wanke-wanke sai wanda ta ɓata take daurayewa, yau gata tana wanke-wanken da ko jaka sai haka.
___________
Koda su Ikram suka dawo suka ji labarin abubuwan da suka faru sun sha mamaki, suna da tarin maganganun da zasu yi da Iman amman ba'a basu dama ba kasancewar an kaita wani ɗakin an rufe. Haka suka kwana suna ta mamakin lamarin.
Washe gari kowa yanata harkokinsa bayan su Haneef sun tafi Abba ya shiga ɗakin da Iman take. Zaune ya tarar da ita ta haɗa kai da guiwa, yai sallama ta dago suka kalli juna, idanunta sunyi jawur gashi sunyi luhu-luhu alamar basu samu bacci ba. Ya girgiza kai tare da cewa.
"Kinyi sallah kuwa?" Ta girgiza kai.
"Karfe tara fa yanzu, fito kije kiyi."
Ta mike tana dafa bango saboda jirin da yake ɗibarta, rabonta da abinci tun kan a daura aure. Bacci kuwa tun ana sauran kwanaki uku a daura aure, saboda hirar da suke sha cikin dare. Sai da ta shiga ɗakin su sannan ya koma falo ya zauna yana jiran ta idar. Areef da ya fito yaga Abba a falo sai yai sauri ya koma ɗaki dan be shirya haɗa idanu dashi ba.
Bandaki ta shiga ba tare da ta kula su Hanan ba. Suma basu kulata ba ganin yadda take cin ɗaci, fuskarta kuma babu annuri gashi daman Mamah taja musu kunne akan kar wacce tayi mata magana indai ba ita ta fara yi musu ba saboda karta sake hargitse musu. Tana idarwa Abba ya kirata ta fito falo tare da zama a ƙasa kan kafet. Sannan ya kwalawa Areef kira, har ya fito ya hango Iman ya koma ciki ya ɗakko hula yasa sannan ya fito. Babu wanda ya kalli inda ɗan uwansa yake, ya samu guri ya zauna yana gaida Abba.
"Nasan kunsan cewar a jiya ne aka ɗaura muku aure, munyi haka ne badan komai ba sai dan mu rufawa juna asiri, duk da cewar naji labarin abinda ya faru jiya. Toh ke Iman kisan cewar wannan hanyar itace rufin asirinki. Kaima kuma Areef zabin nan da mukai maka zai rufa maka asiri nesa ba kusa ba. Dan haka ke Iman zaki tattara duk wasu kayanki ki koma ɗakin mijinki kafin a samar muku gurin zama. Kai kuma Areef sai ka fara nemo hanyar da zaka dinga samun kuɗin kulawa da iyalinka. Bana san shashanci ko wata matsala, nasan kasan hakƙoƙin miji a gidansa, ina fatan zaka kula da matarka kamar yadda addini ya koyar.?"
Areef da kansa ke ƙasa yaja leɓansa da haƙori, gaba ɗaya ya rasa me zai ce da Abba. Muryar Iman ta katse musu shurin da aka yi, cikin kuka kamar wacce ake caccakawa zuciya tace.
"Abba wallahi Yaya Jamil nake so." Cike da takaici Abban yace.
"Kiyi hakuri da auran Jamil saboda fitarki daga cikin famili ɗin nan shine fallasuwar sirrinki Iman. Areef zai riƙeki amana zai kuma rufe duk wani sirri naki har karshen rayuwa."
Kai ta shiga kaɗawa tana shasshekar kuka tace.
"Abba mutuwa zanyi, wallahi bazan iya zama da kowa ba in ba Yaya Jamil ba."
"Areef saki yarinyar nan a yanzu ba sai anjima ba, furta mata kawai taje taci uwar da zataci da Jamil ɗin."
Gabaki ɗaya suka juya suna kallon mai bada umarnin nan. A daidai lokacin ne Jamil yai sallama falon yana cewa ya manta wasu muhimman takardu a ɗakin Haneef, dan haka ya dawo ya ɗauka...........
(Jamil kenan, an san takan tsiya wallahi😒)
*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
2/16/22, 07:40 - Buhainat: *ZO.... GA...N...*
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*
*19*
Babu wanda ya kawo komai a ransa akan dawowar Jamil, kamar yadda ya gaya musu cewar takardu ya manta sun amince da hakan. Kallon Mamah Abba da su Ikram suka yi jin yadda ta bawa Areef umarnin ya saki Iman. Maimakon Jamil ya koma daga waje tunda yaga kamar ana ɗan tattaunawa, a'a sai ya ƙarasa ciki ya samu guri ya zauna. Abba ne kafin aci gaba da magana ya kallesa tare da cewa.
"Jamil me kake jira kuma?" Yace cikin sunkuyar da kai.
"Abba mukullin sashen Haneef za'a bani."
"Okay toh, Hajiya a ɗakko abashi yaje ya ɗauka."
Mamah ta juya tana kallon Ikram tare da bata umarnin taje ɗaki ta ɗakko mukullayen a ɗaki. Iman na ganin Jamil ta sake ruɗewa, kukan da take yi ya ƙara karfi, hankalinta duk ya tashi. Cikin basarwa Jamil yake kallon Abba fuskarsa ɗauke da damuwa yace.
"Wai Abba har yanzu fitinarce? Iman ya kamata ki yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi. Maganar da kike faɗa bamai yiyuwa bace, ni ban taɓa yi miki maganar soyayya ba bare aure, karkija iyayenki suyi tsammanin wani abu."
Jamil ya kuma girgiza kai ta yadda ba zaka taɓa yadda yana da hannu cikin rikicewar Iman ba.
"Abba kuyi hakuri amman ni bance da ita zamu yi soyayya ba, duka-duka kwanana nawa tare daku bare har muyi sabon da zamu kullu aure? Yau ma zan bar gidan ba kuma zan sake dawowa ba sai wani ikon Allah. Ina rokan Allah ya basu zaman lafiya."
"Babu komai Jamil, daman mu bamu zargeka ba, fitinace kawai irinta mata. Areef jeka buɗe masa ya dauki takardun nashi sai ka rufe ɗakin ka dawo da mukullin."
Areef dake jin ransa a bace ya mike yaje ya karɓi mukullin, Jamil ya tashi tare da yi musu sallama suka fita shida Areef. Suna tafiya yana nuna mamakin lamarin Iman, shi kam Areef baya cewa komai saboda haushin Iman ɗin yakeji yadda take cewa ita a dole Jamil take so wanda shi kuma ya buɗe baki yace bece ba. Yasa mukullin ya buɗe ya tsaya daga waje, shi kuma Jamil ya shiga ciki. Ganin Areef ya juya baya yasa Jamil ɗin juyawa ya kallesa yana cizon leɓe.
Yana sane tun daren jiya da Haneef yace zasu bar gidan ya kwaso takardunshi na ofis ya zura ƙarƙashin gado saboda yana so ya dawo gidan. Kwaso su yayi ya rungumo yana kallon Areef yace.
"Ka gansu nan su na karbo a Niger, Allah ya taimakeni ba sai da naje Zamfara na tuna ba."
Dan murmushin yaƙe Areef yayi sannan yasa mukulli ya rufe ɗakin, bejira wani abun ba ya yi hanyar komawa cikin gida Jamil yabi shi.
"Na ɗauka tafiya zaka yi?" Areef ya tambayesa ganin yana shirin kuma shiga.
"Zamuyi sallama dasu Abba." Jamil yai maganar yana bin Areef da kallo.
"Zan gaya musu, saboda idan ka shiga yarinyar can zata kuma yiwa mutane hauka tana ɓatawa iyayen mu rai."
Mamakin Areef ya cika ran Jamil, lallai yaron nan yai mugun raina masa hankali, amman kuma babu yadda zai yi dole ya hakura karya dage akan sai ya shiga su fara zarginsa gashi kuma ba wai hakura yayi ba.
"Hakane, Toh na tafi sai dai zan baka shawara. Ba kowace mace bace take hakuri in ta kama mijinta yana mummunar alaƙa da wata ba, so sai ka kiyaye ka dinga haƙura da wasu matan."
Kallon Jamil Areef yai yana mamakin kalamansa, sai dai bai ce komai ba ya gyaɗa masa kai tare da shigewa ya rufo ƙofar. Cizon yatsa Jamil yai tare da juyawa ya fita daga gidan. Areef na shiga Mamah ya miƙawa mukullin ya koma ya samu guri ya zauna, har lokacin kuma Iman bata dena kukan da take yi ba. Lokacin da su Areef suka fita Abba yace da Mamah karya kuma jin koda wasa tace Areef ya saki Iman, ya bata misali ace a cikin Hanan ko Ikram hakan ta kasance ya zata yi? Ta shaida masa zata jajirce wajan ganin sun fahimci manufarsu. Abba yace toh yanzu ma haka zatayi har yaran su fahimta. Hakan yasa lokacin da Areef ya dawo basu sake tayar da maganar sakin ba, wanda yaso a kuma yi masa.
"Kamar yadda nace haka za'a yi, wato Areef da Iman kuyi amfani da ɗakinka kafin wani lokacin muga yadda za'a yi."
Wato dole sai anbar musu auran nan, suna jin yarinya ta kafe kai da fata akan bata son shi amman anki rabawa saboda kawai a rufa asiri. Shimafa ba cewa yai yana sonta ba bare tace shine ya nace mata, hasalima yana da wacce yake ganin zata iya bashi farin ciki da nutsuwa a rayuwarsa. Kuma shima zai iya botsarewa yace baya so, amman yana tsoran karya kuma tayar musu da hankali bayan wanda suke ciki.
"Ikram ku tashi kuje duk wani abu da kuka san na Iman ne ku mayar dasu ɗakin Areef. Muna yi muku fatan alkairi Allah ya haɗe mana kawunanku."
Mamah, Hanan da kuma Ikram suka amsa banda Iman da Areef kowa da abinda yake damin zuciyar shi.
"Kai kaje ka mayar da kayan sawarka cikin wardrobe ɗaya, itama suje su shiyar mata nata kayan. Areef bana son fitina, zanje asibiti Mamah tana nan zata kula da komai, Allah ya yi muku albarka." A hankali Areef ya amsa da.
"Amin Abba."
Daga nan Abba yai musu sallama ya fita, Iman ta sake fashewa da wani razanannan kuka, duk da ran Mamah a ɓace yake akan abinda Iman ɗin keyi haka ta daure taje kusa da ita tare da janyota zuwa jikinta.
"Kukan nan ya isa haka Iman. Ɗago ki gaya min tun lokacin da kika fara son Jamil saboda babu wanda ya sani hatta shi kansa Jamil ɗin yace besan zancen ba."
Iman ta sassauta kukan da take yi, sai dai ta kasa cewa komai dan ita kanta batasan yadda akai take jin tsakanin son shi ba, zata iya cewa lokaci ɗaya taji idan bashi ta aura ba zata iya samun matsala a cikin rayuwarta. Sake matse idanuwa tayi tare da sanya hannu a ƙirjinta da takejin tamkar zai faɗo saboda ya yi mata nauyi.
"Babu amsa ko Iman? So kike kawai ki hana kanki auran Areef saboda an kamashi tare da wata ko? Mu daman koda hakan bata faru ba munso idan lokacin da muka yanke ya yi zamu haɗa aure tsakaninki da Yayanku Haneef, saboda idan wani bare yazo yace zai aureki wani abun ne daban Iman. Bamu san suwaye ainahin iyayenki ba, wanda dole kobadaɗe ko bajuma dole azo ace mana ina asalinki. Idan an tabaye mu bamu da abin cewa saboda a ƙofar gidan nan da muke ciki Abban ku yaje masallacin asuba yaji kukanki a zanin goyo. Saboda haka kiyi hakuri ki karɓi auran nan da hannu biyu ba tare da an kuma samun matsala ba kinji?"
Iman bata ce komai ba ganin hakan yasa Mamah miƙar da ita suka shiga cikin bedroom ɗinta. Bandaki ta shiga ta zuba mata ruwan wanka a bokiti ta fita tare da ɗakko zani ta bara tace ta ɗaura. Yadda zuciyar Iman ke zafi zata iya zagin Mamah tas saboda ta takura mata. Amman cikin ikon Allah sai batai wani gigiba ta cire kayan ta ɗaura Zani. Kafin ta fito daga wankan Mamah ta fito mata da wasu riga da skirt na atamfa, daman sun ɗinka mata kala goma ba tare da sun sanar da kowa ba.
Iman na fitowa Mamah ta nuna mata kayan tace idan ta shafa mai ta saka. Hatta bra da pant duk Mamah ta fito mata dasu sabbai dal. Mamaki ya dinga cin Iman amman ta kasa yin godiya sai ma wani ɗaci da takeji a zuciyarta. Gaba ɗaya ta zama wata iri nema take ta canza musu ta koma sabuwar Iman ba wacce suka sani ba.
"Aunty Iman kizo muje sai ki dinga nuna mana inda zamu saka miki wasu abubuwan." Hanan ta faɗa cikin zolaya.
"Kuje ku saka mata inda ya dace ba sai tazo ba." Cewar Mamah tana gyara filo.
"Ai Mamah karmu saka mata wani abun a wani gurin tazo taita nema, kinsan halin Ya Areef baya son ana masa shige da fice a cikin ɗaki."
"Kuje kuyi yadda kukaga dama, Amman ba zataje ba." Hanan ta rausayar da kai tabar ɗakin.
Iman tai zamanta a ɗakin Mamah, abinci ma dakyar taci kaɗan tayi sallolinta da komai. Suma su Ikram suna kammala shirya mata kayan ɗakin su suka koma suka yi wanka, da suka shirya suka shiga ɗakin Mamah gurin Iman da ta ɗan fara sakin jikinta. Areef kuwa dama yana shiga ɗaki ya fito da kayansa, can karshen gado ya kaisu yace kar shegiyar da ta taɓa masa, ya fice daga gidan gaba ɗaya.
Aslam yaja suka nufi guest house ɗin Feenah. Suna zuwa Areef ya gaishe da mai gadi, ya kuma ganeshi yai masa bayani cewar zai ɗauki mashin ɗin da yazo dashi da wayarsa a ciki. Babu musu mai gadi ya barshi amman shi kadai yaje ya ɗakko ya fito suka bar gurin. Bai koma gida ba sai da aka yi sallar isha, su Aslam suna ta yi masa tsiya akan sai ya tafi da kaza yace sai dai in ciwon hauka ne ya kamashi amma bazai siya ba.
___________
Yana shiga ya gansu zaune a falo suna hira. Iman na ganinshi ta miƙe da sauri ta ruga da gudu bayan Mamah tana kuka. Yaja wani mugun tsaki tare da shigewa ɗaki ya rufe ƙofar. Wani ƙamshin turaran wuta ne ya tarbeshi, cikin sauri ya lumshe saboda yadda yaji daɗin ƙamshin. Da sauri kuma ya buɗe idon tare da dube-dube zuciyar shi tana gaya masa Feenah ce a ɗakin.
"Feenah.." Ya kira sunan a hankali, daidai lokacin da Mamah ta shiga ɗakin yaji tace.
"Ooh daga wajan ta kake kenan ko?" Areef ya shafa ƙeya tare da girgiza kai.
"Wallahi Allah Mamah banganta ba."
"Naji Toh me yasa kake kiran sunanta?" Yayi shiru saboda rashin abin cewa.
"Hmmm kabi duniya a sannu Areef wallahi kasan cewa bayan duniyar nan akwai ƙiyama. Idan har munga zai yiwu Iman zata zo ɗakin nan yau. Idan kuma munga da matsala zamu barta sai zuwa gobe idan Allah ya kaimu."
Ya sunkyar da kai ƙasa tare da cewa. "Toh Mamah Allah ya kaimu goben." Tai saurin kallonsa tare da cewa.
"Nafa ce idan yau zai yiwu zata taho." Murmushi yayi a can kasan zuciyarshi, a fili yace.
"Duk yadda kukai Mamah."
Ficewa tayi bata sake cewa komai ba. Ɗakinta ta shiga ta tarar dasu Hanan suna karatun al'Kur'ani. Iman kuma tana can tsakiyar gadon Mamah ta sanya fuskarta tsakanin guiwoyinta tamkar wata mai kuka.
"Har yanzu kina jin tsoran ne Iman?" Mamah ta tambayeta.
"A'a, amman kirjina zafi yake kamar zai fashe."
"Babu abinda zai faru Insha Allahu. Kedai kiyi ta yin addu'ar da nace ki dinga yi. Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, La'ilaha illah anta subahanaka inni kuttu minazzalumin. Kiyi tayi babu abinda zai sameki."
Iman ta cije leɓe saboda da ta yi yinƙurin fara addu'oin sai taji tamkar za'a kasheta, tana jin ana matse mara maƙogwaro. Cikin kuka tace.
"Mamah zan mutu, zasu kashe ni Mamah." Iman ta faɗa tana riƙe wuya tare da sassanƙarewa. Cikin sauri suka yi kanta suna rirriƙeta Mamah na cewa.
"Wannan yarinyar akwai abinda yake damunki. Meyake shirin faruwa dake ne Iman? Why duk tsawon rayuwarki baki taɓa yi mana irin wannan abun ba sai yanzu? Menene hakan ne? Waye yake neman illatamu ko ya haukata mune? Waye shi ko wace ita....?!" Ikram da Hanan suka shiga kuka ganin yadda Iman take yi kamar ana zare mata rai.
Mamah tana kacaniyar riƙe Iman tana cewa dasu Ikram suje su kirawo Areef Abba be dawo ba yana can asibiti wajan marasa lafiya. Hanan ta fira da gudu taje tana buga masa ɗaki cike da tashin hankali. Yana buɗewa tace yaje Mamah na kiransa, suka tafi tare daman yana zaune ne yana gyara kayansa. Ganin yadda suka rungume ta ne yasa Areef yi musu kallon sakaka, yaji Mamah na cewa.
"Areef jeka kirawo mana malam Babba yanzu." Ya tsaya zai yi mata iyaye ta daka masa tsawa ya fice da sauri. Babu dadewa kuwa sai gashi ya dawo ya sanar da Mamah cewa yana waje yaba jiranta.
"Kace ya shigo ciki."
"Mamah bedroom fa? Nanzata fitowa zakuyi falo?"
"A haka zamu fita falon tana cikin wannan yanayin Areef? Malam kaje kawai kace ya shigo ciki." Areef ya turo baki yana nannaɗe hannun riga, kan gadon ya hau yana cewa.
"Kuban ita na kaita, amma gaskiya ba zai shigo mana cikin ɗaki ba."
Ya shiga ƙoƙarin ƙarɓarta daga wajan Mamah. Wani irin shegen nauyi yaji, amman saboda baya son wani namiji ya ƙetare falo ya shiga ɗakin mahaifiyarsa ya daddage iya ƙarfinsa ya ɗakkota suka fita. Akan senta kafet (center carpet) ya direta, takai masa wata muguwar shaƙata tana ihu.
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun ku ƙwace shi kartai masa illa." Malam Babba ya faɗa yana naɗe babbar riga.
Mamah da su Ikram suka shiga ƙwatar Areef amman suka kasa. Shi kansa ƙoƙarin kwacewa yake yi amman ya kasa dan wani ƙarfi takeji ba musamman. Malam Babba ya isa wajan tare da dafe goshin Iman yaji wani irin fitinannan sanyi, ya shiga girgiza kai cikin hikima irin tasu ya kwace Areef sannan yasa suka riƙe Iman ɗin da iya karfin su.
"Wannan yarinyar akwai abinda yake damunta. Tun yaushe ta fara yin hakan?" Ya tambayi Mamah.
"Wallahi malam Babba ba haka take ba, amman daga lokacin da aka ce an ɗaura mata aure da shi Areef ɗin shikenan ta birkice mana ta fara cewa ita bashi take so ba."
"Ikon Allah, Toh ko tana da iskokai?" Ya tambaya yana kallansu su duka.
"A'a gaskiya." Mamah ta tabbatar masa.
"Hmmm Hajiya ya akai kuka sani? Ba makarantar kwana tayi ba?"
"Haka ne malam can tayi tun daga js ma kuwa."
"Toh zata iya yiwuwa sun shigeta. Kinsan yawancin yaran a can suke kwaso mutanan nan, kuma mafi yawanci suna shigar da bata dace da ɗan musulmi ba. Su kuma shaiɗanun aljanu suna shiga jikin yaran mu ne ta hanyoyi da yawa. Yawo babu kallabi, ko babu takalmi, shigar banza suna ganin cewa wayewa ce. Amman me yasa tunda hakan