Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   14 / 38

39K to 42K   out of 113.7K words

saba dasu. Kuma wallahi ina son su har cikin zuciya ta. Aslam ina son Mamah, ina sonta fiye da tunaninku. Idan ba itace mahaifiyata ba na shiga uku."

Duk sai jikinsu yai sanyi, tausayin shi ya kamasu. Gurinshi suka ƙarasa kamar jira yake ya faɗa kansu yana kuka tamkar ba namiji ba. Suka shiga lallashi da bashi hakuri tare da ƙarfafa masa guiwa har yai shiru. Sai dai fa zuciyar shi bata dena mamakin haɗashi aure da Iman ba.

****

A ranar aka kai Islam gidan mijinta, a cewar Hajiya kakarsu wato mahaifiyar su Abba gwara a kaita tunda mijin nata ba ɗan cikin gidan bane, kuma jikin kawu Sagir ɗin da sauki duk da cewar ya ƙone sosai. Amman duk da haka Hajiya tace sai Islam ta tafi gidan mijinta dan kota zauna ba wani abun zata yi musu ba. Haka aka ɗauketa tana kuka aka saka a mota aka tafi kaita.

Iman kuwa tana gurin su Mamah kwance, tunaninta kawai ya zasu haɗu da Jamil, ta kasa nutsuwa sam so kawai take ta ganshi a kusa da ita. Ta juya a hankali ta kalli Aunty Husnah dake dama fura da nono, a hankali tace mata.

"Aunty Husnah zanje gurin su Ikram."

"Basa nan gaskiya harda su aka tafi kai Islam." Iman ta rintsa ido tare da cewa,

"Aunty Husnah wai Yaya Areef aka ɗauka min aure dashi?"

"Eh wallahi Iman, muma kamar yadda kukaji abin daga sama haka kowa yaji, yanzu kin zama matar Areef."

Ai tana cewa ta zama matar Areef Iman ta saki ihu hakan ya janyo hankalinsu Mamah. Ihu take tana kuka tana cewa.

"Taya zan auri ɗan uwana? Taya muna uwa ɗaya uba ɗaya zan zama matarsa? Wallahi bazan yadda ba, wayyo Allah na shiga uku."

"Iman kun fimu hankali ne da zaki dinga wannan maganar? Ko kun ɗauka bamuyi islamiya ba? Ance miki haka kurum muka haɗaku? Tunda kuka ga munyi haka kunsan tabbas akwai aure tsakaninku." Mamah na direwa Iman tace,

"Toh wallahi bana son shi ni Yaya Jamil nake so. A rasa wanda za'a aura min sai wanda ya fara lalacewa? Sai da ya zama ɗan iska sannan za'a aura min shi? Bazan yadda ba Yaya Jamil nake so idan har ba zan aure shi ba sai dai ku kasheni."

Tana kaiwa nan ta zura da gudu, kai da ganin yadda take masifa tana magana kasan cewa controlling ɗin zuciyarta ake yi. Kafin a riƙota takai parking lot Jamil dake zaune yana alwala tayi gurinsa tana kuka. Su Mamah da suka biyo ta duk suka tsaya ganin yadda take roƙar Jamil.

"Yaya Jamil dan Allah karka bari su aura min Areef wallahi bana son shi. Dan Allah ka ɗauke ni daga gidan nan ko kaine ka aure ni zan zauna tare da kai."

Jamil ya dinga zaro ido cike da mamakin kalaman Iman, amman a cikin zuciyar shi murna yake da farin ciki. Yai saurin kallonta yana ɗan jan baya kaɗan yana cewa.

"Na aureki kuma Iman? Wannan wace irin magana ce?" Ta sake durƙusawa ƙasa tana haɗe hannaye guri guda alamar roƙo.

"Ka rufa min asiri Yaya Jamil, ina sonka wallahi zan aureka wallahi ba zan iya rayuwa ba idan babu kai."

"Mamah wai meke faruwa ne?" Ya tambayi Mamah tamkar ance masa ta fishi sanin abinda yake faruwa.

"Dan Allah Yaya Jamil karka saurare su, wallahi so suke su haɗani da mazinaci. Kuma ni kaine zaɓin zuciyata dan girman zatin Allah ka aureni wayyo Allah na." Iman ta faɗa tana sake fashewa da kuka.

"Ni nace miki aure zanyi Iman? Ko na taɓa cewa ki soni? Please dan Allah karki haɗani da ƴan uwanki da iyayenki daga zuwa na." Jamil ya faɗa yana ɗaukar buta.

"Wayyo Allah na shiga uku Yaya Jamil karka gujeni, na yadda ka aureni ko baka sona wallahi zan zauna da kai."

"Mamah kushiga da yarinyar nan ciki ni wallahi ba ruwa na." Cewar Jamil yana cillar da butar gefe ya nufi sashen Haneef.

Da gudu Iman ta sake bin bayan shi inda Mamah tasa su Aunty Husnah suje su kamota da alamar ta samu tabin hankali, dan in ba hauka ba babu abinda zai sa ta dinga wannan abubuwan. Koda suka isa gurin zasu riƙota wani irin ihu tayi wanda yasa su Aunty Husnah toshe kunne tare da ja baya, ta fara rarimo abubuwa tana ƙwaɗa musu Jamil ya isa wajan tare da riƙota yana magana a saitin kunnanta.......
_________________
(Hohoho Jamil🚶🏻‍♀️Allah ya rabamu da mugun baƙo. Dama ance mugu bashi da kama) Muje zuwa ƴan Top 10. Karku dauki wannan labarin a matsayin wasa ko nishaɗi. Ko ɗauke shi gasken-gaske. 👇


*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.








*HAJJA CE 👈*
2/14/22, 10:26 - Buhainat: *ZO....GA...N*✍️
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*

*18*



"Kisa a ranki ni naki ne Iman." Jamil ya furta mata a hankali cikin kunnenta. Iman ta sauke wata ƙaruwar ajiyar zuciya saboda yadda taji daɗin kalamansa a ranta. Juyawa tayi a hankali ta kallesa cikin ido tace.

"Dagaske?" Jamil ya gyaɗa mata kai alamar eh.

Ganin ta a tsaya su kuma su Aunty Husnah suka ƙarasa tare da kamota tana ta kallon Jamil suka nufi cikin gida da ita. Suna shiga falo Iman ta fizge hannunta daga riƙon da sukai mata sai faman cono baki take tamkar wacce zatai kuka. Mamah kam banda kallo babu abinda take yiwa Iman, ta bata mamaki matuƙa, tana kuma kyautata tunanin Iman ta zama haka ne ganin Jamil ɗin yana da kuɗi gashi daman ya taɓa yi mata siyayya mai tsada da uban yawa.

"Allah yaji ƙaina ba wai dan na mutu ba. Dama na faɗa mu, idan baku manta ba lokacin da kuka kai min yarinyar nan gida a cikin zanin goyo kuka shaidamin cewar a ƙofar gidan ku kuka tsince ta. Nayi ta fama daku akan kuje ku kaita folisteshan susan yadda zasu yi da ita, keda mijinki kuka dage cewar zaku riƙe ta. Menace muku a lokacin? Tambayarki nake yi Hawwa, ki faɗi abinda nace a lokacin." Hajiya ta dakawa Mamah tsawa.

Tana gidan kawu Sagir akaje aka sanar mata abinda ke faruwa a cikin gidan su Haneef, shine ta taso ta taho. Tana shigowa falon ne idanunta suka sauka akan yadda Iman ta fisge daga rikon da su Aunty Husnah sukai mata. Yadda Hajiya ta dakawa Mamah tsawa ne yasa Mamah yin magana cikin raunin murya tace.

"A lokacin kin ce mana tsintacciyar mage bata zama mage."

"Masha Allah gashi nan kun gama wahala kun rufa mata asiri yanzu ta watsa muku ƙasa a ido. Ke kuma.." Hajiya ta faɗa tana nuna Iman da hannu.

"Kin zama butulu, tunda kike tsawon rayuwarki kin taɓa sanin cewa ke ba jininsu bace? Kakaf dangi kin taɓa ganin wanda ya musgunawa rayuwarki? Ko yanzu ma da suka aura miki Al-mustapha, sunyi ne saboda su ƙara rufa miki asiri ba wai kansu suka rufawa ba. Abinda ya faru da shi akan waccen yarinyar ba zai sa su baki shi ba dan shi namiji ne, mace itace abar tsoro idan ta tsinci kanta a hanyar lalacewa. Aure kuma an riga an daura miki da Al-mustapha sai kiyi wa Allah godiya."

Ai Hajiya na ƙarasa magana Iman ta faɗi a gurin tana kuka tana ce musu.

"Wallahi Yaya Jamil nake so, koda ni bani da asali shine zaku aura min wanda ya lalace? Saboda bani da gatan da za'a barni na zabi wanda nake so shine za'a yi min auran dole? Wallahi bazan zauna dashi ba, Jamil shine sirrin zuciya ta, shi kuma nake s...."

Bata kai karshe ba taji saukar mari a gefen fuskarta, wanda yai sanadin fashewar gefen bakinta jini ya fara fitowa. Haneef ne yai mata wannan marin wanda kalamanta ya sosa masa rai da zuciya.

"Har yaushe kika zama marar kunyar da zaki dinga gayawa mutane magana? Shi Jamil ɗin sa'anki ne da zaki ce shi kike so? Ko yace yana sonki ne? Ke kika kawo shi gidan? Toh koshi yanzu muka gama magana ya tabbatar min da cewa be taɓa furta miki wata kalma ba da ta danganci soyayya. Kyautatawar da yai miki a baya ya yi ne saboda abu uku. Na farko saboda ni, na biyu gudummawa ce ta kammala karatunki, sai na uku darajar sunanki Khadija wanda sunan mahaifiyar shi ne. Idan kina tunanin sonki yake maza ki gaggawar cirewa daga cikin zuciyarki."

Ta shiga kaɗa kai hawaye yana ta zirarowa daga cikin idanunta, a yadda take jin zuciyarta akan Jamil, kome za'ai sai dai ayi amman tabbas ba zata fasa auransa ba. Ji take ko zasu gutsira ta gunduwa-gunduwa sai ta mallaƙeshi kamar yadda zuciyarta ke muradi. Nan fa aka shiga maganganu kowa da abinda yake faɗa. Ita kuwa tana durkushe a tsakiyar falon babu wanda yake yi mata maganar arziki saboda wannan lamarin.

"Saboda Allah kuka yi min komai, dan haka shine zai baku ladan abinda kuka yi min tsawon shekaru. Amman wallahi zuciya ta tana son Yaya Jamil, me yasa ba zaku bani shi ba? Dan Allah ku fahimceni ku gane manufar zuciya ta kuyi min adalci nima." Cewar Iman tana sake fashewa da kuka.

"Tashi ki bawa mutane guri marar mutunci kawai." Hajiya ta faɗa cikin ɓacin rai.

Da sauri ta tashi tare da rugawa hanyar waje zata fice suka yi kiciɓus dasu Areef, besan ita bace hakan yasa shi riƙota ganin zata faɗi ƙasa. Sai da ta ɗago kai suka kalli juna cikin ido, sannan dukkansu sukai saurin janye jiki. Kallon-kallo suka shiga yi kowa da abinda yake saƙawa a rai.

"Ke kuma sai ina?" Uncle Imran ya tambayeta. Wani uban tsaki Iman taja tare da raɓasu zata wuce Areef yai saurin damƙo wuyanta, zafin ransa ya motsa ya shaƙota yana cewa.

"Waye tsaka anan gurin?"

"Sakar min wuya na."

"Anki a saki sai kin fadi ubanwa kike yiwa tsaki."

Ganin yana niyar illatata gashi babu wanda yai yunƙurin kwatarta yasa tasa baki tare da gartsa masa cizo.

"Ahhhh....!" Ya kwalla ƙara saboda cizon ya shigesa sosai.

Yana sakinta ta falfala a guje tayi sashen su Haneef tana kwalawa Jamil kira.

"Anya yarinyar nan tana cikin hayyacinta kuwa?" Mamah ta faɗa dan taga abin yayi yawa.

"Me kike zato Hawwa?" Hajiya ta tambayeta.

"Iman yarinya ce mai jin magana, nayi imani bawai auran da aka yi mata ne yasa ta zama haka ba. Kuna ganin bata ta magana sai ta auren? Yaushe suka saba da shi da har za'a ce sun fara soyayyar da zata sata wannan birkecewar?"

"Babu wani abin da yake damunta banda iskanci da kuma butulci." Hajiya ta sake faɗa cike da tabbaci.

Shigar su Areef cikin falon ne yasa idanu ya koma kansu. Cikin sauri ya sunkuyar da kai yana kallon ƙasa ganin yadda Mamah ke binsa da wani irin kallo. Hajiya ce tace.

"Kaga abinda yarinyar nan take yi ko?" Areef beyi magana ba sai uncle ne yace.

"Wace yarinyar ce?"

"Iman mana, marar mutunci mara kunya. Wai auran ne bata so ita Jamilu take so."

"Jamilu kuma? A ina yake? Saurayinta ne ko kuwa?" Ya tambaya dan shi bema san da zamansa a gidan ba.

"A'a babu ko ɗaya Imrana, Sa'idu (Haneef) ne yazo dashi gidan nan. Shine wai shi take so, tsabar batada kunya ma cewa tayi wai a rasa wanda za'a bata sai ɗan iska, wai Areefullah ne ɗan isa ita wayasan ƴar mecece?"

Areef najin haka yai saurin dago da kai yana kallon Hajiya dake ci gaba da bayani. Ya sake maida dubansa gurin Mamah still yaga bata cikin yanayin da zai iya yin magana.

"Yaron da iyayensa suka rufa mata asiri tun tana tsumman goya, suka kula da rayuwarta shine yau take kallon kwayar idanuwansu tana cewa jinin su ɗan iska. Kai amman dai yarinyar can bata da kirki bare mutunci."

Areef ya sake kallon Hajiya yana zaro ido. 'Kenan shine ɗan gidan? Shi suka haifa ba Iman ba?' Wani irin farin ciki ya mamaye ilahirin zuciyar shi, sai kawai gani akai ya durƙusa a gurin yayi sujjada. Su Irfan da Aslam suka dinga murmushi dan sun tabbatar farin ciki ne ya mamaye shi jin cewa Mamah itace mahaifiyar shi.

"Kai kuma lafiyarka?" Duk suka tambayeshi.

"Daɗi yake ji shine asalin ɗan gidan, da kuka yake tayi Hajiya yana cewa ya shiga uku shi ba ɗan Mamah bane." Aka saki dariya ana yi masa tsiya be ce komai ba sai gurin Mamah da ya nufa.

"Ki yafe min Mamah bazan sake ba."

"Tashi kaje anjima zamu yi magana."

Tashi yayi yana shafa ƙeya saboda har lokacin kunyarta yake ji. Daga nan dakinsa suka shiga shida su Aslam Yaya Haneef da Uncle da wasu mazan suka nuna fi inda Iman ɗin ta shiga. Daman tana zuwa ta tarar da ɗakin a buɗe ta shiga da sauri tana neman Jamil. Shi kuma yana ɗakin bacci yana waya da malaminsa yajiyo ta yai saurin tashi ya fito. Kallen ƙofar yayi ko zai ga an biyo ta yaji shiru hakan yasa shi janyo mata hannu suka shiga cikin inda ya fito.

"Menene."

"Karka barni a gidan nan, dan Allah ka tafi dani inda zakaje." Jamil ya lashi leɓansa tare da shafa kwantaccen sajensa yace.

"Zan tafi dake, nima ai bazan iya barinki a nan ba. Kina sona ko?" Ta daga masa kai da sauri.

Ya saki murmushi tare da janyota jikinsa ya rungume. Iman ta dinga sauke ajiyar zuciya tana sake kwantar da kai a cikinsa.

"Daman nasan ke tawace, dan haka babu mahaluƙin da zai rabamu domin asiri gaskiya ne."

Tana jinsa sai dai bata wani gane komai idan ba son da zuciyarta keyi masa ba. Ya dago mata kai suka kalli juna ya sake sakin wani shu'umin murmushi tare da cewa.

"Duk wanda ya yi gigin shiga tsakanin mu sai naga bayansa. Karki damu ke tawace ina matuƙar sonki."

Jin muryar su Haneef ne yasa saurin kabbara sallah. Su kuma ganin babu kowa a falo yasa su ƙarasawa ciki. Iman na tsaye a kusa da Jamil wanda yakai ruku'u yana kuma satar kallon su.

"Zoki bar ɗakin nan." Uncle ya faɗa.

"A'a." Ta faɗa tana matsawa baya.

"Kambala'i, a'a fa kika ce? Toh wallahi sai kin bar ɗakin nan marar mutunci."

Haneef ya faɗa yana kai hannu sai fizgota, tayi saurin rarimo Jamil da ya nuna dagaske sallah yake yi. Yadda ta kankamesa ne yasa shi yin sallama cikin tashin hankali ya fara.

"Innalillahi ya haka? Ke Iman sakarni mana meye haka ne?"

"Dan Allah karka bari su rabamu Yaya Jamil, nashiga uku zasu kasheni wayyo Allah."

Haneef yasa karfin sa ya fizgota tare da turata wajan ƙofa, su Uncle Imran suka riƙeta suna ja tana tirjewa. Kallon Jamil Haneef yai tare da furzar da wata iska daga bakin sa yace dashi.

" Ka shirya gobe mu wuce kawai, yarinyar can so take ta janyo mana matsala." Haneef na kaiwa nan yabi bayan su Uncle, suka bar Jamil da zare ido jin zasu tafi gobe-goben nan.

Da sauri ya koma ciki ya lalibo wayarsa yana kiran Malam, sai dai ana ta shaida masa cewa not rechargeable haushi da bakin ciki suka sashi buga wayar da ƙasa ta kuwa fashe a take.

Ita kuma Iman suka maida ita cikin ɗaki suka kulle a cewar Haneef gobe idan sun tafi a fito da ita asan abinda ya kamata. Koda Abba ya dawo daga asibiti aka labarta masa abinda yake faruwa kasa cewa komai yayi saboda ji yake tamkar kansa zai buga tsabar tension ɗin da ya shiga a ranar.

Jamil kam da kyar ta iya control ɗin kansa yadda Haneef ba zai gane komai ba. Ya shirya kayanshi tsab sai dai ya sanarwa da Haneef ɗin cewar shi ba Lagos zai koma ba Zamfara zai je daga can zai tafi Lagos ɗin.

Da sassafe kuwa suka je sukai sallama da mutanan gidan, har kuma suka tafi basu saka idanuwan su akan Iman ba. Jamil kuwa shi kadai yasan abinda yake kitsawa ransa na yadda zai dawo ya sace Iman.

_________

Riƙe take da allo irin wanda almajirai ke karatu dashi, a jiki anyi rubutun arabi suratul Aa-ala ce take ta biyawa a hankali. Sanye take cikin wasu riga da zani koɗaɗɗu na wani shuɗin lace da yasha jiki ya san anyo shi cikin duniya. Malam Ɗalha dake riƙe da bulala ya tsula mata a baya tare da cewa.

"Abuɗe baki ayi karatu."

Nafisa tasa hannu tana sosa gurin, cikin zuciyarta tayi masa Allah ya isa tafi biyar. Tunda Daddy ya kawota wannan kauyen take jin tamkar an ɗaure mata jijiyoyin jikinta. Daddy ne da kansa ya kawota gidan malamin yace a horata yadda hora almajirai. Ya kuma shaidawa malamin cewar zai dinga biyansa albashi mai tsoka.

"Nafisa ki bada himma fa, kinga kina da kokari gashi nan kin kusa haddace izifi guda daga zuwanki. Kiyi maza ki haddace wannan mu shiga wata kinji ko?"

Cike da takaici ta amsa masa ta kuma sake rungume allonta tana biyawa. Duk da haka bata daina tunanin ina Areef yake ba, me yake yi a wannan lokacin? Shin da gaske ne kalaman Iman na cewa anyi masa mata? Ko kuma wasa take yi suna so ne kawai su raba tsakaninta da shi?

"Ke Nafisatu bakiji me nace ba?"

"Malam kayi hakuri, banji ba."

"Cewa nayi ki shiga cikin gida Ta Annabi na jiranki zaki yi mata tatar koko." Feenah tayi shiru tana haɗe rai.

"Bazaki tashi ba kenan, ƴan taurin kan sun motsa ko?"

Bata kulashi ba ta mike ta shiga tana hawaye. Daga shi har matarsa sun matsawa rayuwarta tunda aka kawo ta. Tana shiga kuwa Ta Annabi ta nuna mata gurin wanke-Wake tare da nuna mata bokitin markaɗe tana cewa.

"Fara yin wanke-wanken can Nafisa, idan kin kammala sai kiyi tatar."

Feenah tayi murmushin bakin ciki tana gyada kai ta dauki bokita, wajan rijiya ta nufa ta janyo ruwan da zata yi wanke-wanken. Gidan iyayenta bata yi ba saboda suna da tsohowar dake yi. Gidan Sultan da tayi aure babu

14 / 38