Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   35 / 38

102K to 105K   out of 113.7K words

ba iya kacin.

"Thank you sweetheart, ke ɗin ta musammance agurina."

Maida wayar yayi cikin aljihun ya shiga banɗaki dan yin wanka. Yana fitowa ya sake kiran wayar Iman still bata shiga sai kawai yayi shahada ya kira Mamah. Bayan sun gaisa yajita faran-faran har zai tambayeta sai yaji tace.

"Ina Autar tawa?" Gabansa ya faɗi 'kenan Iman bata Kano? Shikenan tana gurin Sen Muhammad.

"Hello Areef?" Yaji Mamah na magana cikin fargaba yace.

"Na'am Mamah."

"Cewa nayi ina Autar tawa?"

"Bacci take Mamah."

"Allah sarki, wai nace bazaka dawo da ita gida bane sai ta haihu a nan babu wani mai taimako?" Saboda tsabar ya ruɗe besan lokacin da yace mata.

"Sai gabo."

"Masha Allah gobe zaku taho kenan?" Yace.

"Insha Allahu Amman ita kadai saboda ban kammala jarabawata ba."

"Toh Kano zata taho?"

"Anya kuwa Mamah? Ina jin sai ta fara hutawa a gurin Babanta kafin ta ƙaraso."

"Hakan ma yayi ai, daman dan kar a barta daga kai sai ita kuma haihuwar fari." Yace.

"Aikuwa dai Mamah."

"Toh bari naje baki gareni a falo." Ta faɗa tana son ajiye wayar.

"Okay Mamah bye."

Ya sauke wayar tare da dafe kai kafin ya yi kundunbalar kiran Sen Muhammad. Cike da fara'a yaji shima yana masa sallama, Areef cike da girmamawa ya shiga gaidashi inda yaji yana cewa.

"Sai da ta ƙaraso take ce min ita kadai tazo, ashe baku gama jarabawar ba?"

"Eh Baba mun dai kusa sauran guda uku."

"Toh Allah ya baku sa'a yasa a fito da Good result."

"Insha Allahu Baba na gode Allah ya saka da alheri ya kara buɗi."

"Amin ya rabbil alamin, ba dai matsala ko?"

"Babu komai Baba."

"Toh shikenan anjima zansa a tura muku kudi ka'ida sauran abokan naka." Areef ya rintsa ido tare da yin godiya marar iyaka a gurinsa, daga nan suka ajiye. Ya sake gwada kiran Iman still be sameta ba. Amman yaji daɗi da har yaji bata gayawa kowa abinda ya barta US ba.

Koda Feenah ta ishe shi da kira kashe wayar yayi, karatun ma kasa yi yayi saboda tunanin halin da Iman ke ciki. Yasan tabbas duk inda take a yanzu tana cikin damuwa da bacin ransa. Ya kuma rasa yadda zai nuna mata Cewa ita ɗin mai daraja da mutunci ce a cikin zuciyarshi da rayuwarsa gabaki ɗaya. Zuwan Feenah karo na biyun nan fitina ce da tashin hankali a gurinsa, sai dai ya rasa me yasa yaki yi mata wulakancin da zai sa ba zata kuma nemansa ba a rayuwarta. Haka ya kwana ya tashi babu sukuni, gashi har lokacin beji muryar Iman ba. Wacce ke Abuja Sen Muhammad ya ɗakko mata mahaifiyarsa suna zaune a gida ɗaya tana bata kulawa ta musamman.
________________

Sai da ta yi sati guda ba tare da su Mamah sunji labarin zuwanta ba, dan su kansu basu samunta a waya sakamakon tunda ta kashe bata sake kunnawa ba. Sai da abin ya ishesu sannan Abba yake tambayar Sen Muhammad yaka sanar dashi zuwanta, harma da abinda ta gaya masa cewar ta dawo ne dan ta haihu a gaban iyayenta. Mamah da Ikram suka shirya Abba yasa driver ya kaisu Abuja dan su gano lafiyarta.

Tunda Iman ta gansu take kuka, gabaki ɗaya ta kasa yin shiru saboda yadda abin yake ci mata zuciya. Gashi sun kada sun raya ta sanar dasu abinda yake faruwa taki. A ranar kuma shima Areefullah ya ƙaraso nigeria, kai tsaye kuma Sen Muhammad yasa aka kaishi inda take, sai dai besan cewar su Mamah na garin ba. Yana shiga dama security duk sun san matsayinsa a gidan hakan yasa basu yi wani tsaye-tsaye ba suka barshi ya shiga. Yasha mamakin ganin su Mamah, hankalinsa kuma yai masifar tashi.

Iman na ganinsa zuciyarta ta kuma harzuƙa dan ba ƙaramin tsanar shi tayi ba. Cikin fushi tsabar idanunta sun rufe ta manta Mamah dake gurin da kuma matsayinta a gurin Areefullah ɗin, ta shiga nuna shi da yatsa tana cewa.

"Ko ka tashi ka fita ko kuma nasa karnukan gidan nan Suyi min yaga-yaga dakai."

"Subahanallahi Iman lafiya?" Mamah ta tambaya cike da tashin hankali.

"Ku rabu dashi zuwa yayi ya ƙarasa kasheni a gidan ubana. Mekazo yi min bayan na barka da ƴar iskarka? Zuwa kai ka tabbatar da ganin bana numfashi a doran duniya ta yadda zakuci gaba da ɓalɓalcewarku kai da ita ko? Toh bazan mutu ba, Insha Allahu sai kaga yadda zan maka nisa, nisa irin wanda komai zaka hau baka isa ka hangoni ba. Kaje wacce kake ganin ta fini komai tayi maka duk abinda kake muradi har karshen rayuwarku."

"Ya isa haka Iman zoki zauna, bakiga halin da kike ciki bane.?" Cewar Hajiyan sama wato mahaifiyar Sen Muhammad dake kula da ita.

"Akwai abinda yake faruwa a tsakaninsu, Hajiya barta tayi magana. Iman me yake faruwa?" Cewar Mamah da jikinta har rawa yake saboda tsabar son jin inda matsalar take. Abinka da mai ciki, cikin ma kuma tsoho da ake saka ran haihuwa yau ko gobe, cikin tsananin zafin zuciya Iman ta sake nuna Areef tana cewa.

"Gashinan da bakinsa ya faɗi abinda yake faruwa, kayi magana ka sanar dasu gaskiyar lamarin." Areef ya fara girgiza kai, cikin nuna rashin sanin abinda take nufi yace.

"Wai me yake faruwa ne? Ni bansan akan abinda take nufi ba. Abu ɗaya na sani na tashi na tarar bata cikin gidana, na kira wayoyinta tun a ranar wallahi bana samu. Dan haka ni kaina ina son sanin damuwarta." Habawa Iman najin sabon rainin hankalin da yazo dashi, ta kuma gigicewa, hankalinta ya sake tashi tace.

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun kaji tsoran Allah Yaya, karka manta idan akwai duniya to kiyama ma ba karya bace." Ta sake juyawa wajan Mamah cikin kuka take cewa.

"Mamah shida Feenah nane, Feenah ta dawo cikin rayuwarsa ta yadda ya ɗauki duk wani abu mai muhimmanci ya ajiye a gefe, baya komai sai na ta ta, idan kinga irin iskancin da suke yi karema ba zai ci ba Mamah. Wallahi tallahi ban masa karya ba, wallahi ya sani Mamah karya yake yi..."

"Yi mana shiru Khadija, mijin naki kike cewa karya yake yi? Ashe baki da kunya?" Cewar Hajiyar sama cikin faɗa. Da yake Iman ɗin tana cikin mood ɗin bacin rai ta kuma cewa.

"Toh Hajiyan sama ya faɗi gaskiya mana ya za'a yi yace besan komai ba? Wallahi ya sani na rantse da Allah ya sani, nikam na gaji dashi ba zan kuma komawa gidansa ba."

Areef ya sake sunkuyar da kai yana rintsa ido kirjinsa na ta tsananin bugu, gabaki ɗaya ya rasa ya zai yi. Nan da nan Mamah ta janyo Iman jikinta tana lallashi, idanunta akan Areef tace.

"Bazaki masa karya ba Iman ai munsan Feenah mun kuma san alaƙarsu. Ashe sun kuma jonewa ko? Amman me yasa baki faɗa ba tuntuni kika bar abin a cikin zuciyarki? Yi shiru ki dena kukan fatan mu a yanzu Allah ya saukeki lafiya. Kuma kamar yadda kika ce ne ba zaki koma gidansa ba, dama ai mu muka haɗaku, a zaton mu hakan masalaha ce a rayuwarku, ashe a gurinsa ba haka bane. Ba komai ni da kaina zan karɓar miki takardarki, kuma dole ya bayar dan ba shi kadai ne namiji a duniyar nan ba. Feenah kuma yaje yaci uwar da zai ci da ita ƙwaɗayayye kawai."

Areef ya dago da sauri ya kalli Mamah, banzar harar da take watsa masa ita tasa shi saurin maida kansa yana muzurai. Yana jin haushin yadda Mamah ke goyan bayan cewa zai rabu da Iman bayan yasan koda bala'i ba zai saketa ba.

"Tashi kabar gidan nan Areefullah." Cewar Mamah tana nuna masa hanya.

"Mamah wallahi a...."

"Bana san jin wata magana, kaje gurin Feenah itace mai gaya maka kaji bamu ba."

"Dan Allah m..."

"Idan ka sake yin magana a gurin nan zan maka abinda baka tunani."

Areef ya tashi jiki babu ƙwari, ya kalli Mamah kamar zai fashe da kuka gashi ta hanashi cewa komai, ya fice da sauri yana yana dafe bango sakamakon wani irin jiri da yake neman kadashi.........











*HAJJA CE 👈*
4/1/22, 13:25 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲)*


*43*



"Oh La'ilaha illallahu! Ke yanzu Iman banda sakarci mahaifiyarsa ce fa, ya zaki sa ta dingajin haushinsa fisabillahi uhmm? So kike ta tsine masa ko kuma so kike ta fita sabgarsa?" Cewar Hajiyan sama iya gaskiyarta.

"A'a ko ɗaya Hajiya karma kice zaki mata faɗa, yadda na raini Areef da hannuna haka na raini Iman, nono ne kadai bata sha ba, shima dan dai a lokacin babu ruwa kuma ciwo suke shi yasa. Kuma ai muna da labarin Feenahr, mun santa ƴar iskar yarinya ce marar kunya mara tarbiya. Na rasa wace irin fitinanniyar yarinya ce ita, yadda kika san Areef ne kawai najin da zata yi wannan iskancin dashi." Mamah tayi maganar cike da takaici da ɓacin rai.

"Toh ya za'ayi? Itama ba sai ta tashi ta kwace mijinta ba, me zata nuna mata wanda bata dashi? Ai sai Itama ta miƙe tsaye wajan ganin ta karɓoshi, ita da suke tare, suke kwana suke cin abinci suke komai, har akwai wata macen da zata girgizaki Iman?" Hajiyan sama ta faɗa cikin haushi. Gabaki ɗaya laifin Iman take gani bata ganin na Areef.

"Ta iya yiyuwa akwai abinda yake jan ra'ayinsa game da yarinyar wanda ke bakya yi masa. Yanzu dai kawai kici gaba da addu'a amman kada na kuma jin kince ya sakeki babu kyau, Allah yana tsinewa duk matar da take ɗagawa mijinta murya ta kuma haɗa da cewa ya saketa Allah yana fushi da ita."

Maganar Hajiyan sama ba bawa Iman haushi matuƙa, tsanar Areefullah kuma ta sake samun guri a ranta. Indai kuwa suka ce ba zasu raba auran nan ba wallahi tallahi za'a zo ana dama ace, dan wallahi yadda takeji tsab zata iya kasheshi saboda ba zata taɓa yadda da rainin hankali ba. Idan wani abu ne bata yi toh ya kyaleta yaje ya ɗakko meyi masa, ita kam harga Allah tasan tana yi masa iya kokari, duk abinda ta gani na gyaran jiki tana yi, kawai hali ne irin na maza.

"Toh yaje can tayi masa, Amman na gaji bazai kasheni ba a banza a wofi ina da sauran kuruciya ta." Iman ta faɗa tana tashi daga jikin Mamah tayi ficewarta daga ɗakin.

Yana tsaye jingine jikin bango duk yanajin maganganunsu harda na karshe wanda Iman ɗin ta faɗa. Lallai yarinyar nan ta ɗauki zafi da yawa, ta wani dage sai ya saketa? Ganin ta wuce wani ɗaki da alama ma ko ganinsa a tsaye ba tayi ba. Tana shiga yabi bayanta, sam bataji shigowar mutum ba, tana tsaye wajan wardrobe sai share hawaye take yi kawai taji an rungumeta. Ƙamshin turaran jikinsa yasa tai saurin waigo da fuska taga shi ɗin ne ba wani ba.

"Sakarni dallah." Ta faɗa cike da tsiwa.

"Meyake damunki ne Iman? Ni nefa, Areefullah ɗinki, mijinki da kekiso fiye da komai." Ya faɗa yana sumbatar wuyanta, cikin ɓacin rai tace dashi.

"Ka matsa min daga nan bana son ganinka. Saboda kasan ina sanka shine kake neman ka illata min rayuwa? Toh ni yanzu bari na gaya maka bana san ganinka. Kuma kaji sai ka rabu dani dan na riga na yanke alaƙata da duk wani ɗa namiji. Kasan me nake so ka sani?" Kafin ya bata amsa taci gaba da cewa.

"Na yanke alaƙata da maza, aure kuma akai kasuwa zan nemo wata macen yar uwata mu dinga rage zafi idan jarabar ta motsa. Kaga ba kare bin damo, kaje ku kare kai da Feenah nima zan nemarwa kaina mafita daman ba wani isata kake yi ba, yauwa karma kayi zaton kai ɗin wani abun damuwa ne. Kuma kaje ka aurota anan zaka banbance aya da tsakuwa." Tana kaiwa nan ta fara cukucukun kwace kanta.

Areef kuwa ji yayi gaba daya kansa yayi wani irin girma, mamaki da al'ajabi ya kusa kasheshi jin kalamanta, da sauri ya zagaya gabanta suka shiga kallon juna. Kyar Iman tayi masa ko ƙiftawa batayi anan ya sake tabbatarwa da kansa cewa lallai zuciyarta ta ƙeƙeshe. Cike da tsantsar ɓacin rai ya soma yi mata magana yana wani ƙanƙance idanuwa.

"Ashe baki da hankali Iman? A gabana kike cewa zaki faɗa harkar maɗigo? Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun waiyazubullah. Ni kike kalla kice bakya jin daɗi? Duk ihun da kike yi kullum shine yanzu zaki kalli tsabar idona kice wai bana isarki? Ki...." Da sauri ta katse shi.

"Kana zaton zanyi maka karya ne? Toh bari kaji, ihun ma da kaji ina yinsa, Ina yi ne kawai dan nasa kaji daɗi amman duk karya nake yi maka, idan ma kana tunanin kai jarumi ne ta wannan ɓangaren toh kadena." Juyawa tayi zata bar masa ɗakin ya sake tare ta dan kuwa ba karamin ɓata masa rai tayi ba.

"Karya kike yi, wallahi na isheki ai ina gani a cikin idanunki. Haba Iman ni zaki rainawa han...." Da sauri ta sake katse shi ta hanyar cewa.

"Idan karya nake yi dan Allah dan Annabi ka auro Feenah yau dan ka banbance tsakanin mu, wallahi duk jarabarku sai kun raina juna, zakuma kasan wacece khadijatul Iman a cikin rayuwarki. Kaga ni ɗan matsa na wuce dan akwai wata ƙwararriyar ƴar m*** da nake son mu ƙulla harka da ita. Jira kawai nake na sauke maka wannan kayan daka jibga min, wanda shine ya tsaida karatun dan tace basa yi da masu ciki."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, ashe baki da hankali?"

"Kaine ka koya min, banbancina da kai shine, kai mace kake nema, ni kuma ƴar uwata mace zan nem...." Ai bata ƙarasa ba ya kwashe kyakkyawar fuskarnan tata da mari, jikinsa har rawa yake yi tsabar fushi yana nuna ta da yatsa.

"Wallahi tallahi baki isa ba Iman, idan har kika biyewa zuciyarki kika aikata wannan ɓarnar na rantse da Allah sai na kasheki, wallahi da hannuna zan ratayeki ki mutu Iman tunda ke baki da hankali. Ubanwa ya gaya miki na taɓa kusantar Feenah? Ni na gaya miki ko itace ta gaya miki? Karki kuskura ki aikata, karki biyewa zuciyarki Iman. Haƙika nasan shaiɗan ne ya biyo ta jikin Feenah har take bin rayuwata, amman wallahi tallahi ban taɓa zina ba."

Yana faɗa ya ƙarasa inda take ya kamota zuwa jikinsa yana son ya buɗe mata fuska saboda ta rufe da hannayenta. Wani irin numfashi ya dinga ja yana saukewa, yayi mata wata irin runguma tamkar ance masa kwaceta za'a yi.

Gabaki ɗaya suka saki kuka ko wanne da abinda yake ji a ransa, su Mamah dake bakin ƙofa suna kallansu ita da Hajiyan sama suka kalli juna tare da janyo Ikram suka bar wajan. A hankali Areefullah ya janyota zuwa kan gado ya kwantar da ita. Iman na ta kuka ya kwanta a bayanta tare da rungumeta, kansa ya tura kan wuyanta, zuciyar shi na zafi yake cewa.

"Am so sorry dear, am sorry for what I did to you. Wallahi ina sanki Iman, ina ganin mutuncinki. Ke ta musammance a cikin rayuwata, duk abinda kikaga nayi wallahi ba dan naci mutunci ko zarafinki bane. Please sorry my dear karki bari shaiɗan ya lalata mu'amular mu..."

Gabaki ɗaya jikinta yayi sanyi, tunda ya mareta taga kuma ya yi saurin janyota jikinsa taji zuciyarta tayi rauni. Ga wani irin yanayi da a yanzu yake neman jefata ta hanyar romance mai firgitarwa. Cikin sauri ta riƙe mararta tare da curewa guri guda ta saki wani irin nishi tana salati.

"Ya Allah, subahanallahi, innalillahi wa'inna ilaihir rajiuna wayyo Mamah...!" Areef najin haka yayi saurin miƙewa zaune yana kallanta.

"Zan mutu, Hajiya zan mutu innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Bayana, ciki na, marata zasu cire." Ai a gigice Areefullah ya fito yana kwalwa su Mamah kira. Da gudu suka fito suna tambayarsa ya nuna musu ɗakin da Iman take.

"Uban me kayi mata kai kuma?" Cewar Mamah tana juyar da Iman.

"Wallahi ba komai Mamah, kawai gani nai tana riƙe ciki."

Hajiyan sama ce ta ɗora hannunta a saman cikin Iman, guri guda taji babyn a dunƙule, ta ɗago tare da kallan Mamah tana cewa.

"Haihuwa ce, gashi nan babyn yayi juyi."

"Alhamdulillahi masha Allah, Iman Allah ya rabaku lafiya asibiti zamuje ne Hajiya?" Kafin Hajiyan sama tace komai Iman tayi saurin kamo hannun Mamah tana cewa.

"Mamah muje, dan Allah dan Annabi kukaini asibiti wayyo Allah na."

Yadda Areef yaga tana cicijewa ne yasa hankalinsa tashi, nan da nan gabansa ya dinga bugawa, tsoransa biyu karta mutu, kar kuma ta haihu ta guje shi kamar yadda ta furta ɗazu. Mamah ta juya ta kalleshi fuska babu annuri bare salama tace dashi.

"Kaiwa babu abinda zaka iya tabukawa ne sai zazzaro idanuwa? Bakaji tace a tafi asibiti bane?"

"Mamah naji wallahi, yanzu ya za'a yi." Ya faɗa cike da fargaba.

"Baku tanadi komai ba na haihuwar?"

"Mun fara Mamah, but bansan inda ta kaisu ba tunda a can muka fara siyayyar kuma duk ta kwashe komai ta taho dasu."

"Hajiya muje asibitin a siya a can, yanzu batama san inda kanta yake ba." Cewar Hajiyan sama tana kokarin tayar da Iman ɗin.

Areef ya isa ɗayan gefen ya kamo Iman suka tafi mota. Dukkan su babu wanda ya zauna suka tafi asibitin, Hajiyan sama dama tace kar a sanar da Sen Muhammad kar hankalinsa ya tashi. Ana shiga da ita lebour room Areef ya kafe sai ya bisu, babu yadda aka iya dole aka barshi bayan Hajiyan sama ta bashi goyan baya. Yana riƙe da Iman yana neman gafararta, bata iya cewa komai sai addu'a a cikin zuciyarta.

"Dear Allah ya sauke ki lafiya, dan Allah dan Annabi karki mutu ki barni. Na rantse da Allah ina sanki, zuciya ta tana tare dake, abinda ya faru tsakanina da f...." Ai wani uban ihu da yaji ta saki shine ya hanashi ƙarasa sunan Feenah da ya fara. Ihun kuma yayi daidai da fitowar kan babyn.

"Yi hakuri dear Iman, bazan sake faɗar sunanta ba, Allah ya saukeki lafi....." Kafin ya gama furucin yaji kukan baby inyaaaaa.....inyaaaa, yayin da ita kuma Iman ta fashe da wani irin kuka mai tsananin ban tausayi.

"Wow-wow-wow Mrs Al-Mustapha, congratulations an samu little Areefullah." Already Mamah da Iman sunje cikin hospital ɗin sun samo abinda suka san za'a yi amfani dashi wajen haihuwar sun kawo.

"Alhamdulillahi masha Allah dear kin haihu..." Ya faɗa cike da farin ciki. A hankali yaji ta zare hannunta daga cikin nashi, jikinsa yayi sanyi ganin ta juya fuskarta da alama son ganinsa ma batayi.

"Nurse..." Iman ta kira ɗaya daga cikin su a hankali. Nurse ɗin taje kusa da ita

35 / 38