yanzu ko ƙofarsa baya son yaji ta motsa bare kuma a shigo gurinsa, jiyake tamkar a lokacin yake manne jikin Feenah. Ƙin ɗago da kansa ya yi tunda yaji muryar yayan su yasan cewar magana zai masa akan abinda ya faru, sai kuma yaji saɓanin haka.
"Ina fatan zaka karɓi abinda iyayanka zasu yi maka da hannu biyu-biyu? Kuma koma wace Abba zai baka ka sani yayi hakan ne da ya rufa maka asiri ya kuma kare mutuncin kansa. Dan Allah Areef kayi biyayya ka riƙe matarka tsakani da Allah."
Ya ɗago da kansa amman bai kalli inda Yaya Haneef yake ba, murya a raunane yake magana.
"Yaya wallahi ban aikata abinda kuke hasashe ba, nasan tabbas muna haduwa da Feenah Amman wlh bantaba kusantarta da sunan zina ba. Please ka yarda dani, kace da Abba karyayi min auran nan yanzu wallahi bana so."
Murmushi Haneef yayi tare da girgiza kai. Lallai Areef yaro ne sosai, banda rainin hankali aganka da mace gida ɗaya cikin wani yanayi sannan yanzu yace wai shi baya son aure yana nuna tamkar bema shirya yi ba. Tashi ya yi yana murmushi wanda yafi kuka ciwo tare da cewa.
"Kana tunanin Abba zai fasa abinda ya furta? Da dai ace ba'a sameka da wannan yarinyar ba. Ni yanzu shawara kawai nazo baka karka ce bazaka zauna da koma wace za'a aura maka ba. Yin hakan zai kuma sawa kashiga fushinsu bayan na yau daka sa su. Allah ya bada zaman lafiya."
Yana kaiwa nan yabar ɗakin, Areef ya buga kansa jikin gadon yana sake zirarar da hawaye. Yau kam ya shiga uku wallahi shi kansa yana son Feenah musamman yadda yaga duk akan shine take shiga matsala a gurin iyayenta. A wannan lokacin ma so yake yaji a wane hali take ciki tunda shi ya riga yasan nashi, wannan auran idan har bada Feenah za'ai ba tabbas akwai matsala.
Kusan agurin ya kusa kwana, yanata tunanin kosu Mamah zasu shigo yaji shiru. Ya daure ya shiga banɗaki yayo alwala da sallolin da ake binshi. Babu wani maganar abinci dan ko yunwa ma bayaji bare ya nema haka ya kwanta yana ta nadamar abinda ya faru a wannan rana.
*************
Washe gari kowa yanata hidindimunsa a cikin gidan amman banda Areef dake ɗaki a zaune ya rasa meke yi masa daɗi. Mashin ɗin Aslam ga rashin sanin halin da Feenah take ciki. Uwa uba kuma baisan halin da Mamah da Abba suke ciki ba, ya kuma kasa fitowa saboda kunyar kowa yake yi.
"Assalamu alaikum."
Iman tai sallama cikin ɗakin. Muryarta da yaji ne yasa shi tsuke fuska ya kuma ki amsawa a fili.
"Yaya Areef ga breakfast."
Yayi shiru dan harga Allah su ɗinma wata muguwar kunyarsu yake ji Amman babu yadda zai yi dole sai yana daure musu fuska yadda ba zasu raina masa hankali ba akan wannan abun da ya faru. Harara ta zabga masa ta baya tare da tabe baki taje ta ajiye masa tray ɗin akan madubi tajuya ta bar ɗakin.
**********
Jamil kuwa tun da asuba yayi sallama da Haneef ko jira akai shi airport beyi ba ya tafi da kanshi. Jiyake duk ya tsani mutanan gidan banda ita Iman ɗin. Abba kuwa da ya furta zai bada ita ga wani ba shi ba, ji yake kamar ya shaƙe shi. Ya tsane shi tsana mafi muni, haushinsa yake ji tamkar ya mammangaresa da hannunshi.
Da kyar ya iya tsayawa aka gama bincike kafin su tashi zuwa Niger. Gaba ɗaya ji yake ya tsani kanshi. Zuciyar shi na zugashi akan dole ya auri Iman tunda yana sonta.
"Wallahi koda tsiya, koda tsiya-tsiya sai ta ZO GARENI. Iman tawa ce Allah ne kuma ya haɗani da ita lokaci ɗaya."
Ya furta a fili yana zaune a cikin jirgi sai jan numfashi yake. Ya kudiri aniyar koshi ko Areef amman ba zai taba yadda ya rasa ta ba.........
(🙄Karfin hali. Wannan mutumin ya matsa da yawa. Sai kace wani ubanta. Hmmm maji ma gani ai.)
*HAJJA CE 👈*
2/14/22, 10:21 - Buhainat: *ZO....GA...N*✍️
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*
*15*
Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi ta shiga cikin gidan, hankalinta a tashe tamkar wata zaburarra. A zauna a falo ta tarar dasu Iman suna hira, cikin sauri duk suka bita da kallo. Ikram ce ta haɗe rai domin ta gane fuskarta rai a bace tace.
"Lafiya?"
"Ina neman Mamah." Ta faɗa jikinta na rawa.
"Sa'arkice ita da kika zo nemanta?"
"Kuyi hakuri da halin da kukaga na shiga, soyayyar ɗan uwanku itace tayi silar rikicewar hankali na. Dan Allah dan Annabi ku nuna min inda zanga Mamah."
Feenah ta faɗa tana jan majina.
"Malama zoki bar gidan nan anƙi a kirawota ɗin, banda abinda kuka aikata ke har iya zuwa gidan su zaki yi? Lallai kin cika tantiriya."
Iman ta faɗa tana jin tamkar ta rufe Feenah da duka, ta tsane bata sonta ko misƙala zarratin. Hawaye suka shiga fitowa daga idanun Feenah, ita kanta tana ganin karfin hali da naci irin na zuciyarta da take yin abubuwa akan Areefullah. Ta kalli Iman tana sharce hawaye tace.
"Iman kidena ganin laifina, ki ɗauka cewa kece ni kika shiga cikin yananin da na shiga, wall....." Da sauri Iman ta dakatar da ita.
"Karki sake cewa na ɗauka nice ke, wallahi ko a mafarki naga na zamake sai na kashe kaina, ballantana kuma ina cikin hankalina. Kizo kibar gidan nan tun kafin muyi miki tsinannan duka."
A haukace ta juya tana kallon Hanan da tayi shiru tana binsu da kallo, bata cewa komai sai ido da take binsu dashi.
"Dan Allah kice Mamah ta fito, dan Allah karku bari a rabumu. Kusani a matsayin ƴar uwarku, ku ɗauka cewa ni jininku ce ya zakuji in na rasa wanda nake so?"
Lokacin Mamah ta fito daga ɗaki Feenah ta ruga da gudu wajanta tare da faduwa ƙasa tana riƙe mata ƙafafuwa. Areef da yajiyo muryar ta ya taso a hankali ya buɗe ƙofa ya leko. Ganin Feenah a gidan su ya sake tayar masa da hankali, ya kuma tabbatar da cewa komai zata iya aikatawa.
"Mamah dan Allah ku rufa mana asiri, Mamah muna son junan mu. Mamah zasu ɗaukeni daga gidan bansan inda suke son kaini ba. Dan girman Allah Mamah kubarmu."
Duk da Mamah tana cikin fushi da ɓacin rai sai da taji tausayin Feenah, duk wannan haukan da take yi soyayyar ɗanta da take yi shine ya janyo. Toh amman mai yasa suka aikata wannan abun? Son zuciya ko ruɗin shaiɗan? Mai yasa ba zasu faɗa ba idan ta kama auran ne sai ayi musu? Ita da aka ce ma bazawara ce mai yasa bata zauna gidan mijin ba? Yarinya ƙarama tasa kanta a cikin matsala.
Amman duk da ta bata tausayi hakan baisa ta nuna ba dan karta bata damar ci gaba da abinda suke yi. Mamah ta janye jikinta daga na Feenah fuskarta a murtuƙe cikin tsananin fushi tace.
"Saboda kina son shi shine zaku dinga aikata sabon Allah? Saboda kuna son juna shine zaku ɓata mana suna? Toh hakan ya janyowa Areefullah fushi mai tsanani, ki tashi ki fita tun kafin raina ya gama ɓaci."
Ai jin kalaman Mamah yasa ta kuma fashewa da wani shegen kuka.
"Wallahi Mamah Areef shine rayuwata, ina son shi Mamah dan girman zatin Allah ku barmu."
"Dallah zo ki fita." Ikram ta faɗa tana ƙarasawa gurin tare da fizgo ta.
Iman ma taje suka shiga figo Feenah suna turawa hanyar fita. Areef dake leƙensu yaga yadda ake janta, ya rintsa ido, shi ba abin yaje ya ƙwaceta ba ya janyowa kansa. Muryar Feenah ta sake sawa ya buɗe ido yana hangota tayi watsi dasu Iman tana kuka tana cewa.
"Ina son Areef, shine rayuwata, muradina farin ciki na. Kuma sai na aure shi babu wanda ya isa ya hanani."
Mamah tayi sakato tana kallon ikon Allah, wayaga karfin hali yarinya kizo har gidan mutane ki nuna kin fisu son ɗan su saboda tsabar ƙarfa-ƙarfa. Duk da haka su Ikram basu ƙyaleta ba sai da suka fitar da ita har peaking lot sannan suka yi mata gargaɗi Iman harda cewa.
"Ki tafi can ki nemi miji irin ki. Yaya Areef tun jiya anyi masa matar da zata rayu dashi, ƴar mutunci da karama ba irinki ba."
Feenah taji tamkar an soka mata mashi a tsakiyar zuciya. Zaro ido tayi tana motsi da baki amman ta kasa cewa komai saboda firgici. Suka ƙara mata takaici ta hanyar shigewa su rufe ƙofar. Mai shara ne ya hango lokacin da Feenah ta faɗi, ya rugo da gudu yana ihu tare da buga ƙofar yana kiran Hajiya.
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun Hajiya bakuwarku ta mutu."
Gabaki ɗaya suka fito ciki harda Areef dake ɗaki a laɓe. Yana zuwa besan lokacin daya rarumeta zuwa jikinsa yana girgizawa cike da tashin hankali. Mamaki ya kama Mamah ganin yadda idanun Areef suka rufe har ya iya rungume yarinyar a gabansu, itama haushi da zuciya yasa ta sauke masa wani lafiyayyan mari tare da cewa.
"Tashi ka shiga ciki ko nayi maka shegen duka a gurin nan."
"Mamah sun kashe Feenah, sun kashe zan tashi in tafi? Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun please Mamah please sun kashe ta..."
Ya shiga zabga surutai barkatai tamkar wani taɓabɓe yana rungume da Feenah cikin tashin hankali. Fitowar Haneef yasa Mamah bashi umarnin ya ɗauke mata Areef ya shiga dashi ciki. Ita kuma Feenah suka shiga zuba mata ruwa harta farfaɗo cikin wani irin ihu. Tana farfaɗowa Mamah ta koma cikin ɗaki da sauri ta ɗakko wayar ta, bugu uku ta kira Aslam ya ɗauka tace yazo yanzu-yanzu. Daman yana ƙofar gidan su hakan yasa babu ɓata lokaci sai gashi.
"Nasan kasan gidan iyayen wannan fitinanniyar yarinyar. Zoka raka Haneef kuje ku mayar musu da ita bana son kuma ganin fuskarta a cikin gida na."
"Wayyo Allah na shiga uku Mamah dan Allah kisoni tare da ɗanki. Dan Allah karku aura masa wata ni yake so wallahi tallahi. Wayyo! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wayyo na shiga uku na lalace."
"Aure an riga da an daura shi yarinyar, sai dai kuma kijira naki da wani amman ba dai jinin mu ba." Cewar Iman tana murguɗa baki.
Feenah ta zabura zata shaƙo Iman su Haneef suka riƙota da sauri suka kaita cikin mota. Sunsha baƙar wahala kafin su saka ta dan har cizo ta dinga gasa musu a hannuwa tana cewa bazata bar gidan ba sai ta auri Areef. Cikin sauri su Iman da Ikram da almajirin sukaje suka buɗe gate aka fita da motar suka rufe.
"Yau naga jarabar duniya, wannan wane irin bala'i ne? Wannan yarinyarma ba masoyiya bace wallahi, jaraba ce a garemu, kuma Insha Allahu ba zata taɓa zama ɗaya daga cikin ahali na ba. Ku wuce ciki shi kuma Areef sai naci ubanshi tunda naga bashi da hankali shima."
Duk suka koma cikin gida Mamah sai faman faɗa take yi. Areef na ɗaki yana ta dukan ƙofar da Haneef ya rufe shi a ciki.
Cikin fushi Mamah taje ta buɗe ɗakin tare da banka ƙofar, Areef yai baya ya faɗa kan gado yana kallon Mamah cike da firgici.
"Kai ka zama marar mutunci ko? Yaushe ka zama fitsararre Areef? Agabana a gaban ƴan uwanka kaje kana rungume mace, abin ma ya shahara ko? Da zan lallaɓa mahaifinka ya janye auran da zai maka, amman yanzu zan jajirce wajan ganin anyi auran nan ka auri ƴar mutunci da daraja sakarai kawai."
Ta fice ta barshi a ɗakin ranta a ɓace. Babu daɗewa sai gasu Haneef sun dawo suka ce ai can gidan su ma ba'a san ta fito ba, mahaifinta yana fitowa daga ɗaki zai kaita inda zata zauna suka nemeta suka rasa. Aikuwa suna kaita ko cikin gidan basu shiga ba mahaifinta yana waje ya karbeta shima yasa a mota suka bar unguwar.
"Oho duk ma inda zasu kaita sukai, wannan yarinyar jarababbiya ce wallahi." Mamah ta faɗa tana sakin tsaki.
*****
Gabaki ɗaya gidan ya kacame da hayaniyar ƴan biki da yake can gidan bikin ƴan uwa sun cika shi sai ƴan matan suka dawo gidan Abban harda ita amarya Islam. Ana ta shiri masu wanka nayi masu kwalliya suna yi waɗanda suka gama shiryawa suna ta ɗaukar hotuna a wayoyinsu. Iman tana ɗaga riga da skirt ɗinta na anko tana cewa itafa bata son a dinga yi mata gidan ƙugu (hips) saboda idan tasa sai gurin ya zama kamar jaka, anata dariya Aunty Husnah ta shigo hannunta riƙe da farin lace da farin mayafi ta miƙa mata.
Karɓa Iman ɗin tayi tana kallon Aunty Husnah dan son jin ƙarin bayani.
"Mamah tace na kawo miki idan kinyi wanka su zaki saka."
Habawa Iman ta buga tsalle tare da rungume kayan ta shiga yin rawar murna tana cewa.
"Yeeeeee wayyo Allah na Mamah I love you... I love you so much ni kaɗai ta yiwa."
"Aunty Husnah ina namu?" Hanan ta tambaya tana karɓar lace ɗin tana gani.
"A'ah ni shi kaɗai aka bani, kuma aka ce ita zan bawa tasa idan tayi wanka."
"Amman kuma waye yai mata?" Ikram ta tambaya.
"Wayasani? Nima aikoni aka yi."
"Uhmmm ƴar gayu nasan yanzu dana tambaya za'a ce na candy ne akai mata bayan kuma tuni an kwana biyu."
Duk ƴan ɗakin suka yi dariya, ita kuma Aunty Husnah tabar ɗakin tana yi musu dariya. Da sauri ta shiga wanka da anata fama taje tayi tana cewa sai kowa ya gama zata yi. Tana fitowa ta shirya cikin farin lace ɗin tana jujjuya a cikin madubi. Kuma Allah ya taimake ta ba'a yi mata gidan ƙugun da bata so ba.
"Wai ya za'ai ace kisa farin lace bayan kuma nima shi nasa? Wannan ai sai a rasa wace amaryar tsakanin ni dake." Islam amarya ta faɗa tana tsuke fuska.
"Ahhh kunjimu da mata, uwata tace nasa saboda kawai kina amarya sai ace bazan saka ba? Sannu ai kin dai san duk jaraba badani za'a daura auran ba. Muktar nakine bana Iman ba." Ta faɗa tana janyo kujerar madubi tana shafa hoda.
"Dalla can daman waye yace dake ne? Kin raina ni yarinyar nan saboda kinga komai muna yi tare dake."
"Oho dai nima irin kayan amarya nasa kuma dole na shiga cikin ku ayi komai dani tare da ƙawaye."
"Sai muce bazaki shigo cikin mu ba daman ai su Farha sune sa'anninki bamu ba." Ikram ta faɗa.
"Hehehehe lallaima, nida nai kandi (candy) sukuwa suna ss2 wallahi bazan shiga cikin su." Iman ta faɗa tana shafa man leɓe.
Haka suka zauna suna ta surutu har kowa ya gama kintsawa sannan suka fito falo. A dai dai lokacin ne Haneef suka shigo shida Dr Jamil da ya dawo yau suna son shiga gurin Mamah dan ya gaida ita karaf idanunsa ya sauka akan Iman wacce ke ta dariya tana dukan Janan. Gabaki ɗaya fara'ar fuskarsa ta gushe ganinta cikin farin lace tayi masifar yin kyau. Kamar ance itama ta ɗago suka yi ido huɗu dashi gabanta yai wani irin bugawa tayi saurin rintsa idanuwa tare da riƙe Jannan da karfi.
Areef ne ya fito shida Uncle Imran daga ɗakinsa sanye cikin farar shadda shima da malun-malun yayi masifar yin kyau abinka da mai kyau sai ya ƙara yin kyau. Uncle Imran yayi murmushi tare da kiran sunanta.
"Iman..."
Ta ɗago a hankali takai idanunta saitin inda ta jiyo ana kiranta.
Ai suna haɗa idanu da Areef ta saki wata gigitacciyar ƙara tare da rugawa da gudu bayan Jamil tana nuna saitin Areef tana cewa.
"Wayyo Allah aljanni, na shiga uku aljani ya shigo gidan mu."
Nan da nan aka fara waige-waige ana neman inda take nunawa ba'aga komai ba, su Mamah suka fito daga cikin ɗaki jiyo ihu suna kallon Iman dake bayan Jamil a tsugunne ta riƙe kai.
"Wane irin aljani kuma Iman? A ina kika ganshi?" Haneef ya tambaya cike da mamaki. Ta sake ɗago kai ta kalli inda Areef yake ta kuma kurma uban ihu tana cewa.
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun zai kasheni, gashi can... Kun ganshi can a tsaye, hasbunallahu wani'imal wakil.... La'ilaha illallahu Muhammad rasulillah s.a.w wayyo Allah na." Ta kuma zabura zata ruga aka riƙota.
"A ina kike ganinsa? Wajan ina ne?" Cewar Mamah tana rungume da ita.
"Gashi can kusa da Uncle Imran. Gashi can yana zaro min ido dan Allah dan Annabi ku fitar dashi karya kasheni."
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun." Cewar Mamah tare da fara addu'o'i tana tofa mata.
"Waiko tana nufin Areef ne Aljanin?" Islam amarya ta faɗa tana dafe ƙirji.
"Wane irin Areef kuma ana zaune ƙalau." Uncle Imran ya faɗa.
"Toh ai saitinsa take nunawa." Islam ta sake faɗa.
"Zo nan Areef." Cewar Haneef tare da janyo shi bayan shi.
"Iman tashi ki nuna mana inda kike ganin aljanin."
Iman ta ɗago daga jikin Mamah a hankali tana shassheƙar kuka ta kalli inda ta fara ganin aljanin amman wayan. Nan da nan ta fara kalle-kalle har idanunta suka sake sauka akan fuskar Areef. Wannan karon kansa tayi da gudu tana furta...........
(Me...? Shin me take furtawa? Yaaa salam😭)
*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
2/14/22, 10:22 - Buhainat: *ZO....GA...N*✍️
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*
*16*
"Wallahi sai na kasheka kafin ka kasheni, ni zaka aura? Bana sonka... Bana kaunarka, dana aureka gwara na auri Yaya Jamil."
Tana magana tana dukan Areef da iya ƙarfinta. Aka dinga ƙoƙarin janyeta amman kamar dutse duk sun kasa, sai Areef ɗin aka janye ta kuwa dinga kuka. Jamil kuwa raba idanuwa ya shiga yi yana nuna kamar shima baiji daɗin abinda yake faruwa ba a wannan lokacin. Uncle Imran ne ya fita waje da Areef suka tafi can inda za'a ɗaura auren wato gidan su Islam.
"Anya yarinyar nan tana da lafiya?" Cewar Aunty Husnah suna rirriƙe da Iman ɗin.
"Banga alama ba, kunaji tana faɗin da ta auri Areef gwara ta auri Jamil. Menene gaminta da shi?" Mamah ta faɗa