NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR8iiiii KDAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 11:19 - Buhainat: *ZO GARENI....*
Free page 8
NA
*HAJJA CE 👈*
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*💡
Areef ya sauke wayar daga jikin kunnansa duk da cewa yana jinta tana magana. Gefen gado ya zauna tare da dafe kansa dake barazanar rabewa gida biyu. Yana ganin ta katse yai saurin kashe wayar gaba ɗaya kafin ya fito zuwa parlor inda su Mamah suke zaune.
Cikin takaici ya harari Iman wace ke faman gyara kai akan cinyar Mamah yace.
"Ke jeki ɗebo min abinci."
Duk sukai masa banza, haushi ya kuma kamashi, ga tunanin Feenah da ya addabe shi yana tsoran kar ya ganta a cikin gidansu.
"Wai ba zaki tashi ba ne kina jina?"
Wannan karan a hasale yai managar kuma kamar zai kai mata duka.
"Dawa kake ne wai Areef?" Cewar Mamah.
"Gatanan sai wani danne miki ƙafa take yi kamar wata ƙaramar yarinya."
"Lahhhh... Kaji Yaya Areef! Wai dani kake? Yo ni ai ji nayi kace ke. Gaskiya Yaya Areef ka dinga kiran sunana meye amfanin sa tsakani da Allah fa." Iman tai maganar tana turo baki tare da mikewa ta nufi kitchen.
"Anƙi a kira sunan naki, ke naga damar cewa." Ya faɗa cikin hasala dan tana mugun ɓata masa rai.
Plate guda haka ta ciko shi da farar shinkafa sannan ta zuba miyar akai tare da salad da tumatur da albasa, hadin dai sam babu tsari a yadda ake shiryawa namiji abinci.
Ita kuma tayi ne da gayya saboda har lokacin haushin fifita budurwarsa akanta take yi bata huce ba. A gaban sa ta dire bata tsaya ba ta nufi fridge shi kuma ya dinga kallon plate ɗin yana kallo inda take tsaye zata dakko masa ruwan sanyi.
"Mamah dubi yadda yarinyar nan tai min. Sai kace ta zubowa gardin kauye." Su Hanan suka tuntsure da dariya bayan sun kalli abincin gabansa.
"Kai ma dai Areef ka fiye matsala, tunda ko daban-daban aka yoma hakan zaka yi meye kuma na magana? Dan Allah kaci kawai bana son dogon bayani."
Ransa ya kuma ɓaci a ganinsa an sake bata damar gobe ma tayi irin haka. Cikin fushi ya miƙe yayi hanyar ɗakin shi Mamah ta kira sunansa.
"Areefullah."
Ya tsaya cak tare da rintsa ido saboda zuciyar shi da yaji tana tafasa kamar zata ƙone dan zafi.
"Ina kuma zaka?"
Cewar Mamah dan tana son tabbatar da abin da yake ranta game da tashin da yayi.
"Na ƙoshi."
Taji ya faɗa tare da saurin shigewa ɗakin ya rufe.
Numfashi Mamah ta sauke tare da bin Iman da harara, cikin faɗa take mata magana.
"Baki da kunya Iman, daman haka ake zuba masa abinci? Ko idan kawayenki sunzo zaki iya basu abinci a haka? Bana son raini da wulakanci, naga kin fara raina Areef da yawa, ki shiga taitayinki kinaji ko?"
Jikin Iman ya yi sanyi jin yadda Mamah ke ta yi mata faɗa. Kwashe kayan tayi ta mayar kitchen ta rufe sannan ta dawo ta zauna, wannan karon duk hirar da ake yi bata cewa komai har Abba ya dawo sukai masa barka da dawowa suka bar parlorn zuwa ɗakin su.
A ɓangaren Areef kuma wanka ya shiga yana yi yana tuno yadda Feenah ke narkewa a jikinsa tamkar wata matarsa. Ya shiga tambayar zuciyar shi akan hukunci da kuma kamatuwa da hakan tsakanin su, wani ɓarin ya zuga shi wani kuma ya nusar dashi rashin kyautawa. Sai dai mai zugar yafi tasiri a zuciyar shi domin yafi ƙawata masa jin daɗin dake cikin yadda yake mu'amala da Feenah.
Yana fitowa ya zura kananun kaya ya sako takalmi ya fito fuska babu yabo babu fallasa.
Besan Abba ya dawo ba, saboda ko muryarsa beji ba hakan yasa shi zuwa zai wuce dan ƙin kallon parlorn yayi, jin an kira shi yasa shi saurin juyawa ya kalli inda sautin kiran yake. Ai kuwa da gaske Abba ne, Allah yasa dai ya manta da ganin motar da yayi. Ya ƙarasa kusa dashi yana masa sannu.
"Abba sannu da dawowa."
"Yauwa Areefullah kana ciki kenan?"
"Eh Abba ina ciki tun ɗazu."
"Fita zaka yi ne?" Abba ya tambayesa.
"Eh zanje nan gidan su Aslam."
"Shikenan Toh kar a raba dare dai."
Tashi Areef ya yi cike da murna jin Abba be yi masa maganar ganin mota ba. Yayi saurin ficewa dan karma Abban ya tuna saboda bashi da amsar da zai iya bashi a wannan lokacin.
Kai tsaye ya nufi bakin titi ya siyo gurasa da tsire, ya biya ya taho da lemo mai sanyi sannan ya wuce gidan su Aslam wato abokinsa. Yana zuwa ya tarar dashi shima dawowarsa kenan daga majalisa yana cin tuwon shinkafa miyar kubewa ɗanya.
"Kai kuma daga ina haka a daren nan?"
Areef ya ja ɗan ƙaramin tsaki tare da zama a gefen katifa yana ajiye ledojin hannunsa.
"Abinci nazo ci sannan na koma gida."
Aslam ya kalli ledojin tare da mai da ido kan Areef dan san jin karin bayani.
"Cewa nayi abinci nazo ci sai na tafi ko bakaji bane ka tsaya kana bina da kallo?" Aslam yaci gaba da cin tuwon sa yana cewa.
"Easy abokina, waye ya ɓata maka rai ne? Bari naje na sako maka tuwon kai ma." Cikin sauri Areef yace.
"A'a nazo da abinda zanci, kasan ai tuwo baya cikin tsari na." Aslam ya kaɗa kai alamar gamsuwa da tabbatar da maganar abokin nashi.
Buɗe ledar yai tare da yiwa Aslam tayi, ai kuwa ganin kaza yasa shi yin gefe da tuwon yana murmushi yace.
"Karkaga laifi na, ga dajjaja babu abinda zai sani ƙarasa cinye tuwon nan."
Areef yai masa banza domin shi ba kowace magana yake tsayawa ya yi ba. Suna cikin ci ne Aslam ya sako zancen Feenah wanda ambato sunan kawai sai da yasa Areef jin bugun zuciya da karfi.
Gabaki ɗaya ta tsorata shi da furucinta na cewa zata je gidan su akan maganar auren su shida ita. Jin an saka masa tsoka a baki ne yasa shi saurin dawowa hayyacinsa, ya kalli Aslam dake ta dariya yana cewa.
"Majanun ɗin Layla. Gaskiya Feenah tana masifar sonka, ɗazu muka hadu da ita akan jection sun fita daga wani mall ita da wata, shine take tambaya ta ina kake? Nace mata munfi sati bamu hadu ba."
"Allah sarki."
Shine kawai abinda Areef ya iya faɗa tare da ɗaukar jarkar lemonsa yasa a baki yana sha.
"Wai Areef ya maganar karatu ne? Ko aiki wane ne ra'ayinka a yanzu.?"
"Duka nake so Aslam."
"Ah haba dalla ai sai ka fara ɗaukar ɗaya kayi sannan sai ka zurma wani."
"Ina son aiki first, sannan naci gaba da karatu saboda wani dalili nawa."
"Dalilin ɗaya ne ai Areef, shine auran Feenah ko?"
Gaban Areef ya sake bugawa, da kyar ya haɗiye naman bakinsa.
Shi yazo dan ya samu sauƙi a gurin Aslam, amman yaga sai ƙara damuwa yake a gurin Aslam ɗin, har gwanda ace yana gida yasan idan ya kule ɗaki babu me takura masa. Kawai yana gudun zuwa da naman gida ne Mamah tai masa faɗa tunda akwai abinci a gidan.
Mikewa yayi yana goge hannu da wani hankicif ɗin Aslam, cikin yatsina fuska tare da cizon leɓe yace.
"Sai da safe."
"Ah haba malam naman kuma fa?"
"Naji ya isheni ne, kuma kasan ba tafiya zan yi dashi ba saboda faɗan Mamah. Idan ka koshi ka bawa wani."
Ya fice daga cikin ɗakin da sauri dan karma ya kuma dakatar dashi.
Da kyar ya iya komawa gida saboda wani irin ciwon kai da yake ji, idanunsa har sun fara ƙanƙancewa dan azaba. Yana shiga ya rufe ko'ina sannan ya wuce ɗakinsa, ganin Iman tana shirin fitowa daga ɗakin nasa yasa shi tsuke fuska tare da fadin.
"Me kika shigo yi min a ɗaki.?" Sai da ta kalleshi tsab sama da ƙasa kamar wacce ke tuhumarsa da wani abu kafin tace.
"Mamah ce tace nazo na duba ko kana ciki, Toh nazo ban ganka a nan ba shine na kwankwasa toilet shima naji shiru."
"Ai kin ganni yanzu ko?" Iman tace.
"Eh! Daga ina kake?"
Yaji kamar ya wanka mata mari, amma ya kasa dan bashi da saurin kai hannu sai dai ɓakar zuciya kamar me.
"Sannu uwata da yi min wannan tuhumar. Idan na gaya miki daga inda nake me zaki yi min?"
"Allah baka hakuri, nifa aiko ni akai." Cewar Iman tana ɗan tabe baki tare da ɗaɗɗaga idanuwa.
"Toh daga barki nake, kedai wallahi kin shiga uku da gulma munafuki kawai, zo ki wuce ko na ji miki ciwo."
Ta fita da gudu har tana tuntuɓe ya ja tsaki kawai tare da mai da ƙofar ya rufe yana dafe goshinsa. Sauri ya yi ya haye gado yana kuma datse haƙoran sama da ƙasa, fuskarsa ya tura cikin filo yana jin kamar zai bar duniya dan rashin jin daɗin zuciya.
Samun kansa yai da buɗe wayarsa, kamar jiransa ake kuwa sai ga kira ya shigo ya duba yaga Feenah ce, ba kuma zai iya ƙin ɗagawa ba saboda shima zuciyar shi tana son taji muryarta.......✍️
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪
*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*
*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*
*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*
*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*
*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*
*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*
*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*
*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*
*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*
KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*
SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*
SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*
*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*
*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*
GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BARI DAMAR NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 11:19 - Buhainat: *ZO GARENI....*
Free page 9
NA
*HAJJA CE 👈*
Wattpad:- Hajjac
*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A 2022*
"Hello Baby.."
Cewar Feenah cikin wata irin kasalalliyar murya wacce ta sake jefa zuciyar Areef cikin tsananin begenta.
"Sweetie..."
Shima ya kirata sai dai shi muryarsa rawa take yi kamar marar gaskiya.
"Baka da lafiya ne?" Ta tambaye sa cike da kulawa,
"Eh! Kai na yake min ciwo."
"Haba mana shi yasa naji duk jikina ya mutu. Kasha magani ko?"
"A'a bani dashi a kusa ne."
"Baby ya zaka kwanta da ciwo a jikinka? Gaskiya ba zai yiwu ba, ni bari na fito na samo maka ai dare beyi ba sosai sai na tsaya a ƙofar gidan ku a miƙo maka."
Areef yai saurin zaro ido jin irin katoɓarar da zata yi masa, ya kuma san tsab zata iya indai akan shi ne. Ya ƙaƙalo murmushi mai ɗan sauti yadda zata iya jiyowa yace.
"A'a ba wai maganin ne babu bafa, yana falo ni kuma ina ɗaki na. Karki fito cikin daren nan kinga ke mace ce, bari na tashi naje na ɗakko."
Gabaki ɗaya sai ta narke masa kamar suna ganin juna, ta marairaice tana shagwaɓa.
"Nifa gaskiya Baby bana son naji kana rashin lafiya ko ya ya ne. Kuma kyau ace kana kusa dani a wannan lokacin yadda zan baka kulawa sosai."
"Karki damu sweetie, bafa wani serious ciwo bane. Idan nai bacci zan dena ji."
"Shikenan duk da nasan ka faɗa ne dan karna ce zan zo."
Yayi murmushi kawai be ce komai ba hakan yasa ta yi masa sai da safe ba dan taso ba sai dan ta barshi ya huta. Samu yai shima ya kwanta tare da addu'a ko kayan bacci kasa tashi ya yi ya sa, da na jikinsa kawai ya kwanta tare da lumshe ido bacci ya ɗauke shi.
A can ɓangaren su Iman kuwa tana zuwa ta sanar da Mamah cewar ya dawo yanzu, amman kuma bata sanar da ita bakar maganar da ya gaya mata ba na cewa daga bariki yake.
___Karin sallar farko Feenah ta kirashi a waya, a lokacin yana ta bacci yaji kiran ya ɗauka tace.
"Kiranka nai ka tashi kai sallar nafila." Yace,
"Toh na gode sweetie."
"Ka roƙar mana Allah ya nuna mana ranar da zamu kasance mata da miji, mu rayu tare a gida ɗaya, guri guda cikin ɗakin baccin mu." Areef ya lumshe ido yana murmushi yace.
"Insha Allahu zan yi." Yana jiyo sanda tai kissing ɗin wayarta tace masa.
"Toh sai da asuba mayi waya." Areef yace.
"Toh shikenan sweetie I love you."
Wani farin ciki ya kama Feenah, ta katse tana wani irin juyi akan katifa, Ramla ta da farka itama a lokacin ta kalli Feenah tare da jan ɗan ƙaramin tsaki.
Gabaki ɗaya yarinyar ta rai na su, gani take kamar itace babba tunda tai auran nan take musu wani gani-gani. Bata kula ta ba ta nufi banɗaki tayo fitsari ta dawo ta kwanta, ita kuwa Feenah da ta kira Areef tace ya tashi ya yi nafila, tana kwance sai juyi take ita baje tayi ba saboda daman tayi ne dan yace tana yi itama.
____Tsab suka shirya cikin dogayen riguna na lace, su uku ne kowacce da kalar nata. Hanan, Ikram da kuma Iman. Gabaki ɗaya sun kasance cikin shirin taryar zuwan babban yayan su, sunyi kyau matuƙa gida sai tashin ƙamshi yake na turare da na abinci.
Sallamar da aka yi ne yasa su ɗagowa duk suka kalli ƙofar falon, sukai saurin mikewa da nufin zuwa taro shi, sai dai ganin Areef yasa duk suka koma gurin zaman su ko wacce taci gaba da harkar gabanta. Ciki ya shigo yana taɓe baki kafin ya zauna suka kuma jin anyi sallama cikin wata irin murya.
"Assalamu alaikum."
Ai wannan karan babu wani ɓata lokaci duk suka tashi da gudu suka nufe shi suna.
"Oyo-yo Captain Yaya Haneef..."
Fuskarsa cike da walwala da farin ciki ya dinga shafa kan ƙannan nashi. Ya juya tare da yiwa wanda suke tare magana cewar ya shigo shima. Sai a sannan suka san cewa ba wai shi kadai yake tare ba harda wani wanda yake sanya cikin riga da wando na brown ɗin shadda.
"Dan Allah ku barsu su ƙaraso ciki haba mana, duk kun maƙale masa an rasa wanda zai barshi a cikin ku."
"Oyo-yo my Mother." Cewar Haneef yana jansu duka suna ƙarasawa gurin Mamah da baki yaki rufewa.
Tashi tayi tsaye yai saurin zare jikinsa ya ƙarasa gurinta suka rungume juna gam. Sun jima suna kwasar ɗumin juna irin na uwa da ɗah.
Daga bisani suka saki junansu abokin Haneef da ya zauna kusa da Areef ya gaishe da Mamah su kuma su Ikram suka gaishe dashi ya amsa idanunsa kur akan su musamman ma Iman wacce ke ta mannewa jikin Captain Ya Haneef.
"Zaku fara cin abinci ne, ko kuma sai kunyi wanka kun huta?"
Haneef ya yi murmushi yana zaune akan kujera mai ɗaukar mutum uku, su Hanan sun saka shi a tsakiya yace.
"Muci abinci tukunna Mamah, dan in muka zauna hutun nan toh zamu iya daɗewa bamu fito ba."
"Toh shikenan, ku kuma sai ku tashi kuje kuyi sarving ɗin su." Mamah tai magana tana kallon yaran nata mata.
Duk suka tashi abokin Captain Haneef sai kallonsu yake kamar yau ya fara ganin ƴan mata.
Su kuma babu wacce ma ta kulashi bare su san me yake faruwa, suka nufi kitchen kowacce ta kama abinda zata dako kafin su fito kusan a tare. Komai suka shirya shi a tsakiyar center carpet, Iman ta tsaya jera glass cup akan tray, mutumin ya kuma gyara zamansa tare da kura mata ido yana nazarinta har sai da ta kammala ta fara zuba musu juice ɗin da aka haɗa na musamman.
"Yaya Captain bismillahi." Hanan ta faɗa tana zuba farfesun kayan ciki da yake ta fitar da tururi a cikin ɗan farin boul.
"Dr Jamil sakko muyi lunch."
Cewar Captain Haneef yana sauka shima daga kan kujera.
Ikram da Hanan suke zubawa, ita kuma Iman tana miƙawa gaban su Yaya Haneef, can ta kalli inda Areef yake zaune yana lumshe ido kamar mai jin bacci ta mike tana yatsina fuska ta ƙarasa kusa dashi hannunta ɗauke da plate ɗin cin-cin. Sai da ta leƙa fuskarsa taga idanunsa na motsi kafin ta ajiye plate ɗin akan hannun kujera tace.
"Yaya Areef tashi kaci." Yana jinta amman ya share. Ba tayi fushi ba ta kuma cewa.
"Cin-cin ne na kawo maka naga ka kwanta kayi shiru. Ka tashi kaji ko zakaji daɗin bakin ka."
"Nagode." Kawai ya faɗa ba tare da ya buɗe idanunsa ba. Ita kuma jin ya amsa yasa ta ajiye masa