Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   13 / 38

36K to 39K   out of 113.7K words

tana kallon inda Jamil ɗin ke tsaye.

"Waye Jamil kuma? Ko saurayinta ne?" Wata dake cirewa Iman ɗanƙwali ta faɗa.

"Gashi can abokin Yayan su ne, duka-duka ma yaushe suka sanshi amman kinji wai gwara ta aure shi sai kace yace mata auranta zai yi." Tana kwance jikin Aunty Husnah tace.

"Mamah zan aure shi idan na tashi yin aure."

Gaba ɗaya suka buɗe baki suna kallonta cikin mamaki, shi kuma Jamil yaja hannun Haneef suka fita daga cikin falon.

"Anya yarinyar nan tana cikin hankalinta kuwa? Bata taɓa nuna tana son muyi soyayya ba amman kaji wai aurena zata yi."

"Abinda na kasa ganewa kenan Dr. Saboda abinda ya faru Abba yace zai haɗa auranta dana Areef, ni nasan daga ita harshi basu da masaniya akan auran. Amman yanzu naga abu yana neman hargitsewa."

"Aure kuma Captain? Iman da Areef zaku haɗa aure? Me yasa? Wa da ƙanwa kuma?" Jamil yayi maganar cikin mamaki tamkar besan da maganar auran ba.

"Labarin is too long. Kuma sirri ne da iyayen mu basu son a fasa shi a duniya. So mubar maganar kawai iya nan."

Jamil ya gyaɗa kai cikin zuciyar shi yana cewa 'Naga ta yadda za'a ɗaura auran nan' amman a zahiri cewa yayi.

"Allah ya kiyaye." Haneef yace.

"Amin."

Sashen Haneef ɗin suka wuce zuciyar Jamil cike da farin cikin ganin yadda haƙarsa zata cimma ruwa, yasan dole in sukaga Iman na wannan abin zasu bashi ita a yau ba gobe ba, dan haka ya sake kwantar da hankalinsa yana jiran yaji daurin auransa. Iman kuwa tuni ta ware sai dai bata da walwala kamar farko, amman kwana biyu da akai kamu akai dinner ta cashe kamar babu irin wannan ranar sai ita. Areef kuwa suna tare da Uncle Imran ya hanashi sakat abisa umarnin da Abba ya bashi na cewa karya sake yabar Areef zuwa ko ina face an ɗaura aure.

Ƙarfe goma sha biyu na rana dubban jama'a suka shaida auran Fatima (Islam) da angonta Muktar. Kawu Balarabe dake hanyar zuwa wajan ɗaurin auran wanda shine zai yi na Iman da Areef yana kusa da ƙarasowa unguwar wata ƙatuwar tirela ta buge motarsa, hakan yayi sanadiyar yin wani mummunan hatsari. Kasan cewar babu nisa tsakanin gurin ɗaura auran da kuma inda akai hatsarin yasa ƴan ɗaurin auran ƙarasawa wajan dan ganewa idanunsu.

Dr Jamil dake can ƙarshen layi yana waya cikin tashin hankali yake cewa.

"Nace maka kowaye yake da niyar haɗa auran nan ka sallame shi, Iman tawace koshi Haneef ɗin idan yayi ƙoƙarin ganin an ɗaura da Areef kayi sanadin da zai bar duniya." Yayi shiru yana sauraran ɗaya ɓangaren, ya sake cewa.

"Ina son ka sake hargitsa min ita ta yadda zata dage ni zata aura, na gaya maka yadda yarinyar ta shiga zuciyata lokaci gudu, bazan iya hakura da ita ba kayi yadda nace maka... Toh shikenan ina nan tare dasu... Eh babu inda zani koda zasu zargi wani abun a kaina."

Ya sauke wayar tare dajan wani dogon numfashi yana ƙanne ido ɗaya. Kamar bashi ba haka ya koma cikin mutane ana ta jajanta abinda ya faru. Abba ya kira mahaifin Islam a lokacin an tafi kai kawu Balarabe asibiti wanda baisan inda kanshi yake ba. Abba yace.

"Zanje asibiti ka wakilci wannan ɗaurin auran, a yau muke fatan a ɗaurashi saboda bana son hankalin Areef ya sake karkata wajan fitinanniyar yarinyar nan." Yasa hannu ya zaro kuɗi dubu ɗari cif ya miƙa masa.

"Wannan sune sadakin da za'a bada, kaje yanzu kafin liman ɗin ya fito."

"Toh shikenan Allah ya rufa asiri nima idan komai ya kare zan zo asibitin." Abba ya wuce shi kuma mahaifin Islam ya koma cikin sitting room ɗin.

Duk da mutane suna ta tare shi ana yi masa Allah ya sanya alkairi sai da ya shiga ya miƙawa liman kuɗin. Yana gama yiwa liman bayani kuwa babu ɓata lokaci aka ɗaura auran Iman da Areefullah. Sai dai tun kafin a gama shafa fatiha aka ga wuta ta faracin babbar rigar liman da ƙasan wandon mahaifin Islam. Tashin hankali Areef dake can gefe tun da ya shiga gurin beko motsa ba sai a lokacin da yaji ance an ɗaura auransa da Khadija, wacce sam be kawo cewa da Iman bane ya tashi ya nufi gurin kawu Sagir.

Da sauri Uncle Imran ya riƙo Areef ganin yana shirin yin ganganci, cike da faɗa yace.

"Menene hakan?" A gigice Areef yake cewa.

"Wuta... Wuta uncle." Ya kuma yin kan wutar uncle ya sake damƙeshi a jikinsa.

Shi kansa Areef ɗin besan yadda akai yake jin son zuwa gurin wutar ba, jiyayi kawai ana fisgarsa ana tilasta masa zuwa garesu bawai dan taimakawa ba. Anata zuba ruwa a cikin wutar wasu kuma suna son fito da Areef. Allah ya basu sa'a aka kashe ta sai dai ta yiwa duk wani wanda ya taɓa kuɗin sadakin auran Iman illa a jiki.

Cikin gidan kuwa ana cikin jimamin hatsarin kawu Balarabe suka kuma jin shailar ɗaurin auran Khadija, nan fa aka fara tambayar wacece Khadija? Mamah tace Iman. A lokaci guda kuma suka jiyo wata gigitacciyar ƙara tare da faɗuwa. Iman ce ta yanke jiki ta faɗi bata koda motsi at the same time kuma suka jiyo labarin wutar da take ci a ɗakin ɗaurin auren.

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun wannan rana kaf ahalin Alhaji Ahmad babu wanda bai shiga cikin tashin hankali ba. Aka shiga ƙoƙarin bawa Iman agajin gaggawa wajan dawo mata da numfashi amman ina komai aka yi mata bata motsawa. Ya subahanallahi Iman ta mutu, ta mutu babu rai a jikinta. Mutane suka dinga faɗa ganin yadda ake zuba mata ruwan sanyi a jikinta amman ko motsi bata yi.

"Hajiya sai dai kuyi hakuri, amman tabbas Khadijatul Iman ta riga mu gidan gaskiya." Mama Rabi ta faɗa tana kwantar da Iman a ƙasa.

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun ta mutu? Ta mutu fa kika ce Rabi? Wannan wace irin baƙar rana ce a gare mu?" Cewar Mamah tana kuma fashewa da wani irin kuka.

"Kuja Hajiya cikin ɗakinta, ita kuma Iman ku ɗakkota muje asibiti su duba."

Mama Rabi ta bawa su Aunty Husnah umarni, nan da nan kuwa suka kama Mamah zasu kai ɗaki ta make su tare da cewa.

"Baku da hankali ne? Ana cikin wannan bala'in zaku kai ni ɗaki? Uban me zanyi a can idan naje? Kubani ƴata ni zan kaita asibitin da kaina."

Tana magana kai da kaga yadda take yi kasan bata cikin hayyacinta, amman babu yadda zasu yi mata dole suka kyaleta aka fita nemo wanda zai kaisu asibiti. Hanan ce daman ta fito kuma cikin sa'a taga Jamil yana ɗibar ruwa a cikin bokiti da alama hardashi a bawa masu kashe wuta gudunmawa. Cikin tashin hankali ta kira sunan shi tana cewa.

"Yaya Jamil kazo ka kai su Mamah asibiti."

Ya juyo yana kallanta cike da tsana a zuciyarsa domin kaf ɗinsu haushin su yake ji. Amman a fuskarshi alamun tashin hankali ne ƙarara, yaja numfashi tare da cewa.

"Lafiya dai ko?" Tace,

"Ina tunanin Iman ta mutu." Sai da kirjinsa yai wani irin bugawa saboda yadda kalmar ta daki zuciyar shi.

"Ta mutu?" Ya tambaya yana zaro ido dan basu yi maganar a kasheta ba.

"Eh Yaya Jamil, kazo Mamah ba ta yadda cewa Iman ta mutu ba."

"Ke dalla yiwa mutane shiru, sai wani ambaton mutuwa kike yi, ubanwa yace muku ta mutu?"

Mamaki ya kama Hanan ganin yadda yake mata masifa, amman sai tayi tunanin ko shima ya kiɗima ne dajin maganar. Bata san haushin kalmar bane yasa shi cikin ɓacin rai. Suka shiga cikin falon tare ya kalli Iman wacce Mama Rabi ta rungume a jikinta, ya rintsa idanuwa tare da cizon leɓansa na ƙasa, cikin dauriya dan karya tonawa kansa asiri yace.

"Muje ko?" Yana kallon Mamah.

Ta tashi ita da Aunty Husnah suka ɗauki Iman suka fito mutane suka biyo su har wajan mota. Basu tsaya ɓata lokaci ba suka shiga Jamil yana shirin tada motar Haneef ya ƙaraso wajan yana tambayar inda zasuje. Mamah ta gaya masa zasu asibiti ganin Jamil ne kadai yasa Haneef juyawa ya kirawo Irfan Abokin Areef yace suje tare koda akwai baƙatar taimako sai ya taya Jamil ɗin. Duk da ran Jamil a ɓace yake hakan baisa ya nunawa kowa a fili ba, sai dai ji yake kamar zai mutu saboda auran nan da aka ɗaura.

Suna tafiya yana jin tamkar yayi sanadin mutuwarsu, ji yake tamkar ya saki sitiyarin motar, sai dai kuma yana hango irin rayuwar auran da zai yi shida Iman a gidan shi. Haka kurum yaji ta maƙale masa can cikin jini da ruhinsa, baya tunanin ya taɓa son wata halitta kamarta, ciki kuwa harda iyayensa, matarsa da ƴaƴanshi. Asibitin da aka kai kawu Balarabe dasu liman nan ya kawo su saboda shine asibiti mafi kusa.

Itama aka kaita imajansi (emergency), Allen sarki Abba haƙika duk wanda yai sanadin wannan abubuwan har ya shiga cikin wannan halin sai Allah ya saka masa, domin gabaki ɗaya ya firgice ya gigice ya zama tamkar wani zautacce. Kuɗi kuwa sai da ya haɗa da rance saboda nashi sun ƙare. Su Mamah suka isa wajan shi yace.

"Ita kuma me ya same ta Hajiya?"

"Babu Alhaji, wallahi ana shela ɗaurin auranta gabaki ɗaya ta faɗi. An zuba ruwan muna tunanin ko suma tayi amman a banza shi yasa nace mu taho asibiti."

"Lahaula fisha'atillah, La'ilaha illah anta subahanaka inni kuttu minazzalimin. Allah ka yafe min idan har laifi nayi ake jarrabatata yau, Hajiya daga haɗa aure kuma sai masifu kala-kala? Me yasa ba'a ɗora duk waɗannan abubuwan a jikina ba? Waɗannan bayin Allahn gayyato su kawai nayi su tayani farin ciki, su zama shaidu. Amman dubi abinda ya faru."

Sai hawaye shar-shar-shar a fuskar Abba. Rana ta farko da ita kanta Mamah ta fara ganin kukan mijin nata. Jamil dake jinsu ya tabe baki, shi yanzu abinda ya dameshi shine yasan asalin Iman, sannan kuma ta farfaɗo ya ɗauketa ya gudu.

Suna nan daga azo ace ana son jini sai azo ace ledar ruwa bata ishi wani a cikin su ba, sai ace sai an siyo wani maganin. Sai daga baya ne Jamil yace sai shiga ya duba marasa lafiyar bayan ya nuna musu ID card ɗinsa. Kai tsaye inda Iman take ya nufa aka dinga ƙoƙarin dawo mata da numfashi ta hanyar sanya mata ossijin (oxygen). Ganin abin ya cutura ne yasa Jamil fitowa can nesa da asibitin ya tafi ya kirawo wanda suke waya ɗazu............

(Oh my God Jamil😒 Bako ya zama jaraba)🤔

*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.








*HAJJA CE 👈*
2/14/22, 10:26 - Buhainat: *ZO....GA...N*✍️
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*

*17*




"Har ita ka haɗa ne ko kuwa? na kasa ganewa fa bata motsi tun ɗazu. Idan ka kasheta ka gaya min wannan wane irin aiki ne." Magana yake yi cikin wani irin yanayi wanda kai daka gani kasan yana cikin damuwa.

"Yallabai kayi hakuri, wajan yin aikin ne aka samu tangarɗa. Kuma y...." Cikin masifa ya sake tare shi.

"Kanayi min aiki da yawa ina ganin kawunsu, wannan karan kana nufin kace matsalar akan abinda nake so aka samu tangarɗa? Wallahi idan har ta mutu akwai matsala, malam kayi yadda zakai wajan dawo min da rayuwarta dan Allah."

"Karka yi min rashin kunya Jamilu, idan ba haka ba yanzu nayi maganinka wallahi."

Jin haka yasa Jamil yin shiru tare da dafa kai, shi kansa lokacin da yake masifar ya manta dawa yake yi. Sai da yaji malamin yace zai yi maganinsa, yasan kuma illatashi zai yi kamar yadda yasan suna yiwa wanda ya tare musu gabansu.

"Kanaji na ko?" Jamil yace,

"Eh Malam ina ji."

"Yauwa Toh kasan yadda zaka yi ka samu silin gashin kanta ɗan kadan kasa a baki ka kora da ruwa. Kasan yadda dai ake shan magani ko?"

"Eh nagane." Cewar Jamil yana buɗe ido a hankali.

"Yauwa kana gama haɗiyewa ita kuma yarinyar zata farfaɗo, idan ta farfaɗo kuma zata biki duk inda kace. Sannan kuma babu wanda ya isa ya rabaku duk duniyar nan, zata soka fiye da rayuwarta."

Murna da farin ciki suka cika zuciyar Jamil, ko jiran wata maganar beyi ba ya koma cikin asibitin. Kamar yadda aka bashi umarni haka ya aiwatar da komai, cikin ƙanƙanin lokaci Iman ta farka da wani irin gigitaccen ihu mai firgitarwa. Sai dai Jamil yayi dabara yabar asibitin ya koma gida saboda karta kuma yin gigin da zai sa a fara zarginsa. Tana farfaɗowa su Abba suka shiga wajanta da gudu, ko umarnin likita basu jira ba. Mamah ta rungume ta a jikinta tana hawayen farin ciki.

"Mamah wai Yaya Areef kuka aura min?" Iman ta tambaya.

"Kiyi shiru kibar wannan maganar har Allah ya baki lafiya. Kuma idan shi muka baki ina son kiyi biyayya da umarnin mu." Ai Iman naji ta fashe da kuka tana cewa.

"Mamah Yaya Areef zan aura? Wallahi bazan yadda ba dana aure shi gwara na auri Yaya Jamil shi nake so shine abokin rayuwar da zan iya zama tare dashi, bana son Areef ba zan aure shi b....." Bata ƙarasa ba Mamah ta katse ta.

"Nace kiyi shiru ko? Daman mu ba amincewarku muke nema ba. Biyayyarku gare mu ita muke so kuyi amfani da ita wajan karɓar zabin da muka yi muku."

Hawaye suka shiga zubowa a idanun Iman, zuciyarta kamar zata ƙone haka takeji idan an ambaci Areef. Abba dake tsaye aka kirawo shi cewar yazo yasa hannu a jikin wata takarda ya fita. Nan fa Iman ta azalzali Mamah ita sai an koma gida bata son zaman asibitin. Dole sai da aka basu sallamarta suka koma gida. Suna shiga kuma Jamil ya hango su ya saki ajiyar zuciya yasa a yau ba sai gobe ba zai ɗauki Iman.

********

Zagaye kawai yake yi a cikin ɗakin uncle Imran, hayaniyar ƴan biki duk ta gallabi cikin kunnuwansa, ya zube akan gado yana cizon leɓe. Tunani kawai yake yi wacece Khadija da aka aura masa a wannan ranar? Ƴar gidan waye? Ya take? Anya zai so wata kuwa bayan Feenah? Saboda ita ɗin ta dabbance, son da take masa na musamman ne. Ita kuwa Khadija fa?

Ya saki tsaki tare da miƙewa ya leƙa ta taga yana hango mutanan da suka cika gidan kawu Sagir. Gaba ɗaya biki ya koma gidan jaje, ana ta jajanta abubuwan da suka faru. Shigowar Uncle dasu Aslam ɗakin yasa Areef samun guri ya zauna.

"Gasu nan na kawo maka su tayaka hira angon Nana." Cewar Uncle Imran yana murmushi.

"Wai uncle sai kace nayi sata an garƙameni a ɗaki, dan Allah a barni tunda an ɗaura auran nan." Areef ya faɗa cikin ɓacin rai.

"Abba yace karna sake na barka saboda yana zargin barinka sakaka zai sa ka sake zuwa wajan ƴar iskar yarinyar da ta ja maka aure."

Cikin zuciya Areef yace 'Feenah ba ƴar iska bace' a zahiri kuma ɗauke kai yayi ga barin kallon Uncle. Aslam yai dariya tare da tsuke fuska yana cewa.

"Wallahi kana gama cin amarci kasan yadda zakai wajan karɓo min mashin ɗina, haka kurum kasani yawo a ƙafa."

"Karka dameni dan Allah. Kuma bazan karɓo ba idan kai bazakaje ka ɗakko ba a barshi. Waya tama duk suna can."

"Wannan kuma kai ya dama, ni mashin ɗina nake magana." Areef yaja tsaki tare da juyawa yana cewa.

"Ni wai waye yace uncle ya kawo min kai nan? Kaje can kaji da rayuwarka tunda ka kasa yi min kyakkyawar fahimta, kaima kana ɗaya daga cikin masu yi min kallon...." Ya kasa ƙarasawa saboda girman kalmar.

"Easy mana angon Dijah, banda ma dai yau tazo da matsaltsalu ai nasan da babu mai hanaka gwangwajewa ko?" Cewar Sultan yana daga gefen gado.

Areef yai mishi banza dan ko zancen auran baya son ana yi masa bare kuma wata Khadija. Burinsa kawai yasan halin da Feenah ke ciki yasan ko'a'ina take bata cikin kwanciyar hankali kamar yadda shima yake cikin damuwar rashinta.

"Nifa abin nan ya daɗe yana bani mamaki, ace wai tsawon shekarun nan bamu taɓa sanin cewa Iman ba ƴar su Mamah bace." Sultan ya faɗa cikin jimami.

"Kai! Nifa tsabar yadda da cewar ƴar gidan ce ko? Gani nayi tana kama da Captain. Wallahi ban yadda ba sai da na tabbatar aure fa aka ɗaura mata da mutumin nawa." Ya ƙarasa maganar yana jifan Areef da filo.

Juyowa Areef yai ya shiga kallon abokan nasa yana kuma nazarin hirar da suke yi yana kuma kaɗa kai cike da tsabar kaduwa.

"Iman kuma?" Ya tambayi kansa,

"Itafa wacce ada muke mata kallon ƙanwarka, a yanzu kuma muke mata kallon matarka." Wani murmushin mamaki ya saki yana kuma kallon Sultan.

"Iman ɗin ce Khadijan da aka aura min?"

"Sosai ma kuwa ango." Aslam ya bashi amsa cike da tabbaci.

"Hauka da naɗe-naɗe, kuma su Abba suna cikin hankalinsu? Ƙanwata zasu aura min? Yarinyar da na goyata a bayana, nai mata tsifa da hannu na, ina tunanin wanka ne kawai banyi mata ba shine ta zama matata? Daman zan iya auran ƙanwata ne?"

Gabaki ɗaya suka zuba mishi idanuwa dan suma duk waɗannan maganganun da ya faɗa sune suke musu yawo a zuciya.

"Answer me please, wannan ai hauka ne." Ya faɗa a fusace kamar zai shiɗe.

"Karka ɗora mana laifi dalla muma so muke muji gaskiyar lamari. Ta iya yiyuwa kaine ba ɗansu ba, ko kuma itace ba ƴar su shi yasa sukai muku wannan haɗin." Cewar Aslam ganin yadda Areef keson ɗora musu laifi.

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun." Areef ya faɗa yana dafe kai, can kuma ya fashe da kuka yana cewa.

"Menene gaskiyar lamarin nan? Ni ko Iman waye ba asalin nasu ba? Sultan idan ya kasance ni ne ba ɗan suba ina asalina yake? Wallahi ban san kowa ba sai su. Su kadai na sani, na kuma

13 / 38