Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   22 / 38

63K to 66K   out of 113.7K words

saurayi sai budurwa shar. Kije kiyi abinda kike so na sakeki saki irin na musulunci wato saki ɗaya."

Yana kaiwa nan ya sake ficewa jikinsa har wani tsuma yake yi saboda bakin ciki. Gaba ɗaya ya rasa dalilin da yasa shi jin irin wannan bakin cikin, ya kasa gane abinda yasa shi jin haushi. Ita kuwa tunda ya zabga mata marin nan ta riƙe kunci wani bakin abu ya tokare a wuyanta, har ya karaci maganganunsa bata gane me yake nufi ba sai da taji kalmar saki kirjinta ya bada wani irin..........

(😭Babu bincike Areefullah? Haushi ne ko kishi? Kai Areef kai Areef dan Allah 😩)


*ZO GARENI yana cikin tawagar Top 10 ki biya kafin ki karanta daga page 11. Zaki iya tuntuɓar wadannan. +447894142004 ko kuma 0706 528 3730*









*HAJJA CE 👈*
3/9/22, 20:09 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
(Random..........)
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*

*27*



Ƙirjinta ya bada wani irin das! Taji tana son auran su ya kasance na har abada amman mai afkuwa ta afku, Areef ya saketa akan dalilin da bata sani ba. Ta tuna lokacin da suna kwance jiya yace mata zai rayu da ita duk tsananin bala'in da zasu fuskanta, sai gashi ya saketa sakin da kowa sai yaji babu daɗi. Why Areef? Why?! Ta dinga jin be kyauta mata ba saboda taso ta rayu koda kuwa ba zasu taɓa yarda da junansu a matsayin mata da miji ba, taso su zauna tare dashi kamar yadda iyayensu suke so, sai dai ya saketa saki mafi ciwo a gareta.

Ta fara tunanin gurin zuwa, bata son komawa gurin su Mamah bata san abinda zata ce musu ba, da kuma taje takai karar ɗansu tunda sunyi mata iya abinda zasu iya dan kare mata mutunci. Sai dai kuma idan ba taje gidan ba ina zataje bayan su tasani? Waɗanda take jin cewa sune ƴan uwanta duk ta sansune saboda su Mamah, idan taje dole su san halin da ake ciki.

Tashi tayi daga inda take durƙushe ta isa wardrobe ta zaro kayan da zata saka, saboda tsakanin bakin ciki ma ta kasa yin kuka. Doguwar riga ta saka tare da fitowa zuwa falo, baya nan ta kalli ƙofar dakinsa bata ga alamar yana ciki ba, ta fara tunanin ina ya tafi da magariba, taso ta yi kwalliya ta musamman da nufin in ya dawo yaga sauyi, hakan yasa ta tsiri yin wanka sai gashi komai ya dagule mata, ta tuna kalamsa da taji sama-sama yana ce mata kwaila ɗuwawu kamar farantin silver.

Hawaye suka fara taruwa a idanunta, ta kalli jikinta, tabbas ba karya ya yi ba, amman idan be manta ba Allah ne ya halliceta yaso ganinta a yadda take, ikon sa ne ya girmar dasu haka zalika ikon sa ne barinta a haka. Iman ta samu kanta cikin kunci da damuwa, bata tashi daga gurin ba sakamakon period da take yi.

_________

Shi kuwa Areef da kyar ya iya kai kansa bakin titi, wani masallaci ya tsaya tare da yin alwala ya bi su jam'i, ana idarwa ya fito daga masallacin yana dafe kai. Wata ƙiyayyar Iman ce take masa zagaye cikin duk wani motsinsa, yaji baya son ganinta koyaya ne. Sai da aka yi isha'i ya tsaya yayi sannan ya kuma nufowa gidan yana jin zuciyar shi na zafi. Sai da ya zo gab da shiga ya sake ganin saurayin nan ya fito daga cikin gidan, suka kalli juna ko wanne da nasa kalar tunanin.

Areef ya juya tare da rarimo wani dotse a kusa dashi, ya juya zai kwaɗa masa yaga ya ruga da gudu yana murmushi. Ya shiga gidan ransa na tafarfasa ya samu Iman kan kujera zaune, tun kafin ya gama ƙarasawa ciki ya fara yi mata masifa.

"Mekike min a cikin gida har yanzu baki fitar min ba?" Ta kalleshi cike da tashin hankali tana cewa.

"Ina zani da daddaren nan?" Yace cikin fushi.

"Kekika sani munafuka, wato dana fitama dawowa yayi kuka ƙarasa ko?" Yadda yaga tana kallonsa ne ya kuma ɓata masa rai, kallo take masa irin na rashin fahimtar nan, yaja wani mugun tsaki yana cewa.

"Kisan inda zaki tafi dan ba zakici gaba da zauniya a gidan nan ba kije ki janyo min masifa. You're free to do anything Iman, amman ki sani bariki harkar banza ce, iyayen mu kuma sunyi kokari akan mu wajan kula da tarbiyar mu. Tsakanina da Feenah ba komai bane sai tsantsar soyayya, ke kuma da aure a kanki shine kike aikata baɗala, na tsaneki Iman bana son kuma ganinki cikin rayuwa ta." Cikin kukan da yafi ƙarfinta, jiki na tsuma take masa magana.

"Na kasa gane abinda kake nufi, tunanina duk ya kwance Yaya Areef kasani cikin duhu na kasa fahimtar inda maganganunka suke son zuwa. A ina kaga ina duk wadannan abubuwan daka lissafo? Karka yi min sharri ko ƙazafi dan Allah ba zai barka ba wallahi, ba halina bane duk wannan abubuwan daka faɗa. Kadena dangantani da zina Yaya ban aikataba ban san yadda ake yi ba wallahi tallahi ban aikata ba."

Ta ƙarasa cikin zubar da wani hawaye. Yaja tsaki yana yi mata kallon banza.

"Ni zaki rainawa hankali Iman, naga kun fito daga wanka keda shi ɗan iskan naki? Na fita na dawo naga ya sake fitowa daga nan, karki raina ni ki maida ni marar wayo. Bana son kara ganinki cikin idanuna, bana son kuma saki cikin ido na, zuwa safiya kisan inda dare yai miki."

Ya tafi ɗakin tana jinsa ya rufo ƙofar da karfin tsiya, kuka ya sake kwace mata a gurin ta zauna tayi ta tayinsa. Cikin dare suka kawo wuta, taje tasa chaji tare da kunna karatu, yana juyowa saboda shi kansa ya kasa bacci, haka dukkan su basu rintsa ba har gari ya waye. Tun asuba ta gama haɗa kayanta bata da wata mafita sai ta komawa Kano, can ɗin ma babu madafa sai gidan su Areef. Taja trolley ɗin ta tun be fito ba tabar gidan.

Alokacin ba maganar wani tsoro, ita kanta so take tabar gidan zuciyar ta zafi take yi idan ta tuna ya saketa amman tana tare dashi a gida ɗaya. Bakin titi taje ta samu guri, akan trolley ɗin ta zauna babu kowa sai ita kada tamkar aljana. Har gari ya fara wayewa motoci suka fara wucewa sosai sannan ta tashi taci gaba sa tafiya ba tare da tasan inda zataje ba. Tana ta tafiya har Allah ya kaita wajan wani mai shayi da yake kokarin haɗa wuta, ta nemi alfarma ya bata ruwa tayi sallah yana ta mamaki ganinta budurwa kyakkyawa har ya fara tsoran ko aljana ce.

Sai da tayi sallah sannan tai masa godiya tace gaba da tafiya ba tare da sanin inda zata ba. Wata tsaleliyar mota ce tayi parking a kusa da ita, Iman bata kalli mai motar da yake ta yi mata magana ba sai da yaji tace.

"Yan mata ki bari na taimaka miki ta hanyar kare miki martabarki ta ɗiya mace. Babu kima ganin ki cikin wannan yanayin wanda alamu suka nuna kina cikin matuƙar damuwa. Kiyi hakuri kizo na rage miki hanya." Sai da yayi shiru taga cewa idan bata bari an taimaka mata ba, bata da wata mafita sai ma sake sanya kanta cikin matsala.

Kallansa tayi a karo na farko tun farkon tsayawarsa, wa'iyazubullah tayi saurin kawar da kai ganin wani tsalelin mutum zauna a cikin motar, tunda ta kwafo hotansa a cikin idanunta takejin wani irin bugun zuciya. Ta sake kai idanunta gare shi suka haɗa ido Iman ta kuma dauke kai, bata da zabi banda ta sake tafiya duk kuwa da tana matuƙar bukatar taimakon. Ya sake tuko motar tare da tare gabanta ya fito, Iman ta rintsa ido ta kuma sakin kuka tamkar ranta zai fita, ya durkusa a gabanta guiwa har ƙasa, saurin zaro ido tayi tana kafeshi da idanunta da suka kankance saboda kuka.

"Ki taimaka kizo na rage miki hanya yake mafi kololuwar daraja da kima. Bazan iya barin ki haka ba bayan nasan kina bukatar irin taimakon da nake son yi miki." Iman ta gyada kai kawai tare da buɗe ƙofar ta shiga ta zauna bata ce komai ba. Ganin haka yasa shi miƙewa shima ya dauki trolley ɗin yasa a booth sannan ya zagaya mazaunin mai tuki ya zauna. Sai da ya kalleta yaga ta sanya kai cikin guiwa tana kuka sannan cikin wata zazzakar murya da ta sanya Iman jin faduwar gaba yace.

"A yadda naka damuwa da bakin ciki tattare dake, zan iya tsayawa na taimakeki duk kuwa da cewa Kano nayi yau ɗin nan." Tana jin ya faɗi haka tayi saurin dagowa ta kallesa, ya ɗaga mata kai alamar tabbacin maganar da yayi. Iman ta samu da kyar ta iya buɗe baki tace masa.

"Kano zani nima." Cike da jin dadi yace.

"Tafiyar zatai daɗi kenan?" Bata bashi amsa ba yai murmushi ganin yadda ta kawar da kai yaja motar suka tafi.

______________

Areef besan cewar Iman bata gidan ba, sai da ya gama komai ya shiyar zai fita sannan ya wuce ɗakin ta da niyar ja mata kunne. Babu kowa a cikin ɗakin ga alamar an kwashe kaya nan a cikin wardrobe ya ɗaga kafada tare da rufe ɗakin shima ya fito ya rufe. Duk da ba wani damuwa yai da ya ganta a wannan lokacin ba, hakan be hanashi kale kalle ba ko Allah zai sa ya ganta a wajan ba. Harya isa bakin titi baiga mai kama da ita ba bare ya ganta.

Haka ya tari mota ya tafi aiki ba tare da yasan ina Iman ta tafi ba. A hanya ya yiwa Abba da Mamah taxt message cewar Suyi hakuri su yafe masa akan duk abinda zasu ji, yana ganin sakon ya tafi ya cire sim ɗinsa ya ajiye. Yana sauka ya biya shagon da ake siyarwa ya sai sabo aka yi masa register ya ɗora a wayar, shagon su ya nufa zuciyar shi duk babu daɗi.
____________
Duk sunga sakon sai dai a ciki yaki sanar dasu cewar ya saketa, hakan yasa Abba da Mamah suka fara tunanin kuma zuwa suji abinda ke faruwa. Wayar Iman ɗin suka dinga kira ana shaida musu cewa a kashe take, Mamah tace.

"Kira mana Areef ɗin muji dan saƙon nan kawai bai gamsar dani abinda yake son faɗa ba, taya zai ce Iman na shigo masa da maza cikin gida harda yin wanka tare." Abba ya kira amman wayar shima a kashe, hakan ya kuma ɗaga musu hankali saboda basu san taƙamaimai abinda yake faruwa dasu ba a wannan lokacin.

"Anjima sai a sake bugawa, bari naje ɗakin kawu Balarabe an barshi shi kadai."

Ya faɗa yana tashi ya fita zuwa dakin Haneef inda a nan aka dawo da shi kafin a maida shi asibitin. Su liman duk an sallame su sun warke sai abinda ba za'a rasa ba. Gabaki ɗaya jikinta a sanyaye yake musamman da har zuwa lokacin bata san halin da yaranta suke ciki ba.
______________

Iman kuwa suna hanya suna ta sharara gudu a mota babu mai cewa komai, da ya gaji ne da jin shirun ya ɗan saci kallanta ya mayar kan hanya yana cewa.

"Kiyi hakuri yanayinki ya nuna cewa kina cikin matuƙar damuwa, gashi muna tafiya hanya ɗaya amman bamu san juna ba." Yayi shiru yana sake dubanta kafin ya maida hankali ga tuki yaci gaba da cewa.

"Anyway! Sunana Jabir ko zan san sunan ƙanwar tawa?" Iman na jinsa sai dai har lokacin ta kasa dena jiyo amon muryar Areef cikin kunnanta da yake gasa mata magana. Ta rintsa ido hawaye suka shiga zirarowa, ganin haka ya ɗaga masa hankali ya shiga bata hakuri ba ƙaƙƙautawa. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske kafin ya tsaya a wani restaurant yace mata.

"Muje kici abinci." Tace,

"Naƙoshi." Mamaki ya kamasa, ko cikin idonta ka kalla zaka san tana jin yinwu, amma yanzu taci ta koshi.

"Ki daure muje kici please." Yayi maganar cikin sanyin murya.

"Bana jin yunwa muje kawai."

"Idan bakici ba zan barki anan." Ya faɗa cikin son ya tsoratata, sai yaga tana kokarin buɗe ƙofar tana cewa.

"Laaaahhh nagode ai ko anan ɗin ka ajiye ka yi kokari Allah ya saka da alheri.." Ta kasa buɗewa saboda a rufe take, ta kalleshi ya kalleta yana murmushi mai matuƙar burgewa.

"Shikenan kiyi zamanki a ciki bari naje na siyo ruwa da ɗan lemo."

Iman bata ce masa komai ba, ganin haka yasa shi buɗewa ya fita, yana fita ya kulle motar. Lemo, da ruwa sai gasasshiyar kaza da shawarma ya siyo, yana dawowa ya tarar da ita tana gyangyaɗi.

"Sorry na barki ke kadai." Ta kakalo murmushi tace.

"Ba komai." Ya ajiye kayan a tsakanin su, motar ya tada suka fara tafiya yace taci amman Iman taki, babu yadda beyi ba amman tayi kemudugus.

Babu yadda Jabir beyi ba akan Iman amman taci abinda ya siyo amman bataci ba, kalma ɗaya take gaya masa wato ta koshi, daga karshe ma bacci kawai tayi ta kyaleshi. Kamar jira tana yin bacci cikin ƙanƙanin lokaci taji farka sai ganin su tayi a cikin kano, wani irin farin ciki ya lulubeta, sai dai ganin ya yi parking guri guda yasa ta yin magana.

"Har munzo Kano, nagode sosai." Jabir ya sakar mata kyakkyawan murmushi wanda yasa Iman saurin kawar da fuska daga kallon shi da take yi.

"Bari na sauka a nan zan ƙarasa gida thank you very much." Ta murda ƙofar amman taji a kulle, kallansa ta sake yi tace.

"Tunda na dakkoki tun daga can Abuja ai nayi hakuri na kaiki gida. Wannan tsayuwar da kikaga nayi jira nakeki tashi ki bani umarnin wace unguwa zan kaiki." Ta rike baki.

"Ni na isa yin wannan karanbanin? Ko a haka ka barni kayi min abinda ba zan iya yiwa kaina ba, kaga ko godiya tayi kaɗan." Yayi murmushi tare da cewa.

"Toh ina muka nufa yanzu?" Iman taja ɗan gajeran numfashi tare da sanar dashi unguwarsu, ba wani bata lokaci yaja motar suka ƙarasa.. A bakin fate yayi parking ta kalleshi.

"Bakina yayi kadan wajan nuna godiyarta a gareka, na gode sosai Allah ya cika maka burikanka na alkairi." Yace.

"Amin thank you."

"Suna na khadijatul Iman." Ta faɗa cikin kawar da fuska. Kai ya gyada har ya hakura da cewa zata faɗi sunan.

Ɓalle murfin tayi ta fito, wajan booth taje tana jiran ya buɗe ta ciro trolley ɗinta. Fitowa yayi da kanshi ya ciro mata ta karɓa ya girgiza mata kai tare da kiran wani almajiri dake can gefe a zaune, ya bashi trolley ɗin da ledojin da ya siyo abubuwan nan yace ya shiga dasu ciki. Ita dai Iman bata sake cewa dashi komai ba tabi bayan almajirin suka shiga.

Duk suna falo a zaune sukaji ana sallama suka amsa jin namiji ne yasa basu ce ya shigo ba, tun kafin su ce menene kawai suka ga Iman tashigo. Tana hango Mamah a zaune ta ruga da gudu suka rungume juna, suna ta mamaki suna kuma juyawa ko zasuga Areef ya shigo amman shiru, sai almajiri da ya shiga da kayan ta. Yana fita kuwa wanda ya kawo Iman ya bashi ɗari biyar, godiya ya shiga yi babu kyakautawa. Mota ya koma yaja tare da barin unguwar.

"Ke kuma kedawa?" Cewar Mamah tana dago Iman wacce hawaye suka jiƙawa fuska.

"Ni kadai Mamah." Ta faɗa cikin raunanniyar zuciya.

"Ɗazu ya yi mana message cewar kuna cikin wani hali sai dai muna ta kiransa dan jin karin bayani dakema gaba ɗaya muka kasa samunku a wayoyinku." Iman tayi ɗan murmushi tace.

"Wayar ce a kashe."

"Kukan me kike yi toh?" Mamah ta tambayeta tana yi mata kallon kurullah.

"Ba komai Mamah." Ta sake faɗa hawaye na zuba.

"Karya ne a kawai wani abun, ki sanar dani karki ɓoye min komai." Zuciyarta ta karye, kuka sabo ya sake kwace mata tace.

"Ya sakeni Mamah, Yaya Areef baya son ganina." Ta ƙarasa maganar tana ɗora kai saman kafaɗar Mamah........

(SO SAD 😔 da alama su Iman an fito cikin nasara🤸‍♀️sabo dal... Inyeeee😂)

*ZO GARENI yana cikin tawagar Top 10 ki biya kafin ki karanta daga page 11. Zaki iya tuntuɓar wadannan. +447894142004 ko kuma 0706 528 3730*









*HAJJA CE 👈*
3/11/22, 23:58 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*

*28*



Cikin zabura da tashin hankali Mamah ta miƙe tsaye tana riko Iman, jitake tamkar a mafarki ake gaya mats, ta shiga girgiza kai alamar rashin yadda da abinda kunnuwanta sukaji.

"Iman ce min mafarki ne dan Allah." Kuka ya sake kwacewa Iman tace.

"Mamah da gaske nake yi wallahi." Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Anya yaron nan yana cikin hankalinsa kuwa? Wane dalili ne yasa ya sakeki Iman?"

"Wallahi Mamah ban sani ba, kawai dai naji yana ta faɗa." Atake a gurin Mamah ta kuma kiran wayarsa bata yi tace.

"Shikenan shi yasan abinda yake a ransa, Allah ya shirya shi. Iman kiyi hakuri dan Allah dan Annabi, hakika mun cutar dake wallahi, amma babu komai."

Tun daga nan Mamah ta kwantar mata da hankali tace karta damu kanta. Abba yana dawowa aka sanar dashi kusan kullum sai sun kira amma basa samunsa, sai suma suka tattara suka kyaleshi.
___________

A ɓangaren Iman kuwa abun ne yazo mata a baibai, gabaki ɗaya ta rikice, tunda ta baro gidan Areef taji gabaki ɗaya bata son rabuwa dashi. A ƴar rayuwar da sukayi tare dashi a gida ɗaya, ɗaki ɗaya ta canza mata duk wani lissafi nata akan shi. Wani masifaffan kewarsa takeji, kunnuwanta suna matuƙar son jin muryarsa. Kwance take akan gado sai faman juyi take, idanunta a rufe tana faman cizon lebɓanta. Ikram ce ta shiga da ƴar waƙa a bakinta taga yadda Iman keta faman juye-juye, cak ta tsaya tana kallon ikon Allah kafin ta gaji tayi magana.

"Lafiya dai ko?" Iman najin muryar Ikram ta dena abinda take yi, Ikram ta saki murmushi tare da cewa.

"Sai kace wacce take cikin shaukin so sai faman juye-juye kike tayi." Iman tace cikin ranta 'SO?' Sai kuma ta zaro ido tamkar ba bakinta taji ya furta ba, tasa yatsu ta bugi kirjinta wai zuciyar tace ta Ayyana Amman ba ita ta yi.

"Abba yace health technology zaki tafi." Cikin sauri Iman ta miƙe cike da murna tace.

"Dan Allah da gaske?"

"Wallahi kuwa naji yana waya yana cewa ko nawa ne zai biya,

22 / 38