"Uhmm ina yi maka, amman kaima sai kayi taka tsantsan domin mace shu'umace, karka daukeni a cikin lamarin dan nima idan na nuna maka nawa iskancin zaka sha mamaki." Yace.
"A'a rufa min asiri, your the only one I love." Ya faɗa tare da sumbatar goshinta. Da haka suka shiga mota sai gida.
3/26/22, 22:57 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲)*
*41*
Suna komawa gida tun daga bakin kofa ya fara zare mata vail, suna shiga falo ya fara kokarin rabata da rigar jikinta, gashi lokacin sallar magariba ya yi. Ta ɗan zame daga jikinsa tana yin hanyar ɗaki tace.
"Wai kai menene haka, sai kace bakaga lokacin sallah ya yi ba?"
"Naji mana, amman shima wannan ɗin ai ibada ce mai matuƙar lada. Zo muje na baki labari."
Iman ta girgiza kai tasan babu labarin da zai bata, haka ta bishi suka nufi ɗakinsa. Kamar yadda suka saba haka tayi masa babu ɓata rai ko damuwa ko wani abu da zai shi gane cewa har lokacin haushin sa takeji. Duk da yananin cikin jikinta nuna masa tayi harkar tafi ta kullum daɗi, suna kwance yana shafa kanta yaji tace.
"Nasan dai duk masifar mace duk kuma bala'in namiji idan yayi wannan abin a waje sai anyi sana sani. Dan haka aure rahama ne, idan wata aka gano ana son abu a jikinta wanda matar gida ta rasa, sai ayi kokari a yo auren dan a tsinci uwar da za'a tsinta kafin a kuma gano wasu." Areef ya girgiza kai tare da yin murmushi ya janyota jikinsa yana cewa.
"Gaya musu dai my dear, ni dai alhamdulillahi ke dakaice a cikin zuciyata. Duk macen da zaki gani tare dani wallahi tallahi ba zata kai matsayi da darajar da kike da ita ba. Wallahi koda zaki ganni da wata, kawai na ɗan lokaci ne amman ba wai dan kin gaza min ba. Ina sanki Iman ki yarda dani dan Allah."
Ta taɓe baki, batace dashi komai ba. Har zata miƙe sai kuma ta gyara kwanciyar tare da riƙe ƙugunta tana cewa.
"Toh haɗa mana ruwan wankan, ni wallahi wani irin jiri ma nake ji." Ya sauka daga kan gadon ya nufi banɗaki yayin da ita kuma tabishi da kallo cikin zuciyarta tana cewa.
"Ya Allah ga bawanka nan Al-Mustapha, Allah mijina Areefullah ka tsare min shi a duk inda yake, ya tsole duk wani idon shaiɗaniya, ka karemin shi badan halina ba ya Allah ni dai bazan iya ba amman ka iya min dan Annabi da qurani." Ta sauke numfashi tare da lumshe idanuwa.
Wayarsa dake cikin aljihun wandonsa dake ajiye a gefen gado take ta ringing, zuciyar Iman nata angiza ta akan cewa ta ɗauka, yayin da wata ke tuhumarta cewa why? Ba ruwanki karki taɓa masa. Harta juya ta kwanta taji an sake kira kawai ta miƙe tazo ta ciro, S.H ta gani, har zata ɗaga sai kuma taji ƙiwa ta mayar ta ajiye masa, komawa tayi ta kwanta. Ya fito jikinsa daure da towel yana cewa.
"Taho muje." Daga kwancen ta miƙa masa hannu yaje har kusa da ita ya rikota suka shiga toilet. Da alwalarsu suka fito kowa yasa kaya suka gabatar da, magariba, suna kan sallayar lokacin isha yayi suka tashi Areef ya kuma jansu sallah. Wayarsa da aka kira yasashi miƙewa ya dakko, S.H, ya dauka tare da karawa jikin kunne yana cewa.
"Zan kira idan na samu time sorry." Kafin tace wani abu tuni ya kashe ya koma kusa da ita ya zauna ganin ta ɗaga hannu tana addu'a sai faman 'Amin' yake cewa.
"Allah ya saukeki lafiya dear, Insha Allahu lafiya lau zaki haihu da yardar Allah." Ta shafa tare da shafa masa shima a fuska tana cewa.
"Amin sugerpie." Ta faɗa tana shafa zagayayyen gashin bakinsa.
Suna daɗe tare kafin ya tashi tsaye, jallabiyar ya cire ya maida kananun kayansa da ya cire yana cewa.
"Shirya muje mu samu abinci." Iman ta dafe kai tare da cewa.
"Bacci nakeji wallahi, gashi kaina yana sarawa, kaje kawai ka samo mana."
"Shikenan me kike so?"
"Duk abinda kasan ina so zan iya ci ka siyo min." Yana gyara wuyan riga yace.
"Uhm-uhm, kefa zabi gareki, wallahi tunda cikin nan ya shiga sai kin zabi abinci." Tayi dariya tare sa fadin.
"Toh dai yau an baka damar sai ka zabo."
Kwanciya tayi akan gado yana dariya ya fice. Mamah ce tayi mata waya suka daɗe suna yi kafin bacci ya ɗauke ta.
_________________________
Yana fita ya kira Feenah cikin salon jan hankali murya ƙasa ƙasa tamkar zatai kuka, kai daga jin muryar kasan cewar ana sane aka canzata tace.
"Sorry babylove, Afuwan nasan kila kana tare da matarka shi yasa baka ɗauka ba. Kayi hakuri nima zuciya tace bata min adalci, soyayyarka ce ta min yawa kayi hakuri bazan sake kirankaba indai ba kaine ka kirani ba." Yana tafiya a ƙasa yana rike da wayar a jikin kunne yace.
"Babu komai, amman abu ɗaya nake so ki sani. Dole sai munyi hakuri da junan mu, bawai dan bama son juna ba. Kawai dan hakan ba mai yiwuwa bane, ki hakura ki koma wajan shi kuci gaba da rayuwa kamar yadda kowa ya karɓi abinda Allah ya bashi. Insha Allahu hakan sai ya zame mana farin ciki a rayuwar mu." Feenah ta sake narke masa.
"Hakane, kaga shima sai naci yake akan na koma muci gaba da rayuwa, wai duka-duka duniyar nawa take. Ya faɗi gaskiya amman kuma zuciya ta tana tare da taka, ina sonka ina so mu kasance tare da juna. Wallahi banajin daɗinshi, kai nake so koda na rana ɗaya ne." Areef ya yi murmushi tare da lasar lips yace.
"Toh shikenan naki kika faɗa a fili, amman ni kaina ina masifar son ganin mun kasance tare, amman idan har akwai dama sai kiga mun auri juna Allah babu yadda baya yi da bayinsa."
"Yanzu kana ina?"
"Uhmmm! Nazo siyan abinci."
"Madam ta fito da kai kenan?" Yaji ta faɗa cikin wani irin yanayi na takaici.
"Madam ce, kinsan Allah Iman bata da matsala, kawai ita bata son rainin hankali ne, idan kayi mata sai inda ƙarfinta ya kare." Ta tabe baki kamar yana gurin.
Har yaje ya dawo suna waya, sai da zai shiga sannan suka ajiye yasa a aljihu tare da shiga bakinsa da sallama. Tashin ta yayi taci ta koshi sannan ta sake kwanciya taci gaba da baccinta. Shi kuma ya koma falo sukaci gaba da yin chatting ɗin su shi da Feenah.
__________
Koda Iman taga babu lambar Feenah a wayarta abin dariya ya bata, tana dawowa daga asibiti daman ta kirashi tace yana ina yace shima yana makaranta dan haka sai kawai ta shigo mota ta dawo gida, shigarta keda wahala ta ganshi kwance a falo yana waya. Sam beji dawowarta ba sai ganinta yayi a tsaye tana murmushi, cikin sauri ya katse tare da miƙewa yana cewa.
"Oyo yo my dear."
Rungume ta yayi takaici kamar ta mutu, a hankali ta zame hannunsa daga kafadarta, kallon sama da ƙasa tayi masa tare da cewa.
"Kana tunanin zaka fini dabara ne Yaya? Harni zaka gogewa lambar Feenah a waya? Ka manta ba kai ka bani ba nice na samu da kaina? Toh ka ganta." Ta faɗa tana nuna masa lambar a cikin wayar, yana gani ya tabbatar da cewa itace kuwa.
"Sau dubu miliyan zaka goge bazan rasata ba tunda dama bakai ka bani ba. Wai tsaya, soyayya kuke da gasken gaske ko kuwa junanku kuke rainawa hankali? Ni zaka dinga ciwa mutunci Yaya Areef? Idan auran Feenah zakai kaje ka aureta mana, ni bana san rainin hankali da wulakanci. Hudu Allah ya baku ikon yi dan me yasa sai ka tsaya kana bankaɗani a duniya? Duk wani motsinka na sani, har wayar da kuke yi da asuba ko cikin dare, bana son cin fuska idan zaka aurota kaje ka aurota tazo mu zauna meye a ciki? Kaine dai ko? Toh ka kawota ko wacce ai da halinta zata zauna..."
Tashin hankali, yadda yaga ta birkice masa ne ta bashi matuƙar mamaki, ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
"Na hanaka aurenta ne? Kaje ka aurota kuzo kuci uwar da zakuci da juna bana son munafunci."
Areef ya riƙeta gam a jikinsa yana son ta nutsu amman abun ya cutura, dole ya sakar mata hannu ya shiga dafe kai. Shima da ya rasa mafita sai kawai ya zube a ƙasa tare da dafe kai. Ganin haka yasa Iman jan tsaki ta shige daki zuciyarta kamar zata faɗo. Tana shiga ta faɗa kan gado sai kuka, girgiza kai kawai take saboda bakin ciki. Areef yana matuƙar bata mamaki, wai ya dage shi a dole soyayya suke da Feenah. Meye bata masa? Ta ina ta gaza masa? Duk iya tsananin wahalar da take ciki bata iya hanashi duk abinda yake so.
Tana jinsa ya shigo ɗakin wani tuƙuƙin takaici yabi ya tsaya mata a wuya. Zama yayi a kusa da ita tare da nuna mata wayarsa bayan ya kwanta a bayanta tare da rikota jikinsa.
"Karanta kiga saƙon dana aika mata dashi." Cikin tsiwa tace.
"Bazan karanta, ina ruwana da messages ɗinku, abu ɗaya nasani shine kuji tsoran Allah. Wallahi Yaya Areef mace zata iya jefaka cikin masifar da zaka daɗe baka yi mutunci ba. Feenah ba sonka take yi ba munafuka kawai." Ya sake miƙa mata wayar yana cewa.
"Nidai dan Allah ki karɓa ki karanta, umarni ne a matsayina na mijinki." Ta share hawayen fuskarta tare da karɓar wayar tana karanta saƙon da Feenah ta turo masa.
"Haƙika nasan kayi min nisa, nisan da zan iya cewa hangenka ma zai iya yi min wahala. Shin Allah so na ne bayayi da har ya haɗa zuciya ta da taka? Ina mamakin yadda nakejin rayuwa zata iya yi min wahala ba tare da kai a kusa dani ba. Wallahi zan iya mutuwa idan har baka amince dani, zan rataye kaina na mutu alhaki a kanka." Tunda ta fara karantawa zuciyarta ke suya karta gama, yace
"Karanta na ƙasan ki gani." Wanda yayi mata reply. Iman ta shiga karantawa.
"Ki dena faɗar haka, ta iya yiwu Allah ya dasa mana hakan ne dan ya jarraba imanin mu, ki daure kiyi hakuri da mijin da Allah ya baki yake kuma san ganinku a tare, sai kiga ya sanyaya miki zuciya. Ta yiyu ni dake ba alkairi bane. Ina miki fatan alkairi a duk inda kike Allah kuma ya raya mana takwarana, ya bashi lafiya, ƴaƴanki nawa ne, nawa maki ne kisa wannan a ranki. Kici gaba da addu'a zakiji kina samun sa nutsuwa a ranki."
Daga nan ya karbi wayar tare da ɗora kansa saman ƙafaɗunta yana cewa.
"Nayi blocking ɗinta, ta kirani da wata numbern, na sake yi ta kuma kirana dole sai da naje na buɗe mukaci gaba da hira. Iman Feenah tana sona fiye da tunaninki, munyi soyayya sosai wacce munyi alkawarin kasancewa tare amman aka shiga tsakanin mu d......" Wani uban tsaki da yaji Iman ɗin tajanyo ta saki shine yasa shi yin shiru ba tare da ya ƙarasa maganar ba. Cikin ɓacin rai da kalamansa tace.
"A yanzun wani ne ya hanaku auran juna? Kuyi auranku muma mu huta musan wane matsayi muke ciki. Amman duk kun tsaya kuna ɓatawa junanku lokaci kamar marasa aikin yi. Kai da kake da exam kaki ka maidai hankali. Ni na mata magana cewar idan kun shirya kawai kuyi auranku bana san rainin hankali."
"Idan Allah ya yi zamuyi ba sai kin faɗa ba Iman. Nace miki a yanzu dai babu wata maganar aure tsakanina Feenah, ki yarda ko karki yadda ya rage naki." Yana kaiwa nan ya tashi ya bar mata dakin, ganin haka yasa ta kuma fashewa da kuka.
Haka sukaci gaba da rayuwa kullum Areef da Feenah suna daɗa shaƙuwa dan har yaje asibitin ya gano ɗan. Idan yana gida zai dakko takardu ya barbaza ga waya ana dannawa, shi a dole ga mai karatun exam, idan ta bincika sai taga chat suke yi kuma yanzu mai muni saboda takai ta kawo Areefullah baya rabuwa da fitowar maziyyi. Gashi Iman ta shiga watan haihuwa. Kullum basu da kwanciyar hankali ita da shi, ta dena yadda dashi duk abinda zai gaya mata, tun randa yace mata yana so tasan cewa kowace mace da kalar nata arzikin take zuwa, dan haka shida Feenah sai yadda hali yayi.
Tayi kuka tayi bakin ciki tare da danasani na aurensa. Ganin batada mafita ne yasa ta nemo hanyar da zai sa shima yaji zafin abinda yake mata. Wayarta ta janyo gabaki ɗaya ta goge lambar Feenah tas, shima Areef ɗin duk tayi blocking ɗinsa, saboda ko kallansa bata san yi. Sai da ta bari ya tafi makaranta sannan ta shirya kayanta, komai ta ɗauka nata, duk wani abu da tasan zai gani nata sai da ta ɗauke sannan taje ta nemo taxi yazo ya ɗaukar mata kayan yasa a mota, cikin sauke ajiyar zuciya tace masa.
"Airport zaka kaini."
Ya buga mota suka tafi tana da addu'a cikin zuciyarta.....
*0706 528 3730 for more information.*
*HAJJA CE 👈*
4/1/22, 13:24 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲)*
*42*
Tunda ta shiga motar banda kuka da addu'a a cikin ranta babu abinda takeyi, wani irin ɗaci takeji a cikin zuciyarta wanda yayi sanadin da takejin ɗacin har a saman harshe. Suna isa ta bashi kuɗinsa ya sauke mata kayanta. Sai da duk aka gama komai sannan ta shiga jirgi tana riƙe baya sakamakon wani irin ciwo da taji yana yi ma. Bayan ta zauna ne ta fara tunanin inda ya kamata taje, Abuja ko Kano? Idan Kano ne ina zataje? Gidan Innarta ko kuma gidan Mamah? Toh idan tamaje me zatace musu ta dawo yi? Tayo yaji ko kuma ta faɗi halin da ake ciki?!
Numfashi taja tare da rintsa ido tana dafe goshi. Har jirgin ya lula sama bata gama yanke hukuncin inda zataje ba. Taci gaba da addu'a tana shafa cikinta da yake ta motsi yana harbawa tamkar kifin dake cikin ruwa. Suna sauka a garin Abuja ta kira Sen. Muhammad cewar gata a Airport azo a ɗauketa. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya turo an taho ɗaukar masa yarsa ɗaya telo a doran duniya.
Tana zaune a reception wata matashiyar budurwa tazo ta samu guri kusa da ita ta zauna. Kusan gabaki ɗaya fuskarta a rufe take idan ka ɗauke idanunta, wannan kuma salon gayunta ne da sabarwa kanta dashi. Babu wanda ya yiwa ƴar uwarsa magana sai daga baya ne ɗayar tace.
"Afuwan nazo na zauna ba tare da nayi miki sallama ba, Assalamu alaikum." Ta faɗa tana miƙa mata hannu da nufin su gaisa. Iman taja numfashi tare da ciro hannunta wanda ke rungume da cikin jikinta ta bata sukayi musabaha.
"Sunana Zainab bin Uthman but ana kirana da Jasmine, (Ta cikin book ɗina SAWUN GIWA) nice to meet you." Iman tayi ɗan murmushi tare da zare hannunta daga na Jasmine, murya a sanyaye tace.
"Khadija Ahmad, ana kirana da Iman, nice to meet you too." Daga haka duk sukaja baki suka yi shiru.
"Kinzo gida ne ko kema kina jiran jirgin zuwa Kano?" Jasmine ta tambayeta. Iman tayi shiru tana nazari kafin can ta numfasa tace.
"Zan kwana biyu a nan kafin naje Kano idan Allah yayi."
"Allah sarki, Toh shikenan idan kinzo sai mu sake gaisawa." Cewar Jasmine.
"Taya zamu sake gaisawa bayan ni ko gama gane fuskarki banyi ba?" Iman ta faɗa cikin sanyi fuskarta kuma da murmushi.
"Haka ne Toh bari na buɗe fuskata." Jasmine ta faɗa tare da buɗewa suka kalli juna suna murmushi.
"Babana shine sarkin Kano, ni kadai ce yarsa mace sauran duk maza ne. Ina fatan zamu yi zumunci duk da cewa yaune kawai muka fara haduwa, Gashi da alama keɗin matar aure ce."
"Haka ne ni matar aure ce. Babana da ya haufeni shine senate president, amman ba shi ya riƙeni ba. Mariƙina yana Kano kuma shine surukina a yanzu haka."
"Wow! Masha Allah. Allah ya saukeki lafiya." Iman tayi murmushi tare da amsawa, lokacin ne kuma masu ɗaukarta suka iso. Musayar lambobi suka yi kafin Iman ta juya ta nufi wajan mota ta shiga suka tafi.
_____________
Koda Areefullah ya kammala exam ɗinsa kai tsaye inda suke haduwa da Feenah yaje, suka sha hirarsu da yawace-yawacen kafin ya maida ita. Cike da nishaɗi ya dawo gida, falo babu Iman, ya ajiye jakarsa tare da shiga cikin ɗakinta yaga nan ɗin ma bata nan. Hannunsa riƙe da pizza ya shiga bedroom ɗinsa inda yake da tabbacin tana ciki amman babu ita, yaje ya buga banɗaki ya bude nan ma babu Iman. Ya fara zare idanuwa sai yanzu ya lura da babu wasu daga cikin abubuwan da yasan dasu a ɗakin.
Jiki na rawa ya zaro wayarsa ya kira amman taki shiga, yayi-yayi amman besamu ta shiga ba, nan da nan hankalinsa yayi mugun tashi. Inda ya ajiye tickets ɗinsu ya duba yaga babu nata sauran nashi kadai, wannan ya tabbatar masa da cewa Iman ta gudu Nigeria. 'Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun ya shiga uku, ina zata fara sauka? Ya rintsa ido yana cilli da pizza ɗin, dama ita ya siyowa kuma gashi yazo ya tarar bata nan. 'Allah yasa karkije gurin Babanki, please kije Kano dan girman Allah. Idan kikaje gurin Baba yasan halin da ake ciki me zance masa? Ita kanta me zatace musu yayi?
Shigowar message ne yasa shi saurin buɗe wayar yaga S.H. Buɗewa yayi inda yaga ta turo masa cewar.
"Nagode babylove da ka kasance dani ayau, haƙika nayiwa Iman murna da ta sameka a matsayin mijinta. A gaskiya duk macen da Allah ya bawa kai, na tabbatar ba zata so ku rabuba. Kai idan ma an rabu sai ta dawo da ƙafafuwanta wallahi, saboda kai ɗin na musamman ne, komai naka a tsare Allah yayi makashi. Ina son nima wata rana naji ɗuminka a jikina ko zan kuma samun nutsa da kwanciyar hankali. Ka huta lafiya ɗan sawalwalina."
Yana gama karantawa ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya. Sai dai be iya yi mata dogon reply