Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   6 / 38

15K to 18K   out of 113.7K words

ba.

Wasu hawaye suka zubo mata tana ta yiwa Sultan godiya, da haka ta bar gidan ba tare da ta kuma bi ta kan Feenah ba. Suma duk fita suka yi aka barta ita kadai taci kukanta, tsabar ta lallasu ko hannu bata iya d'agawa. Cikin zuciyarta mamaki take yi 'wai duk saboda Sultan Mommy ta dage iya karfin ta babu ko tausayi da tunawa cewa ita ta haifeta, ta dinga zabga mata bulala kamar wata jaka.'

A ranar Feenah da zazzabi ta yini. Inda Allah ya taimaketa Sultan yana nan bayan ƴar uwarsa ta bar gidan ya gama shirya kayansa na komawa gurin karatunsa ya shiga d'akin da take bakinsa ɗauke da sallama. Yayi mamakin yadda ya ganta inda suka barta, sai dai kawai wannan karan a kwance take tana jan numfashi da kyar. Ya karasa gurin da sauri ya durkusa yana tambayar ta.

“Feenah lafiya? Menene?? Ta girgiza masa kai alamun a'a ba lafiya duk da cewa bata son jin koda muryarsa.

“Me ya sameki? Ko abinda Mommy ta yi miki ne?? Ta d'aga hannu a hankali tana nuna masa goshinta.

“Kanki ne yake ciwo? Subahanallahi sannu kinji? Bari naje na kira wata tazo ta baki taimako.?

Babu yadda ta iya dole ta barshi ya bata taimako dan babu abinda zata iya tab'ukawa a wannan halin da take ciki. Babu ɗadewa sai gashi da wata nurse tazo ta d'agota tare da maida ita kan gado, ta yi mata allura tare da d'aura mata drip.

“Insha Allahu zata samu sauki engineer.? Cewar Nurse d'in tana gyarawa Feenah skirt d'in jikinta.

“Na gode sosai bari na zo na mai dake.?

“A'a Engineer ka barshi kawai zan samu abin hawa na tafi. Kai dai kaci gaba da kulawa da ita, Allah ya kara lafiya.?

“Amin nagode sosai.?

Suka yi sallama ta tafi, Sultan kuma ya koma gurin Feenah yana kallon yadda Mommy ta sab'a ma ta kamanni, idan ka ganta ba zaka ce Feenah bace saboda sab'a mata kamanni da kumburin dukan ya yi. Ganin tana lumshe ido ya tabbatar masa da cewa bacci zata yi, sai ya kyale ta ba tare da ya yi mata maganar da yaso yi mata ba. Tashi ya yi Ya bar gidan gaba ɗaya saboda zai hadu da wani abokin sa a lokacin.

______A can gidan su Feenah kuwa, Alhaji Nura na shiga d'aki ya wuce cike da tashin hankali. Diary d'in sa katoto.. Gundumeme ya dakko ya duba sunan karshe wato Nafisatu Nura, ya duba date of birth d'inta da kuma time d'in da aka haife ta da ranar da watan, ya zauna dabar a bakin gado yana share zufa. Tabbas ƴarsa ce ta cikinsa ma kuwa. Kuma haihuwar gida aka yi bare ya yi tunanin ko a asibiti aka canza masa baby aka bashi wannan da tazo zata sa shi ciwon zuciya baiji ba bai gani ba.

“Innallilahi wa'inna'ilaihir raji'un.?

Ya furta da karfin gaske yana sauke numfashi mai tattare da takaici. Tunda yake be taɓa shiga kotu da sunan kallon sharia ba bare kuma ace shi aka kai. Yau gashi ƴarsa ta cikinsa ta kai shi ƙara saboda kawai ya aura mata wanda yake ganin zai iya rike ta da gaskiya.

Bema san Hajiya Saratu ba ta gidan ba, sai da ya kwalla mata kira cikin masifa sannan babbar ƴarsa Asma'u ta sanar dashi cewa taje gurin Nafisa. Yasan kome zai kaita gidan Feenah ba me daɗi bane tunda itama tana cikin tashin hankali, amman yaso yasan ta tafin da ya bata sakkon cewa ta gayawa Feenah cewa karta dawo masa gida, taje tayi abinda taga ya dace da ita.

Haka ya zauna sai d'acin rai yake yi har hajiyan ta dawo, nan ta sanar dashi komai har yafe kudin da Sultan ya yi. A sannan ne yaji ya kasa cewa Mommy kar Feenah ta dawo masa cikin gida, yasan ba zata tab'a jin dad'i ba, ya barwa kansa wasu abubuwan dan ba komai zai yi mata ba na rayuwa idan ta zo, tana gani zai yiwa sauran yaran shi amman ban da ita tunda ta tozarta shi.

____Koda Sultan ya dawo still bacci yaga tana yi, ya ajiye mata ledar yogurt da snack d'in da ya taho mata dashi, ya ajiye mata a kusa da ita yadda idan ta farka ba zata sha wahala ba wajan d'auka. Ya zare mata drip d'in ganin sauran kad'an sannan ya koma bedroom d'in sa. Bata farka ba sai kusan karfe uku na dare. Lokacin fuskar ta kara kumbura bakinta da idanunta sunyi suntum dasu kamar wacce aka sawa yeast.

Tana hawaye ta sakko daga gadon saboda fitsari da ya addabi mararta. Ta dawo ta kwanta tare da buɗe ledar sai dai ba zata iya ci ba saboda har lokacin zuciyarta cikin rad'ad'i da zafin dukan da Mommy tayi mata take. Haka ta kwana tana sak'e-sak'e tare da tunanin yadda zata hadu da Areef idan ta koma gidan su. Koda gari ya waye Sultan ya shigo ya tarar da ita a kwance, idanunta na kallon kofar shigowa kamar wacce take jiran wani.

Kawar da kai tayi gefe da alama bata son su had'a idanuwa, ya girgiza kai a ransa yace. 'mai hali baya canza halinsa.' A zahiri kuma ƙarasawa ya yi inda take yana tambayar ta jiki tayi shiru dan bakin ba bazai buɗu ba kasan cewar ya kumbura sosai. Yana tsaye gabanta yace.

“Zan tafi na koma inda nafi wayo, ina miki fatan alkairi cikin Feenah. Na gode da kasan cewar ki gare ni a baya. Nasan family ɗina ba zasu barki a cikin gidan nan ba, amman naso na baki shi koda su Daddy zasu hanaki shiga nasu gidan, nasan ni na janyo miki fushin su dana dage kan cewar sai mun auri juna alhalin ke bakya ra'ayi na. Amman duk da haka.?

Ya fad'a tare da zaro wani mukulli daga cikin aljihunsa ya ajiye mata kusu da ita yana cewa.

“Duk da haka ga mukullin guest house d'ina nan, kiyi amfani dashi daga nan har zuwa lokacin da Allah zai fito miki da mijin da kike so. Ba kowa yasan da gurin ba sai brother ɗina kuma baya ƙasar nan. Ina miki fatan alkairi da samun nutsuwar zuciya a koda yaushe.?

Yana gama fad'ar haka ya ajiye mata dubu hamsin ko zata bukaci kudi, ya juya ya fita. Feenah kuwa ko tausayi be bata ba haka taci gaba da zama a gidan har ta warke ras da ita. Kayanta ta kwasa ta kira taxi ya kwashe ta bayan ta barwa mai gadin gidan mukullayen ta nufi gidan su........✍️


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR8iiiii KDAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.








*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 11:18 - Buhainat: *ZO GARE NI...*
Free page 7

NA
*HAJJA CE 👈*

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*💡



Duk da cewar ba wani mugun tsoran shiga cikin gidan take yi ba, amman da mai motar ya gama parking sai da taji tana shakar shiga. Kamar tace ya juya da ita gwara ta tafi guest hause d'in da Sultan ya bata damar zuwa, sai kuma taga gwara ta shiga idan ma kasheta zasu yi gwara su yi.

Ta fito tare da bawa mai motar damar sauke mata kayan ta a nan kofar gidan nasu. Bayan ya kammala saukewa ta zaro kuɗinsa ta bashi ya tafi ita kuma ta ɗauki ƙaramar jakar da zata iya shiga da ita. A hankali ta sanya ƙafarta ciki sai raba idanuwa take yi. Daddy yazo fitowa suka yi kicibus da juna, Feenah tayi saurin yin baya kanta a ƙasa ta durkusa tana gaishe shi.

“Daddy ina kwana?? Ta fad'a kasancewar safiya ce.

Alhaji Nura ya gota ta tare da ficewa kai kace be san da wata halitta a gurin ba, bare ya nuna cewa yaji gaisuwar da ake yi masa. Da kallo Feenah ta bishi har ya fice daga gidan, ta mike ta shiga ciki bakin ta ɗauke da sallama.

“Assalamu alaikum.?

Daga cikin parlor aka amsa mata, jin muryar Yayarta ce yasa ta shiga kai tsaye. Kallan-kallo suka shiga yiwa juna, inda Yayarta mai suna Zainab ta yanke musu kallon da suke yi ta hanyar d'aga murya tace.

“Feenah...!? Furucinta ya fito da sauran ƴan uwan daga d'aki.

Duk suka tsaya suna kallonta kamar sabuwar bakuwa. Itama kallon su tayi daga bisani ta tab'e baki taje ta ajiye jakarta ta kuma fitowa kofar gida. Almajiri ta samu duk ya shigar mata da komai cikin gidan ta biya shi sannan itama ta shiga, wannan karan Mommy ta fito da taji suna cewa harda kayanta tazo.

“Mommy.? Feenah ta kira sunanta cikin sanyin jiki.

Mommy tai murmushin takaici tana bin Feenah da kayanta ta tab'a baki.

“Tun da haka kika zab'arwa kanki Nafisa, sai kizo muyi ta zama tare.?

Tana kaiwa nan ta bar gurin ta shiga kitchen dan ƙarasa abin da take yi. Feenah kuma ta samu guri ta zauna tana jiran taji waye zai yi magana a cikin ƴan uwan nata.

“Kin dai ji kunya Feenah wallahi, ki rasa wanda zaki tozarta a idanun duniya sai iyayenki.? Cewar Zainab tana harararta.

“Toh idan fitsari banza ne kaza tayi mana. Kije ki d'an-d'ana auran sai kizo kiyi min maganar da kike so.? Feenah ta fad'a cikin gatsali.

Ran Zainab ya yi matuƙar baci, ta nufe ta a fusace tare da shak'o mata wuya suka fara fad'a. Su Asma'u suka shigarwa Zainab hakan yasa suka yi galaba akan Feenah. Mommy najin su tayi musu banza har suka yi suka gama, dan idan da sabo ta saba da jin hayaniyar su.

“Yarinya idan kika ce zaki raina mu dan kinje kin zama tantiriya a ƙasar turawa, wallahi jikinki ne zai gaya miki. Marar kunya fitsararriya, mun fiki iya iskanci idan shi kike je, bar ganin kin yi aure kina ganin kamar zaki Iya taka mu yadda kike so.?

Ba tayi magana ba dan tasan kowa ya tsane ta, ita kuwa indai dan ta kaso aure ne ake mata wannan abubuwan to zasu mutu suna yi dan ba komawa za ta yi ba. Tashi tayi ta ɗauki kayan ta kai dakin su, wanda a da kafin tayi aure ɗakin Mommy take zaune, yanzu kam ko gigin zuwa can ba tayi ba, ta shigar dasu dakin ƴan uwanta.

Da yake kato ne d'akin guri guda ta ware ta jera akwatunan ta da sauran kayan ta, suna kallonta ba bu wanda ya kula ta har ta shimfid'a sallaya ta zauna tare da ciro wayar ta tana dannawa. Kowa da nashi tunanin a zuci, dan ba karamin firgitasu tayi ba da ta kammala jera trolleys d'in ta, abin sha'awa kai kace yanzu aka kawo kayan lefen.

Da rana aka kammala abinci Kowa yaje ya zubo yana ci ba a yi mata tayi ba, ita kuma tana tsoran a yi mata gori. Tashi tayi da hijabi a jikinta wanda tayi sallah ba ta cire ba. Kofar gida ta leka ta kira wani yaro d'an makotan su, ta bashi kudi ya siyo mata tsire da wainar shinkafa mai kuli, sai lemon jarka Fanta mai d'an karan sanyi. Ya kawo mata ta shiga cikin daki ta zauna tana cin abin ta hankali kwance.

Ramla ce tun da taga Feenah ta wuce da leda taji tana son sanin menene a ciki, hakan yasa bayan kamar minti goma da wucewar Feenah daki, itama ta tashi ta shiga. Zaune ta ganta a kan sallayar da ta shimfid'a tun zuwanta gidan, sai cin namanta take yi babu wata fargaba. Ramla ta juya ta fita da sauri sai dakin Mommy taje ta kwashe komai ta sanar da ita.

“Rabu da ita, kuna nan zaune kuɗin zasu kare dan kaniyarta dole ta ci wanda aka dafa a gidan.?

Cewar Mommy, duk a zaton su Feenah ta yi haka ne dan gadara basu san tsoron cin abincin gidan tayi ba dan kar a yi mata wulakanci. Haka Ramla ta tashi daga gaban Mommyn su har zata zauna a parlor sai taji tana son cin tsiren nan fa, kawai sai ta shiga d'akin ta kwanta a gado tare da janyo wani littafi ta shiga karantawa. Da yake Feenah ba ta da rowa, ta kalli Ramla tana cewa.

“Ya Ramla ga tsire.?

“A'a ki barshi.? Ta fad'a kamar gaske.

“Dan Allah kizo kici.? Feenah ta fad'a cikin kulawa.

“Yanzu na gama cin abinci.? Ramla ta kuma daurewa wajan nuna be dame ta ba.

“Shikenan gashi nan zan ajiye, idan zakici ko zuwa anjima, ni dai na koshi.?

“Toh na gode.? Ramla tayi mata godiya ba tare da ta juyo ba.

Haka ta ci gaba da rayuwa a gidan su har ta koma makaranta ta karasa secondary school ɗin ta. Duk a lokacin dama ta nemo Areef sun ci gaba da soyayyar su wacce tafi ta baya zafi, sai dai wannan karan Feenah tana shigar masa da wasu sababbin al'amura waɗanda shi kansa Areef be yarda su dinga yi ba, Amman baya iya yi mata magana akan ta dena, ga gudun ɓacin ranta da yake ji.

(Mu koma cikin labarin mu).

***** ******

A kunyace Areef ya miƙe kai tsaye ɗakinsa ya wuce Mahmah tana binsa da kallon Allah ya tsare shi. Gado ya faɗa tare da lumshe ido yana tunanin yadda ya baro Feenah cikin wani irin yanayi. Yasa yatsunsa guda biyu yana mustsuka idanunsa tamkar wanda yake jin ƙaiƙayi a ciki. Shi kam yana son Feenah zuciyar shi tana matukar son kasan cewa da ita duk da cewa ta taɓa yin aure.

Wayarsa ya ciro daga aljihun wandonsa ya lalibo sunan ta tare da dannawa yana bin alon wayar da kallo. Cikin kuka yaji muryarta daman yasan dole zai tarar da hakan idan ta ɗaga, ya lashi leɓunansa duka biyun a lokaci ɗaya tare da haɗiyar wani baƙin yawu yana cewa.

“Bana son kukan nan kiyi shiru ko na kashe waya ta.?

Feenah tayi saurin goge hawayen jin yace zai katse tasan tsab zai iya dan ba iya lallashi ya yi a waya ba sai suna tare.

“Abba ne ya kira yace yaga motar shi a nan gurin, tsoro ya kamani karya shigo yaga daga ni sai ke rai na ne zai ɓaci ya kuma hanani zuwa. Ki dena kukan nan dan Allah my sweetie.?

Taja numfashi tare da sauke shi da karfi har Areef yana jiyowa, cikin kasalalliyar murya take masa magana.

“Bana son na rasaka baby, idan aka yi yinkurin raba mu da kai zan iya mutuwa wallahi. Dan Allah ka zo ka aure ni muyi rayuwar mu tare.?

Sai da ya kalli ƙofar ɗakin nasa jin kamar motsi, ganin babu kowa yasa ya kuma gyara kwanciyarsa yace.

“Mubi komai a hankali sweetie, a yanayin shekaruna yanzu su Abba ba zasu taɓa yi min aure ba. Ko da na dawo ma sai da Mahmah tace min karta kuma jin ance nayi budurwa bare ace an ganni da ita a mota. Kiyi hakuri mu jira lokaci.?

“Har yaushe ne lokacin baby na? Bazan iya kara koda shekara ɗaya ba ban mallakeka ba. Kallonka kawai idan nayi baki ji abinda nake ji ba wallahi. Ka gaya musu kai zaka iya aure ai basu zasu zauna maka ba please ka ceci rayuwata dan Allah..?

Kuka ya kuma kwace mata. Al'amarin Feenah fa wani lokacin yana bashi tsoro sosai, idan ta birkice sai ta koma masa tamkar wata ƴar barki, ya kuma san bata ɗaya daga cikin watsatsun mata, akan shi kawai take neman watsewa saboda mugun son da take yi masa.

“Kayi shiru baby baka ce min komai ba.? Ya shafa dogon hancinsa.

“Na rasa me zan ce ne shi yasa.? Cikin tashin hankali tace.

“Zan zo gidan ku ni zan gayawa Mahmah yadda muke son juna, su yi hakuri su barmu muyi auren.?

Bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba jin kalamanta, ya kuma san ba ƙaramin aikinta bane zuwa gidan nasu. Ya shiga zagaye ɗakin yana dafe da goshinsa yace da ita.

“A'a Feenah karki zo gidan nan, zuwan ki zai sa su yi zaton ko baki da kunya.?

“Ai indai a kan kane tabbas bani da ita baby, zan iya tsayawa gaban duk wanda yake shirin rabamu na wanka masa mari.?

“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. Zamu ɓata dake kuwa indai zaki aikata wannan ɗanyan aikin.?

“Shikenan na fasa zuwa, amman sai ka yi min alkawari babu wanda zai raba mu da juna.?

Areef ya rintsa idanunsa, yau kam ya shiga uku da fitinar Feenah, be san ya zai mata ba kamar yadda yasan koda wasa ba zai iya zuwa ya tunkari iyayensa da maganar aure ba, ko yayansa be yi ba bare shi da yake ɗan tatsitsi dashi.........✍️



*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:-

6 / 38