Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   8 / 38

21K to 24K   out of 113.7K words

tare da barin gurin ta koma wajan Mamah ta zauna.

"Ƙanwata zoki bani ruwan sha." Dr Jamil yai maganar yana nuna Iman.

"Iman abokin Yayan ku yana magana." Cewar Mamah da ita taga lokacin da ya nuna Iman ɗin.

A hankali taje ta zuba mishi ta mika masa, yaso haɗawa da hannunta amman be samu dama ba, yaji ta kalli Yayan na ta tana tambayarsa shima.

"Yaya Captain kai ma a zuba maka ruwan ne?" Yana shan romo ya girgiza kai alamar baya bukata, yaci gaba da yiwa Mamah magana.

"Da fatan dai harda ke aka yi wannan girke-girken?" Iman taji Dr Jamil ya faɗa, ta kallesa taga tabbas da ita yake, hakan yasa ta saki murmushi tana ɗaga masa kai alama eh da ita ne.

"Woww... ! Shi yasa naji daɗin abincin na musamman ne, ashe kanwar tamu ma gwana ce a fanin girke-girke." Ta kuma sakin murmushi wanda yake sake ƙawata fuskarta tana cewa.

"Muna dai koya ne, kuma nayi Home management a secondary school."

"Uhmmm! Kaji dalili, kice nan gaba kaɗan zaki koma ki shiga catering school?" Wannan karan girgiza masa kai tayi tare da cewa.

"A'a gaskiya, ina son nayi pharmacy. Shine dalilin da yasa na shiga science class."

Dr Jamil ya shiga jijiga kai yana kuma lumshe mata idanunsa masu kama da na mai jin bacci. Lura da yanayin yadda Iman ta fara sakewa da abokin Haneef ne yasa Mamah kiran sunanta bayan ta amsa tace.

"Zokije ɗaki ki ɗakko min jakar da naje aiki jiya."

Iman ta amsa tare da mikewa ta nufi inda aka aike ta. Mamah ta sake satar kallon Jamil taga shima yana satar kallon hanyar da Iman tabi, sai da ya dena ganinta sannan ya sauke idanunsa yaci gaba da cin abincin.

Nan da nan zuciyar Mamah ta shiga cikin wasiwasi tana jin wani tsoro da fargaba na tasowa daga can cikin ƙasan zuciyarta. Bata son wani abu ya shigo cikin rayuwar yaran, hakan yasa take taka tsan-tsan akan su, duk da tasan bata da tsumi ba ta da dabara, amman tana fatan Allah ya shiga lamarin ta da nasu kar azo ayi abinda rai zai so su.

Dawowar Iman shi ya katsewa Mamah tunanin da ta shiga. Karɓar jakar tayi Iman ta fara shirin komawa gurin Jamil dan itama ta fara jin daɗin hirar tasu, Mamah ta kuma cewa da ita.

"Iman kuzo ku koma ciki ku barsu suci abincin su a tsanake."

"Kyale su Mamah ai hira muke." Mamah taji Jamil ya faɗa cike da fara'a. Ta sake yago wani guntun murmushin tare da cewa.

"Akwai aikin da suka fara a cikin ɗaki, idan suka zauna shikenan ba zasu ƙarasa shi ba Jamil. Idan suka kammala yanzu kuwa anjima sai ku sha hirarku."

Shi dai kam Jamil beso hakan ba, so yayi a bar koda Iman ce a wannan lokacin har ya samu damar cusa mata kansa ta yarda ba zata dinga jin nauyi ko shakkarsa ba wajan hira. Amman babu yadda zai yi dole ya rabu da ita ya barwa kwanaki biyun da zai yi a gidan kafin ya wuce Nijer.

Tashi suka yi suma ba dan sun so ba suma, dan babu wani aikin da suke dashi, sanin halin Mamah da suka yi ne idan ba ta son ganin su a guri sai tace suna da aiki a cikin ɗaki. Suna tafiya itama ta mike tabi bayan su, aka bar Haneef da Jamil sai Areef a gefe yana cin cin-cin babu abinda ya dame shi dasu Haneef bare yaji hirar su.

Sai da suka kammala tsab sannan suka mike, Haneef yai musu jagoranci zuwa sashen shi dake cikin harabar gidan. Suka shiga komai a gyare tamkar dama can yana gidan, gashi babu abinda babu sai wanda ba'a rasa ba. Haneef ya shiga toilet yayi wanka tare da ɗauro alwala, ya fito Jamil ma ya shiga yayi, suka shirya tare da gabatar da sallah tare.

Suna kammalawa Haneef yace su kwanta su huta kafin zuwa anjima, shi dai Jamil ba wani so yake yi ba, amman rashin abin yi gashi besan kowa ba sai Haneef dan shi asalinsa ɗan garin Zamfara ne, ya biyo Haneef ne kasan cewar yana son zuwa Niger kafin ya wuce Zamfara.

Ba ƙaramin mamaki yake yi ba jin yadda a lokaci ɗaya Iman take yawo a cikin zuciyar shi, wanda ya tabbatar da cewa wani muhimman abu yana son shiga tsakaninsu. sosai yake jinta ta a jininsa tana yawo cikin ko wace jijiya da Allah ya dasa a jikinsa. Sai dai ita kuma fa? Tana jin yadda yake ji a yanzu ko kuwa shine aka fara gwadawa? Shi kam ya ganta ya kuma yaba da ita, zuciyar shi ta yarda ta zama mata ta biyu a gareshi koda kuwa ita ɗin bata son shi, bare ma yasan dole ta so shi duba da yadda yake da tarin masoya ƴan mata da zawarawa kala-kala..........👌


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BARI DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.







*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 11:20 - Buhainat: *ZO GARENI...*
Ƙarshen
Free page 10

NA
*HAJJA CE 👈*

Wattpad:- Hajjac

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A 2022*💡



Kasa yin bacci Jamil yayi shi kuwa Haneef tuni ya jima da yi saboda gajiyar dake jikinsa, kullum suna kan ruwa tsawon shekaru dole idan mutum ya samu irin wannan damar ya more ta kafin ta sake kufcewa. Yayin da Jamil ya kasance ma'aikacin lafiya dan babban likita ne da ake ji dashi a ƙasar nan, duk wani aikin kwakwalwa da zuciya yasan yadda zai yi maganin sai dai idan Allah daman ya riga ya kaddara mutum ba zai tashi ba.

Likita ne shi da duk wani asibiti mai ji da kansa suke nemo shi dan yazo ya magance matsalar da ta gagare su, wannan dalilin yasa ko asibitin kanshi be samu damar ginawa ba dan baya samun wani isashen lokacin kansa.

Yana da aure matar tana can garin su wato Zamfara state, yaransa biyu mace ɗaya namiji ɗaya daga nan ya takurawa matar sai da aka cire mata mahaifa saboda baya son tara yara bayan ya yi mata alkawarin ita kadai ce ba zai mata kishiya ba.

Trolley ɗinsa ya janyo ya buɗe tare da ciro laptop ɗinsa da ya sanya ta cikin tsakiyar kaya. Bayan ya kunna ya shiga yana ta danna danne tsawon lokaci.

Gajiya ya yi ya rufe laptop ɗin tare da mikewa ya maida kayansa da ya cire, ya dakko wayarsa ya fito zuwa harabar gidan yana ganin yadda tsarin yake.

Ba wani uban kuɗi aka zubawa wajan gina gidan ba, saboda ba wasu shahararrun masu kuɗi bane, sai dai suna da rufin asiri sosai ta yadda ba za'a gansu a raina su ba. Yana ta zagayawa ne ya hango ƴan matan sun fito ko wacce rike da jaka alamar fita zasu yi.

Cikin sauri ya ƙarasa inda suke yana murmushi har fararen haƙoransa suna fitowa.

"Ƴan mata ina zuwa haka?" Duk suka kalleshi cike da fara'a.

"Gidan kawu Sagir zamuje."

Ikram ta faɗa tana zuge jakar hannunta. Ya buɗe ido cikin son jin karin bayani tare da cewa.

"Waye hakan?"

"Yayan Abban mu ne."

Cewar Iman tana gyara daurin dankwalinta ta cikin madubin motar Mamah dake ajiye a gurin.

"Yayi kyau, gaisuwa zaku je kukai kenan?" Wannan karan ma Iman ce ta bashi amsa still tana duba fuskarta.

"Rihazal zamu." Jamil ya kuma buɗe ido yana kallonta ga shi zuciyar shi na ta harbawa da sauri da sauri.

"Meye kuma Rih...., Nama kasa maimaitawa." Duk suka kyalkyale da dariya.

Iman ta dago ta kafe shi da ido tare da ɗora jakarta saman motar ta fara yi masa bayani kamar mai karatun jarida.

"Kawu Sagir ne zai aurar da ƴarsa, Toh shine aka shirya irin rawa da wakar da za'a yi a gurin events ɗin, mune ƴan rawar shine za'a koya mana yadda zamu yi cikin tsari yadda zamu burge ƴan biki da amarya da ango."

Yadda take bayani da yadda tayi masa masifar kyau duk da cewa ba wani makeup tayi ba, farin lipstick ne tasa irin mai danƙon nan sai kwalli da ta zizara a cikin idanunta shikenan nan, amman karku so kuga yadda tayi kyau. Ya kuma kallonta yana kanne ido ɗaya yace.

"Ku yanzu dai duk ƴan zuwa rawar ne ko?"

"A'a banda Hanan ita bata iya ba bama tayin rawa." Cewar Ikram.

"Kune ƴan mazari kenan?" Ya tambaye su cikin dariya ƙasa ƙasa.

Duk suka saki dariya suma, yadda suke yi kai kace sun daɗe da saninsa. Jakar Iman ya ɗauka wacce ke saman mota ya buɗe yana ganin kayan ciki, ita kuma ta rufe ido cike da kunya dan babu komai a ciki sai lipstick da wasu alawoyi guda biyu a ciki.

Ɗagowa yayi ya kalleta ganin ta rufe ido su kuma Hanan da Ikram suna ta dariya yasa shi dariyar shima tare da cewa.

"Ashe ba kuɗi a ciki? Haba madam ai ba girmanki bane, jaka mai kyau amman babu ko sisi a cikin ta?."

Duk suka kuma yin wata dariya har da ita kanta Iman ɗin dan dole abin ya baka dariya duba da yadda tai kyau ɗin da gaske.

"Tawa kawai ka gani Yaya Jamil, amman wallahi suma kayan kwalliya ne a ciki." Hannan tai saurin cewa.

"Karya ne ina da kuɗi a ciki."

"Kawo a gani idan ba tsoro ba."

Iman ta faɗa tana ƙoƙarin fizgar jakar hannun Hanan amman taki sakar mata sai dariya suke ɓaɓɓakawa. Jamil ya zira hannunsa cikin aljihun wandonsa ya zaro kuɗi ƴan ɗari biyu-biyu da yawa ko kirgawa beyi ba ya sakawa Iman a cikin jakarta ya zuge tare da mika mata yana cewa.

"Gashi nan sai ayi harda liki idan anje."

Duk suka ware ido ganin yawan kuɗin kuma sabbabi dal dasu, cike da shakka Iman tace.

"A'a gaskiya ka karbi abin ka mun gode."

"Ai ba rokata kukai ba ni naga damar baku." Ikram tace,

"Mamah zata yi mana faɗa wallahi."

"Ba zatai ba zan gaya mata." Ya faɗa cikin nuna musu ba damuwa.

Godiya suka yi masa daga nan suka wuce shi kuma yabi bayan su da kallo har suka bar gidan. Wani nannauyan numfashi ya sauke tare da jan dogon hancinsa yana wani irin shu'umin murmushi.

Bayan sun bar gidan ya ciro wayarsa tare da kiran lambar Nigar, bugu ɗaya aka ɗaga Jamil ya koma daga can gefe ya zauna, bayani yake yiwa dattijon tare da tabbatar masa da zuwansa, daga nan ya katse kiran yaci gaba da danne-dannensa.

Yana zaune a gurin yaga Areef ya fito daga ciki da sauri har baya ganin gabansa, yana shirin fita Jamil ya kira sunansa.

"Areef.."

"Na'am." Ya amsa a gigice yana ɗan kallon kofar gate.

"Ina zuwa da sauri haka?" Areef ya yatsina fuska, cikin ransa yana cewa 'ko ina ruwansa?' tare da cewa.

"Filin ƙwallo." Ya faɗa a gajarce.

"Lahhhh tsakanin suwa ye za'a take wasan yau?"

"Madrid da Barcelona." Ya bashi amsa a gajarce,

"Bari muje tare na kalla duk da ni ba wani son kwallo nake ba."

Ya kuma saurin kallon gate ɗin saboda tsabar tsoran da yake ciki har sautin tafiyar takalmin mata yake ji a cikin kunnansa. Feenah ce duk ta ruɗashi yanzu da ta kirashi tace yazo tana kofar gidan su a tsaye idan ba zai iya fitowa ba kuma sai ta shigo. Areef yasan ba ƙaramin aikinta bane gashi Mamah tana gida baya son Feenah ta janyo masa matsala a cikin gidan su.

"Bari ina zuwa." Cewar Areef yana fita da gudu.

Cikin ɗaga kafaɗa Dr Jamil ya koma ya zauna daman ba wani damuwa ya yi da son zuwan ba, yama fi son yana zaune yaga dawowar su Iman.

Daga can gefen gidan wajan wata bishiya Areef ya hango Feenah tsaye tana jiran fitowarsa, tana tsaye sanye cikin doguwar riga purple ta yane kanta da mayafin rigar, sai jaka fara suwaga da wani aranan trainers dake sanye a ƙafarta mai masifar kyau.

Ba kaɗan ba tayi kyau tana ganinsa ta fara sakin murmushi kamar wacce aka yiwa albishir da gidan aljanna. Duk da cikin fushi ya fito akan zai yi mata faɗa ta dena zuwa ƙofar gidan su, sai dai yana sata a cikin idanunsa yaji sam ba zai iya ba.

"Baby na." Cewar Feenah cikin farin cikin ganinsa.

"Baby daga ina kike?" Ta tambayeta yana juyawa ya kalli gidan su.

"Gidan su zee zanje na karbo anko, kasan fa bikin ta za'a yi."

"Yayi kyau." Ya faɗa.

"Ba zaka yi min rakiya ba?" Tamkar jira yake yi ta bashi umarni daman so yake su bar wajan, da sauri yace.

"Muje to."

Suka jera suna tafiya daɗi duk ya cika zuciyar Feenah tana jin tamkar ta bashi kyakkyawar runguma, sai dai idanun mutane ya yi yawa tasan idan ta aikata haka Areef ba zai ji daɗi ba. Sai da ya kai ta har ƙofar gidan ta shiga shi kuka sannan ya juya ya koma gida.

Gidan su Aslam ya wuce kai tsaye ya shiga ciki suka gaisa da Umma ya tambayi ina Aslam ta sanar dashi yabi Baban shi kasuwa, haka ya fito ya nufi gidan su Shuraim ya yi sa'a yana nan suka ɗan taɓa hira tsawon lokaci sannan ya koma gida, yasan lokacin duk jarabar Jamil ba zai ce suje kallon bal ɗin ba.

Koda su Iman suka dawo daga gidan Kawu Sagir basu ga Jamil ba, suka shiga ciki nan suka tarar dasu a parlor Captain Haneef da Jamil ɗin suna zaune a kujera mai cin mutum biyu, yayin da Mamah ke zaune a ƙasa kan kafet suna ta hira.

"Ya Haneef kasha bacci har muka fita baka farka ba." Ikram ta faɗa suna ƙarasawa kan kujera mai cin mutum uku.

"Na kwaso gajiya ne Iki, hakan ma tashi kawai nayi saboda anyi magariba."

Duk suka jinjina kai a lokacin ne Iman ta zaro kuɗin da Dr Jamil ya basu. Mamah ba ta karɓi kuɗin ba sai Jamil da ta kalla cike da mamaki take cewa masa.

"Wannan kuɗin fa Jamil?" Yayi ƴar dariya.

"Mamah ƙannena na bawa su saka a jaka."

"Haba ai sun yi yawa Jamil, ya zasu yi da wannan uban kuɗin?"

"Mamah ki bar musu, kyauta ce fa tsakanin Yaya da ƙannansa. Yanzu idan Sa'eed ya yi musu kyauta sai ki ƙi karɓar musu?" Cikin sanyin murya Mamah tace.

"Amman ai kuɗin sunyi yawa, ya zasu yi dasu Jamil?"

"Babu yawa Mamah ni baki san abinda Sa'eed (Haneef) yake min ba da sai kince lallai duk abinda nayi musu ban fadi ba."

Ganin zasu tsaya yin jayayya yasa Mamah yin shiru bata sake yi masa gardama ba sai godiya da tayi masa. Aka ci gaba da hira shi dai Jamil duk idanunsa yana gun motsin Iman, sannan duk maganar da zai yi sai ya sako ta a ciki, rana ɗaya har an saba dashi ya shiga zuciyoyinsu gabaki ɗaya gidan idan ka cire Areef.

_WASHE GARI_

Bayan sun gama duk ayyuka da ya zame musu wajibi suka yi karin kumallo daga nan sai hira Mamah daman tuni ta tafi gurin aiki kasancewarta mataimakiyar shugaba a wata makaranta. Dr Jamil ne ya shigo falon ya taki sa'a ƴan matan suna zaune su kadai, ya saki ajiyar zuciya lokacin da idanunsa suka hango mishi kyakkyawar fuskar mutuniyar tashi.

Ya ƙarasa ciki tare da samun guri ya zauna fuskarshi kunshe da fara'a. Ɗaya bayan ɗaya suka dinga gaishe dashi yana amsawa.

"Hira kuke yi?" Iman tace.

"Eh Yaya Jamil."

"Allah yasa za'a yi dani?" Suka kalleshi suna dariya.

"Mai zai hana in kana so." Ikram ta bashi amsa.

"Toh ina so."

Ya basu dariya da yanayin yadda yai maganar, sai dai kuma sun kasa ci gaba da yi kowacce kamar an daure mata baki.

"Ya naji kuma kunyi shiru? Ko kun fasa yi dani ɗin?" Idanunsa kyar akan Iman dake yanke farce.

"Babu abin yin hirar, wani ya bamu labari."

"A'a Toh ke zaki bamu tunda ke kika fara cewa babu abin hira." Ya faɗa yana sake gyara zama, so yake taita magana idan tana yi jikinsa har wani sanyi-sanyi yake saboda shauki.

"Anjima ku shirya muje yawo." Cewar Dr Jamil yana bin su da ido.

Su kuma duk suka buɗe idanu ko wacce riƙe da haɓa, ya gano cewa ba zasu ba suna tsoran Mamah zata hana su.

"Ya naga duk kun zare min ido lafiya?"

"Yaya Jamil karma ka fara dan babu wanda zai barmu fita yawo." Yana matuƙar jin daɗi yaga ya yi magana Iman ta bashi amsa hakan ba ƙaramin faranta masa rai yake ba.

Shigowar Haneef tasa duk suka kalli ƙofar, tun kafin ya shigo ciki suka fara gaishe dashi harya samu guri shima ya zauna yana kallon ƴan ƙannen nashi.

"Ashe nan ka taho? Ina ta faman dubaka nace karfa ko kafita ina tsoran kaje ka ɓata."

Su Iman suka tuntsure da dariya, suma su Haneef ɗin suka biye musu.

"Haba Captain me ka mai da ni?"

"A'a ni bance komai ba, kar dai kaje ka ɓata nace."

"Kasan dai bazan ɓata a cikin garin Kano ba, ina zuwa fiye da yadda kake zuwa Alhaji." Jamil ya faɗa yana hararar abokin nashi.

"Naji kana zuwa, Amman ai

8 / 38