Iman ta kalleta tare da cewa.
"Kuce masa ya fita daga cikin ɗakin nan please." Ta faɗa tana dafe saitin kirjinta tana kuma rintsa ido tare da cije leɓenta na ƙasa. Areef ya zaro idanuwa yana kallon Iman cike da tsagwaran mamaki.
"Dear a fitar dani fa kika ce? Ni za'a fitar sweetheart?" Sai kawai sukaji ta fashi da kuka, cikin sauri nurses ɗin sukayi kanta suna lallashi, ɗaya daga ciki ta ƙarasa wajan Areef saitin kunnansa tace.
"Kayi hakuri kaje daga waje kaga yanzu ta haihu jininta zai iya hawa. Idan har da gaske kana kaunarta Toh kafita kamar yadda ta bukata, kayi hakuri."
Toh ya zai yi idan ma bai fita ba? Ya zauna ma ba ganin mutuncinsa zatai ba gwara ma kawai ya fito ɗin. Jiki a sanyaye ya miƙe tsaye, sai da ya kalleta sosai yana jin tamkar in yabar wajan wani abu zai faru, sai kawai ya juya ya fita da sauri. Su Mamah na zaune ya wuce ba tare da ya tsaya a inda suke ba. Suma babu wanda ya bishi har nurse ta kawo musu babyn cikin towel ɗinsa bayan sun sanya masa kayan sanyi. Gabaki ɗaya farin ciki ya mamaye su, Mamah farin ciki tamkar zatai hauka anyi jiki, Hajiyan sama kuma an samu tattaɓa kunne daga tsatson Sen Muhammad.
Mota Areefullah ya shiga gabaki ɗaya ya rasa abinda zai yi, duniya tayi masa zafi. Jiki na rawa ya kira Sen Muhammad suka gaisa yace.
"Baba Iman ta sauka."
"Ban fahimceka Al-Mustapha." Sen Muhammad ya faɗa cikin rashin fahimta.
"Baba ina nufin ta haihu yanzu an samu takwaranka."
Areefullah ba sauki🤣 wato ta nan ya ɓullo. Murna da farin ciki suka mamaye ilahirin zuciyar Sen Muhammad, a kuma take yace da Areef gashi nan zuwa dan ba zai iya jira ba sai yazo yaga jikansa kuma takwaransa da aka yi mai yanzu-yanzu. Ajiyar zuciya ya sauke tare da jingina bayansa a kujera, sunan Abba yaso sanyawa amman yanzu ya canza har ya sanar da Sen Muhammad cewa sunansa ne, so yake ya samu zuciyar Iman cikin sauki ba tare da yasha wahala ba, yasan tabbas zataji daɗi idan taji sunan mahaifinta yasa. Ya kira su Aslam ya sanar dasu suka dinga yi masa iskanci, be biye musu ba ya share saboda baya cikin jin daɗi.
Kansa ya kifa jikin sitiyari kunci duk ya damu zuciyarshi. Wayarsa ce ta shiga ruri, jiki ba kwari dan yasan kila ƴan barka ne yana dubawa yaga Hearty, ya ɗaga tare da karawa jikin kunnansa ba tare da ya yi magana ba yaji tace.
"Babylove ina ka shiga ne yau?"
"Na dawo Nijeriya Feenah." Ya faɗa a sanyaye.
Mamaki da tashin hankali suka sameta, Feenah kuma kai tsaye? Meke faruwa haka? Anya Areef ɗinta ne da ta sani tunda-da? Feenah fa ya kirata kai tsaye, batajin tunda suka fara soyayya ya taɓa kiranta da wannan sunan sai dai in cikin tsokana, yanzu kuma ba maganar tsokana da gaske Feenah ya kirata. Amman da yake ita ɗin itace sai ta hana zuciyarta amince da kiran, cikin sanyayyar musu tace.
"Nijeriya kuma? Meke faruwa haka?" Kai tsaye yace da ita.
"Feenah ina cikin problem wallahi, alaƙatarmu tana son janyo min fushi mai tsanani wanda yafi na baya a gurin su Mamah. Please Feenah ina son mu hakurewa junan mu, Allah kuma ya yafe mana kurakuran mu." Ai kawai sai ta saki kuka, hankalin Areef ya sake tashi sai dai yayi ta maza yace.
"Iman ta haihu yanzu, Feenah Iman bata da matsalar komai, tana sona. Kiyi hakuri kinsan ina sonki amman kaddara ta riga ta shigo tsakanin mu. Ki koma gurin mijinki kici gaba da hakuri wata rana sai labari." A mamakance yaji tayi dariya tare da cewa.
"Hakane, nima na kiraka ne dan na sanar dakai cewar Sultan zai zo mu koma Nijeriya zan kuma koma gidan shi saboda ɗan mu Areefullah. Nagode sosai da kulawarka gareni, Allah kuma ya raya mana babyn mu. Bye-bye Al-Mustapha nima dai yau ɗaya na faɗi sunanka a kunnanka." Murmushi yayi cike da farin ciki cikin kuma zolaya yace.
"Da gaske kin hakura zaki koma gidan Sultan?" Tace.
"Zan koma tunda yaki saki na, anyi-anyi amman yaki Toh ya zanyi?"
"Kai masha Allah amman naji daɗi sosai, Allah ya baku zaman lafiya da juna."
"Uhmmm." Abinda Feenah tayi kenan ba tare da tayi magana ba.
"Sai anjima ƙanwata, a shafa min kan takwara."
"Zaiji daddy." Ta faɗa suka yi dariya tare da katsewa.
Sai a yanzu ya samu ƙwarin guiwa, yasan cewa sun rabu da Feenah har abada, wannan labarin dole ya kaiwa Iman shi yasan sai tafi kowa farin ciki dajin daɗi. Ya fito daga motar ya nufi cikin reception inda su Mamah suke zazzaune. Guri ya samu ya zauna ya zungiri Ikram tare da cewa.
"Dallah karbo min ɗan keda baki san kije kiji meke damuna ba. Karɓo min shini ƙaruwar kawai."
Ikram tayi dariya ga haushi yana cin ta na jin labarin Feenah. Jaririn yana hannun Hajiyan sama ta Karɓo shi ta miƙa masa. Ya ɗan buɗe towel ɗin da aka rufe jajirin yana leƙansa, wani irin farin ciki ya mamaye shi cikin ransa yace. 'Allah ya dawo min da hankalin Mamanka' Sannan ya kai bakinsa saitin kunnan babyn yana yi masa khuɗuba......
(Washhh Allah na🙄Yasin na kagu na gama🤣ku min addu'a please 😫) Comments ɗin ku fa yayi 💪 domin kun ɗauki abin kamar yadda nima na dauka a lokacin da naji labarin
*HAJJA CE 👈*
4/1/22, 13:25 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲)*
*44*
Babu daɗewa Sen Muhammad ya ƙaraso asibitin, a lokacin an gama gyara Iman ta koma resting room anata hira da ita, ba zaka taɓa cewa itace ta haihu yanzu ba saboda yadda take ta zuba labari tana kyalkyale dariya. Areef tare ya shiga shida su Sen Muhammad, sosai yaga farin ciki a fuskar Iman ɗin, Sen Muhammad ne ya ƙarasa kusa da ita suka rungume juna ya shafa kanta fuskarsa a washe yana ta murna.
"Sannu Imanini, sannu da ƙoƙari yarinya ta, irin wannan farin albishir haka? Naji daɗi sosai da samun takwara na, Allah yai muku albarka ya raya mana shi ya kawo ƙannansa kamar guda ashirin, kunga na samu yara da yawa nima." Duka gurin babu wanda beyi dariya ba, tausayinsa ya kama Hajiyan sama.
"Ina roƙanku dan Allah karku yi wannan planing ɗin da akeyi, yanzu mutane sun ɓaci haihuwa ɗaya kiji mutum yace yaro ya isheshi. Ni dai kuyi tayi zan dinga karɓa ina raino, nan gaba idan Allah ya barmu a raye sune zasu zama abin hira ta. Kunga dai bani da wasu yaran, Iman ce kadai itama kuma ba wani shakuwa mukai da ita ba, but little Muhammad zai zama aboki kuma aminina Insha Allahu."
Mamaki ya kama Iman ɗin ta kalli inda Areef ɗin yake, ya sakar mata murmushi ita kuma ta watsa masa harara tare da kawar da kai tana yiwa Sen Muhammad murmushi. Tasha mamaki dan ita dashi sunyi magana akan cewar za'a sanya sunan Abba, sai kuma yanzu taji saɓanin zance. Taji daɗin hakan amman saboda karya gani yasa taki nunawa a fili, dan ita har yanzu so take taga yana bacin rai.
"Ya kamata dai a koma gida tunda an haihu lafiya ba tare da wata matsala ba." Sen Muhammad ya faɗa tare da kallon mahaifiyarsa dan jin abinda zatace.
"Haka ne, dama likita yace a ɗan dakata kafin a bada sallamar."
"A kirashi ya bada yanzu, gwara ku koma gida komai zai fi yi muku sauki." Yayi maganar yana cewa ɗaya daga cikin securities ɗin shi yaje ya kira likita. Babu jimawa sai gasu a tare, nan Sen ya bukaci a sallamesu, babu wani ɓata lokaci kuwa ya bada magunguna da sauran abubuwan da zasu yi mata, aka ɗakko ta sai gida.
Mamah ce tai mata wankan farko, haba Iman tasha kukan ruwan zafi. Da taji an ɗora mata towel ɗin nan zata saki uban ihu tana rirriƙe hannun Mamah, cikin kuka take cewa.
"Wallahi Mamah da zafi, dan Allah a sirka."
"A'a Iman wannan shine gatan da zanyi miki, wanka shine sirrin jego, idan har baki gasu ba yanzu to akwai matsala, yarinya wari zakiyi ki dinga ɗoyi mijinki kuma ya rainaki. Idan baki gasu ba wallahi zaki cuci kanki, musamman kinga yadda yanayin mijinki yake mai shegen idon gane-ganen ƴan mata. Kyaleni na wankeki tas yadda zaki kara ƙima da mutunci a gurinsa."
Haka Iman tana ji tana gani Mamah ta salleta tas sannan ta barta tayi wankan soso da sabulu sai faman tuturo baki take. Lallai mata na shan wahala, kayi laulayi, rainon ciki, haihuwa ga ruwan zafi na wanka, uwa uba rainan ɗan idan yazo duniya, ga ciwon nono idan za'a yaye baby. Allah sarki Allah yasan hikimar da yasa ya yiwa mata daraja. Toh amman me yasa aka ce sunfi yawa a cikin wuta? Haƙika suna cikin ƙalubale. Ta rintsa idanuwa tare da shigewa cikin ƙwamin wankan.
Su Mamah basu samu damar komawa Kano ba sai ana jibi suna ta tattara ita da Areef suka dawo, wanda duk iya jarabarsa nasan ya hadu da Iman ya gagara tun randa akai haihuwar rabonshi da ita. Koda ya dawo Kano ma bashi da wani sukuni. Gabaki ɗaya ya rasa madafa saboda Mamah ta saka masa ido, tace karya sake ya koma Abuja sai bayan suna dan karma ya ɓatawa mai jegon rai.
Waya kuwa sai ya kira sau nawa amman Iman bata ɗauka, a gabansa kuma Mamah zata kira yaji suna ta magana, suna ajiyewa zai kirata taki kulashi.
______________
Hajja Samira kam da kyar take yin wasu abubuwan saboda takaicin ganin jikan Sen Muhammad. Gashi duk iya masifarta ta kasa gano inda manufar zuciyar Sen Muhammad ɗin take akan ƴar tashi da kuna jikan da aka haifa masa, saboda baya taɓa nuna soyayyar Iman ko kuma ta boy ɗin a gabanta dan yana gudun ta cutar masa dasu. Sen Muhammad shine ya yi komai da komai na suna, shanu kuwa sai masha Allah waɗanda aka yanka. Ƴan ƙauyan su Iman ma yasa aka kawo su sai dai inna Habiba mahaifiyar Iman ɗin bata biyo su ba saboda alƙunya kamar yadda Mamah itama bata tsaya anyi taron suna da ita ba.
Anci ansha anyi guzuri, Hanan tazo itama da nata tsohon cikin suna ta yi mata tsiya, da yake mai shiru-shiru ce bata iya basu amsa sai dai murmushi kadai. Maijego an fito shar, yan fitilun nan sun ciko tamkar basu ba, sun daɗa girma ga kyau na musamman da tayi. Hajiyan sama bata yi mata da wasa wajan ganin taci abin da zai kara mata kuzari da kuma ruwan nono.
Yaro yaci suna Muhammad Al-Mustapha Ahmad (Daddy), yasha kyaututuka daga wajan ƴan siyasa shida Mamansa tamkar babu gobe. Washe gari ko Mamah bai yiwa sallama ba ya fice ya tafi Abuja, ƴan aiki suna ta suyar nama ƙamshi ya busasa ko'ina. Sallama ɗauke cikin bakinsa ya shiga falon babu kowa ya wuce ɗakin da yasan tana ciki wato inda yake nata. Cak ya tsaya a bakin ƙofar yana hangenta zaune gefen gado tana shayar da Daddy.
Murmushi ya saki ganin yadda tayi kyau cikin pink ɗin lace anyi mata riga da skirt. Ikram na kusa da ita tana gyara mata gashin kanta. Kamar ance ta juya ta kalli bakin ƙofar ido buɗe tace.
"Yaya Areef." Da sauri Iman ta juya tana kallon ƙofar shigowa, ya sake faɗaɗa murmushinsa.
Juyar da kai tayi shi kuma ya samu damar ƙarasowa cikin ɗakin. Alama ya yiwa Ikram da ta bar ɗakin, ta ajiye cum ɗin tana Cewa Iman.
"Ina zuwa." Ta fice da sauri.
Shi kuma ya rufe ƙofar ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Gaba ɗaya turarensa da na jikinta suka hadu suka bada wani ni'imataccen ƙamshi a gurin. Bata kulashi ba duk da tana ji yana zungurinta da ƙafaɗarsa. Ya tsira musu ido ita da babyn yaga yadda yake ta zuƙar nono ido a lumshe. Hannu yasa tare da zare babyn yana cewa.
"Kai ka gama sha haka." Cikin sauri tace.
"Bangane ba, kamar ya zaka ce ya gama sha.?" Yadda tai maganar a tsiwance shi ne yasa Areef kallonta, tayi saurin kawar da kai saboda idanunsa suna da wani tasiri da in har tana kallansa takanji ya yi galaba akanta. Yasa hannu tare da maida mata shi cikin riga yana cewa.
"Kai! Gaskiya ka gama shan Nonon nan, Kinga yadda suka sake zama so cute? Wowwww gaskiya kin ƙara kyau my dear wife." Ya faɗa yana sumbatar ta a gefen kumatu.
"Ka bari bana son kana taɓani. Kuma ma da zakace bazan bawa yaro nono ba me zan bashi bayan yana sha?"
"Yanzu zanje na siyo masa madara, madara za'a bashi gaskiya a bar min kayana." Haushi da takaici suka rufe Iman ta gyara rigarta tare da miƙewa tsaye tana cewa.
"Gaskiya ba zai yiwu ba, ni ban samu damar sha a gurin mahaifiyata ba. Yanzu ace ɗan da na haifa shima irin rayuwar da nayi zai yi? ina cewa saboda su Allah ya halatta mana shi a jikin mu, dan haka shi zai sha saboda samun kusanci mafi daraja a tsanin mu." Shima Areef ya miƙe tsaye tare da lasar lebansa da ya fara bushewa yace.
"Ina ce nawa ne ko?" Cike da mamaki tace.
"Menene naka?" Yaja numfashi tare da cewa.
"Waɗannan Fitilun." Yayi maganar yana pointing kirjinta. Haushi da takaici ya sake kama Iman tace.
"Eh na jikinka ba."
"Karya ne na jikinki ma nawa ne tunda aure ya bani." Taja ɗan ƙaramin tsaki wanda iyakarsa saman harshenta tace.
"Kaji dashi, abinci kuma sai yaro yasha abinsa tunda dan su Allah ya yo mana." Tayi maganar tana janyo kayan da aka cirewa Daddy tana ninkewa.
Ƙarasawa kusa da ita yayi kawai taji ya rungumeta ta shiga fizgewa amman ya matseta tsam har sai da ya tabbatar ta hakura da son kwace kanta. Ya shiga yi mata yawo da fuskarsa mai ɗauke da zagayeyyen sajen bakin gashi, Iman taji wani yanayi tare da rintsa ido tana jujjuya kai. Sannu a hankali har sai da ya zaunar da ita akan gado still yana riƙe da ita, ya kwanto da ita suka haye kan gadon yana mata magana cikin salo na zace zuciya, saboda Areef ya riga yasan duk wani salo da yake birkita duk wani lissafi dake kan matar tashi.
"Kiyi hakuri dear, ki dena wahalar dani kina wahalar da kanki. Ki barmu mu rayu ciki jin daɗi dan Allah." Iman taja numfashi tana kauda fuska tace.
"Shi yasa na barka kaje kuyi rayuwa da kaida mai sanka, kasha gaya min cewa Feenah tana mutuwar kaunarka, ni kuma ai kaga ƙinga nake yi ko? Toh na barka ai menene kuma na damuna? Ni yanzu karatu na shine babbar da muwata."
"Okay ba nine damuwar taki ba kenan?" Ya tambayeta yana kwantar da kansa a saman bayanta.
"Naga ɓatawa kaina lokaci nake yi, ina gida a zaune ashe kai kana can kana wulakantani ta hanyar yin soyayya da wata, watan ma kuma bazawara, hmmm." Ta faɗa zuciyarta na suya tare da kuma kiciniyar fizge kanta.
"Kai innalillahi, dama ance ƴan shawal-shawal ɗin nan sunfi tsiwa. Mata masu ƙiba hakuri garesu, da Feenah ce ina cewa tayi hakuri zata hakura ba zata min musu ba." Habawa Iman najin kalamansa bata san lokacin da ta nausar masa ciki da guiwar hannunta ba, ya saketa yana riƙe ciki tayi saurin sauka daga kan gadon.
Cikin ɓacin rai ta kalleshi tana huci haushinsa kamar ya kasheta tace masa.
"Shi yasa nace kaje ka aureta zakafi samun nutsuwa da kwanciyar hankali. Kuma Muma ai bamu muka halicci kan mu a haka ba, karka sake zuwa inda nake kaji na gaya maka." Tana kaiwa nan ta suri Daddy cikin sauri tabar ɗakin tana zubar da hawaye.
Gaskiya maza basu da kirki, wai ita yake cewa tana da tsiwa, amman Feenah bata da ita. Wai wata banza can yake yabo a gabanta. Idan har da gaske tana da hakuri meya fito da ita daga gidan mijinta? Me yasa bata yi hakuri ta rayu da mijin da Allah ya bata ba har tazo tana cewa wani shi take so, shi take sha'awa harda cewa ayi mata koda sau ɗaya ne? A hakan wai lallashinta yazo yi ta koma gareshi lallai ma. Ta shige can sashen Sen inda babu wanda zai iya zuwa sai ita kadai.
Areef ya sakko daga kan gadon yana cije leɓe. Ya rasa dalilin da yasa Iman bata son yayi maganar Feenah a kusa da ita. Hularsa dake kan madubi ya ɗauka ya fito yana gyara wuyan rigarsa. Yana fitowa suka hadu da Ikram ta zubo naman a plate zata kai masa tace.
"Yaya ya ka fito har ina kawo maka ɗanɗane?" Yaja tsaki.
"Na ƙoshi ina Iman ta shiga?" Cikin mamaki tace.
"Kai da na baroku tare da ita."
"Ai ta fito ita da Daddy."
"Bari muga ko tana ɗakin Hajiyan sama." Ta juya ta wuce. Yana ta safa da marwa sai ga Ikram ta dawo.
"Yaya bata can, kuma gaskiya banganta a can area ɗin dana baro ba."
"OH my God!" Ya faɗa tare da shafa haɓarsa.
"Wai kuwa Ikram kina janyo min hankalin Iman kuwa? Mamah taki lallaɓa min ita shine kema zaki yi watsi dani?"
"Yaya ni meye nawa a ciki? Yanzu me tace maka.?" Yace.
"Wa?"
"Iman ɗin." Yace.
"Ta kuma yin fushi wallahi."
"Toh... Amman kai Yaya me yasa ka fiye barin kuna faɗa tsakani da Allah."
"Wallahi daga yi mata example akan Feenah shikenan ta fice ta ban guri."
"Lallai ma yaya Areef, waye yace maka mace tana son a dinga yi mata kwatance da wadda tasan akwai alaƙa tsakaninta da mijinta? Tabɗi jam, Toh wallahi ka dena, Iman matarka ce. Idan ka bari ta kubuce maka zaka sha mamaki."
"Na sani Ikram, but yanzu meye abin yi?"
"Wallahi ban sani ba sorry."
"Mtwww." Yaja tsaki tare da ficewa ya barta a tsaye.
Har dare Iman taki fitowa, yaje ya dawo ya kai sau goma amman an rasa inda ta shige. Hakura yayi yaje ya kama hotel Washe gari kawai ya wuce Kano. Satinsa guda koda aka kawo masa naman suna beci ba ya wuce dashi US, suka hadu dasu Aslam suka cinye. Duk wata hanya yabi wajan ganin ya sakko da zuciyar Iman amman ya kasa har tayi arba'in a lokacin ne kuma ya fara shirin komawa nigeria ayi ta ta ƙare......
(Uhmmm nace ba! 🙄Maza mutanan mu🚶🏻♀️hmmmm... Uhmmm)
*0706 528 3730 ga mai bukatar karanta book ɗin.*
*HAJJA CE 👈*
4/1/22, 13:25 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please