Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   16 / 38

45K to 48K   out of 113.7K words

tana irin waɗannan abubuwan me zai hana shi yaron ya saketa mugani ko zata dawo dai dai...?"

Gabaki ɗaya suka kalleshi, kalamansa sun girgiza dukkan su. Suna farin ciki da wannan auran ace lokaci ɗaya an ruguza shi?

"Wannan shine hanya mafi sauki wajen dawo da nutsuwar yarinyar nan."

(Tana gaba tana dabo! Wai shin waye zai tonawa Jamil asiri? Allah sarki Iman ɗin mu ta mutunci🤢)

*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.








*HAJJA CE 👈*
2/16/22, 21:34 - Buhainat: *ZO...GA....N...*✍️
*TOP 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*



*20*





"Malam Babba sakifa kace? Wane irin saki kuma ana zaune ƙalau? A dai duba malam a sake samo mana mafita."

"Hajiya harkar aljanu ne fa, ina ganin ma auren ta suka yi kinga kuwa babu ta yadda za'a yi su barta ta auri wani." Suka yi shiru kowanne yana ta saƙa zancen a ransa.

"Hajiya ku barshi ya saki yarinyar nan, Allah ya haɗa kowa da rabonsa. Idan kuma kukaƙi ina tausaya muku, kar kuma kuce ban gaya muku ba, na tabbatar ba zasu bar yarinyar nan ta zauna da wani ba. Irin wannan matsalar an kawo min ita tafi ɗari."

"Kenan malam sai abar aljanu su dinga yiwa bil'adama mulkin mallaka? Yanzu dai tunda har ka gano cewa aljanu ne, muna bukatar addu'arku da kuma ruƙiya tunda dai basufi ƙarfin alƙur'ani ba. Tunda dai ko Areef ya saketa ta auri wani ba zasu bari ba duk maganar ɗaya ce." Mamah tai maganar tana kallon malam Babba.

"Amman kuma tana cewa ita Jamil take so shi zata aura." Cewar Ikram tana gayawa malam.

"Jamilu kuma? Waye shi? Ƙilama sunan aljanin dake jikinta ne."

"A'a malam ba aljani bane wannan. Wani abokin Yayan sune suka zo tare da shi tun daga Lagos."

"Ahhh Toh ashema tana da wanda take so? Toh ku dalilin me yasa ba zaku bawa yarinya zabinta ba? Yanzu ana samun matsaloli fa akan auran dole da ake yiwa yaran zamanin nan, yadda zakiji mace ta kwarawa miji ruwan zafi, ko ta soka masa wuka, ko tasa masa guba cikin abincinsa, ko kuma ita ta kashe kanta kowa ma ya huta. Ina mai baku shawara da ku tsaya kuna kashe kuɗi kuna wahalar da kanku, yaro dai ya saukaƙa mata kurum."

Maganar malam ta shige su har Areef ya fara murna sai kuma ga Abba ya shigo a hargitse. Sannu suka shiga yi masa ya maida kallonsa wajan malam Babba tare da cewa.

"Da gaske ne raba auran nan za'a yi.?"

"Shine kawai mafita Alhaji Ahmad." Malam Babba ya faɗa cikin gasgatawa.

"Gaskiyar Liman ne, ɗazu a asibiti ya farka daga bacci yayi wani mummunan mafarki akan lamarin auran nan. Ya kuma tabbatar min da cewa duk wuya duk tsanani karmu sake a rabasu, rabawar shine mafarin ƙara rikita duk lamarin nan."

"Kenan so yake yace asiri akai musu?" Malam Babba ya tambaya.

"Banida tabbas gaskiya dan be ce min komai ba baya ga wannan."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, shi Jamil ɗin yana sonta ne?"

"A'a malam Babba, shi kansa yace baya sonta itace dai take ta shirmenta." Cewar Mamah.

"Shikenan duk yadda za'a yi kar a kuma bari su haɗu da Jamil ɗin nan. Zata iya kasancewa mai aiwatar da wannan aikin ya yi amfani da hakan ne dan ya sake hargitsa komai. A dage da addu'a. Ko kuma idan zata yiwu ina angon yake?" Abba ya nuna Areef.

"Shine wannan."

"Au wai wannan shine mijin nata?"

"Eh shine." Malam Babba yace.

"Toh san samu dai su haɗu ta hakan ne za'a iya karya koda asirin ne."

Mamah da Areef ne kawai suka fahimci maganar malam, amma ko Abba abinda ya fahimta dabban da manufar malam Babba.

"Dawa zasu haɗu malam.?" Abba ya tambaya.

"Ina nufin suyi kusanta."

Malam ya faɗa yadda zasu gane. Suka zaro ido dukan su.

"A gwada wannan abin a gani, tunda ai auran ne ba'a so tayi ko?"

Ikram da Hanan suka fara dariya ciki-ciki, aka maida hankali wajen Areef da ya kawar da kai tamkar besan abinda ake cewa ba. Abba yace.

"Shikenan malam ba matsala ai za'a yi yadda kace."

Suka yi sallama da malam bayan yace a dinga sanya karatun al qura'ani a gidan. Abba na dawowa ya kalli Areef yace.

"Kai...!" Areef ya ɗago tare da cewa.

"Na'am."

"Nasan kasan abinda malam ke nufi, kuma A gurinka daman ba wani sabon abu bane kasan yadda zaka yi. Tashi ka ɗauki matarka ku tafi ɗaki Allah ya bamu alkairi. Kuma idan baka yi abinda malam Babba ya faɗa ba, kana ɗaya daga cikin wanda zasu cuci yarinyar nan."

"Abba wallahi tallahi ban...." Cikin sauri ya katse Areef ɗin.

"Kaga ni ba wani rantsuwa nace kayi min ba. Tsahi ku shiga."

"Abba bari su Hanan su kai ta dan Allah."

"Ba damuwa Mamah ni bari na shiga ciki kai na ciwo yake." Ya wuce ɗakin shi yana dafe goshinsa.

"Ku kaita Ikram." Cewar Mamah, tashi sukai suna dariya suka rungume Iman suka kaita ɗakin Areef wanda yake matsayin inda zasu rayu.

"Areef kaji abinda aka faɗa ko?" Kamar zai fashe da kuka yace.

"Amman Mamah ya z...." Tayi saurin katse shi itama ta hanyar cewa.

"Kayi biyayya kawai, na fahimci manufarka ina yi muku fatan alkairi tashi ka tafi."

Ya tashi duk da haka sai da hawaye suka zubo mishi ya shiga gogewa. Yana kokarin shiga ɗakin su kuma su Hanan suna fitowa, har zasu yi masa sai da safe Allah ya rufa musu asiri sukai shiru ya shiga su kuma suka tafi nasu ɗakin suma. Tana kwance a takure kan gado, yadda suka ajiyeta bata motsa ba bare tasan inda suka kawota. Areef yai kwafa tare da ƙarasawa ya ɗauki kayanshi yana jerawa cikin wardrobe ɗinsa.

Wayarsa da ta Feenah ya dakko yasa tashi jikin chaji ta Feenah kuma ya kunna yana dubawa. Shine mutum na karshe da sukai waya, haka kuma shine wanda ta turawa SMS na karshe. Murmushi yayi 'Allah sarki ko tana ina yanzu?' Ya tambayi zuciyar shi yaci gaba da duba wayar yana ganin hotunanta da tayi a ciki. Sai da ya gama ya rasa abin yi ya juya zai kwanta ya kalli Iman da har zuwa lokacin bata motsa ba. Wai nan an kawo ta ana jiran su raya sunnah, banda abin su Mamah taya ma zai iya bare har yayi?

Wani shu'umin murmushi ya yi tare da hawa kan gadon ya kwanta yana ware hannaye, cikin shaƙiyanci yace.

"Oya taho na cire miki asirin dake kanki."

Shiru ko motsi Iman bata yi ba bare yasa ran zatai abinda yace. Gyara kwanciya yayi yana cewa.

"Ke za'a temakawa ki dena wani maganar Jamil ko waye, idan kina buƙata kizo idan bakya so shikenan sai kiyi ta zama."

Bata kula shi ba ya kuma jan tsaki tare da janyo bargo yana warwarewa zai rufa ya saka hannu tare da janyo nata yana cewa.

"Umarnin Malam ne da kuma tirsasawar iyayena, dan su kawai zanyi ba wai dan ina so ba ko kina so."

Habawa da ta buɗe idanuwa tayi kan Areef ta shaƙe masa wuya kasa motsawa yayi. Banda kuka da ihu babu abinda Iman keyi, burinta kawai taji baya numfashi, kai daga ganin yadda take yi akan ruwan cikinsa kasan cewa ba mai hankali bace. Areef kuwa tun yana iya janyo numfashinsa yana kokarin kwatar kansa har sai da ya fara ganin dishi-dishi a idanunsa alamun ya kusa barin hankali da tunaninsa. Garam aka buɗe ƙofar Abba ne ya fito zaije ya rufe gidan yaji ihu mai firgitarwa daga cikin ɗakin amarya da ango shine ya shiga da gudu dan ganin ko lafiya ya tarar Iman na kan Areef ta shaƙe shi.

"Ke Iman meye haka?" Ya faɗa yana shirin kwatar ta. Ta kai masa wani irin naushi a fuskarsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun. Zasu haukata mana yarinya Hawwa...! Hawwa....!! Hawwa...!!!" Ya shiga kiran Mamah da karfi.

Sake nufar Iman ɗin yayi da kyar ya ɓanɓare ta daga kan Areef. Mamah ta shigo yace ta ɗakko ruwa aka shafawa Areef.

"Mayar da ita ɗakinki, banda Allah ya kawo ni da safe sai dai muga mummunan abu. Akwai matsala wallahi, kuma koma meye Insha Allahu sai Allah ya yi mana maganinsa. Muje na kai miki ita na dawo gurin Areef ɗin."

Mamah ta kalli Areef dake jan numfashi da kyar, kamar zatai kuka haka ta fita daga cikin ɗakin suka nufi nata. Abba ya kwantar da Iman kan gadon Mamah ya koma ɗakin Areef dake rike da wuya yana shafa inda ta maƙure masa.

"Abba wallahi wannan yarinyar ta haukace kasheni zata yi." Ya faɗa yana matse ido.

"Insha Allahu babu abinda zai faru sai alkairi Areef, kamar yadda liman yace kar a kashe auran nan to kayi hakuri karka furta. Wannan shawarar ta malam Babba ka gwada yi ne?" Da sauri Areef ya shiga girgiza kai alamar a'a.

"Toh dole dai a sake wata hanyar tunda yanzuma ɗaki kawai aka haɗa ku ina maganar kwana guri guda. Sannu kaji Allah yayi kana da sauran kwana a gaba. Bari zuwa gobe sai musan yacce za'a yi."

Areef ya gyada kai Abba ya fita ya nufi ɗakin Mamah inda ya tarar tana ta fama da Iman.

"Lafiya?" Ya tambaya yana shiga ciki.

"Gatanan tunda ka bar gurin nan take ce min zasu kamata, ni kuma na duba banga komai ba a cikin ɗakin nan. Alhaji wannan wace irin masifa ce? Anya..anya kuwa mutane suna tsoran Allah? Yanzu duk wanda yai irin wannan abun yana tunanin samun nutsuwa a rayuwarsa? Wannan wace irin jaraba ce yarinyar tana zaman-zamanta daga yin aure zasu kassarata?"

"Uhmmm Hajiya kenan, imani ne yasa kike da irin wannan tunanin. Amman su da basu dashi ai abinda sukaga dama kawai suke yi."

Ya samu guri ya zauna shida Mamah suka shiga yi mata addu'a. A ranar Mamah da Abba da Areef babu wanda ya iya rintsawa a cikin su.

___________

Washe gari tun Iman ta farka Mamah take mata magana amman tayi shiru taki magana, kallonta kawai take yi da ido bata cewa komai.

"Iman kina ji ina tambayarki zaki iya yin sallah?" Still tayi shiru taki cewa komai.

Iman ta fara hawaye ta sauka daga kan gadon ta nufi inda jakar Mamah take, biro da takarda ta ɗauka ta shiga yin rubutu, tana gamawa ta mikawa Mamah takardar. Mamah ta karɓa da sauri ta fara karantawa.

_"Mamah banajin komai, naga bakinki yana motsawa kina kuma kallona."_

Tana gama karantawa kirjinta ya buga, tai saurin kallon Iman ɗin tare da janyo fuskarta tana dudduba cikin kunnenta tamkar zata hango abinda ya hana Iman ɗin jinta. Babu komai a ciki ko datti babu bare asaka ran shine yai yawa har ya hanata jin maganar da ake yi mata.

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun yanzu Iman baki ji na? Bakiji abinda nace ba? Na shiga uku ni Hawwa wannan wace irin masifa ce."

Mamah ta faɗa wasu hawaye masu zafi suna biyo kumatunta..........

(Allah sarki😭wannan masifar ta taɓa faruwa akan ƙawata. Allah ya kara miki lafiya😭 ya kawo karshen abubuwan da suke damunki)


*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.









*HAJJA CE 👈*
2/21/22, 09:23 - Buhainat: *ZO...GA....N...*✍️
*TOP 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*



*21*



Abanza mankare, suma wadannan maganganun da Mamah keyi duk baji take yi ba, sai kallo kawai da take bin ta dashi. Da sauri Mamah ta janyo Iman ɗin zuwa jikinta tai mata wata muguwar runguma mai tattare da tsananin tausayawa, jikinta banda rawa babu abinda yake yi. Ikram da ta shigo hannunta ɗauke da jug da plate, tai mamakin ganinsu a tsaye sun rungume juna kamar wanda za'a nisanta da ɗan uwansa. Sai dai babban damuwar kuma Mamah na hawaye tana shafa bayan Iman ɗin tana cewa.

"Allah ya fisu Iman karki damu, babu abinda zai sameki sai alkairi da izinin Allah."

"Mamah me kuma ya faru?" Ikram ta tambaya tana ajiye kayan akan madubi.

Mamah ta zaunar da su a gefen gado tana kuma rungume Iman, cikin raunin zuciya tace.

"Ikram ƴar uwarku ta haɗu da babbar kaddara, kuyi mata addu'a tare da ku kan ku, Allah ya tsare ya wargaza duk wani kulli da aka yi mata. Wallahi yanzu haka duk maganar nan da mukeyi dake Iman batajin mu, sun toshe kunnuwanta ban san abinda suke so akan yarinyar nan ba." Ta faɗa tana kuma fashewa da kuka.

Lallai tashin hankali ya kai inda yake, yau Mamah ce ke kuka tamkar ƴar ƙaramar yarinya. Ikram cikin mamaki take kallon Iman da alama bata yadda da abinda taji daga bakin mahaifiyartasu ba. A hankali ta shiga yiwa Iman magana wai ko zata amsa amman taji shiru, tasa hannu ta taɓa ta Iman ta kalleta sai kawai itama Ikram ɗin ta fashe da kuka. Abba da Areef suka shigo nan suka tarar da wani tashin hankalin.

"Wannan abun fa ya fara zama masifa Hajiya, shin me suke so su maida yarinyar nan ne iyeee? Me ta tare musu suke neman illata min ta? Idan danni ake yiwa yarinyar nan abinda be dace ba, ayi hakuri ayi min koma menene a barta kamar yadda kowa yake rayuwarsa."

"Nifa Abba ina zargin Jamil ɗin nan wallahi kwata-kwata ni dama zuciya ta bata yarda dashi ba." Mamaki ya kama dukkan su. Abba ya yi murmushin takaici tare da cewa.

"Areef kenan, taya tunaninki zai baka cewar Jamil ne yai wannan mugun kullin? Idan ban manta ba Jamil be san da auran nan ba, daɗin daɗawa kwanansu nawa da zuwa ya tafi inda zaije? Saifa ran daurin auren yazo yana ta mamakin dama tuntuni da zancen auren ne, ko kuwa a ranar kawai aka yanke hukunci? ko kun manta?"

Areef ya dafe goshi alamar ya sha'afa, sai dai duk da haka zuciyarshi bata kwanta da Jamil ɗin ba, dan haka yace dasu.

"Amman duk da haka mu dena bari yana shige mana sosai, ya fiye shisshigi da yawa wallahi." Cikin sanyin jiki Hanan tace.

"Allah na tuba astagfurullah zato zunubi koda ya kasance gaskiya ne, ni kuma wallahi nafi zargin Nafisar nan budurwarka, saboda yarinyar nan daga ganin yadda take masifar sonka zata iya yin komai dan ta hanaka zaman lafiya, astagfurullah Allah ka yafe min."

Duk suka zaro ido suna gyaɗa kai cike da yarda da maganar Hanan, Ikram ce mai cewa.

"Kinsan daman ranar da tazo nan gidan, Iman ta sanar da ita cewa aure za'a yiwa Yaya Areef, wanda ina tsammanin shine yasa ta suma a lokacin."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, tabbas hakan zata iya kasancewa. Wallahi babu abinda mutane ba zasu iya yi ba dan suga sun cutar da wani. Tsab yarinyar nan zata iya shi yasa ma batayiwa Areef ɗin ba ta yiwa Iman saboda idan ta yi masa tasan zai cutu."

Nan da nan ran Areef ya ɓaci jin an maida akalar abin akan Feenah, bece komai ba har Abba yace a shirya Iman su tafi gurin wani malami ko za'a dace a gano inda matsalar take. Kowa ya fita aka bar Iman Mamah tana shiryata, tasa tayi sallah tasha kunu kaɗan.

"Ku kuma dalla ana maganar serious kun shigo da Feenah ciki, Toh na rantse da Allah in har ba ita ta aikata wannan abin ba kukace itace sai Allah ya saka mata. Ku yanzu da daɗi saurayinku yana son ku a ce kunyi masa asiri? Toh yadda kuke a gurin samarin ku haka Feenah take a gareni." Ya zabga musu harara ya wuce dan gyara parking.

Suka bishi da kallon mamaki tare da tabe baki, 'ashe dai har yanzu yana maƙale da soyayyar ta a ransa? Lallai iska na wahalar da mai kayan kara.' suka wuce kitchen dan ƙarasa abinda suke yi saboda ba dasu za'aje gurin malamin ba. Areef ne ya zauna a mazaunin direba, yayin da Abba ya zauna a gefen shi, Mamah da Iman suna baya a zaune yaja suka bar gidan.
_____________

Jamil kuwa yana fitowa daga gidan ya wuce ya kama hotel, a ranar ya dace ya koma Zamfara amman ɗan tahaliƙin ya fasa, ba zai tafi ba sai ya tabbatar da auran Iman ya mutu shi kuma ya kafa kanshi a gareta. Fitowarsa daga wanka kenan yaga ana kiran wayarshi, ya ɗauka da sauri ganin sunan malaminsa ne wato bokansa yana cewa.

"Kayi yadda zaka yi wajan ganin ka kawo mana ɓaƙaƙen tinkiyoyi guda biyu da ƙasar sahun ƙafarta, daga lokacin da ka kawo zamu ƙarasa maka aiki ka, Iman kuma ta zama mallaki ka ba wanda zai iya juya ta sai kai..!"

"Karka damu malam Insha Allahu zan kawo, ai har zuwa lokacin nan basu gano cewa nina sanadin komai ba. Ina son kuma ka sake karkatar min da hankalinsu koda wasa karsuyi zargina akan lamarin yarsu."

"Karka damu a iya binciken mu akan yarinyar, tama daɗe cikin asiri, mun buga ƙasa, ƙasar ta nuna mana cewa ba asalin yar gidan bace." Jamil ya saki murmushi tare da cewa.

"Nasani malam tunda gashi sun haɗa auranta da ɗan su. Ina son Iman malam kayi duk abinda zakai dan ganin na mallaketa."

"Za'ayi yadda kake so." Suka yi sallama Jamil ya faɗa kan gado yana mirgina-mirgina akai.

Gabaki ɗaya ya manta cewa duniya ba gidan zama bace, ba kuma matabbata bace, jin daɗinsa shine a gabanshi ba farin cikin wani ba. Toh daman an riga

16 / 38