Mamah na falo tana yanka kayan marmari taji sallamarsu, maimakon taji su cikin murna sai taji kowanne yana sallama a ciki-ciki. Tasha mamakin ganin su gabaki ɗaya tankar tare suka fita. Tayi musu sannu tare da bin mijin nata da kallo wanda yake rufo ƙofar falon.
Kamar dama jira yake yi a shigo gidan, Areef dake tsaye kansa a ƙasa yaji wata razananniyar tsawa Abba na cewa.
"Zaka wuce ciki ko sai na harba maka wannan ƙafar tawa.?" Cikin mamaki Mamah ta kallesu tana son jin kamun labari.
"Wannan yaron ne zai ɓata min suna a idanun duniya. Wai yanzu Areef har yasan yaje gidan mace? Macefa Hajiya a can aka kamasu ko uban me suke yi oho."
Mamah ta mike a zabure tana dafe kirji, cikin tashin hankali ta kalli inda Areef yake tana jan numfashi da kyar tace.....
(Kash kome Mamah zata faɗa oho. 🙄Allah sarki uwa duk wani tunaninta yana kan yaranta. Shin dame Areef zai kara kan shi yau? Masu karatu nima fa ban sani ba🤥)
*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 19:01 - Buhainat: *ZGN*✍️
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*
*13*
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun. Hasbunallahu wani'imal wakil. La'ilaha illallahu Muhammad rasulillah..." Gabaki ɗaya gurin suka amsa da.
"Salallawa alaihiwasallam."
Tasa hannu ta dafa kujera jin kamar ana shirin kayar da ita. Wani jiri ya dinga ɗibarta, zuciyarta na tsanantawa fiye da yadda ake buƙatar bugunta. Muryar Abba ta sake karaɗe cikin falon, shima yana magana muryarsa tana rawa.
"Toh wallahi tallahi ni ba mazinaci ba. A kuma yadda nasan mahaifiyar ku itama ba mutuniyar banza bace, iya ƙoƙari muna yi wajan karewa kan mu mutunci da kuma ku gabaki ɗaya. Kai dan ubanka yaushe har ka tafasa ballantana ka ƙono iyeee?"
Abba ya tambayi Areef cikin tsananin fushi. Areef ya kasa koda kwakkwaran motsi, hakan yasa yaci gaba da cewa.
"Idan Aure kake so me yasa bazaka gaya manaba mu nemomaka ƴar mutunci mai hankali da sanin yakamata? Shikenan zan yiwa tufƙar hanci, ranar da za'a daura auran Islam kaima zan sa a ɗaura maka aure da yarinyar dana zaɓo maka."
Gabaki ɗaya gurin babu wanda bai razana dajin kalaman Abba ba. Duka-duka fa sauran sati biyu bikin Islam ɗin, wacce su Iman zasu raƙashe a ranar shine za'a ce za'a haɗa da Areefullah? Tashin hankali wannan wane irin fushi Abba ya yi? Gashi kalamansa basu tabbatar musu da cewa da Feenah za'a yi ba. Yana gama magana kuma ya shige ɗakinsa, su Haneef duk jikin su ya yi sanyi.
Hankalin Areef ya tashi jin cewar za'a yi masa aure kuma ba da Feenah ba wacce yake so. Gwiwarsa tayi sanyi ta yadda ta kasa riƙe shi sai da ya durkusa ƙasa. Mamah ta kalli su Iman idanunta sunyi jawur tamkar mai ciwon afulo tace subar falon. Jamil ma ganin yanayin da take ciki kuma shima ba wani ɗan gidan bane, sai ya juya ya fita. Amman ya laɓe daga bakin ƙofar yadda zai dinga jin abinda zasu tattauna.
Jiki a sanyaye Haneef ya isa gurin Mamah da har lokacin bata dena jan numfashi a wahale ba. Cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya yake mata magana.
"Kiyi hakuri Mamah ki zauna sosai. Ina kuma rokonki da karki yi masa mugun furuci ko ki sallamawa duniya shi. Mamah duk abinda Areef ya zama namu ne ko muna so ko bama so. Kiyi hakuri dan Allah Mamah."
Ai kamar ya taɓota sai kawai sukaji ta fashe da kuka, sosai kamar ƙaramar yarinya. Haneef ya kalli inda Areef yake zaune yaga shima ya fashe da kukan sai ya rasa abinda zai faɗa. Lallashinta ya shiga yi har tayi shiru sannan yace.
"Abba ya yanke hukunci zai yiwa Areef aure nan da sati biyu, Allah kadai yasan wacce zai bashi. Mamah ki bashi hakuri dan Allah ya kara lokaci har su fahimci juna da yarinyar da za'a aura masa."
"Tashi ka bamu guri."
Mamah ta kori Areef daga falon. Ya tashi da kyar ya kai kansa ɗaki. Jamil dake bakin ƙofar shiga falon ya hango mutum na tahowa yai saurin barin wajan. Aslam ya shiga da sallama, kafin yayi magana Haneef yai masa nuni da ɗakin da Areef ya shiga. Kamar wani munafuki ya yi sum sum sum ya shige yana rufe ƙofa.
"Mamah wa kike zaton Abba zai aurawa Areef? Ina nufin a iya tunaninki.?"
Cikin share hawayen da suka ɓata mata fuska tace.
"Kana tunanin zai masa zabi marar kyau?"
"A'a Mamah, kawai dai bana son a samu matsala ne. Kinsan idan namiji bashi yace yana son mace ba, akan samu matsaloli a gidan auran."
Mamah ta kuma jan numfashi.
"Mafarkina ne yake shirin rugujewa, ina tunanin burina ba zai cika ba indai har zatona ya tabbata gaskiya."
Ta faɗa yayin da wasu hawayen suke sake biyo mata fuska.
"Kina tunanin wani abun ne dabban?"
"Kwarai da gaske Haneef, naso ace kai za'a bawa saboda kafishi hankali. Kuma zakafi kulawa da ita dan bana tunanin zasu daidaita kansu. Amman duk da haka zanyi magana da Abban naku naji idan ba ita yake shirin aura mishi ba."
Haneef ya shiga mamaki da jin kalaman Mamah, gabaki ɗaya tunaninsa ya kasa gano wacece suke ta son haɗa zuriya da ita. Ganin ya kasa ganowa ne yasa shi cewa.
"Wacece wannan Mamah? Dan Allah ki gaya min dan dagaji nagartacciya ce."
Sai da ta rintsa idanu kafin tace.
"Iman. Iman naso na baka ganin kai baka da niyar samo wacce zaka aura. Idan har ya tabbata itace wacce Abbanku ya zaɓar masa, kaga burina da kuma mafarkina sun zama ba haka ba."
Haneef ya shiga zaro ido jin wacce za'a bashi. Sam be taɓa kawowa cewa za'a iya wannan tunanin a cikin gidan nan ba, duba da yadda aka rufe duk wani sirri ta yadda sauran yaran ba zasu gano cewa ba ahalin su bace. Shi sam be taɓa tunani ko yaji zai iya auran Iman ba, saboda kallon da yake mata na ƙanwa wacce suka fito ciki ɗaya.
"Mamah mai yasa kuke wannan tunanin? Mai yasa zaku yi sanadin farin cikin Iman tsawon shekaru. Sannan rana ɗaya kuyi silar rugujewar duk wani jin daɗi nata? Ni ban taɓa jin zan aureta ba ina jin ta tamkar ciki ɗaya muka fito. Kuma nasan shima Areef ɗin hakan take a gurinsa."
"Kana ganin bayanka akwai wanda zai riƙe sirrin Iman? Akwai wanda zai aureta bai cizgunawa rayuwarta ba ta hanyar tozarta asalinta? Kai kadai ne nasan zaka bata kulawa ba kuma zaka fallasa sirrin da ko ita kanta bata sani ba. Kana ganin shi kansa Areef ɗin da nake tunanin shi Abban ku yake son bawa Iman, dubi abinda aka kamashi yana aikatawa. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun."
Zuciyarta ta kuma tsinkewa, kuka ya sake kwace mata Haneef ya janyota jikinsa yana bata hakuri.
Dr Jamil dake tsaye a bakin ƙofa yaji maganganunsu hankalinsa yayi matuƙar tashi. Kenan ba ƴar asalin gidan bace? Iman za'a aurawa wancan ɗan iskan yaron? Idan ba ita za'a bashi ba kenan Haneef abokinsa kuma amininsa shi za'a aurawa Iman ɗin da ya gani yaji duk duniya babu wanda ya kai shi sonta? Abinda ba zai taɓa bari ya faru ba kenan, wato ya rasa Iman a cikin rayuwarsa. Yaja ƙafa da ƙyar ya koma ɗakin Haneef zuciyar shi na tafasa.
**********
"Kai dallah yiwa mutane shiru uban me kuma kake yiwa kuka? Na rantse da Allah da nasan abinda ke faruwa kenan da ka gane cewa ni ba abokinka bane. Kuma kasan yadda kayi mashin ɗina ya dawo."
Afusace jin kalaman Aslam yasa Areef waigowa ya shaƙo masa wuya. Tsabar fushi so kawai yake yaga ya dena numfashi bare har ya samu damar yi masa wata ɓakar maganar. Cikin masifa da bala'i irin na masu baƙar zuciya Areef ke magana.
"You're very stupid, very stupid Aslam."
Ya sakar masa wuya tare da rungume shi ya shiga kai masa kiss ta ko'ina a jikinsa. Tashin hankali na musamman ya ziyarci Aslam da yaga abin mamaki gurin abokinsa. Yai ta niyar ƙwatar kansa amman ya kasa har sai da Areef ya gaji dan kansa sannan ya tunƙuɗe Aslam ɗin yai baya tare da faɗawa kan gado.
"Banda irin wannan moment ɗin babu abinda yake shiga tsakanina da Feenah." Areef ya faɗa yana zuba guiwarsa ƙasa a gaban Aslam.
"Shima wannan ɗin ba'a san raina ba wallahi. Me yasa idan kowa ya gujeni kaima zaka gujeni? And ina cikin fushin iyayena kazo kaima zaka ƙara min wani why Aslam? Why?"
"Karka yaudare ni mana Areef, karka raina min hankali. Waye yace kuyi irin wannan ɗin? Addini ne ko al'adar ɗan bahaushe? Idan bakaje inda take ba zata zo har gida ne ta rungumeka har ta shiga sumbatarka a yadda ka gwada min yanzu? Banza kawai duk ka tayar min da hankali na ɗauka nima lalatani zakai."
Cewar Aslam yana kuma goge saman lebansa da Areef ya sumɓata.
"Wallahi kasan yadda za'ai mashin ɗina ya fito, babu abinda ya dameni da ance ko a hanya aka ganku da ita sai hukunci ya hauku. Kawai gobe kaje ka dakko min a inda ka kaishi."
Aslam na kaiwa nan ya miƙe yabar ɗakin. Ko sallama be yiwa su Mamah ba dan yaga alamar basa maraba da kulasun da zai yi ya fice daga gidan gaba ɗaya. Ya baro Areef a ɗaki yana buga goshinsa a jikin katakon gado.
*********
Gabaki ɗaya suka zauna akan gado ko wacce tayi zugum tare da zabga uban tagumi. Da alama kowacce tunaninta daban dana ƴar uwarta duba da yanayin fuskokinsu. Ikram ta katse musu shirun ta hanyar cewa.
"Yaya Areef za'a yiwa aure, dawa za'a haɗa su? Bafa wacce Abba zai haɗasu da ita ba yake so, waccen yarinyar da aka kamasu itace yake so tunda har gashi Allah ya tona musu asiri."
"Kinjiki da wata magana, shikenan kuma sai abari ya auri ƴar iska ko? Kinaji kuma aka ce bazawara ce ma. Ni na rasa me Yaya Areef ya gani ajikin shegiyar yarinyar can har ya makalemata. Kodan tana ce masa baby ne oho." Iman ta ƙarasa maganar tare da jan ɗan ƙaramin tsaki, dan ba ƙaramin tsanar Feenah take ba.
"Allah dai ya shirya ya kuma karemu baki ɗaya, baku san illar SO ba wallahi. Ni da yake ya ZO GARENI na ɗanɗana shi ina tausayin su indai basu auri juna ba." Gabaki ɗaya suka kalli Hanan ɗin.
"Yes da gaske ina cikin soyayya sisters amman baku san shi ba." Ta Tabbatar musu ganin suna mamaki.
"Wakike so Hanan?" Ikram ta tambayeta dan duk basu taɓa tsammanin tasan so ba saboda yawan shirunta.
"Malamin mune." Iman ta kyalkyale da dariya tana nuna Hanan da yatsa. Sai da tayi mai isarta Hanan bata kula ta ba sannan tace.
"Toh shi yana sonki ko? Ah wayaga Hanan ana soyayya danƙari." Ta kuma kwashewa da dariya harda dukan katifa.
"Toh menene na dariyar?" Cewar Ikram tana hararar Iman ɗin.
"Wai Hanan da soyayyar wani. Ai ni in kinga na fara soyayya ma bare aure, Toh nayi digiri na kama aiki. Jikin mu ai bana auran wuri bane ba."
Karaf a kunnan Haneef da yazo shiga cikin ɗakin nasu. Ya haɗiyi yawun takaici tare da yin sallama ya shiga.
*******
Feenah kam banda kuka babu abinda take yi a cikin motar, daddy nata surfa masifa da tayi mishi shiru amman kamar zuga sai ma kara yi da take. Yayi peaking a ƙofar gidanshi tare da buɗe bayan motar ya janyo Feenar, rigar Areef da ta yi ɗankwali da ita yasa hannu ya toge tare da jefawa cikin ƙwatar ƙofar gidan.
Yajata da karfi suka shiga ciki mutane nata gulma sun san wani abun ta kuma aikatawa. Mutum mai mutumci da hakuri, amman kankanuwar yarinya ta maidashi kamar wani mahaukaci.
Tun daga nesa ya fara kiran Mommyn su, tana zaune ita da su Zainab suna mamakin inda Feenah ta tafi har yanzu bata dawo ba. Jin muryar daddy yasa duk suka mike suka yo tsakar gidan.
"Kafin gari ya waye kiyi tunanin inda zan kai miki wannan munafukar yarinyar. Idan kuma kema baki da gurin ajiye ta ni zan yanke hukuncin da yake a raina, tun kafin tayi sanadin kaini kushewa a binneni..."
Ya faɗa yana kallon Mommy wace kirjinta yake dukan million-millions.........
_(Tashin hankali 🤔 abubuwa suna ta ƙara damulewa. Auran Areef da Iman zai yiwu? Gefe guda ga Dr Jamil zai yadda ya hakura da Iman? Ina daddy zai kai Feenah idan har Mommy tace bata da gurin kai ta? Muje zuwa muji ya zata kaya next page)_ 💃
*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 19:01 - Buhainat: *ZO....GA...N*✍️
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*
*14*
Wata irin raruma Mommy takaiwa Feenah dake zaune dirshan, ido rufe ta shiga tsinka mata mari a duka kuncinta amman ko a jikin Feenah, kai bakace ma ita ake yiwa ba. Hankalinta da tunaninta yana gurin rigar Areef da Daddy ya cilla cikin kwata.
"Dan ubanki yau kuma me kika kuma jajibo min Nafisa? Ke wace irin yarinya ce ne?" Zuciyar Mommy sai tafasa take yi.
"Toh nima ban iya dake ba bare kuma in kaiki wani gurin. Na rasa ya zanyi dake, fitinarki tayi yawa Nafisa."
Ta faɗa tana dafe kanta da yake mata wani azazabban nauyi.
"Mommy shine zaɓina, shi nake so Mommy dan Allah ku barmu tare."
Cewar Feenah tana ɗagowa ta kalli mahaifiyarta dake tsaye.
"Kina son shi shi wa? Waye shi damu san shi ba?" Kafin tayi magana Daddy ya sake fitowa tsakar gidan yana fadin.
"Wani ɗan ƙaramin yaro ne naje na same su akan juna, wai ashe gidan ma nata ne Sultan ya ara mata. Kinji kara daurewa yarinyar nan ƙugu. Yaro ne ƙarami da na tabbatar su Zainab ma sun girmeshi nesa ba kusa ba. Toh wallahi kinyi karya ki zauna cikin gidan nan kina wulakantani a gari, mutane suna yi min kallon sakarai."
Duk mamaki ya kamasu suka dinga kallonta, Daddy yace.
"Wallahi Nafisa da haihuwarki gwara ɓarin ki. Kisa a ranki kuma sai kinbar gidan nan." Ya fita ya kulle gida ya sake komawa cikin ɗakinsa yana faɗa.
"Allah ya shiryeki Nafisa yasa ki gane cewa bayan duniyar nan akwai lahira sannan akwai hisabi. Nidai ba irin tarbiyar dana baki ba ce kike yi, Allah yagani ya kuma sani."
Mommy ta juya da sauri ta shige dakinta tabar su a gurin.
"Waike Feenah dan Allah me kikeji idan kin ɓatawa iyayen ki rai? Kinsan hukuncin mai sabawa iyaye kuwa?" Cewar Asma'u jiki a sanyaye.
"Kiji tsoran Allah Nafisa, kisan annabi yazo mana da hanyoyi na shiriya. Wannan duk ba jin daɗin rayuwa bane. Allah ya shiryeki kamar yadda Mommy tai miki addu'a." Zainab ta faɗa ta shige ɗaki itama.
Duk suka shiga ɗaki suka barta a gurin, ta sake fashewa da kuka ganin babu wanda ya tausaya mata. Anya sunajin abinda take ji a ranta kuwa? Sunyi mata adalci? Sun taɓa jin makamancin abinda takeji akan Areef? Da kyar ne, domin ta iya yiyuwa Daddy da Mommy auran sadaka akai musu ba auran soyayya sukayi ba.
Sai da taci kukanta taga babu mai kulata sannan ta rarrafe ta shiga falo. Akan kujera ta kwanta tana ta saƙe-saƙe. Ga babu waya a hannunta tana can guest house bata kuma san yadda za'a yi ta ɗakko ba. Ta rufe idanuwa tare da jan leɓanta da haƙori tana neman mafita.
*******
A hankali ta buɗe ƙofar ɗakin tamkar mai jin tsoran shiga. Yana zaune a tsakiyar gado yana duba wasu takardu wanda a zahiri sudin yake dubawa, amman cikin ransa tunanine rututu da yake neman birkita masa lissafi. Mamah taje itama ta zauna a gefen gadon tayi ƙasa da kanta zuciyarta na ƙarfafata wajan buɗe baki tayi magana.
"Hukuncin daka yanke yayi dai-dai, gwara ayi masa auran tunda yana da sha'awarsa. Allah yasa dai ba da yarinyar daka gansu zaka haɗa ba."
"Allah ya kiyaye, wallahi ko mata sun ƙare a duniyar nan bazan bawa yarinyar nan ɗana ba. Ina ganinta nasan bata da kunya bare tarbiya, a gaban mu ta dinga ihu tana cewa Dpo wai yace abari ya aure ta. Mtww ina jin ma wallahi tana da taɓin hankali. Kafin naji mummunan labari a tare dasu gwara na aura masa Iman hankali na kwance."
Mamah taji wani dumm, shikenan ta tabbata Iman zai bawa Areef. Iman da duk a duniyar nan babu wanda ta raina irin Areef, shine za'a bata. Amman dai bari ta ɗan lallaɓoshi ko zai canza wannan tsarin.
"Amman Alhaji baka ganin wannan hadin akwai matsala? Iman da Areef fa? Wallahi basu jituwa ko kaɗan, yadda kasan saƙo da saƙuwa ina ganin kamar zaman su ba zai yi tsari ba."
"Kina tunanin akwai wanda zan bawa Iman ne ya riƙe min ita yadda nake so?" Ya faɗa yana ɗagowa ya kalleta.
"Nida nafi yin sha'awar mu haɗasu da Haneef."
"Zanso hakan Hajiya, sai dai a wannan gaɓar wannan hanyar itace kawai mafita a gurin mu gabaki ɗaya."
"Toh Allah yasa hakan ya zama alkairi."
"Amin Hajiya wannan addu'ar itace abar buƙata yanzu."
*******************
Haneef na shiga ɗakin ya samu guri ya zauna, suma duk gyara zaman su suka yi tare da yi masa bangajiya. Kallonsu yayi tare da jan numfashi yace.
"Kunga duk abinda ya faru ko?" Suka ce.
"Eh Yaya capt."
"Toh wannan abun ya zama sirri agaremu. Kar wanda ya kuma tayar da maganar nan. Sannan duk abinda iyayen mu suka yanke kar wanda ya musa musu ko yayi gardama ko rashin kunya kunaji na?"
"Bazamu yi ba Yaya." Iman ta faɗa tana buɗe ledar kayanta. Murmushi ya saki ganin duk ta fisu magana, yasan tabbas akwai matsala gurin zamanta da Areef saboda shi ɗin ba mai hayaniya bane, sai dai akwai rainin hankali. Tashi yayi yabar ɗakin ya nufi na Areef, a buɗe yake hakan yasa ya shiga tare da yin sallama.
Areef dake zaune yasa kan shi tsakanin guiwarsa yaji sallama sai da kirjinsa ya buga, shi