Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   23 / 38

66K to 69K   out of 113.7K words

su Abba ana cikin kuɗi kinga yadda yake jaddadawa mutum cewa ko nawa ne yana so a samar miki a wannan shekarar."

"Allah sarki Abba na, Allah ya saka masa da alkairi yasa su rabu da Hajiya lafiya. Wallahi I really love him."

"Mu kuma fa?" Cewar Ikram tana tabe baki.

"Uhmmm! Toh kuma haka, but Abba da Mamah na dabban ne a cikin zuciyata." Ikram tayi murmushi kawai ta shige toilet. Murya a sanyaye Iman tabi toilet ɗin da kallo tare da cewa.

"Yaya Areef ma yana neman ya zame ya canza min lissafin rayuwa, bayan shi yana can yana rayuwarsa."

"Magana kike?" Iman ta jiyo Ikram daga cikin bandaki tana tambayarta. Kin magana tayi da sauri tabar ɗakin dan karma ta fito ta ganta.
_________________

Cikin ƙanƙanin lokaci Iman ta samu gurbin karatun lafiya, su kuma su Ikram suna can BUK. Jabir kuwa tun randa ya ɗakko Iman a garin Abuja yabi ya tsangwami rayuwarta, be kuma zo da wasa ba domin labarin sakin da Areef yayi mata duk ya baza gari, ita kuwa abinda yake ɓata mata rai baya wuce taji ance Areef ya saketa, duk lokacin da taji kalmar sai taji tamkar a lokacin yake furta mata ita. Gefe guda kuma cikin zuciyar wani marayan abu ne yake neman fin karfin duk akan Areef, tunaninta da hankalinta, ta yadda bata yadda ta kula kowa, shine yake mamaye a ranta. Jabir ma tashi sanar dashi cewar ita tana da miji amman yaki hakura, sai kashe mata kuɗi yake yi kamar babu gobe.

Ganin tana neman bashi matsala ne yasa shi tarar Abba da maganar. Kai tsaye Abba ya sanar da Jabir gaskiyar abinda suka sani akan Iman, ya ɗora da cewar.

"Ba auranka da Iman ne bama so ba, ranar da zaka gama cin moriyarta a karshe ka wulakanta mana ita."

"Babu wannan mafarkin Abba, zan auri Iman a duk yadda Allah ya tsara mata rayuwa. Kuma iyayenta ma zasu bayana ko ba yanzu ba indai suna raye a doran kasa." Cewar Jabir dan bashi da buri irin yaga ya mallaki Iman a matsayin mata.

"Shikenan idan har tana sonka ai babu wani matsala mu farin ciki zamuyi." Jabir yayi murmushi yana ta faman sadda kai ƙasa.
___________

Tunda Abba yayi mata maganar aure daman itama Hanan Allah ya taimaketa wanda take masifar so ya waiwayota da addu'a da kuma barwa Allah zabi ta hanyar yin istihara yace zai kawo kuɗi, dan haka Abba ya sanar da Iman idan har tana son Jabir tayi magana a haɗa a aurar dasu lokaci guda. Iman ta dauki maganar wasa har Abba ya karbi kudin auran Jabir aka tsaida lokacin aure watanni biyar kafin azumi.

Karatunta kawai take hankali kwance, duk da baƙaƙen maganganun da Areef yake yaɓa mata akan halittarta, ta kasa cire shi a rayuwarta. Wata rana ta dawo daga makaranta mai napep ya sauketa ta bashi kudinsa. Wasu mutane dake tsaye a wajan wata farar bus suka tsaida ita suna tambayar ta.

"Gidan Alhaji Ahmad muke nema." Ta kallesu ɗaya bayan ɗaya cike da mamaki dan bata taɓa ganinsu a gidan ba, ganin suma ita suke kallo yasa ta ɗan yi murmushi tare da cewa.

"Gashi nan gidan mu ne ai."

"Ahhh masha Allah suna ciki mutanan gidan?" Cewar wata dattijuwa da zata kai shekaru tamanin a duniya.

"Eh toh gaskiya bazan ce ba saboda nima yanzu na dawo daga makaranta. Kuzo muje daga ciki."

"Masha Allah kema ƴar gidan ce kenan?" Tsohowar ta kuma tambayar ta.

"Eh." Cewar Iman tana gyara rikon jakarta.

Kusan su goma ne mata shida maza huɗu, haka suka bi bayan Iman riiiii kai daga ganin su kansan ƴan asalin qauye ne, duk sunyi fururu dasu daurin zani kuwa sai wanda ya gani. Mazan suka tsaya a parking lot matan kuma suka bita har cikin gidan bakinsu ɗauke da sallama. Suna kokarin zama a ƙasa Iman tace su hau kujera amman sukaki haka ta kyalesu, Mamah ta fito daga ɗaki tana amsa sallama da suke yi.

"Baki ne yanzu suka ce nan gidan suke nema." Cewar Iman tare da wucewa ɗaki. Mamah ta samu guri ta zauna suka shiga gaisheta.

"Sai dai ban ganeku ba wallahi daga ina?"

"Ai gaskiya daman ba zaki gane mu ba tunda bamu taɓa ganin juna ba. Yau ma Allah ne ya yanke hukuncinsa har muka samu damar zuwa." Cewar dattijuwar cikin su.

"Haka ne Toh Allah ya kara taƙaitawa." Duk suka haɗa baki wajan cewa.

"Amin.. Amin Hajiya."

"Toh da yake dai bamu kadai muka zo ba, akwai maza suna daga waje, idan babu damuwa dai muna so harsu a hadu guri guda ayi maganar da ta kawo mu gidan nan." Wata mata ta faɗa wacce a shekaru ba zata girmi Mamah ba.

"Toh akan me za'a tattauna na faraji ko?"

"Ehhh Toh daman ba akan komai bane sai wata jaririya da aka taɓa ajiyewa tsawon shekaru a ƙofar gidan nan..."

Daram!.. Dam!!.. Dam!!! Zuciyar Mamah ta dinga wani irin harbawa, kadan ya hanata ragargajewa saboda yadda maganar ta bugeta. Ita kanta Iman da ta nufi kitchen dan kawo musu ruwa, tana jin abinda suka faɗa tayi saurin fitowa ta tsaya tana kallansu.

"Amm.. Amman taya kuka san wannan labarin?" Cewar Mamah bakin ta yana kyarma tamkar wacce ta yiwa sarki karya.

"Ai kuwa mune asalin dangin yarinyar, an kuma tabbatar mana da cewar har zuwa yanzu tana raye kuma a cikin wannan gida da muke yanzu." Cikin kaduwa Mamah tace dasu.

"Amman tayaya zan tabbatar da cewa kune asalin danginta? Sannan wane dalili ne Yasa kuka watsar da rayuwarta tun tana cikin tsuman goyo ko cibiyarta bata gama warkewa ba?"

Wata daga tsakiyarsu ta ɗan juya tare da nuna wata mata da bazata wuce shekaru talatin da biyu ba, dafa kafaɗarta tayi tana kuma kallon Mamah tace.

"Wannan da kike gani itace mahaifiya ga jaririyar, shi yasa muka ce miki ki bada izini mazan su shigo ko kuma mu mufita zuwa gurinsu idan baku so maza su shigo ɗakin, maganace mai muhimmanci wace idan da hali ma zamu iya zuwa kotu dan a tabbatar da wannan maganar." Jikin Mamah yai mugun sanyi, a hankali ta juya ta kalli Iman wacce ta kurawa matar da aka ce itace ta kawota duniya ido.

"Kawo musu ruwa da lemo Iman." Cewar Mamah tana kallonta. Iman batace komai ba sai juyawa da tayi jiki a sanyaye ta dakko tray ta daura lemukan akai. Mamah tace dasu.

"Shikenan aje ace mazan ma su shigo daga ciki babu matsala." Wata a cikin su ta miƙe taje ta kirawo su, a lokacin Iman ta kawo ta ajiye musu, ta koma jikinta duk babu kwari ta zubo musu abinci jallop macaroni da tasha naman zabo. Suka gaishe da Mamah bayan sun samu guri sun zauna.

"Ku fara cin abinci ku gama kafin sannan mai gidan ya dawo sai a tattauna." suka sake amsawa gabaki ɗayan su.

Tashi tayi tana kiran Abba a waya tana magana har ta shige cikin ɗakinta. Iman kuwa a kitchen ta samu guri ta rakube, tunani barkatai babu wanda baizo mata cikin rai ba. Tayi zaton idan ta tashi ganin mahaifiyarta zata ganta irin mai buɗaɗan idanuwan nan, wacce za'a ce tana sane tayi cikinta har ta haifeta. Kenan yanzu wannan itace ta haifeta? Mace kamila, nutsatsiya wane tausayi yaja mata haifo abinda za'a yar? Da ta kalletafa taga suna ɗan yanayi, musamman hancinsu da wajan girarta.

Tana jiyo su suna hirar gidan wai gidan ƴan gayu ne, suna ta nune-nune baga mazan ba baga matan ba, tiffical ƴan kauyen ne gabaki ɗayan su. Suna nan kuwa sai ga Abba shima cikin fusata, dan cewa Mamah yayi karya ne shiri ne kawai siyo su akai aka biya za'a zo a raina musu hankali.

Sama-sama ya amsa gaisuwar su ya kira Mamah ta fito a lokacin su Ikram sun dawo daga makaranta suma. Duk aka zauna a falon, wacce ake nunawa a matsayin itace mahaifiyar Iman sai sharar hawaye takeyi da kasan mayafinta, Allah-Allah take a nuna mata ƴar tata duk da cewa tun gamuwarsu da Iman take jin bugun zuciyarta na sauyawa. Amman tana ta hana zuciyar ta amincewa, tafi son a nuna mata ace wannan ita aka tsinta a cikin su Ikram, Iman da kuma Hanan. Zatafi jin daɗi da kwanciyar hankali.

"Muna jinku, taya zamu yarda da abinda kuka ce?" Malam Bello ya kalli Abba cikin serious ɗin shi yace.

"Nine nan mijin Habiba, gatacen a zaune, kuma itace mahaifiyar jaririyar da aka ajiye a ƙofar gidanka, an tabbatar mana da cewa Kaine ka dauki ƴar tana kuma hannunka har zuwa yanzu da muke wannan maganar." Yaja numfashi tare da saukewa yaci gaba da magana.

"Bani ne mijin Habiba na farko ba, mijinta na farko sun rabu sanadin makirci irin na kishiya. Tunda yai aure bai taɓa haihuwa ba tsahon shekaru ashirin da biyu, sai Allah ya kaddara rabon a jikin Habiba yake ya ganta ya aure ta. Tunda labarin cikin nan ya bazu shikenan Habiba bata kara lafiya ba, dalilin da yasa mijin ya dawo da ita gida akan a kula da ita har Allah yasa ta haihu. Kullum bawan Allahn nan yana tafe zuwa duba ta har zuwa lokacin da Allah ya sauketa lafiya.

"Tun randa aka sanar dasu cewa Habiba ta sauka ta samu ɗiya mace, shikenan hankalin uwar gidanta ya tashi, saboda sunyi-sunyi tun tana da ciki ya lalace Allah beyi ba sai da ya fito dashi duniya. Mijin Habiba yazo yaga ƴar yayi mata huduba da suna Khadija, wanda a yadda aka sanar damu ance an rubuta sunanta a jikin kwali an sa mata a cikin rigarta, da nufin duk wanda ya tsinceta yasan cewa an raɗa mata suna. Toh mu dai tunda yai hudubar nan bamu sake ganin sa ba har ana jibi suna, a dai dai gabar ne kuma aka sace jaririyar sama ko kasa aka nema aka rasa. Ashe-ashe kishiyarce tayi surƙullenta ta raba tsakanin Habiba da mijinta, sannan ta yi sanadin barin jaririyar daga Nonon mahaifiyar ta. Habiba na zaune cike da tashin hankali ya aiko mata da takardar saki uku.

"Ni na aureta muka yi auran zumunci, saboda babana yayan babarta ne, har yanzu kuma muna tare da zuriyar da Allah ya bamu. Satin baya ne Allah buwayi mai yaye bakin ciki zuwa farin ciki ya karya duk wani makirci da aka yiwa su Habiba, kunga waccan." Yayi maganar yana nuna wata a cikin su.

"Gata can a rakube." Ya shiga nuna ta, tun zuwan su daman bata da sukuni yace.

"Itace ta sace Khadija, ta kuma rasa inda zata kaita, Allah ya kawota ƙofar gidan nan ta direta ba tare da kowa ya ganta ba, tayi hakan ne akan kuɗin da aka bata dubu uku."

Girgiza kai Abba da Mamah suka dinga yi saboda mamaki, kasa hakura Abba ya yi sai da yace.

"Yanzu ke baiwar Allah ina dubu ukun da aka baki take yanzu?" Tayi shiru tana ta muzurai yaci gaba da cewa.

"Kinsan bakin cikin da kika sanya bayin Allahn nan kuwa? Ita kanta yarinyar kin cuceta kin hanata samun damar shan Nonon uwa mai cike da albarka. Kiji tsoran Allah ki tuba ki nemi yafiyarsu dan wallahi kin cutar dasu. Allahu Akubar, hakika munji daɗi matuƙa da Allah ya bayyana ku a dai dai wannan gaɓar domin kuwa Allah ya kawowa Khadija mijin aure, har an sanya lokacin biki ita da ƴar uwarta."

Gabaki ɗaya suka ruɗe da farin ciki duk da cewar har lokacin basu san waccece Khadijan tasu ba. Sai da Kawu Sule yace.

"Toh gasu nan dai reras dasu Tubarkallah, waccece Khadijan a cikin su?" Cike da farin ciki Abba ya juya yana kallon yaran nashi, murmushi yaki barin saman fuskarsa yace.

"Zo nan Iman." Ta miƙe hawaye suna fitowa daga can cikin zuciyarta, ta isa gurinshi jiki babu kwari. Hannunta ya riƙe yana murmushi yace.

"Gatanan, wannan itace Khadijatul Iman, jeki gaisa da su." Kamar jira take a bata umarni, jikinta sai rawa yake yi ta ruga da gudu ta nufi gurin mahaifiyarta.

Kuka suka saki a lokaci guda tare da ƙanƙame junan su cike da so. Duk gurin aka saki dariya, yar Dattijuwar ce tace cikin barkwanci.

"Shine ni bakizo kin fara gaisheni ba kika tafi gurin mahaifiyarki?" Suka yi dariya baki ɗaya falon. Ikram da Hanan kuwa ji suke tamkar sune a cikin wannan farin cikin, sai faman washe baki suke yi suna kallon yadda Iman ta riƙe mahaifiyarta.

"Kukan ya isa haka Habi, farin ciki zakuyi ba kuka ba." Daga nan hira ta ɓarke Abba kuma ya sanar da su auranta da Areef, sam basu ji daɗin yadda abubuwan suka faru ba, a karshe dai suka bar abin kan cewar nufin Allah ne, domin duk sanka da abu indai Allah yayi nufin kwacewa sai ya rabaka dashi, bare kuma al'amarin da aka haɗa da asiri, tunda gashi kiri-kiri aure babu tsakanin mahaifiyar Iman ɗin da kuma mahaifinta..........

(Rangen! 💃Rangengen!! 💃💃Iman congratulations 🎊 🤸‍♀?)

*ZO GARENI yana cikin tawagar Top 10 ki biya kafin ki karanta daga page 11. Zaki iya tuntuɓar wadannan. +447894142004 ko kuma 0706 528 3730*









*HAJJA CE 👈*
3/11/22, 23:58 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*

*29*



Hira tayi daɗi ga iskar fanka kasancewar an kawo nepa, baki sun manta da komawa kauye an baje ana ta labari kai kace sun saba da juna. Iman dasu Ikram sun koma ɗaki suna tasu hirar cike da mamakin yadda abubuwa suka faru. Daɗi da farin ciki kuwa yaki barin zuciyar Iman, ko banza tafi karfin wulakanci a gurin Areef tunda zargin da yake yi ba haka bane.

Sai kusan karfe takwas na dare lokacin sunyi sallar isha sunci tuwon semoviter suka fara shirin tafiya. Mamah ta kwaso kayan da take ganin zata bayar ta basu, tsohuwar kuma ta bata kuɗi tace ta sai goro. Mahaifiyar Iman tana jin tamkar tace a bata ƴar ta, sai dai tasan yadda Iman tayi rayuwa a wannan gurin ba zata iya rayuwa a kauye ba, yarinyar wayayyace ƴar gayu musamman harkar karatun lafiyar nan da take yi ta sake zama wata ta musamman.

"Zamu zo Insha Allahu tunda kun gaya mana kauyen, idan sun gama jarabawa zamu zo dukkan mu, amman kafin lokacin ni zan fara zuwa naga guri." Cewar Abba bayan sun fito yi musu rakiya.

Iman da mahaifiyarta suna jere amman babu mai cewa kowa komai, ita mahaifiyar ta harda alkunya na ƴar fari ba zata zame wajan yin magana da ita ba. Yayin da Iman kuma rashin sabo yasa ko uffan bata iya cewa duk kuwa da zuciyarta na son yin magana. Shiguwar mota ƙofar gidan yasa duk suka zuba ido dan ganin ko waye a ciki.

Jabir ne yazo gurin Iman cikin wata narkakkiyar shadda sky blue yasha babbar riga tamkar ranar ce ta daurin aure. Gaskiya Tubarkallah Jabir yana da masifar kyau fiye da yadda alƙalami sai rubuta. Cikin sauri ya ƙaraso wajan Abba ya shiga gaida shi sannan ya gaishe da sauran. Abba fuska cike da walwala yace dasu kawu Sule.

"Wannan shine sirikinku, wato wanda zai auri Khadija." Ai duk sai suka ware idanuwa suna kallansa. Shi kuma ya sunkuyar da kai yana ɗan murmushi. Baba Sunusi ya dinga kallon shi cikin wani irin yanayi, Jabir yai saurin ɗagowa jin tamkar ana yi masa kallon kurullah, aikuwa suka yi idon huɗu da Baba Sunusi wanda hakan yasa Jabir komawa cikin mota sa sauri.

"Alhaji kace wannan shine zai auri Khadija?" Abba ya kalli Baba Sunusi cike da murmushi yana cewa.

"Shine malam." Baba Sunusi ya girgiza kai yace.

"Wannan ba asalin mutum bane ba, gashi nan ruhina da nashi sunki haduwa, tabbas wani mutum ne aka yi masa suffa irin wannan ta hanyar yin amfani da aljanu."

Kafin kace menene Jabir ya koma asalin Jamil, yana ta kokarin tada mota dan yasan yau duk wani shiri nasa ya ruguje, su Abba sukai saurin kallon motar ya kuwa jata da karfin masifa har yana buɗe su da kura. Iman kuwa zubewa tayi a gurin saboda mamaki da al'ajabin tana mu'amala da aljani ba tare da ta sani ba.

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, malam na kasa fahimtar abinda kake son sanar dani, ta ya za'ai ace Jabir ba mutum bane bayan komai nashi na mutane ne?" Cewar Abba da gabaki ɗaya kanshi ya fara juyewa saboda tsabar mamaki.

"Tunda kaji ya faɗi haka tabbas hakane domin yana da mutanan ɓoye da suke ganin junansu. Indai kaji ya faɗi abu to hakan yake." Cewar kawu Sule. Suma sauran ƴan uwan suka tabbatar da zancen kawu Sule dan su ko a kauyen su Baba Sunusi kowa yasan shi da harka da aljanu.

"Yakamata ku kwana a garin nan dan Allah, saboda akwai abubuwa da yawa da suke faruwa a tare damu, musamman ma kuma ita Iman ɗin. Ku tsaya muyi magana sosai gobe sai ku tafi." Abba ya faɗa cikin lallashi.

"A'a tafiya zamu yi gaskiya, saboda bamu sanar da Cewar zamu kwana ba."

Abba da Mamah suka dinga yi musu magiya amman fur suka ce bazasu kwana ba tafiya zasu yi. Sai Baba Sunusi ya ciro wani abin wuya tamkar azurfa ya bawa Abba yace a sakawa Iman a wuyanta da izinin Allah duk wani sharrin aljani ba zai dosheta ba. Tun a gurin ya mikawa Mamah taje ta saka mata, cikin sanyin murya mahaifiyarta tace.

"Kina addu'a kuwa?" Iman ta gyada kai, mahaifiyar ta sake cewa.

"Bakya yi sosai ki dage yanzu ki dinga yi domin asiri gaskiya ne, hakama aljanu gaskiya ne, sannan addu'a itace maganinsu, karki ce ai kinyi-kinyi amman Allah be amsa ba, kici gaba domin addu'ar mumini bata faduwa ƙasa sai Allah ya amsawa bawansa."

Iman ta amsa cewa zata dage, indai har aljani zai iya yin wannan shigar lallai zai iya yin komai a gareta ba tare da tasani ba. Suka shiga mota su Abba na ta yi musu fatan sauka lafiya. Gida suka koma cike da al'ajabin Jabir, yadda yazo musu cikin kamala da girmamawa ashe ashe bana tsoran Allah bane. A ranar da abu biyu ahalin gidan suka kwana, farin cikin ganin dangin Iman, da takaicin ɓata musu lokaci da Jabir ya yi, dan ma basu san cewar Jamil bane.
_______________

Kasan cewar son karatun a jininta yake, hakan yasa duk da tana cikin damuwa da tsoro bata fasa maida hankali ba. Suna ta shirye-shiryen fara jarabawa ta dawo gida a gajiya ga ciwon kai da yake addabarta, tana

23 / 38