yaro?"
Mamah tai saurin fita daga ɗakin jin zancen sai sauya salo gashi Hajiya na gurin gasu Ikram.
Iman kuwa abin mugun mamaki yake bata idan taji ana cewa Areef ne mijinta, gashi yanata yi mata yawo a cikin idanunta, sai dai hotan yafi nuna mata wanda tasan shi tare da Feenah. Taya zata zauna da wanda yaje ya siyar da ƙima da mutuncinsa a gurin wata? Sam ba zata iya rayuwa da wanda ya zubar da girman da Allah ya bashi a idanunta ba. Maganin aka bata tasha tana yatsina fuska saboda bauri.
Kwanansu ɗaya Hajiya tasa aka kaisu wajan wani yayanta wanda malami ne a cikin kauyen wanda manyan mutane suke zuwa gurinsa neman taimako. Yana ganin Iman ya tabbatar musu da cewa akwai mai nemanta a jikinsu, ya basu shawarar nisantata da gidan gabaki ɗaya. Jin haka yasa Mamah kiran Abba tayi masa bayanin da Baffa Audi ya yi musu, Abba yaji daɗin haka domin abin yazo akan gaba Areef yana can Abuja har Alhaji Sammani ya bashi muhalli.
A ranar da zasu taho Abba yaje kauyen ya ɗauke su gabaki ɗaya banda Hajiya da tace ita ba zataje ba sai wata rana. Daga can kauyen suka yiwa Abuja dirar miƙiya, kai tsaye gidan da aka bawa Areef Abba ya kaisu. Wanda dawowarsa kenan daga katafaren shagon da zai dinga aiki, yana cin abincin da ya siyo yaji muryoyinsu. Beyi tsammani ba dan Abba bai gaya masa ba.
"Ahhh lallai Yaya Areef an samu duniya irin wannan harka haka?" Ikram ta faɗa tana miƙa masa hannu suka tafa.
"Duniyar me na samu Iky?" Ya tambayeta yana yiwa Mamah sannu da zuwa.
"Gashi kuwa, duk da dai ba ƙato bane ai mai kyau ne ba laifi. A'a daga ɗaki ɗaya gashi ga samu gidan kanka." Duk suka kyalkyale da dariya yace.
"Ni duk ba wannan bane damuwata, kayana duk suna gida wallahi. Gashi ban sanarwa da kowa ba har su Aslam, ni dai Abba da Alhajin nan ya barni zuwa next month sai na zo na fara aikin." Abba ya girgiza kai.
"Kanaji dai yace basai ka koma gida ba zai baka komai saboda idan baka fara yanzu ba koda yaushe za'a iya zuwa muku supervision. Kayi hakuri kawai zan kuma saka rana na kawo ma kayan. Mudai fatan mu kawai Allah yasa alkairi, ga matarka nan zamu bar maka, Insha Allahu za'a kawo muku kayan ku." Cikin tsananin tsoro Areef yace.
"Abba! Wa'aka kawo min?" Yai maganar cikin tashin hankali saboda be manta abinda tayi masa a ɗakinshi ba.
"Iman." Cewar Abba.
"Amman kun manta a...."
"Basai ka ƙarasaba Areef, mun kawo maka ita shine silar zuwan mu Abuja. Komawa da ita can gida shine hatsarin inji Baffa Audi. Zan bar maka su Ikram ranar da aka kawo kayanku sai su koma."
Areef ya ɗaga ido ya kalli inda Iman take suka haɗa ido ya janye nashi da sauri. Ba ƙaramin tsoro take bashi ba yanzu ta yadda baya son ko hanya su haɗa.
Yanzu su Abba basa tsoran barin shi gida ɗaya da Iman? Shikenan yasan ma kwanansa ya ƙare a duniya ya tabbatar itace sanadin barinsa doran ƙasa.
"Zamuyi kokarin yo muku furnitures tunda babu, fatan mu a gareku shine kuyi zama irin na amana, duk mai matsala a cikin ku ya gaya min ko ya sanarwa da mahaifiyar ku. Areef ka riƙe matarka da amana, bamason muji wani ɓatanci ya fito daga gareka, idan har hakan ta kasance zaka fuskanci fushin mu." Shidai Areef kasa cewa komai yayi, hankalinsa a matuƙar tashe yake akan barinsa da Iman cikin gida ɗaya.
Mamah da Abba a ranar suka juyo aka bar sauran a can. Dalilin Ikram da Hanan yasa hankalin Areef nutsuwa, yaje ya samo musu abinda zasuci da abubuwan da zasu buƙata a gidan.
_____________
Jamil kuwa duk ya damu ganin har tsawon kwanaki biyu babu wani labarin mutanan gidan, tun yana zuwa ya zauna a ƙofar gidan har ya fara gajiya, ga kiraye-kirayen wayoyi daga asibitoci ana nemansa ya bada taimako ya kasa zuwa ko'ina.
Washe gari da sassafe kowa ya nufi gidan inda ya tarar da tabbacin sun dawo saboda ya duba yaga an cire kwaɗon da aka kulle gate ɗin dashi. Yayi attamting ɗin shiga gidan yafi sau goma amman ya kasa, bashi da cikakkiyar hujja da zai bayar na zuwansa a wannan lokacin. Lambar Iman ya kira da sim ɗin da bata dashi, taita kaɗawa amman ba'a ɗauka. Ita kuma a lokacin tana falo su Ikram sun haɗa musu karin kumallo suna ci wayar kuma tun jiya da suka zo bata ciro daga jakar Hanan ba.
Wani almajiri ne zai shiga gidan yin bara, Jamil ya kirawo shi yace yaje yace ana sallama da Ikram. Almajirin na shiga ya samu Mamah zata fito ya faɗi sakon Jamil. Mamah ta sanar masa bata nan, ya koma ya sanar da Jamil. Sake tura shi yayi ya kirawo Hanan, wannan lokacin Abba ne yace yaje yace duk basa nan sunje unguwa. Sake komawa almajirin yayi ya sanar da shi abinda aka gaya masa. Ɗari biyu ya bashi, ganin ana shirin buɗe gate ne yasa shi yin saurin barin wajan, ya buya su Abba suka fito a mota, parking yayi ya koma ya rufe sannan ya shiga suka bar wajan dan zuwa asibiti duba su kawu Balarabe.
Jamil ya dafe goshi domin bega Iman ba a cikin motar, daga Abba sai Mamah. Toh ina suka tafi? Wa zai tambaya yaji inda suka tafi? Tabbas idan besan inda Iman take ba kuma besan ranar dawowarta ba yana cikin tashin hankali. Ya rasa rayuwar ƴarsa Meenal saboda ya samu Iman gashi wankin hula yana shirin kaishi dare.
Wayarsa ya ciro, malam ya kira suka yi magana mai matuƙar tsaho, wacce a karshe tasa Jamil sakin wani kayataccen murmushi. Allah kadai yasan karatun kurma, su kadai suka san kudurinsu akan baiwar Allah da batajiba ba kuma ta gani ba. Kuma annabi Muhammad s.a.w yace Allah bai taɓa jarabar bawa da wani bala'i ba alhalin yana tafarkin wannan bala'in, face sai Allah ya tsarkake shi daga cikin bala'o'in da yake ciki. Tabbas Iman tana cikin jarabawa sai dai ayi addu'ar Allah ya kuɓutar da ita cikin gaggawa.
Mota ya koma ya shiga yabar unguwar da sauri. Kai tsaye Zamfara ya koma zuciyar shi cike da farin ciki, yasa a ransa koda bai samu Iman ba tofa ba zai bari wani ya mallaketa ba domin malam ya sanar dashi cewa, wannan son da yaji a lokaci gudu Allah na nufin Iman tashi ce, ya yi iya yinsa wajan ganin ya mallaketa.
(Hakika wasu bayin Allah sukan yi amfani da wata yar dama da Allah ya ara musu suyi ta lalata zuciyoyin mutane. Misali mu da Allah yasa zamu yi rubutu na littafi, akwai wasu daga cikin mu da suke amfani da alƙalaminsu wajan ruguza ko jefa mutane ga halaka. Ɗaukaka daga Allah take, basai ka rubuta masha'a cikin rubutu za'a soka ba. Karmu manta da cewa Alƙalami fa yafi takobi) da yawa malamai kanyi amfani da malunta suna jefa mutane cikin sabon Allah. Allah ka haɗa mu da Malaman alkairi wadanda maganganinsu da mukeji har muyi abinda suka karanto suka fassara mana ya zama alkairi.
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪
Akan 500 kacal.
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BARI DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
3/2/22, 19:49 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*
*24*
Sam Areefullah baya bari su haɗu da Iman, daya hangota a guri yake canza nashi saboda yaga ta kuma zama so silent tamkar ba Iman ɗin da ya sani ba a baya. Ɗaki ɗaya ya basu mai ɗauke da katifa domin sauran dakunan duk babu komai a ciki, shima akan center carpet yake kwana. Cikin shirinsa ya fito na riga da wandon jeans da ya siyo jiya sakamakon bashi da kaya basu san zasu kwana ba farkon zuwan su, sai gashima an hanashi komawa gida baki ɗaya. Yana fitowa suka yi karo da Iman ɗin ta taho kai masa breakfast.
Kirjinsa ya buga da sauri ya koma gefe yana musurai kamar gaske. Ta kalleshi tana miƙa masa plate ɗin indomie da soyayyan kwai akai. Babu musu yasa hannu ya karɓa yana addu'a a cikin zuciyar shi kar Allah ya bata damar cakumarsa. Cikin wata irin murya da baisan ma tana da irin ta ba yaji tace dashi.
"Kayi breakfast kafin ka fita, bari na kawo maka shayi, bunu ko asa maka madara?"
Areef da mamaki ya kusa kasheshi kallonta kawai yake yi har beji abinda take cewa ba, sai da yaji tana yi masa ɗas..ɗas..ɗas da ƴan yatsunta sannan ya dawo cikin hanyacinsa yana cewa.
"Mai kika ce?" Iman ta dalla masa harar besan lokacin da yace mata.
"Eh.. A'a."
"Menene kuma eh a'a? Asaka madara ko kafi son baki." Yayi saurin faɗin
"Kar a saka."
Bata sake magana ba sai juyawa da tayi tabar wajan, ya bita da ido tare da tauna leɓensa. Komawa ya yi ciki ya dire plate ɗin akan carpet ya ƙarasa wajan glass window ɗin ɗakin yana leƙa harabar gidan. Muryarta ce ta sake dawo dashi ya juyo yaga tana ajiye masa tea ɗin a kusa da indomien.
"Nasa sugar amman idan bai isa ba kayi magana sai a ƙara."
Mamaki ya dabaibaye shi ganin da a baya ne masifa zai mata yace wayace ba'a zuba a cikin dahuwar tea ɗin ba sai dai ayi barbaɗe. Yayi shiru saboda har hango yadda zata kuma tumurmusashi yayi, gashi ya tabbar idan ta damke shi su Hanan ba zasu iya ƙwatarsa ba dole yabi komai a hankali har Allah ya kawo lokacin da zai saita mata zama.
Sai da ya tabbatar da ta fice daga cikin ɗakin sannan ya ƙarasa gurin ya zauna yana cin indomie ɗin. Lallai tayi hankali kenan tunda yaga tana yi masa komai cikin mutunci, Amman kuma yana son yasan suwaye ahalinta, a ina aka haifeta? Da aure ko babu aka sameta? Shin zai iya zaman aure da ita kuwa? Bayan zuciyarshi da tunaninsa gaba ɗaya suna gurin Feenah. Itace wacce ta fara nuna masa so murar an, wai shin yanzu tana ina?
Da wannan tunane-tunanen ya gama ci ya tashi, wayoyin ya ɗauka ya fito. Ɗakin su ya shiga ya tarar da su suna cin nasa suka kalleshi cike da fara'a banda Iman da ta kurawa plate ɗin indomie ido, ya yi gyaran murya amman bata ɗago ba yace dasu.
"Bari naje na dawo karku buɗe gidan nan kunga babu wanda muka sani."
"Kayi kyau fa mijin Iman."
Cewar Ikram tana dariya. Be kulata ba ya juya yabar ɗakin yana yatsina fuska.
"Kun dace da juna fa Aunty Iman." Ikram ta sake faɗa tana ɗebo indomie takai cikin bakin ta.
Wani banzan kallo Iman tayi mata tare da jan karamin tsaki ta yadda ba zasuji ba, miƙewa tayi tabar wajan ta haye kan katifa hawaye na zubowa daga cikin idanunta. Gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi, burikanta na rayuwa duk sun ruguje, tana son yin karatu mai zurfi kafin tayi aure saboda ganinta ƴar caraf tayi zaton har masters sai tayi, ita da take yiwa sauran mate ɗin ta dariya tana cewa zasu yi candy marriage. Sai gashi ita daga yin candyn anyi mata.
Hanan ta miƙe taje gurinta tana taɓa bayanta, jiki a sanyaye tace mata.
"Kiyi hakuri Aunty Iman nasan bakya son shi, amman ki dena kuka saboda zai iya samiki ciwon kai." Kamar zuga ta tayi sai kawai ta fara kuka na gaske kuma na fili.
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun wai da gaske kuka kike yi? Maganar ce ta ɓata miki rai kome?" Iman ta kasa magana saboda zafin da taji kirjinta yana yi.
"Ni ku kyaleni, ku rabu dani dan Allah." Ta faɗa cikin raunin zuciya.
"Tohhh! Allah ya baki hakuri, mukam Allah yasa yau a aiko ɗaukar mu." Ikram ta faɗa tana kwashe kwanukan.
Bata kuma lulasu ba har suka ƙaraci lallashinsu suka gama kowacce ta ɗakko wayarta. Ita kuwa Iman ko wayar ma bata son gani bare kuma abinda ake yi a cikin ta. Tana da manya-manyan damuwoyi a cikin zuciyarta har guda uku waɗanda ba ta san ta ina zata fara samun warwarewarsu ba. Tashi tayi bata kula kowa ba ta nufi kitchen. Kayan miyan da Areef ya kawo duk a jiya da ya ɗan yo musu siyayya su ta shiga gyarawa, Hanan ta leƙo ganin aiki take yi kuma da alama bata son kowa ya rabeta yasa ta zauna a falo taci gaba da chatting ɗin ta. Tana cikin yi ne aka kirata ta ɗauka cike da murna.
"Hello Mamah."
"Uhmmm Hanan ya kuke? Ina Iman?"
"Tana kitchen."
"Lafiya dai ko? Ba wata matsala da kuke fuskanta?" Mamah ta tambaya cike da kulawa.
"Eh toh gaskiya dai Iman bata cikin walwala dan yanzu ma kuka ta dinga yi muna ta bata hakuri ta tashi shine ta shiga kitchen ta hau gyaran kayan miya." Kamar Mamah zatai kuka haka taji, ta daure tace.
"Kubita sannu a hankali kunga dai ba son auran nan take yi ba, har yanzu ta kasa gane gatan da aka yi mata. Kuma kunga ba isasshiyar lafiya ce da ita ba. Kubita a hankali har ku taho."
"Yaushe zamu taho Mamah? Kinsan fa zamu yi jamb." Cewar Hanan tana shagwaɓa fuska tamkar tana gabanta.
"Zaku taho cikin satin nan, da yake bayan mun taho a hanya yayanku ya turowa Abban ku kuɗi nima ya turo min, Toh shine muka tsaya anan hanyar Abuja muka zabi kujeru, wardrobe da gado. Daman akwai kuɗin da Jamil ya bayar da kuma ƴan ragowar na hannuwanmu, za'a sai musu kayan kitchen da kuma na sawa kafin Allah yasa shima Areef ɗin ya fara jin alert."
Murmushi ya suɓucewa Hanan, tayi farin ciki sosai da samun iyaye irin nasu marasa kyashi da nuna wariya, ta tabbatar koda itace a matsayin Iman iyakacin abinda zasu iya yi mata kenan.
"Allah ya saka da alheri Mamah ya bar mana ku cikin ƙoshin lafiya."
"Amin Hanan ki gaida sauran ƴan uwan naki bari naje nayi aiki."
Suka yi sallama Hanan ta miƙe ta shiga kitchen ɗin. Kallon Iman tayi wacce ke gyaran risho alamar wani abin zata ɗora tace mata.
"Aunty Iman Mamah tana gaisheki." Ba tare da ta juyo ba ta amsa.
"Ina amsawa." Tacigaba da aikin ta.
"Kawo nayi kije ki zauna." Cewar Hanan tana ƙokarin karɓar lagwanin.
"Bashi kawai zan yi bana son zama ne." Iman ta faɗa tana jin wani irin ɓacin rai.
Kyaleta Hanan tayi ta kama wanke-wanke kowanne da abinda yake saƙawa a zuciyar ta. Jallop ɗin tayi suka yi a tare suna gamawa suka zuba a cooler kowacce taje tayi wanka suka shirya tsab tamkar ance zasu zaɓen sarauniya. A dai dai lokacin da Areef ya dawo bakinsa ɗauke da sallama. Da Ikram ya fara haduwa ta sakar masa murmushi tare da cewa.
"Harka dawo?" Yamutsa fuska yai tare da cewa.
"Abba ne ya kirani wai ya turo a kawo furnitures, ya bani lambar waɗanda zasu kawo sunce gasu nan ƙarasowa. Ina sauran suke?"
Ya ƙarasa magana yana waige-waige. Ikram ta saki dariya ganin ya farayin abubuwan manyan mutane, bata faɗi abinda yake cinta a ciki ba dan tasan zai iya kullatarta dan haka kawai tace dashi.
"Suna ɗaki bari na kira su."
Sai yaji be hana taba tana tafiya shi kuma ya zauna tare da ciro wayar Feenah saboda yana ganin horunanta da sauran abubuwan da zasu hanashi mantawa da ita.
Hanan ce a gaba sai Iman ita sanye take ma da wata doguwar rigar atamfa, ta matseta sosai har ba'a gane akwai bra a jikinta, daman kuma fitilun kirjin biyu ba wai girma garesu ba dole ce tasa take sakawa dan kar ace har tayi candy bata fara sakawa ba. Ya kalleta sosai, kyakkyawa ce ta ajin farko domin Allah ya tsara mata halitta irin wacce kowa zai so ace shine mai ita. Babbar matsalar kawai bata da auki. Ya kalli hotan Feenah wacce take bulbul gasu a tsaye tamkar bata haihu ba, koda yake daman bata bari babyn yasha mata ba.
"Yaya Areef har ka dawo?" Hanan ta tambaya tana daga bayan Iman.
"Wai bakwa son na dawo ne da kuke cewa har? Ƴan rainin hankali kawai." Suka yi dariya banda Iman da take kallon gefe.
"Kaya za'a kawo ku fara shirya su." Yana magana yaji ana buga musu ƙofar gidan, duk suka kalleshi ya ɗan ware idanu tare da cewa.
"Bari naje ƙila sune suka ƙaraso." Ya fita su kuma duk suka yi cirko-cirko suna kallon hanyar da ya fita.
Yana zuwa kuwa ya tarar sune, dawowa yayi ya sanar dasu Ikram suka maida komai gefe sannan aka shigo da kayan. Tare dashi ake ta aikin, su Hanan suka tsara yadda zasu yi musu Ikram taja Hanan ɗin suka tafi ɗakin da suka kwana suna jera kayan, shi kuma Areef aka barshi shida Iman babu mai yiwa ɗan uwansa magana. Wayarsa ya ɗakko a aljihu ya sanya karatun qurani.
Inda ya saka fuskar gadon ita kuma ta janyo ta sauya gurin. Da mamaki Areef ya kalleta tare da cewa.
"Ya haka?" Cikin raunin fuska tare da cuno baki tace masa.
"Anan yafi kyau." Yace.
"Nan shine ɗaki na ai ina da right ɗin zaɓar inda nake so." Ta ɗago suka haɗa idanuwa, ta juya zata fita tabar masa ɗakin, besan lokacin da ya riƙota ba.
Hawaye ya gani a fuskarta waɗanda yasha mamakin abinda ya kawo su, shifa ba babu abinda ya yi mata, kawai daga cewa ga yadda yake so shikenan sai kuka? Ya sake damƙe hannun yana cewa.
"Ki dawo asalin Iman ɗinki da na sani, ki dena min wannan lange-langen bana son rainin sense." Ta gyada masa kai tayi shiru.
"Ki buɗe baki kiyi min magana ko bakin ne ya sake rufewa?" Ya faɗa cikin nuna isa.