: *ZO GARE NI....*
*NA HAJJA CE*👈
Free page *1*
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💡
*mg's skincare*
Shin Ina matan suke🗣️🗣️🗣️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi😃🤩
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum👌hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy 🤗ga amare duk wnd yy using set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali😘just start placing ur orders dearies DNT be left behind
Available product👇
Herbal whitening black soap:3k
Beauty kit:11k
Blacksoap/molato whitening soap: 3500
Bridal kit:20k
Muna maraba da masu siyan daya ko sari
Chat
08062991549
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go🤩
Then @mgs skincare gat you covered 💯
Now is time to glow😍
Pamper ur skin🦵
Shine like bride👰🏻♀
Glow🧖♀?
💯 tested nd trusted🤝
Guarantee
Sannan munada frames masu kyau shima siyan daya ko sari 07046881166
08062991549
Sannan gamai bukatan abinci, cakes,meatpie,samosa nd spring rolls, traditional juices nabiki shima yy hanzari yy mgn 08062991549
Mungode🤝
_________________________
GGSS GABORI....
Sanye ɗaliban suke cikin kayan makaranta wando da riga dark green da farin ɗankwali da hijabi. Fitowarsu kenan daga zana jarabawar karshe ta fita daga matakin sakandire wato neco. Mafi yawancinsu basu da jiki masu ƙiba da ɗan kumarin kaɗan ne, Iman tana ɗaya daga cikin mararsa ƙiba kuma mararsa kumari don ko bra be cancanci ta sanya ba saboda kankantar halittun kirjinta. Amman sabida kar a raina ta a cikin kawaye ace har akai candy bata sawa ya sa take saka abarta.
Amina ta kalla tana dariya tare da bubbuga tast book d'in dake hannunta a cinya tana cewa.
“Amcy kune fa ƴan candy marriage, dan Allah idan za'a yi bikin ki, karki manta dani ki kawo min.?
Kasan cewar Amina tana da jiki shi yasa duk Sanda irin wannan shakiyancin na kawaye idan ya tashi sai suyi ta mata dariya ita da sauran masu ƙiba da kumari a cikin su. Kan Iman tayi zata finciko ta amman Iman tayi saurin zillewa tana dariya ba kakkautawa, tana tafiya da baya-baya cikin dariyar mugunta tace.
“Mu wallahi sai munga karshen biro da takarda sannan zamu yi aure.?
Habiba da take sahun su Amina ta harari Iman tana taɓe baki tace.
“Sai kinje garin kuri mutuwa tazo tayi awan gaba dake kiyi babun baɗilahu. Kuma yarinya wallahi bazan miki kara ba wajan saka sunanki a ƴata ta fari.?
“Ahhh kaji mugun fata, Toh bakin ki ya tsari kashin safe mai tiriri na malam Mansoor.?
Gabaki ɗayan su kusan su goma shaaa suka tuntsure da dariya banda Habiba wacce aka yiwa fatan. Kwafa kawai tayi suna ci gaba da tafiya, itama Iman ta dawo jerinsu sukaci gaba da hira tare da tattauna yadda zasu ci gaba da zumunci ko bayan sun fita daga makarantar.
Gaban staff room suka ƙarasa inda sauran ƴan mate ɗin nasu suke za'a yi musu assembly na karshe. Suna tsaitsaye malamai suka fito sannan vice princeple da senior master kafin daga karshe shugabar makarantar (princeple) itama ta fito, malam Garba ya buɗe taro da addu'a aka shafa sannan shugaba ta fara yi musu nasiha.
Wasu na sauraro yayin da wasu ke hirarsu ƙasa-ƙasa har ta kammala sannan tayi musu fatan nasara bayan barin su wannan matakin. Sauran students suna ta leƙawa ta windows wasu na zagin waɗanda suka yi dispelling ɗin su, yayin da wasu kuma ana yi musu addu'a da samun nasara a rayuwar su ta gaba. Iman tana dayae daga cikin prepet ɗin da ake so, saboda mutum ce ita mai faramfaran da mutane, bata duka bata zagi sai dai kawai tayi hargagi amman bata da mugunta ko kaɗan. Hakan ne yasa wasu yaran har kuka suka yi saboda tafiyar da zata yi ta barsu.
Ana buɗe gate motoci da babura da masu napep suka dinga shigowa cikin makarantar, candidates aka fara murna da ihu ana wake-wake.
Iman tana ɗaya daga cikin masu wake-wake domin mutum ce mai matuƙar san nishaɗi. idanunta akan motocin da suke shigowa, burinta da fatan ta shine taga ta mahaifinta, dan tun ana sauran kwanaki biyar tayi waya gida tace tana son Abban su yazo da kanshi ya ɗauketa dan ya nuna mata jin daɗin shi na kammala karatunta. Idanuwa ta shiga gogewa lokacin da ta hango motar da aka zo daukar ta da ita, nan da nan annurin fuskarta ya goshe, ta kalli ƙawayenta da suka ce zasu bita idan anzo ɗaukarta kasan cewar garin su ɗaya.
Wurin da akai perking d'in motar ta nufa, hango mayafin da tayi a perssinger seat shine ya kwantar mata da hankali ta san ba zataji kunya a gurin kawayenta ba na disgin da zai yi mata idan tace za'a tafi da su. Cike da ɗokin son ganin Maman su tayi knocking d'in glass, aka zuge a hankali, Iman na shirin buɗe ƙofar kawai taga ashe ba Maman su ba ce, wata budurwa ce wacce ba ta taɓa ganin koda me kama da ita ba sai yanzu.
Kallon yayan nata tayi tana son jin ƙarin bayani daga bakinsa amman yaki koda kallonta bare ta saka ran zai kula ta. Taja tsaki ciki-ciki dan ta tsani wannan halin na Yaya Areef na rashin sakarwa ƙannansa da yayunsa fuska sai wasu banzaye mararsa aji da yake sakarwa fuska irin wannan da yake tare da ita. Harara ta dinga zabga masa saboda takaici, sai ji tayi yana cewa.
“Idan kin gama hararar tawa sai ki zo ki rufe ni da duka idan yaso sai ki taho mu tafi marar kunya.?
Baki ta murguɗa dan tasan munafukin ido gare shi, sai ya yi kamar ba kai yake kallo ba saboda Iya ɗauke kai. Ta juya tare da komawa gurin su Ummi suka kwaso kayan suka kai cikin booth sannan Iman ta koma ɓangaren da Areef yake ta zumburu bata.
“Kazo muje kayi min sign out.?
“Babu inda zan fita yarinya, idan zaki shigo mu tafi ki shigo ba za ai sign out d'in ba.?
Yayi maganar cikin gadara, daman tasan indai shi za'a turo ya ɗauketa toh sai ta sha wulakanci saboda basa shiri ko kaɗan, Mutane sukan ce ai dan dai sakon ta ne duk da cewa ya bata shekaru.
Hawayen bakin ciki ne ya kama Iman tayi saurin matsayawa daga gurin tun kafin kwallar ta zubo ya kuma yi mata rashin mutunci. Can nesa ta samu guri tsugunna tana ta kuka mai ɗaukar hankali, Mutane suna ta tambayarta menene yasa ta kuka tayi shiru, wani mutum da a kalla zai yi shekaru hamsin yana tsaye yaransa suna saka kayan su cikin booth, ya ƙarasa kusa da ita yana magana.
“Wacece take kuka haka?? Mutumin ya tambaya yana jiran jin amsa.
Hawaye shaɓe-shaɓe a saman fuskarta ta d'oga tana kallansa da idanunta wad'anda suka rune zuwa ja. Ganin bata san mutumin ba yasa ta ɗan fara ja da baya kamar yace zai yi mata wani abun mugunta. Dattijon ya girgiza kai ganinta a tsora ce, ya fara kale-kalle har Allah yasa ya hango wani malami, cikin azama ya ƙarasa gurin shi yana yi masa nuni da Iman wacce ganin ya bar gurin yasa taci gaba da kukan ta.
“Ke kuma kukan me kike yi?? Cewar malamin yana daga tsaye.
Iman ta d'ago kai jin muryar malam Mansoor, shima ganin itace yasa shi mamaki tare da kuma yin magana.
“Khadijatul Iman, ya aka yi kike kuka haka??
Bayan hannu tasa tana goge kwallar dake ta faman zobawa, tare da mikewa tsaye tana kallon motar Yaya Areef tace.
“Na ce bana son a turo Yaya Areef zuwa d'auka ta, gashi nan an turo shi yazo yana ta min wulakanci.?
“Subahanallahi yana ina shi Yayan naki??
“Gashi can a cikin mota.?
“Zo muje nayi masa magana, yau ai ba narar kuka bace a gurin ki Iman. Kiyi hakuri kinji??
Bata kula shi ba dan tasan besan rashin mutuncin Yaya Areef ba shi yasa har yake zaton ko abin da ya yi mata ɗan hakuri ne a wannan ranar a kuma wannan lokacin. Koda suka ƙarasa can nesa ta tsaya, shi kuma malam Mansoor ya ƙarasa gurin motar yana yiwa Areef knocking a jikin glass. Tamkar ba zai sauke glass d'in ba saboda baya son yaji ana bugar masa glass d'in saitin shi. Malam Mansoor har zai juya yama ɗauka ko babu kowa a cikin motar saboda tinted ne, sai kuma yaji an zuge ya waigo. Yaro ne da ba zai wuce shekaru 21 ba, amman yanayin sa da yadda shigar jikinsa ta razana shi sai ya yi tunanin sa'an shi ne.
Sallama ya yi masa Areef ya amsa ciki-ciki dan shi be san shi ba. Malam Mansoor ya kuma matsawa gurin yana cewa.
“Naga Iman ne a can tana kuka, shine aka tambaye ta tace wulakanta ta kake yi. Dan Allah kayi hakuri kasan yaran nan sai an bisu da salama, ka barta tazo ku tafi yau ranar farin ciki ce a gurin su.?
Tunda Areef yaji surutun ya fara yawa ya dakko waya yana dannawa, har malam Mansoor ya kammala be ce komai ba bare yasa ran amsa. Lekawa Areef ya yi ya ga Iman sai faman kifta idanuwa take yi, ta kuma ƙi bari su haɗa ido da shi.
“Ta zo ku tafi ko?? Malam Mansoor ya kuma yin magana yana leken ta gefen Areef d'in.
“Rabu da ita, idan ta gama kukan tazo mu tafi.?
“Haba kai kuwa bawan Allah, ta ya za....?
Ƙin bari ya yi ya ƙarasa maganar kawai ya zuge glass d'in sa yana jan ɗan siririn tsaki. Haushi ya kama malam Mansoor ganin yaro kankani ya wulakanta shi, sai yaji tamkar ya huce akan Iman d'in amman ba zai Iya ba saboda yarinyar akwai tarin ilimi fiye da tunanin mai tunani. Gurin ta ya koma ya bata hakuri yace ta sake zuwa ta yi masa magana idan yaki sai tazo ya bata waya ta kira Abban su.
Ta fara takowa a hankali ga kawayenta da zasu tafi tare sai magana suke mata akan ya ake ciki ta rasa me zata gaya musu. Shi kuma ganin ta karaso yasa shi sauke glass ɗin tare da baza mata kunne yana jiran abin da zata faɗa. Cikin raunanniyar murya tana faman sosa ido tace masa.
“Kazo kayi mana signing ɗin.? A mamakance yace mata.
“Har ke dawa??
“Kawaye na da zamu tafi dasu.? Yaja dogon tsaki tare da buɗe murfin ya fito yana cewa.
“Ke kadai zan yiwa wallahi kinji ma na rantse babu shegiyar da zan yiwa.? Cikin damuwa dan karya ba ta kunya tace.
“Dan Allah dan annabi Yaya Areef kayi musu kawaye na ne fa, tare kuma zamu tafi dasu.? Ya juyo tare da wulla mata harara.
“Ce miki akai ni driver ne da zan ɗauki tarkacen ƙawayenki? Ke kadai aka ce nazo na ɗauka, idan ba zaki taho ba kuma ki zauna sai nayi tafiya ta ina da aikin yi.?
Shiru tayi har suka ƙarasa wajan da ake signing mata sai kallon Areef suke yi wasu ma har zuwa suke wajan Iman suna tambayar ta dan Allah shine Yaya Areef d'in da take basu labari, duk da cewar idan ta tashi labarin bata taba nuna musu yananin tsarin halittarsa ba, sai dai tace musu bashi da mutunci. Ganin sun ishe ta da tambaya ga ɓacin ran da ya gama sanya ta yasa ta ce musu bashi bane ba, wannan driver d'in gidan su ne.
“Yanzu wannan kyakkyawan saurayin duk da ma dai yaro ne, shine driven ku Iman??
“Zan muku karya ne?? Iman ta tambaye su cikin gatse.
“A'a mun isa mu karya ta ki, keda kuke tare dashi. Amman fa ya haɗu ba karya wallahi.? Cewar daga cikin kawayen na ta.
Da yake kunnuwansa irin mai saurin ɗaukar magana ne, duk da yana gurin cike-ciken takardu yana jin duk hirar da suke yi. Ya kammala nata sai gata da sauran kawayen ta da zasu tafi tare tana cewa sauran su, ya yi mata banza tare da yace komai ba ya wucewa mota. Ragowar kuɗin ta dubu biyu ta ciro ta mika musu tare da basu hakuri tace su shiga mota su taho shi yace zai biya ta wani gurin ne Abba ya aike shi. Duk da basu ji daɗi ba amman babu yadda zasu yi dole suka je suka cire jakunkunan su daga cikin booth ɗin motar suka yi sallama ta shiga baya ta zauna.
Har suka bar cikin makarantar suka hau titi babu wanda ya yi magana, sai wadda suke tare da Areef ɗin ce ta katse shirun ta hanyar cewa.
“Baby wai yarinyar nan bata iya gaisuwa ba ne?? Jin ta kira ta da yarinya bayan kuma daga ganinta kasan da kadan ta girme ta, yasa Iman tayi saurin cewa.
“Ke wacce yarinyar?? Cikin gadara tace.
“Gashi nan da yake kin san dake nake ai gashi kin kula maganar da nayi
“Mtwww bariki babu sauki, Allah ya kiyaye.? Iman ta faɗa tana maida kanta wajan glass dan hangen abubuwan da suke wucewa.
“Kambala'i baby kaji abin da take gaya min?? Yarinyar ta faɗa tana kallon Areef da yake jin duk wasu maganganu da suke yi.
Gangarawa ya yi ganin ya yi parking ya buɗe ƙofar shi ya fito, yasa Iman matsawa can ɗaya side d'in, yana buɗe ƙofar ita kuma ta fice ta ɗayan kofar ta matsa can yadda ba zai Iya kamata ba sai murguda baki take yi tana cewa.
“Wallahi akan wannan banzar yarinyar ba zan tsaya kasa hannunka a jikina ba. Ka ɗauke ta kuje can ku ƙarata da iskancin ku ba zan shiga motar ba ashe...!?
Jin kalaman da suke fitowa daga bakin ta tana danganta shi da mazinaci yasa ransa kuma shiga ƙololuwar bacin. Tsuke fuska ya yi Iman ta taɓe baki ba zata yadda ta koma cikin motar can ba koda zai kashe ta ne, ballantana tana ji tana gani cikin hankali da nutsuwarta. Yaje can yaji da ƴar iskar da ya ɗakko, kuma sai ta faɗa a gida tunda har karuwai yake yawo dasu. Ganin ba ta da alamar tahowa yasa shi zuwa wajan glass d'in yarinyar yana mata magana kamar zai yi kuka.
“Sweetie! kiyi hakuri kizo na samar miki mota ki shiga. Wannan yarinyar matsala zata bani a rayuwar mu, kiyi hakuri idan na kai ta zan zo geast house d'in na same ki, please do this to me please.?
Ji tayi kamar ta fashe saboda baƙin ciki, lallai sai tayi maganin wannan ƙanwar tasa tun da har taja sanadin ta zasu raba tafiya da shi. Cikin bacin rai da huci ta bude ta fito tare da yin gaba fuuu bata jira cewar sa ba. Ya zai yi? Dole yabi bayanta kamar wata uwarsa ya tarar mata bus ta shiga ya zaro kudi ya bawa kwandastan, be tafi ba har sai da yaga motar ta kulewa ganinsa sannan ya sauke wani dogon numfashi. Kallon Iman ya yi rai a bace yace tazo ta shiga, ya zauna cikin motar yana jiranta tana tahowa a hankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.......✍️
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
2/4/22, 11:15 - Buhainat: *ZO GARE NI...*
Free page *2*
*HAJJA CE*👈
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💡
Baya ta nufa zata shiga ya dakatar da ita ta hanyar nuna mata seat d'in gaba. Doster d'in motar ta janyo tare da goge kujerar duk yana kallonta beyi magana ba. Ta shiga ta zauna tare da rufewa, tun kafin ya tada motar ta fashe da kuka tana rike ciki tare da wulkitawa gefe tana shure-shure.
“Wayyo Allah ciki na wayyo na shiga uku zan mutu.?
“Wallahi idan baki min shiru ba zan lallasaki a cikin motar nan yar rainin hankali.? Ya fada tare da yiwa motar key yaja a fusace.
“Abba zan mutu ciki na Abba wayyo Allah na.?
Abin nata ya fara damunsa, ya mika hannu ya dafo kafadarta yana magana cike da shakka.
“Iman are you serious ciwon ciki kike?.?
“Ya Areef mutuwa zan yi na shiga uku, ko dai waccen yarinyar mayya ce baka sani ba??
“Dalla yiwa