an saba neman abu bata hanyar Allah ba, aikin likitancin da yake yi ma bawai kokarinsa ya kai shi ba duk sanadine na tsafi da asiri ta kaishi da samun babban matsayi a ƙasar nan. Wayarsa tai ringing ya janyo yana dubawa yaga sunan matarsa, ya kara a kunne cike da iko yai magana.
"Ya akai?"
"Haba Abban Meenal wannan wace irin tambaya ce?"
"Okay tuhuma ta kike yi ma?"
"A'a Allah ya baka hakuri, daman kira nayi na gaya maka Amir bashi da lafiya."
"Magani ne babu ko me? Kinga Salima bana son tsirfa da kinibibi. A gidana babu maganin da babu amman saboda ki takura min shine sai kin kira kin sanar dani cewar wani bashi da lafiya? Toh Kinga idan har an bashi magani be warke ba ki kaishi asibiti, karki sake kirana akan kowacce irin matsala saboda na ajiye muku isassun kuɗi da ba zaku takura min ba."
"Amman kuma Abban Meenal kuɗi kawai ai ba zasu yi mana maganin komai ba. Dole ina da buƙatar naji ka na kuma san halin da ake ciki."
"Shikenan tunda basu isheki rayuwa ba sai kin uzzara min, ina da abin yi sai anjima." Yana kaiwa nan ya katse tare da jan tsaki ya koma ya kwanta.
Washe gari duk da bashi da mafita wajan shiga gidan haka ya shirya cikin kananun kaya riga da wando, ya yi kyau a ido kamilallan mutum da bazaka taɓa cewa ya iya zagi ba, amman a zuci shaiɗan ma sara masa yake yi saboda mugunta. Guri ya samu ya zauna inda zai dinga hango masu shiga da fita a gidan, ya hango mota ta fito. Da sauri ya mike tsaye inda ya hango Areef da Abba sai kuma Mamah, sam bega Iman ba kasan cewar kwanciya tayi ta ɗora kansa akan ciyar Mamah.
Sai da suka yi nisa sannan ya tafi gidan yasan ma kawai yau zai sace Iman ya gudu da ita tunda iyayen basa nan. A hankali ya murɗa ƙofar falon ya leƙa, babu kowa. Ya nufi ɗakin su Iman ɗin ya hango Ikram tana danna waya ya dinga leƙe-leƙe ko zai hango Iman ɗin amman bai ganta ba. Ya juya zai tafi yaji Hanan dake fitowa daga toilet tana cewa.
"Allah sarki Iman tana bani tausayi wallahi. Allah yasa idan sunje malamin ya basu maganin warakarta har abada."
"Amin sisi, ni wallahi yanzu lamarin tsoro yake bani. Haka kurum kana tare da mutum amman ya cuceka ko kunya."
Jamil bai jira jin komai ba ya juya ya fita daga cikin gidan hankalinsa a tashe jin ance an tafi kai Iman wajan malami, yasan dole taimako zasu je karɓowa abinda shi kuma sam bazai so ba. Ya kira malaminsa yana dagawa ya sanar dashi abinda yake faruwa, malam yai buge-bugensa tare da cewa Jamil.
"Idan har muna son aikin da zamu yi maka yai kyau, dole sai mun samu jinin mutum ɗaya daga cikin ahalinka. Idan har mukai amfani dashi to babu malamin da zai iya basu maganin warakar Iman sai kai kanka."
Babu tsoro bare fargaba a batun da aka sanar masa, ya tambaya a cikin wane ahalin? Malam ya sanar dashi cewa ko ƴarsa, ko kuma mahaifiyarshi. Ba wani ɓata lokaci Jamil ya buɗi baki yace a dauki na.....
___________
A ƙofar wani ƙahon gida suka yi parking, Abba ya buɗe ya murfin gefenshi ya fita yana cewa.
"Ku bari na shiga na kafa mana layi, kunsan malamin akwai tarin jama'ar dake zuwa neman taimako a gurinsa, baga yara ba baga manya ba. Dan haka Hajiya ku kula da kanku da ita Iman ɗin. Areef kunna muku karatun al Kur'ani."
"Toh Abba."
Ya faɗa yana lalibo inda suke a cikin wayarsa. Shi kuma Abban ya shiga cikin gidan yana gyara babbar riga. Iman ta ɗaga hannu tana yiwa Mamah alama tana riƙe mara, Mamah tace.
"Cikinki ki ke ciwo?" Iman tai shiru saboda baji take ba tana sake shafa mararta.
"Okay ciwon mara ne?" Still gurin take riƙewa kamar zatai kuka ta kuma jijiga kai.
Hawaye suka gangaro daga cikin idanun Mamah suka ɓata saman kumatunta, cikin raunanniyar zuciya Mamah tace.
"Areef duba ka gani ko zaka gane abinda take nufi." Ya waiga yana kallon Iman. Ganin yadda take cije baki hannunta a can ƙasanta yasa shi saurin kawar da kai yana cewa.
"Kai gaskiya ban gane ba, ta iya yiwuwa fitsari zatai."
Babu zato bare tsammani Iman tana hawaye ta saki fitsari a gurin, sai hannun Mamah ta kamo tasa a dai dai gurin tana nuna mata. Zaro idanu Mamah tayi tana kuma fashewa da kuka tana cewa.
"Wannan wace irin masifa ce? Areef kaga kuwa fitsarin takeji gashi nan tayi a kwance."
Areef ya juyo a zabure yana gwale ido, mamaki tsababa a fuskarshi yace.
"Fitsari kuma? A haba dai kodai gumi ne Mamah?"
"Wallahi fitsari ne Areef, to an rufe kunnan da bakin ta ya zata iya cewa zatai fitsari uhmmm?"
"Toh ba sai ta buɗe taje kodaga can gurin tayi ba, wani abun ma dai tana sane take yinsa."
"Saboda iskanci kawai zata saki fitsarin Areef? Oh har yanzu kenan baka tausayin halin da take ciki ko? Ka ɗauka bama sonta muka haɗa auranku? Shi yasa ni sam bakai naso a bawa auran nan ba Haneef da ya fika hankali shi naso a aurawa Iman. Rufa maka asiri kawai mukai ganin kana neman janyo mana surutu a gari, sakarai kawai. Ka fita kaje ka samo min ruwa na zuba a wajan."
Ya buɗe ƙofar ya fita yana cicin magani. Wani shago dake kusa dasu ya shiga ya siyo pure water guda ɗaya yaje ya bawa Mamah, cike da ɓacin rai tace.
"Guda ɗaya ne zai ishe mu?" Yai shiru yana turo baki taja tsaki tare da fadin.
"Kaje ka karo min."
Ya juya kamar zai kurma ihu saboda takaici. Sai gashi ya dawo da leda guda, Mamah ta bishi da kallo. Wato saboda tace ɗaya yai kaɗan shine yaje ya siyo leda ɗaya, lallai yaran yanzu sai dai ka bisu da addu'a amman idan ka fiye takura musu wata rana shegen duka zasu yi maka.
Already wanda ya fara kawowa Iman ce ta karɓa tashanye shi. Mamah ta fasa wani tasa a inda Iman tayi fitsarin, ragowar kuma ta shiga dashi cikin motar bata sake yiwa Areef magana ba. Abba kam ya daɗe kafin ya samu layi yazo kansu. Ganin sauran mutum ɗaya yasa shi zuwa kiran su Mamah.
"Sannunku Hajiya, kuna ta zama yau akwai jama'a ne shi yasa."
"Babu komai Alhaji yanzu ya ake ciki?" Ta tambaya tana kallonsa.
"Allah sarki Khadijatu bacci tayi ashe?"
"Eh wallahi kaga fitsari ma tayi a kwancen daga nan kuma sai bacci ya ɗauketa." Abba ya sauke numfashi tare da cewa.
"Ba komai Insha Allahu daga yau waraka tazo, kamota mu shiga an kusa zuwa kanmu."
A hankali Mamah ta tashi Iman, ta farka a firgice tana ƙanƙameta. Addu'a ta shiga tofa mata har sai da taga ta sassauta riƙon da tayi mata sannan tace.
"Tashi mu shiga ciki Iman."
Buɗe ido tayi tana kallansu kafin ta fara yunƙurin tashi, nan fa tayi-tayi ta fito da ƙafarta amman ta kasa. Abba dake riƙe da murfin ƙofar yace.
"Fito Iman kar wasu su shige mana layi."
Kallon bakin su take yi wanda shine yake yi mata nuni da abinda suke furtawa. Ta sake kokarin ɗaga kafa amman ta kasa, sau kawai tayi murmushi tare da fashewa da kuka wanda babu ƙara sai zubar hawaye kawai. Wani irin tunani ne ya zowa Abba, da sauri ya kamo hannunta ya fito da ita, jikinsa yana rawa yace.
"Taka muje toh."
Ta girgiza masa kai alamar ba zata iya ɗaga ƙafafuwan ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Hajiya muna cikin masifa, ƙafafuwan ma ba zata iya tafiya dasu ba." Cikin shakka Areef yace.
"What?!" A gigice Abba ya dinga cewa.
"Gashi kuwa, gashi kuna gani ta kasa ɗaga ƙafafuwan. Wai shin me ake so ayi mana? Me yarinyar nan tayi ake neman salwantar da rayuwarta? Wannan lamarin ya fara bani tsoro, ya kuma fara sanya tunanina yana canzawa. Imanina yana neman ya raunana, zuciya ta tana yin duhu ku taimaka karta kaini ga halaka."
Mamah da jikinta yayi matuƙar laushi, ta rungume Iman. Yanzu kam ta kasa koda zubar da kwalla bare tayi kuka. Amman da an kalleta ansa zuciyar ce ta fara ƙeƙeshewa, lamarin ya fara yin gini a cikin jininta. Ta ɗaga ido ta kalli Areef da ya rasa abin yi saboda ganin Abban su yana neman birkecewa tace dashi.
"Zoka ɗauketa mu shiga ciki."
Babu musu saboda shi kansa yanzo abin ya fara bashi tsoro, ya ɗauki Iman a hannunsa yai mata riƙon jarirai.
"Muje." Cewar Mamah tana ciccijewa.
Suna tafiya Areef idanunsa yana kan fuskar Iman sai kallonta yake yi. Idanunta suna rufe saboda rana da take hasko su, sam besan zata buɗe ido ba sai gani yai ta kura masa nata idanun, jiyai yana shirin sakinta da sauri yaji ta ƙanƙameshi tare da kwantar da kanta a jikinsa saboda tsorata da tayi. Abba da Mamah dake bin bayansu suna ta tattauna yadda wannan tashin hankalin yake binsu salo-salo.
Basu jima zaune a gurin ba aka kirasu. Shiga sukai bakunansu dauke da sallama, Areef ya samu guri ya kwantar da Iman a wajan. Falo ne ƙaton gaske yashi kyau, daga can gefe shimfiɗar malamin ce inda yake ganawa da mutane. Su Abba suka gaishe dashi ya amsa sama-sama yana kallon Iman, tun kafin ma su gabatar da abinda yake tafe dasu sukaji yace........
(Masu karatu nasan akwai wadanda zasu ce abubuwan da Iman ke fuskanta suna yawa. Kamar yadda za ku yi mamaki haka nayi kafin na tabbatar da fiye da wannan masifar. Wasu abubuwan bazan iya sakawa ba saboda karma ku karyata ni da yawa. Amman a duniyar nan babu abinda ɗan adama ba zai iya yiwa ɗan uwansa ba. Allah yasa mu dace duniya da lahira 🤲)
*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
2/24/22, 08:53 - Buhainat: *ZO...GA....N...*✍️
*TOP 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*Wattpad:- Hajjac*
*22*
"Na bada ya ta, ayi duk yadda za'a yi malam karsu samu maganin matsalar nan. Bana son Iman ta auri kowa sai ni, dan haka a cikin irin aikin ka ina son ka raba auran da akai mata da Areef."
Malam ko kuma ace bokan Jamil yai dariya son ranshi tare da cewa.
"Na yadda kana san yarinyar tunda har ka bada rayuwar yarka. Idan aka kammala aikin nan kasa a ranka cewar ta zama taka halak Malak."
Daɗi ya mamaye zuciyar Jamil, babu abinda ya dameshi akan abinda yake gudanarwa na son rai. Yadda zuciyar shi ke a ƙeƙeshe yana da yakinin in duka rayuwar danginsa ake da bukatar bayarwa zai bayar. Ai kuwa ko barin gurin beyi ba wayarsa ta shiga neman agaji, yana dubawa yaga matarsa ce, ya kara a kunne yana tarin munafunci. Cikin kuka yaji tana yi masa magana cewar.
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun Abban Meenal na shiga uku na lalace."
"Menene haka kuma? Haba ai sai ki ɗaga min hankali wane irin kin shiga uku harda su lalacewa.?"
"Meenal ta mutu Jamil, ta mutu na shiga uku."
Duk da cewar shine sanadin mutuwar ƴar tasa, kukan da yaji matarsa nayi ya ɗan sosa masa zuciya, Amman da ya tuna cewa Iman zai mallaka sai ya ɗan dake cikin nuna tashin hankali da damuwa yana cewa.
"Meenah na mutu? Ban gane ba kin sani a duhu garin ya ya?"
"Ciwon kai na minti biyu wallahi."
"Gani nan Insha Allahu zan taho." Tana jin yace haka ta katse.
Wayar bokansa ya sake kira nan ya shaida masa cewa aikin ake yi. Kai tsaye ya koma hotel ya tattare kayansa ya fito ya nufi jahar Zamfara.
_________________
"Subahanallahi! Wannan yarinyar fa? Abinda yake jikinta yafi karfin tunaninku, waye yake mata wannan abun?" Malam ya faɗa cike da tashin hankali.
"Wallahi malam wannan shine dalilin da yasa muka zo nan, mun kasa gane kan yarinyar nan daga lokacin da aka ce za'a ɗaura mata aure shikenan muka kasa gane mata, yanzu haka malam babu ƙafa ba kunne bare kuma ta buɗe baki tayi magana."
"Tabbas haka ne Hajiya, dan abinda na gani a jikin yarinyar nan yafi karfin baki na. Agaskiya duk wanda yai mata wannan abun zai iya yin komai a rayuwarsa. Sai an tashi tsaye sosai akan ta dan kuwa tana cikin tarkon da sai anyi da gasken-gaske za'a iya samun kanta."
"Toh yanzu malam ya zamu yi?" Abba ya tambaya yana goge zufa da take tsatsowa daga fuskarsa.
"Addu'a! Idan nace addu'a ina nufin addu'a ta gaske mai tsananin kyau. Zan baku magunguna da in akai amfani dasu Insha Allahu za'a samu dacewa, amman fa sai an miƙawa Allah lamarin dan shine yake warware duk wata matsala ta rayuwar mu. Allah sarki baiwar Allah, ubangiji ya dubi rayuwarki ya kawo miki sassauci nan kusa." Duka suka amsa da.
"Amin."
Ya juya tare da ɗakko wani ruwan zam-zam dake gefensa yai addu'a tsawon lokaci sannan ya miƙawa Areef dake kusa dashi yace a tada ita a bata tasha. Da taimakon Mamah suka bata ragowar malamin yace a shafa mata a ƙafafuwan ta idan anje gida. Ya haɗa musu da wasu layoyi da garin maganunguna, yace duk yadda ake ciki idan da ci gaba ko babu su kuma dawo da ita.
"Malam wasu sukan ce wai a raba auran shine masalaha, kai ya kake ganin lamarin.?" Abba ya yi maganar cikin sanyin jiki.
"La'lah alhaji, koda wasa kar a raba wannan auran koda kuwa barin shi zai sa wani ya rasa rayuwarsa a cikin su. Allah ne yace ayi aure, kuma da ikonsa da buwayarsa ya haɗa wannan abun, Toh dan me saboda wasu shaiɗanu makiya Allah mashurikai zasu dinga sawa ana yin abinda Allah baya so? Kubar musu auran su aje a haka."
Wannan kalmar ta aje a haka ta ƙarfafa musu guiwa matuƙa, musamman Abba da har ɗan ƙaramin murmushi yayi. Areef kam ya gama tabbatar da cewa wannan auran ba me rabuwa bane bare ya saka ran za'a ce dole ya saketa dan shi babu macen da ta kwanta a ransa sama da Feenah, yana nan kuma yana jiran dawowarta bai fidda rai ba. Mamah ta saka magungunan a cikin mayafi shi kuma Abba ya zaro kuɗi ya bawa malam yana ta godiya.
"Ɗakkota mu tafi Areef." Cewar Abba.
Areef ya shiga jijiga hannu shi a dole suna yi masa zafi sai yatsina fuska yake yi yana tattare hannun riga kamar mai shirin yin dambe.
"Wai meye hakanne?" Cewar Mamah tana kallon Areef.
"Mamah yarinyar nan shegen nauyi gareta wallahi, carbohydrate ya yi mata yawa, bakiji yadda kafaɗuna ke ciwo ba." Ya faɗa yana shafa gurin.
"Ko zasu karye sai ka kaita mota, duka-duka Iman ɗin nawa take..?" Cewar Abba yana mikewa.
"Abba wallahi a ido ne kamar ba zatai nauyi ba."
"Anji Toh, yanzu ma daure ka ɗakkota mu tafi Abban ku zai koma asibiti gurin su liman." Kamar ƙaramin yaro haka ya turo baki ya ɗauketa.
Suna komawa gida Mamah ta haɗa maganin kamar yadda malam ya gaya musu yadda za'a yi haka tayiwa Iman. Suna dawowa daman Abba ya juya ya wuce asibiti, Areef kuma ya shiga ɗaki ya dauki wayar Feenah ya haɗa da tashi yabar gidan. Koda maganin ya fara ratsa Iman wasu miyagun abubuwan tsoro ta dinga gani, da kyar Mamah ta samu Iman ta nutsu da addu'a.
Sai dare Areef da Abba suka dawo gidan, Mamah suna ɗaki saboda yanayin Iman yasa suka rage zama a falo sai bedroom ɗin Mamah. Areef ya shiga bakinsa da sallama, ya yiwa Mamah ya mai jiki ta amsa su Ikram suka yi nasa sannu da dawowa ya kalli kan gadon inda Iman ke kwance gefenta MP ce an saka mata karatu tana saurara, bece komai ba ya juya yabar ɗakin.
___________
Jamil na isa ya tarar har an daɗe da kai gawar, ya samu matar tashi har lokacin ba ta bar yin kuka ba, tana ganinsa ta kuma fashewa da kuka tare da rugawa cikin ɗaki. Ana ta yi masa gaisuwa yana amsawa jiki a sanyaye, wata mata ce dake bakin kofa tace yaje ya lallasheta tun ɗazu ake bata hakuri amman bata bar yin kukan ba. Shi dama dake yasan musabbabin da zai sa taki denawa, yana shiga kuwa da maganar ya fara cin karo.
"Shikenan Jamil na rasa Meenal, sauran Amir kadai gareni a duniyar nan ba zan kuma samun irin su ba Jamil."
Jikinshi ya janyo ta yana faman lallashi, irin kukan da yaga tana yi ne ya tabbatar masa da cewa duk lokacin da tasan shine yai sanadin mutuwar ƴarsa abin ba zai yi kyau ba, ya tabbatar sai tayi sanadin da zai sanyaya mata rai akan shi.
"Kiyi shiru Salima kukan nan fa ba zai dawo da yarinyar nan ba. Addu'a kawai zaki mata, kuma kinsan mutuwar yaro ba abin kuka bane dan yanzu haka tana cikin ni'imar Allah. Kiyi hakuri muyi fatan Allah ya bar mana Amir har girmansa." Cikin kuka tace,
"Me yasa bamuyi wannan tunanin ba kafin a cire min mahaifiyar nan? Me yasa bamu bari mun haifa da yawa ba? Kai ne duk kaja muka yi wannan gangancin, ina tsoran lokacin da zaka bukaci wasu ƴaƴan gashi ni ba sake haihuwa zanyi ba." Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka mai taɓa zuciya.
"Kiyi shiru Salima, ni kinsan ba wani son tara yara nake yi ba wanda har yanzu ba wai na canza bane. Allah ne daman ya bamu Meenal kuma ya karɓi abarsa, duk karfin mutum kuma ba zai iya dawo da ita ba. Kiyi hakuri dan Allah kar kukan nan ya saki ciwon kai." Ta shiga share hawaye tare da cewa.
"Yanzu babu yadda za'a yi na kuma haihuwa?" Jamil ya kalleta cike da mamaki.
"Salima...! Haihuwa kuma?"
"A matsayinka na kwararraren likita nasan ba zaka rasa yadda zaka yi ba wajan ganin na