Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   30 / 38

87K to 90K   out of 113.7K words

gwada BP da drip ya dawo, yana zuwa ya kalli fuskarta tana yi masa wani irin murmushi wanda yasa kirjin Jamil bugawa, nan take yaga ta langaɓe a jikin Salima alamar rai yayi halinsa. Salima ta kurma wani gigitaccen ihu tana rungume Umma, a ruɗe take jijjigata tana cewa.

"Umma dan Allah karki mutu... Karki mutu Umma na shiga uku wayyo Allah na." Ganin yadda Salima take kuka tamkar uwarta ce ta faɗi ta mutu, shine yasa jikin Jamil yin sanyi. Tun farko da ita ya bayar amman ya cewa boka su dauki rayuwar mahaifiyarsa, saboda itace ta kwana biyu a duniya.

"Sakarta Salima wannan kukan yayi yawa." Ya faɗa yana ta janye Salimar daga jikin gawar.

"Umma karka ce min itama Umma ta mutu? Na shiga uku duniya ina zata kaini ni Salima? Ita nake gani naji daɗi Jamil, itace ke share min duk wani kuka idan kayi nesa dani. Yanzu ya zanyi?" Ta sulale a jikinsa tana riƙe kirjinta sakamakon wani zugi da taji yanayi.

"Kwanan Umma ya kare Salima, sai hakuri."

"Dama nima na mutu." Yaji ta faɗa tana sake fashewa da kuka.

"A'a ba yanzu ba, akwai lokaci Salima, sai mun tsofa tare dake sannan idan mutuwarce sai tazo. Bari na kira mutane."

Ya tashi yabar Salima a gurin gawar Umma wacce idan kana kallonta sai kayi zatan bacci take yi yadda fuskarta take shar gashi tamkar tana murmushi. Haka mutane suka cika gidan lokaci guda, Allah sarki mutuniyar kirki, mace mai ibada, kyauta da zumunci, bakajin maganar komai sai na kirkinta da karamci gurin kowane mutum dake zaune a gidan. Sauran ƴan uwa duk an yi musu waya na nesa dana kusa, mata da maza, wasu sun zo ƴan nesa kuma sun taho.

Jamil kam babu kunya bare tsoran Allah dashi aka ɗakko gawar Umma cikin makara, da hannunsa ya taya aka ɗauketa zuwa ƙofar gida, dashi akai mata sallah mutane sai gaisuwa suke yi masa yana amsa musu tamkar shima yana cikin damuwa. Bayan an dawo daga kaita ya zauna aka ci gaba da karɓar gaisuwa dashi. Duk Wani abu da ake buƙata a gidan shi ake sanarwa ya bada kuɗi a siyo. Yan uwansa maza da mata su sha kuka, dama mahaifinsu ya jima da rasuwa, sun zama marayu, inda Allah ya taimaka ma duk sun mallaki hankali babu wani da za'a ce shine abin tausayi.

Har aka yi bakwai Jamil baya zuwa ko'ina yana zaune dan karɓar gaisuwa. Bayan an watse ne ya zama sai ƴan gida ya fara tunanin tafiya Niger, yace musu zaije yin wani aiki mai matuƙar muhimmanci. A daren ranar daya gama komai na kwanciya ya kwanta har ya fara bacci, Salima ta fito daga bandaki kawai taga ya zabura yana ja da baya. Mamaki ya kamata cikin jin haushin ganin yadda yake tsoranta tace.

"Menene haka?" Jamil ya shiga girgiza kai yana dakatar da ita da hannu.

"Dan Allah Umma karki kasheni."

"Umma kuma?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Meenal.. Meenal.. Umma please karku taɓani, banaso.. Ku dena bana so."

"Wai menene haka Jamil? Babu kowa a ɗakin nan daga ni sai kai. Kayi addu'a mafarki kakeyi." Jikinsa ya taɓa yaji shi sharkaf da gumi tamkar wanda ya fito daga wanka.

"Ka ganka kuwa Jamil? Duk ka wani firgice a cikin kankanin lokaci. Me yake faruwa? Meke damunka please tell me."

"Dole na gigice Salima, duk wannan tashin hankalin da nake fuskanta Iman taki ta ZO GARENI. Na rasa abubuwa masu matuƙar muhimmanci duk saboda ta ZO GARENI amman abu ya faskara. Salima Umma da Meenal suna miki min wani ice mai ɗauke da rurin wuta a jikinsa, suna kuka suna sake kusantoni me yasa.?" Ya faɗa yana dagowa ya kalleta. Tun sanda taji ya ambaci Iman taji zuciyarta na zafi, suna haɗa ido ta zabga masa harara tana cewa.

"Wacece Iman? Menene a tsakaninku da har ka rasa abubuwa masu muhimmanci a gareka?" Sai da ta faɗa ya gano irin katoɓarar da yake son shiryawa kansa, ya gyara zama tare da janyo mata hannu ta zauna a kusa dashi.

"Baki san Iman ba Salima? Iman fa? Aikuwa yana cikin shika-shikan musulunci, nasan kuma kin san su sai dai kice kin shaafa."

Yanaji ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, ya janyota zuwa jikinsa yana kissing duk da cewa zuciyar shi ba a gurinta take ba. Yana yi ne kawai dan kar tace baya damuwa da ita. Sai da suka gama ya goma gefe yana jan wani irin ɓacin rai, Salima kuwa bacci ta juya tana yi ta barshi yana ta fama tsaki. Jamil ya kasa rintsawa sakamakon daya rufe ido na ɗan lokaci zai dinga ganin Umma da Meenal, gashi duk da wannan abu da yakeji hakan besan yaji zai hakura da zuwa gurin bokan nashi ba. Washe gari kuwa tun da farar Safiya yayi musu sallama ya bar gidan.
__________________

Iman ba ƙaramin daɗi takeji ba a garin, komai nasu burgeta yake yi, sai nan nan suke yi da ita tamkar wata kwai. Maman ta da yake cikakkiyar bafulatana ce, bata iya yin doguwar hira da ita, sosai take jin kunyarta. Kwananta uku da zuwa kauyen ta warke daga azabar da Areef ya jefata ciki. Ranar da ta cika sati ne mahaifinta yazo kauyen cikin convoy na latsa-latsan motoci. Bata taɓa zato ko tsammanin zata ga haka ba, hasalima babu wanda yace mata mahaifinta wani ne a cikin fadin Nijeriya.

Kusan motoci guda ɗari da wani abun ne sukayo masa rakiya tun daga cikin kwaryar Kano har zuwa cikin kauyen. Sen. (Dr) Muhammad Abubakar GCON (the senate president and chairman National assembly) shine mahaifin Khadijatul Iman. Cikin kwarewa da kuma sanin makamar aiki securities suka bashi kariya tun daga fitowarsa daga mota har zuwa cikin gidan malam khamis.

"Where's my daughter? Show me the love of my life please."

Ya faɗa yana ware hannayensa biyu, abinka da ɗan boko wayayye wanda yasan fari da baki na yadda za'a nuna soyayya ga ɗan Adam. Babu wanda yake famintar abinda yake cewa, saboda salon turancin ma ba kowane zai gane ba sai wanda ya yi zaman aji na musamman. Tunda ya shigo yana maganar idanun Iman suna kanshi, ta tabbatar da shine mahaifinta musamman da taji abinda yake cewa, dan haka tun kafin a bata umarnin zuwa ta tashi da gudu ta shige cikin jikinsa, be tsaya wani dubawa dan yaga wacece ba shima ya maida hannayensa ya rungumeta tsam a jikinsa.

"Masha Allah, alhamdulillahi ala kullu halin." Abinda Sen. Muhammad ya faɗa kenan bayan ya ɗora habarsa saman kan Iman. Sauran mutanen kauyen suna ta mamakin yadda suka gane juna tunda ba bayani akai musu ba.

"Ku shigo daga cikin ɗaki ranka ya daɗe." Cewar Baba sunusi yana ɗaga labule.

"Ina Habiba?" Sen. Muhammad ya tambaya yana kallon mutanan gurin.

"Gata nan tana kuka." Wata mata daga ƙofar ɗaki ta faɗa.

A hankali Sen. Muhammad ya dago da Iman daga jikinsa, suka kalli juna. Kallonta yai yana mamakin yadda ya ganta very need, sam beyi tsammanin ganinta so cute ba, sai gashi ya ganta fiye da yadda baya tsammani. Da alama ta shiga hannu nagartacce. Yaja hannunta suka shiga cikin ɗakin da mahaifiyar Iman ke ciki, securities suka tokare ƙofar wanda yake ciki ya tsira wanda yake a bakin ƙofar kuma sun hana su shiga.

Zaune take ta haɗa kai da guiwa tana kuka, ya samu guri ya zauna domin ko lokacin da yana zuwa taɗi gurinta baya kyankyamin zama inda take.

"Kukan na menene Habiba? Baki murna da zuwa na bane, ko kuma dama tun kafin nazo kina cikin kukan?"

"Gaskiya bata cikin kuka ranka ya daɗe, sai dai ko wani abu yasa ta yin kukan." Inna Jummala yayarta ta faɗa wacce ke kusa da ita.

"Toh kiyi hakuri Habibi, komai da kika gani ikon Allah ne. Idan zuwa na ne yasaki kuka kiyi hakuri ki gafarceni dan Allah. Nazo ne dan ganin gudan jinina da Allah ya bani tare da ke. Kinsan dole idan naji cewa ina da magaji a duniya, ba shakka dole zanje ganinsa koda a bayan duniya ne. Bani da kowa da zan nuna nace ni na haifa sai Khadija, dole nazo naganta ta ganni. Kiyi hakuri idan har akwai abinda yake taɓa miki zuciya. Hakika Samira ta cuce mu(matarsa) itace silar rabuwar mu badan muna so ba. Ke kinyi sa'a kin kuma yin aure har da zuri'a. Ni kuwa ita ɗin ce dai ta zame min jarabar da bansan ranar rabuwar mu ba. Kona koreta sai tasan yadda tai naje na dawo da ita koda bana so. Wannan dalilin ne yasa ban sake korarta ba, na barta tayi iya abinda zata yi, duniya ce, wanda bezo bama jiransa take yi."

Tayi shiru ita dai batace komai ba, sannan ba zata iya sanar dasu dalilin yin kukanta ba. Kukan yazo mata ne kawai dan tasan tabbas an tarwatsa mata rayuwa, an rabata da ƴarta gashi dai ta dawo amma babu wani shakuwa a tare dasu saboda rashin daɗewa da zasu yi tare. Tana da aure dole zata tafi gidan mijinta. Shi kuma Sen Muhammad tasan a yanzu haka albarkacin Iman ne a tsakanin su, banda haka babu wani abu.

Hawayen fuskarta ta shiga gogewa tana kuma korar shaiɗan daga cikin zuciyar ta, wanda shine yake neman kawar mata da imani yana tuna mata da soyayyar tsohon mijinta. A hankali ta rissina tana gaishe shi, ya amsa ganin ta dan saki jikinta harma ta dago sun kalli juna, ta sauke ido tana wasa da kasan mayafin jikinta. Anan ya samu labarin su Abba da Mamah iyayen Iman, da kuma auran da suka yi mata da gudan jininsu duk da cewa a lokacin basu san asalinta ba. Yaji daɗi matuka harma ya dauki alkawarin idan ya shiga cikin Kano zai biya ta gurin su.

Ya daɗe a tare dasu harma ya roki alfarmar a bashi Iman su tafi Abuja tare shima tayi masa kwanaki biyu. Iman ta dinga murna baki yaki rufewa saboda daɗi, kayanta duk ta rabawa sa'anninta na kauyen. Shi kuma Sen. Muhammad yayi musu alƙawarin gyara musu kauyen tunda sunce su ba zasu koma cikin birni ba. Daga nan suka yi sallama bayan ya bawa mai unguwa kuɗi yace a bawa duk jama'ar kauyen, Habiba kuwa nata daban ya bata yace taja jari kafin ya dawo. Yaki mata da yawa saboda mugayen mutane karsu biyo ta.

"Inna kidena kuka, zan dinga zuwa ina ganinku Insha Allahu." Cewar Iman tana riƙe da hannun Mahaifiyarta.

"Karki damu, kiyi kokari dai ki koma gidan mijinki kinji?" Cike da jin kunya Iman tace.

"Toh Inna." Haka take kiranta kamar yadda taji sauran ƴan uwanta na faɗa.

Daga haka tabi mahaifinta ana ta ɗaukarsu hotuna har suka shige cikin luntsumemiyar motar da yazo a ciki. Tun a hanya Iman ta yiwa Abba waya tace gasu nan zuwa ita da Babanta. Abba na wajan aiki dole ya baro komai ya dawo gida aka fara shirye-shiryen tarbar baki. Su Ikram babu zama haka suka dage shaf-shaf dan ganin an shiya abubuwa dan a fita kunya.

Suna zuwa layin gidan Abba ya fito da sauri dan ya tarosu, bakinsa har kunne, dama tun a media sukaga gani suka kuma san cewa senate president shine mahaifin Iman. Abba ya saki murmushi ganin yadda ake ta kare Iman da mahaifinta, wacce ita kuma ta nunawa Sen. Muhammad Abba, nan da nan ya nufe shi cikin fara'a kai kace sun daɗe da sanin juna, yana zuwa suka rungume juna tamkar wasu mata.......


*Paid book ne idan kina so ki karanta sai ki tuntubi wannan lambobin. 0706 528 3730 or +447894142004 dan karin bayani. Top 10*









*HAJJA CE 👈*
3/22/22, 19:32 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲*


*37*




Cikin farin ciki suka saki juna suna sake yin musabaha, kowanne ka duba fuskarsa zaka samu yana murna da ganin juna. Abba ya nuna musu hanya kai tsaye securities suka mara musu baya. Iman ta shiga ciki da gudu tana kiran sunan Mamah, bata yi aune ba sukai karo da Areefullah. Da yake jikinsa ta faɗa kai tsaye yasa hannu ya rungumeta ƙaƙam.

"Welcome back dear wife." Ya faɗa yana sake matseta. Hango tawagar da zata shigo falon ne yasa shi saurin sakinta da sauri.

"Da baka sakeni ba sai na gayawa Abba." Ta faɗa tana rugawa cikin kitchen da take jiyo muryoyinsu a can. Hanan da Ikram ne a ciki, Iman ta rungume su kafin ta kalli Ikram tace.

"Kika ce guy ɗin can yana Abuja, ya akai yanzu na ganshi?" Ikram cikin farin ciki da yaki gushewa a zuciyarta tace.

"Ke yanzu ya shigo, wallahi muma kawai ganinsa mukai, ina ji yana gayawa Abba wai zuwa yai yaje ya dakkoki daga can kauye ku koma tare." Iman ta shiga zaro ido, bata ce komai ba ta juya zuwa ɗakin Mamah.

Cike da ladabi Areef ya tarbesu, Sen. Muhammad na ganinsa ya saki murmushi yana kamo kafadun Areef.

"Ince wannan shine sirikin nawa ko alhaji?" Abba yayi dariya yana nuna masa wajan zama yace.

"Shine ranka ya daɗe."

"Wow masha Allah I'm so happy, ya sunan?" Areef na faman sunkuyar da kai yace.

"Al-Mustapha."

"Nice name my son. Aiki fa?" Da sauri Abba yace.

"Ai da yake kasuwanci ya fara yanzu, karatun ne beyi nisa ba tunda aka kammala. Ba a ɗora ba."

"That's good, Gwara da be zauna hakan nan ba, yanzu sai yazo ya ɗora dan karatun yana da matuƙar muhimmanci, nan gaba ba'a san me zai zama ba. Ɗana idan komai ya nutsu sai sanar dani duk ƙasar da kake son kaje kayi karatun a can. Sai ka haɗa da abokanka biyu yadda zakaji daɗi a gurin da zakaje."

Murna da farin ciki a gurin Areef ba'a magana, har besan lokacin da ya rungume Sen. Muhammad ba.

"No.. No.. No, ba damuwa ai kun min abinda ba zan iya biyanku dashi ba. Kun riƙe min yarinya ba tare da kunsan waye mahaifinta ba, komai kunyi shi cikin tsoran Allah ba dan agani a yaba ba, Allah ya baku gidan aljanna."

Ikram da Hanan suka fito da wormers na abinci, masu kyau ne akaje gidan Islam aka aro dan a fita kunya. Sai da suka ajiye sannan suka gaishe da Sen. Muhammad cikin girmamawa, yana murmushi yace.

"Yara na ne ko?" Abba cike da murmushi yace.

"Sune rankashi daɗe. Sofiyya ce da kuma Fatima."

"Masha Allah ubangiji Allah ya raya mana su."

Tashi sukai dan ƙarasa kawo sauran abubuwan. Sannan suka zo suka zubawa kowa. Ba laifi Sen. Muhammad yaci abincin sosai dan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba. Sai da suka gama sannan Mamah tazo suka gaisa da Sen. Muhammad Abubakar, yai mata godiya tare da jinjina mata na kokari da tayi wajan bawa yarsa ilimi da kuma tarbiya. Daga nan ya roki arzikin a bashi su Iman dasu Ikram ya tafi dasu, Abba yace sai dai Iman domin su har yanzu suna lectures.

"Ahhh hakan ma yana da kyau muna sa rai idan sun samu lokaci sai a kawo mana ziyara. Nima ai ɗan asalin garin Kano ne." Nan ya shiga sanar dasu inda yake, harkar siyasa ce ta kaishi zama a garin Abuja.

"Amma idan zamu tafi tare zamu wuce da kai ko Al-Mustapha?"

"A'a ai yau yazo ranka ya daɗe, wai zuwa yayi su tafi tare da matarsa, gashi yanzu ka nemi alfarmar zata bika na ɗan wani lokacin. A bari next time zai zo idan ya komawa gurin aiki tunda duk Abuja ne."

Areefullah kamar ya yi kuka jin Abba na neman hanashi ya bisu, cikin sa'a yaji Sen. Muhammad yace.

"A'a tare zamu tafi dashi tunda dai ba zama yazo yi ba shima. Ka rabu dashi dan Allah."

Babu yadda Abba ya iya dole ya kyaleshi. Areef kuwa murna ba'a magana, haƙika surukin nashi bashi da wani problem, zai iya cewa yayi dacen samunsa. Tsab su Mamah suka taya Iman haɗa kayanta a cikin trolley, suna cikin hira sai ga Abba ya shigo yana ta fara'a ya kalli Mamah.

"Wai har yanzu baku kammala ba? Jiranku fa sukeyi."

"An gama komai Alhaji."

"Toh ai sai ta fito, daman gashi da Areef zasu tafi." Iman tayi ƙasa da kai tana murmushi. Ahhh wasa-wasa fa tana san guy ɗin nan, saboda ana cewa dashi za'a taji wani sanyi a zuciyarta. Mamah dasu Hanan suka kalleta dan jin me zata faɗa amman tayi shiru sai kuma sunkuyar da kai take.

"Toh ai sai ku fito kar yai ta jiranku dana a private jet ne bare ace dare zai yi."

"Abba jirgi fa kenan?" Cewar Ikram tana zaro ido.

"Eh jirgi, kinsan ko waye Ikram?" Suka yi dariya dukkansu, Abba ya kara da cewa.

"Uhmmm karkuji nan gaba kaɗan ya siyawa Iman daman itace ƴarsa telo ko Imanini?" Duk suka kuma tuntsirewa da dariya.

Tare suka fito zuwa falo, Areef yana saƙale da hannun Sen. Muhammad. Ikram ta riƙe baki tana yi masa tsiya da idanuta, yai mata banza saboda karma ta badashi a gaban surikinsa.

"Sai munyi waya Hajiya, Allah ya saka da alheri."

"Amin ranka ya daɗe muna godiya." Mamah ta faɗa cike da nutsuwa.

"Alhaji sai kazo kenan." Abba yai dariya tare da cewa.

"Haba dai ba damuwa ranka ya daɗe, fatan mu kawai Allah ya taya riko."

"Toh amin sai munyi waya." Suka sake yin musabaha daga nan suka nufi mota sai faman ɗaukar hotuna ake yi.

Areef da Iman suna bayan mota ɗaya, yayin da Sen. Muhammad ke cikin wata daban dan zuwa malam Aminu Kano International Airport. Ko a motar ma uzzara mata yayi musamman daga su sai driver shima kuma a gaba yake ba a kusa dasu ba. Da ta gaji da kwarzabar da yake mata ne yasa ta juyo gabaki ɗayanta tare da sanya idanunta cikin nasa, kyar suka dinga kallon juna kafin Areefullah ya janyota kusa dashi yana goga mata karan hancinsa a kan nata.

"Inata tambayarki ya jiki kina faman shareni why?" Iman ta sunkuyar da fuska ƙasa tare da cewa.

"Wai gani kayi ina ɗingishi ko kuwa?" Ya sake janyota yana cewa.

"Congratulations." Ta shiga ture shi tana cewa.

"Akan me?" Ya sumbaci gefen kumatunta yana sake matse ƴan yatsunta a hankali.

"Zuwan Abbanki, gashi muma daga haduwa har mun shiga cikin arzikinsa. Kinsan me yai min?" Murmushin jin daɗi tayi tana girgiza kai alamar bata sani ba.

"Hakafa yace zan koma karatu, ya bani zaɓin duk ƙasar da nake so zai kaini. Wow dear, wani abin abin daɗin ma ya ƙara da cewa na zaƙulo bests friends guda biyu mu tafi tare." Iman ta kallesa cike da murna tana cewa.

"First one

30 / 38