Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   10 / 38

27K to 30K   out of 113.7K words

kunya bane yaron can, sai kunyi da gaske zai kulaku marar mutunci kawai."

Ɗaya daga cikin ƴansandan ne ya fito daga bayan kanta ya nufi wajan Areef. Hannunsa ya damko suka koma bayan kantar, duk da haka Areef bai ɗago ya kalli kowa ba bare yasan adadin mutanan dake wajan. Feenah tai saurin ɗaga kai tana kallon Areef idanuwa cike da hawaye. Ganin ba ita yake kallo ba yasa ta rintsa idanuwa tana jin babu daɗi cikin zuciyar ta.

"Kai menene sunanka?" Ɗansandan ya sake tambayarsa.

Areef ya motsa bakinsa da kyar, a can ƙasan maƙoshi da in ba kasa kunne kayi ba bazaka ce ya yi magana ba. Yace,

"Al-Mustapha."

"Al-mujittafa ko Al-Mustapha? Ka buɗe baki kai mana magana malam." Cewar ɗanSandan yana haɗe rai.

"Mustaphaaaaa.!" Areef ya faɗa a ƙufule saboda tambayar ta isheshi.

"Karka ƙarawa kanka laifi yaro, kama haɗiye duk wani fushi dake ɗawainiya kai." Dansandan dake yi masa tambayar ya faɗa yana rubutu.

"Gayo mana lambar mahaifinka."

Areef yaji ɗansandan ya faɗa, kirjinsa ne yai wani irin bugawa. Nan da nan hankalisa ya tashi dan baya so iyayansa suji halin da ake ciki a yanzu.

"Kai bakaji ne? Aka ce ka bada lambar Babanka." Kawai ya samu kanshi da cewa.

"Ya mutu."

Da sauri Feenah ta kalli inda yake tana zaro ido, maganar ta bata mamaki wai ya mutu. Bata san tsabar tsoro da fargaba bane suka dirar masa har ya furta hakan.

"Toh bamu da mahaifiyarka." Cewar ɗansandan yana ta rubuce-rubucensa.

Areef yai shiru yana tunanin abinda zai kuma faɗa, dan shi gaskiya ba zai yadda a kirawo iyayensa gurin nan ba. Yasan tabbas sai ransu yai mugun ɓaci, musamman ma Mamah da taja masa kunne akan kula ko wace mace.

"Kai bakaji bane? Ka bamu lambar da zamu kirawo danginka dan susan kana nan a hannun mu." Jin sun bashi zabi ne yasa shi fara basu lambar muryarsa na rawa yace.

"08000000099." Yana gama faɗa musu ya ciji leɓansa na ƙasa tare da ɗagowa ya kalli inda Feenah take.

Ganin a yadda take ne yasa shi rintsa idanuwa, babu ɗankwali bare kuma maganar mayafi. Ya ciro rigar jikinsa Alhaji Nura yana kallonsa yana jiran yaga abinda zai yi. Feenah ya cillawa zuciyar shi na rawa bakinsa na karkarwa yace.

"Ki rufe kanki."

Ta kallesa kallo na musamman domin bata taɓa samun damar ganinsa babu riga ba. Vest ce baƙa a jikinsa, wacce ta ƙarawa fatar jikinsa kyau. A take Feenah taji wani abu yana taso mata akan shi, tun daga babban yatsan ƙafarta har zuwa tsakiyar kanta.

"Zakuci uban, a nan ɗin ma sai ka nunawa mutane cewa kai tantiri ne ko? Kana gaban hukuma baka fasa iskancin ba ko?"

Areef ya yatsina fuska a ransa yana cewa. 'Ka kasa suturtata dan ka samu ma na rufeta ko? Uhmmm zaka san waye ɗan iskan a cikin mu yau ɗin nan.' ya sake yin ƙwafa yana hura hanci.

_____Banda hira babu abinda suke yi cikin motar, kowannensu farin ciki ya mamaye su yau sun fito shanawa kamar yadda yaran masu dashi suke fita. Dr Jamil ne mai yawan kawo maganar da za ai ta yi Ikram da Iman suna biye masa, jefi-jefi kuma Hanan tana saka musu baki tare da ƴar dariya kasancewarta mace da bata da hayaniya.

Wani katon peak suka shiga, Haneef yana tayi musu dariya ganin sai santi suke yiwa gurin. Iman tai saurin tsayawa a gabansa tace.

"Yaya captain aron wayarka muyi hotuna." Haneef yasa hannu cikin aljihu ya fara lalube yaji wayam, yasa hannunsa saman goshi tare da cewa.

"Ya salam! ashe ban taho da ita ba." Karaf Jamil yace.

"Kamar ku ace baku da wayoyin hannu? Me yasa Mamah ko Abba basu siya muku ba little.?" Yana tambayar ne idanunsa akan Iman.

"Kai..! Tab Mamah tace ba zata siya mana ba, wai sai dai kowaccen mu in tayi aure mijin ya sai mata."

"Haba dai, in dai ba hanaku riƙewa zatai ba, abokina Muje a siyawa kowaccen su." Ya ƙarasa yana kallon Haneef.

"Okay Muje to, kuma ya za'a yi dama Mamah ta hanaku riƙe waya bayan zamani yazo na hutar da samari sintirin zuwa zance. Muje sai su siyo harda kayan kwalliya duk da ƙannan nawa basa yi sai dai asa lipstick."

Farin ciki ya kuma mamaye su duk suka rungume juna suna tsalle-tsalle. Sai da suka gama shanawa sannan suka fito, kai tsaye wani mall suka shiga idanuwan Jamil sun rufe duk abinda ya gani na ƴan mata na burgewa sai ya ɗakkowa Iman duk tsadar abun har suka gama akaje gurin biya. Mamaki ya kama Haneef ganin uban kayan, ya kalli abokin nasa.

"Wannan kuma fa ina zaka kai?" Jamil ya saki murmushi.

"Na little ne na sai mata." Dukkansu suka kalli junansu, Ikram na faman zare ido. Haneef ya sake duban Jamil yana dariya.

"Banfa gane wannan abun ba, komai kace little. Menene gaskiyar magana?" Jamil na dariya yace.

"Kasan Khadijatul Iman sunan Mamana ne. Ni kuma idan naji mai sunan a duk inda take nakanji wani farin ciki. Ina son sunan abokina, kuma ina girmamashi." Da wannan kalamai duk suka yarda dashi har suna yiwa Iman tsaya.

"Toh ke ashe ɗanki ne ma a gabanki."

Cewar Haneef. Suka yi dariya ita dai Iman tsabar daɗi kasa cewa komai tayi.

Ana faɗar adadin kuɗin kafin Haneef ya zaro Jamil ya miƙa ATM card ɗinsa.

"Bari a ɗauka anan, ai ni na gayyace su yawan." Gaba ɗaya suka shiga yi masa godiya yana cewa babu komai ai ƙannansa ne.

Ana gama zuba musu a ledoji daman ledar Iman daban take ta kumafi ta kowa girma, Jamil ya ɗaukar mata suka tafi mota daga nan sai gida.

_____Acan ɓangaren su Areef kuma, ɗansandan da ya karbi lambar da Areef ya basu ya shiga kira. Bugu biyu aka ɗauka amman ba'a yi magana ba da alama jira ake shi da ya kira ya farayi. Ɗansandan yai sallama tare da cewa.

"Yauwa daga folisteshen ne, mun karbi lambar ne daga wajan Al-mustapha ko zaka iya ƙarasowa?"

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, me ya yi?"

"Idan kazo zakaji."

"Toh wane folisteshen ne?" Nan ya faɗa masa tare da katse wayar.

Kujera suka bawa Alhaji Nura ya zauna itama Feenah aka bata amman taki zama. A lokacin ne DPO ya dawo suka gaisa da Alhaji daga nan aka labarta masa abinda ya faru ya karɓi kes ɗin. Ana kiran magariba yana ƙarasawa ofishin ƴan sandan, dan haka sai da aka yi sallah sannan aka fito da Areef daga inda aka kulleshi. DPO yace.

"Kai aka kira ne?"

"Eh an kirani cewar nazo an kama Al-mustapha."

"Ya sunanka?" Dpo ya tambaye shi.

"Aslam."

"Ya kuke dashi wannan ɗin?"

"Amini na ne."

Dpo ya kallshi cike da mamaki, ya kuma juyawa ya kalli Areef cikin ɓacin rai yace dashi.

"Kai..! Hukuma zaka rainawa hankali? Numbern abokinka muka ce ka kawo mana ko ta iyayenka?"

Areef ya yi shiru yana cizon leɓensa na sama. Alhaji Nura ya gyara zama yana cewa.

"Ai ranka ya daɗe da alama wannan yaron bashi da tarbiya. Ƙanƙani dashi yasan ta yadda ake duniyanci." Rai a matuƙar ɓace Dpo ya miƙawa Areef wayarsa yana cewa.

"Saka min lambar mahaifinka ko mahaifiyar ka karka kuma bani wacce ba ita na tambaya ba."

Ji yayi kamar ya fashe da kuka saboda bakin ciki, lallai Feenah ta saka shi cikin masifa dan be san mai zai cewa da Abba da Mamah ba matuƙar suka same shi anan. Gashi zuciyar shi ta hanashi basu hakuri bare ya nemi alfarmar a barshi ya kira yayansa duk da bashi da lambar a kansa. Wayar shi kuwa tana can guest house ɗin da tausayi ya ciro daga cikin aljihu ya ajiye ta.

Ya saka lambar Abban su tare da miƙawa Dpo wayar, ya koma gefe suna kallon juna shida Aslam. Lokacin da yaji Dpo yana gaisawa da Abban nashi ji yayi wani mugun fitsari ya ɗaure masa mara, hakan yasa shi rintsa ido tare da sunkuyar da kai.

"Toh kai muke jira ka ƙaraso.. Toh shikenan sai kazo ɗin." Ya katse yana kallon Alhaji Nura.

"Bari mahaifinshi yazo sai ayi komai a gabansa."

Alhaji Nura ya gyada kai alamar gamuwa, daga nan suka koma reception. Aslam da Areef suna gefe suna magana.

Mamaki ya cika zuciyar Abba jin cewar wai ana nemansa a folisteshen an kai ɗansa Areef, yana mamaki girman abinda yaron yayi har ta kaishi ga ƴan sanda. Yasan cewa Areef ba mutum bane mai hayaniya ko mai son rigima, a'a shi ɗin mutum ne da ba komai yake shiga harkarsa ba. Zuciyar shi cike da ɗimuwa ya ɗakko wayarsa daga gefe tare da nemo sunan Haneef, bugu ɗaya ya daga

"Kana ina yanzu Haneef?"

"Gani a hanyar gida Abba, lafiya dai ko naji muryarka a cikin ruɗu?" Ɗan tsaki Abba ya saki yace.

"Kazo folisteshen yanzu aka kirani cewar an kama Areef." Ya sanar dashi biranc ɗin.

"Kuyi hakuri mu fara zuwa ofishin ƴan sanda, wai an kama Areef."

"Me..!" Su Iman suka faɗa cikin mamaki.

"Toh yanzu Abba ya kirani yake cewa naje."

"Innalillahi, shi kuwa me ya yi musu?" Jamil ne ya faɗa yana riƙe haɓarsa.

"Sai munje zamuji komai." Haneef ya faɗa yana sake jan motar da karfi.

Abba na dira a mota suma suka faka tasu, ya yi mamaki da ya gansu duka ya tambaye su daga ina Haneef ya gaya masa. Tare suka shiga inda suka tarar da Areef a can gurin kanta ƴan sanda guda biyu sun sashi a tsakiya. Kallo su ya yi a hankali nan fa yaga gidan ne baki ɗaya in aka cire Mamah. Nan fa ya saddakar cewa Mamah taji abinda ya faru dashi.

Sanar da ƴan sandan gurin ya yi cewa su gayawa Dpo gashi yazo, ɗaya a ciki ya shiga ofishin ya sanar dashi aka bada umarnin duk su shiga. Iman kuwa mamaki ne ya kusa kashe ta ganin Feenah a gurin domin ba zata taɓa mantawa da fuskarta ba. Me tazo yi nan ita kuma? Ko dai sanadinta aka kawo ɗan uwanta gurin nan? Lallai ruwa baya tsami banza dole akwai abinda yake faruwa. Haka ta dinga tambayar zuciyarta abubuwa har suka shiga cikin ofishin Dpo.

"Alhaji Nura ne ya kawo ƙarar ɗanka Al-mustapha, yaje ya kama su a wani guest house suna aikata ɓarna, amman fa bai gansu tsirara ba. A yadda ya shaida mana yace suna kwance jikin junansu, ita ƴar gurin naza tuni shi Al-mustaphan ya cire mata ɗankwali da mayafi. Haka ka faɗa mana ko Alhaji.?" Cewar Dpo yana kallon mahaifin Feenah.

"Kwarai kuwa ranka ya daɗe." Ya kuma bada tabbaci.

"Toh kaji abinda ake zargin ɗanka dashi."

"Hasbunallahu wani'imal wakil Areef ɗin? A ina aka kamashi yana wannan abun?"

Caraf Alhaji Nura ya karbe ya shiga yi masa kwatancen gurin da kuma gidan. Abba ya shiga jinjina kai ya tuno tabbas ya taɓa ganin motarsa a bakin gate ɗin gidan har ya kirawo Areef ɗin yaji tabbacin shine a ciki.

"Toh amman shi gidan na waye?" Abba ya tambaya cike da damuwa.

(Areef fa ya shiga tarko, koya zata kaya? Shin Feenah zata yi nadamar kamasu da aka yi? Ni dai ban sani ba, amman Muje zuwa)


*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.







*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 19:00 - Buhainat: *ZGN*✍️

*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*

*12*



Yana tambayar idanunsa akan Areef da kansa yake a ƙasa, kunya da takaici sun mamaye shi. Wata tsawa da Abban ya yi masa ce yasa besan lokacin da ya furta.

"Na tane." Ba

"Nata ne ita wa?" Abba ya kuma tambaya a fusace.

"Nafisa." Areef ya faɗa tamkar zai fashe da kuka da alama an matsantawa zuciyarshi a wannan lokacin.

Gabaki ɗaya daga Dpo, Abba da Alhaji Nura dasu Iman babu wanda bai zubawa Nafisan idanu ba, jira kawai suke suji ta bakinta me zata gaya musu.

"Gidanki Nafisa? A ina kika samu gidan har ya zama naki?" Kamar ba zatai magana ba, can kuma tace.

"Sultan." Daddyn ta ya yi mata wani irin kallo mai tattare da tsana yace.

"Mu zaki rainawa hankali? Ki gama zabgawa yaron rashin mutunci karshe ki tozarta shi, shine zaki ce gidan shine? Wato kinsan yana da hakuri zai iya kareki a duk inda yake."

"Allah Daddy nashi ne ya bani." Feenah ta faɗa tana tura baki.

"Ya baki? Ya bakifa kika ce Nafisa?"

"Wallahi da gaske nake yi maka Daddy."

"Amman saboda bakida hankali, kuma baki ɗauke mu da mutumci ba shine baki gaya mana ba ko? Naji toh a cikin ku waye gwanin gayyatar zuwa can kuna abinda kukaga dama?"

"Ya isa Alhaji wannan tambayoyin duk mune zamu yi musu ita." Cewar Dpo yana sosa cikin kunnansa da ƙasan biro.

Daddy banda zufa babu abinda yake yi, sosai yayi mamakin jin gidan da ya kama su na Feenah ne Sultan ya bata. Amman mai yasa ya mallaka mata ba tare da ya yi shawara dasu ba? Yana ganinsa mai hankali ashe shima yaro ne be sani ba. Muryar Dpo ce ta katse masa zancen zucin da yake yi, inda yaji yana tambayarta.

"Mallaka miki ya yi ko kuwa? Kiyi mana cikakken bayani." Duk suka zuba mata ido, ta murguɗa baki tare da cewa.

"Ya bani ne a tunaninsa ba zaku barni na dawo gidan ku ba. Shine yace na zauna a ciki har Allah ya kawo min wani mijin."

"Shine kuke holewa dake da wannan ko? Kinki gidan mijinki mai hankali da tarbiya kinzo kina bawa wani jikinki ko?." Daddy ya faɗa yana shirin kai mata mazga.

"Zauna Alhaji karka doketa." Cewar Dpo.

"Haba malam ka taɓa ganin namiji ya lalata mace ba tare da amincewarta ba? Musamman irin wannan da za'a kama gida guda." Abba ya faɗa cikin ɓacin rai ganin yadda Daddy yake nuna lallai Areef ne yake neman lalata masa ƴa.

"Kunga mu bamu taraku anan dan kuyi mana hayaniya ba. Koma dai waye ya fara yanzu dai tare aka kamasu. Alhaji kace cikin suturar su ka gansu ko?"

"Haka ne ranka ya daɗe, amman ai babu dankwali da hijabi ya cire mata su da banje ba A..."

"Ya isa abinda na tambaya ka bani amsar. Ganinta babu mayafi ko dankwali ba zai bada shaidar cewa shine ya cire mata ba. Kuma kunji gidan nata ne, kenan shine yaje ya sameta a can haka ne Nafisa?" Feenah babu tsoran Allah bare kunya tace.

"Eh, babu kuma abinda yake shiga tsakanin mu. Ranka ya daɗe wallahi muna son juna tuntuni, wanda suka aura min ba shine zabin rai na ba, dan Allah kace su barmu tare dan...."

Daddy besan lokacin da ya ciro wayarsa ya maka mata ita ba. Kaji yarinya marar kunya. Areef da yake namiji da kyar yake bada amsar tambayoyin da ake masa, amman ita sai zabga bayani take harda wanda ba'a tambaya ba.

"Alhaji kana gaban hukumafa, ya kamata ka barmu mu yanke muku hukunci karka illata yarinyar nan."

Maganar Dpo ta sake bawa Daddy haushi yayi dana sanin kawo karar, ji yayi dama tun a can gidan yaci ubansu. Bayan jin bayani daga kowane sashe Dpo ya kalli Daddyn Feenah cikin ido yace.

"Yanzu me kake so ayi Alhaji?" Da sauri Daddy yace,

"Ina son a rabasu, bashi ba ita kawai." Ya maida ganinsa gurin Abba shima ya tambaye shi.

"Alhaji me kake so ayi?" Abba ya ja numfashin takaici yace.

"Bana jin ina da matsala a wannan abun. Yaro na ba yanzu zai yi aure ba domin har yanzu ni ne nan nake masa sutura na kuma biya masa kuɗin makaranta. Kaga kenan babu maganar aure."

Rubuce-rubuce Dpo yayi sannan ya kalli kowane sashe yace.

"Dukanku kuna nufin a raba tsakanin yaran nan ko?"

"Kwarai kuwa."

Duk suka amsa a tare. Feenah ta fashe da kuka tana ihu ta shiga uku ita wallahi ba za'a rabasu ba. Kunya duk ta cika Daddy, shine ya kawo ƙarar amman karshe shine yaji kunya dan abinda Feenah keyi a wannan lokacin dole duk rashin kunyarka kaji babu daɗi. Tun a lokacin ya fara nadamar nemawa Feenah ƴanci, ya kuma tabbatar da cewa ita ɗin bata da kunya matuƙa.

"Shikenan kai Al-mustapha babu kai babu Nafisa. Ko a hanya mukaji labarin ka tsaida ita zamu yi maka hukunci dai dai da laifinka."

Ya kalli Feenah itama dake ta faman ihu yayi mata kashedi irin na Areef wato ba ita bashi har abada. Su Abba ne suka fara fita su Haneef suka shiga motar su Areef ya shiga ta Abba abisa umarnin shi. Feenah kuwa Daddy ne yasa wasu ƴan sanda mata suka ɗakko ta yace su sata a mota yaja yabar gurin.

"Kai amman fa Areef ya bani mamaki wallahi, shiru-shiru dashi ashe-ashe haka yake." Jamil ya faɗa cike da mamaki.

"Akwai abinda nake hasashe, kamar fa yarinyar itace ke nemansa dan daga ganinta bata da kunya. Bakuga yadda take yin magana ba, hatta mahaifinta bata mai dashi komai ba wallahi." Cewar Haneef kansa duk ya ɗaure da ɗinbin mamaki.

"Uhmmm ni wallahi daman nasan wannan yarinyar budurwar Yaya Areef ce, yo baby fa take ce masa shi kuma yace sweetie. Tare suke yawo wallahi Yaya captain." Iman ta faɗa cike da gasgatawa.

"Kwanaki fa da Mamah tace naje na duba ɗakinsa ko yana nan, sai da na gama dubawa ko ina ban ganshi ba. Yaya captain nazo fitowa na ganshi ya dawo nace daga ina yace min daga bariki. Kilama wallahi gurinta yaje."

Ta sake basu tabbacin lallai Areef zai iya aikatawa domin tasha ganin abubuwa tattare dashi.

"Nidai ban yadda cewa Yaya Areef zai aikata ba, ta yiwu dai ita yarinyar ke nuna masa w...."

Ikram ta kasa ƙarasawa saboda kunyar kalmar, amman duk sun gano abinda take son faɗa. A haka suka ƙarasa gida suna ta zancen, da yake motar Abba ce a gaba duk kusan a tare suka shiga. Areef kuwa daman tunda suka shiga motar yaga Abban baice masa kanzil ba, yasan cewa akwai tashin hankali idan sunje.

Su Iman ne suka fito da kaya a ledoji, suka bi Areef da kallo wanda gaba daya a muzance yake.

10 / 38