Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   38 / 38

111K to 113.7K   out of 113.7K words

sai ta kuma yi masa baraza.

"Ka dena damun kanka, yanzu muna bukatar nutsuwarka da lafiyarka. Allah ya baka lafiya ka dawo muci gaba da rayuwarmu." Yace.

"Amin." Yana faman lumshe idanuwa.

Tun daga nan Iman ta shiga kula dashi, su Mamah ma sunzo sunga jikinsa yayi kyau kyau lafiya kuma ta samu fiye da baya. Ya warke ras har an basu sallama. A ranar ne kuma Sen Muhammad ya kai Areefullah campany siyar da motoci da babura da duk wata harka da take safarar kayan wuta wanda ya buɗe mishi anan garin Abuja. Farin ciki marar misaltuwa ya mamaye su musamman Mamah da har hawaye sai da tayi tsabar jin daɗi da kuma murnar samun suruki irin Sen Muhammad. Daga nan yasa aka kaisu gidan da aka gina musu a asokoro shida Iman ɗinsa, ya bashi har da takardun gidan cewar ko bayan ransa nashi ne bana Iman ba.

Murna kam har rasa wace iri Areef yayi, addu'a da neman dacewa duniya da lahira babu wacce ya iya da beyiwa Sen Muhammad ba. Daga nan suka koma gida aka yi walima aka raƙashe, Washe gari su Mamah suka koma Kano su kuma suka koma sabon gidan su. Da yake Aslam yana nan tare da su, sai da sukaje sabon office ɗin Areef inda shi yake a matsayin MD/CEO, Aslam kuma ya bashi Director, Irfan Project manager, Sudais G.M finance uncle Imran G.M Operations Sai sauran ƴan uwa da ya kwaso suma duk ya basu abun yi a gurin.

"Guy's zanje gida." Areef ya faɗa yana tattare kayansa yana sawa cikin jaka.

"Tun yanzu?" Cewar Sudais yana danna waya.

"Ina da abin yi ne idan naje that's why."

"Karya ne kadai fadi gaskiya malam. Wanke-wanke zakai ko shara ko wanki?" Aslam ya faɗa cike da takaici.

"Sirri ne wanda mai iyali ne kawai yake ganewa." Duk suka kwashe da dariya dan sosai yake gasa musu magana akan wannan auran nasa. Sai da ya rataya jakar a kafadarsa sannan ya kallesu yana cizon leɓe yace.

"Mtww guy's na tausaya muku wallahi, ku daure kuyi aure saboda rahama ne."

Yana kaiwa nan ya fice dan yasan tabbas ya bar musu abin tattaunawa. Lintsumemiyar motarsa da Sen Muhammad ya bashi ita yaje ya buɗe ya shiga cike da farin ciki. Wayarsa ya ciro ya fara turawa Iman saƙo, bayan ya tabbar sakon ya tafi ne sannan yaja mobar yabar gurin.

Tana kitchen ta gama fasa kwai zatai egg source taji karar shigowar text message, bata juya ba tasa mai aikinta ta miƙo mata. Sunan shi da ta gani ne yasa ta saurin buɗewa ta karanta.

"On my way home dear. Kinsan yadda zaki dani idan nazo." Murmushi Iman tayi ta ajiye wayar cikin sauri taci gaba da aikin har ta kammala.

Ɗaki ta shiga inda ta tarar da Daddy ya farka yana ta tsotsar hannu, ta zauna ta bashi yasha sannan ta shiga sake gyara ɗakin. Already tayi wanka ta cire kayan jikinta tare da ɗaukko turaruka ta fashe jikinta dasu. Lafiyayyar khumrar da aka yo mata ta yerwa incense and more a Kano ita ta kuma bin duk wani lungu da saƙo na jikinta ta shafa, dama ga ƙamshin bath khumra wanda Mamah duk tasa aka yo mata na yerwa saboda matar babu kalar kayan ƙamshin da bata haɗawa, su mopping khumra, washing khumra, turarukan wuta da dai sauransu ga masu bukata 08095215215 su tuntubi wannan lambar.

Wasu ƴan guntayen riga da skirt jajaye tasa a jikinta, already ta gama shan supplement na gyaran jiki da ta siya a wajan stylish na matsi mai kuma saukar da ni'ima 08164457511 dan kuma ku siya naku. Ta gama shiryawa tsab ko'ina an gyara shi ta zauna tana chatting da Hanan tana gaya mata halin da take ciki. Yana ƙarasowa mai gadi ya buɗe masa gate ya shigar da motar. Shi kansa yau wani irin farin ciki yakeji, zuciyar shi na cike da jin daɗi a haka ya ɗakko jakarsa da kuma wani ɗan ƙaramin kwali da ya taho da shi.

Mai aiki kawai ya gani tana goge TV ta gaishe shi sannan ta fita da sauri zuwa nata sashen, wannan duk umarni ne na Iman da tayi mata cewar duk lokacin da mai gidan ya dawo komai take yi a falo ta barshi ta koma ɗaki duk kuwa da cewar ba budurwa bace ba koma tsohuwa ba. Sam taji motsin shi ba sai ji tayi an murɗa handle an shigo, da sauri ta juya suka haɗa ido tayi saurin sunkuyar da kai saboda kunya.

Jin yaki shigo yasa Iman sake kallonshi sai kawai taga ya buɗe hannayensa, fuskarshi ɗauke da murmushi yace.

"ZO GARENI my farin cikin zuciyata, ZO GARENI ko zanji sanyi a raina." Iman ta tashi da sauri ta isa gurinshi yai mata wata irin narkakkar runguma wacce tasa Iman wani iri a jikinta.

"Uhmmm!" Ya faɗa lokacin da hanci ya shaƙi ƙamshin jikinta, ya ajiye abubuwan hannunsa da suke neman yi masa cikas wajan kusantar inda take.

"Sannu da dawowa Daddyn daddy."

"Kinsa naji kunya my dear. Idan na tuna daddy sai nayi mamakin wai ɗa na ne fa ko?" Iman ta ɗan kalleshi da sauri ya ɗora bakinsa saman lips ɗin ta yana kashe mata ido ɗaya.

"Muje ki nuna min abinda kika tanadar min, kinsan ba iya rashin lafiyar nan ta accident kadai ke damuna ba." Suna nufar kan gado tana jikinsa a jingine take cewa.

"Kai sugarpie kar ka tayar min da hankali fa, wane irin ciwo yanzu gareka?" Ya saketa ta tsaya a tsaye shi kuma kawai ya faɗa kan gado yana sake ware hannu cikin wani irin yanayi na jan hankali yace.

"ZO GARENI ki bani farin ciki ko zan samu nutsuwa da kwanciyar hankali." Iman ta faɗa saman cikinsa tana dariya ya mayar da hannunsa ya matse ta a jikinsa.

"Haba kin wahalar dani dear, kin sani cikin wani ɗaki mai tsananin duhu kin rufe. Allah ne ya bani ke a lokacin da idanuna suka rufe, na kasa bambance so da kuma sha'awa. Sai yanzu na gane tabbas da na auri wata lokaci ƙanƙani zanji ta fitar min daga rai. Amman kinsan Allah? Dai-dai da lokaci ɗaya ban taɓa jin bana son kasancewa da ke ba. Ko yanzu da kike ganin kamar ƴan fitilun nan naki basu ɗaukar hankali na, to can gurin fa?" Yayi maganar yana nuna mata da hannunsa.

Fuskarta ta tura cikin jikinsa tana jin wata irin kunyarsa, ko kaɗan Iman bata taɓa tunanin zata ji kunyarsa ba, ba kuma ta taɓa zaton zata soshi tamkar yadda take ji a yanzu ba. Ta gyara jikinta tare da ɗan matsawa kusa da fuskarshi ta kai masa kiss wanda yayi sanadin da yasa Areefullah janyota yana aika mata da sakwanni masu birkita tunani. Cikin wata irin kasalalliyar murya Areef yaji Iman na furta.

"ZO GARENI...! Sugarpia ka ZO GARENI please...! Karka barni, idan kana bari na zuciya ta tana aiko min da sakwanni marasa kyau. Kasancewarka GARENI shine yake sanya min nutsuwa da kwanciyar hankali. ZO GARENI habibi kayi yadda kake so, saboda ni kaina ina matuƙar buƙatar ka." Wata zazzafar sumbata ya kai mata wacce tasa Iman sakar masa jiki gabaki ɗaya. Yana rage kayan dake jikinsa a gaggauce saboda duk ta tayar masa da wani tsumi dake jikinsa, ya rikota da karfi yana cewa.

"Gani na ZO GAREKI my one, a yadda kike wallahi kin ishine rayuwar duniya. Toh ma wai shin me na rasa a wajanki? Bismillahir rahmanur rahim." Ya faɗa bayan ya tabbatar da sun zama abu guda. "Wowwww! Taji ya faɗa yana sake rintsa idanuwansa.

(Ba ruwa na da sa ido😜 karma ace nace ehh! ba ruwana my people😹)

Cikin ƙanƙanin lokaci sun samarwa da junansu farin ciki marar iyaka, sun kawar da duk wani ɓacin rai da bakin cikin da suka kwasa a baya. Tana jikinsa yana shafar bayanta yace da ita.

"Da da akwai yadda zanyi wajan ganin har na mutu ban ɓata miki rai ba da nayi miki hakan. Amman Insha Allahu zan gwada zan kuma ci gaba da kula wajan ganin ban saki fushi ba. Dear idan har kin ganni da wata ya mace, ina son kiyi min adalci wajan ganin baki ɓatawa kanki rai ba. Nifa a ra'ayina, a kuma yadda nake jina wallahi bazan iya zama da mata biyu ba. Ina son na kwaikwayi Abban mu, dan haka ke kadai ce a zuciyata. ZO GARENI ki sake kwantar min da hankali na ta yadda zan yarda da cewa saƙo na ya gamsar dake.."

Iman ta kuma rungume shi, kalamansa sun sanyata cikin nutsuwa, ta yarda da cewa mijinta mai san ganin farin cikin tane. Ta yarda shi ɗin na dabban ne domin a cikin mazaje da yawa basa iya gayawa matansu sirrin su. Amman shi komai sai ya gaya mata, idan ma bai faɗa ba in ta gani yana zaunar da ita yayi mata bayani har ta fahimce shi. Ta kuma yarda da cewa ita kadai ce a cikin zuciyar shi. Daga nan tashi sukai suka nufi bathroom suna manne da juna, daddy daman tun ɗazu baccinsa yake yi.
_________________

*BAYAN SHEKARU TAKWAS*✍️


Iman ce tsaye jikin mota ta jingina bayanta sai faman waige-waige take yi. Sanye take cikin riga da skirt na atamfa green da ratsin fari a jiki, hannunta sakale da farar handbag, jefe-jefi takan kalli agogon hannunta, daga can nesa ta hango yaran sun taho su uku namiji ɗaya da ƴan mata biyu. Namijin shine babba a ciki da zai yi shekaru bakawai, sai ƴar shekaru huɗu da kuma mai biyu da ƴan watanni.

Ganin sun rugo ga hannunsu duk ya ɓaci da danƙon chacolate yasa tayi saurin matsawa dan kar su ɓata mata jiki. Ta kallesu ganin yadda duk suka tsaya suna cuno baki tace musu.

"Ahhh! Sai na tsaya ku ɓata min jiki? Ina Abbie ɗin.?" Amani itace mai surutu kuma wacce ake gane maganarta sosai, itace tace da Iman.

"Ammie Abbie yana wajan wata mata." Kirjin Iman ya bada wani ras, tayi saurin rintsa ido tana karanto addu'a.

"You're very stupid Amani, Ammie karya takeyi fa, kuɗi zai biya yace muyi gaba." Cikin fusata Iman ta kalli Daddy dake karyata Amani tace.

"Kai tafi ka bani guri, kai daman kana faɗa laifin ubanka ne? Haka kwanaki Amani tace kunji yana waya yana cewa sorry baby, da na tambaye ka cewa kai karya take, amman da na binciki baban naka ai ya gaya min gaskiya."

Cikin takaici ta kalli hanyar har lokacin babu shi ba alamar shi, taji kamar tabi bayan shi sai dai bata son dakkowa kanta raini dan haka ta koma cikin mota ta zauna cike da bacin rai.

"Lia.. Sai na gurji bakin ki."

Cewar Daddy yana yin alamar kaiwa Amani naushi. Cikin yin ɗan ƙaramin ihu Amani tace.

"Ammi kinga Yaya ko."

Iman ta sake rintsa ido jin suna neman canzata mata kwakwalwa, tayi shiru bata kulasu ba duk kuwa da irin yadda taji suna ta faman rigima. Buɗe motar kawai sukaji anyi ƙamshin turaransa yasa tasan shine hakan ya bata damar kin ɗagowa bare har tasan a wane irin hali yake. Areef ya kalleta ya juya ya kalli yaran, caraf Daddy yace.

"Abbie Amani ce tazo tace da Ammie kana wajan wata mata."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun kaji min yarinya, ke!" Ya faɗa yana riƙe habarsa tare da zabgawa Amanin harara.

"Sai na zaneki da yin gulma."

"Sorry Abbie, Ammie ta tambwyemu ina kake shine na gaya mata." Areef ya maida kallonsa wajan Iman dake tajan ɗan ƙaramin tsaki, ya kamo hannunta ta kasa fisgewa saboda idanun yaran yana kansu.

"Wannan yarinyar da kike gani tsab zata iya rabamu, kinsan ko wacece muke tare.?" Haushi da bakin ciki suka taru suka cika wuyan Iman.

"Ni ban tamvateka ko wacece ba, wannan matsalar kuce. Please dan Allah ja muje su Hajiyan sama suna can suna jiran mu."

"Customer ce wallahi dear, mota take so shine yanzu da ta ganni take tambayar yaushe za'a kawo mata."

"Kaga ni ban tambayeka ba, kaja mota kawai mu tafi tunda kun gama abinda zaku yi."

"Cininkin mota ne kuma an gama, banda shi babu abinda ke tsakanina da ita."

Ita dai ci kanka bata sake faɗa ba har suka isa isa gidan. Da gudu duk suka nufi ciki suna kiran Hajiya sama. Shi kuma Areefullah yayi saurin riƙe Iman ɗin wace zuciyar ta ke ta faman tafasa. Ita wallahi ko kaɗan bara son taji an rabeshi, idan taji labarin yana gurin wata gaba ɗaya rasa gane tunaninta takeyi.

"Ni bansan me zan miki ki yarda dani ba, ya kike so nayi miki dear?" Jin yadda yayi maganar yasa ta san cewa duk a cikin damuwa yake.

"Tsakani da Allah ta rasa inda zata yi maka zancen mota sai da ka baro office? Kuma duk ina su Aslam da bazata nemesu ba dole sai kai? Bana san rainin hankali wallahi."

"Yanzu kenan idan har na baro office babu ni ba ci gaba da business ko Hajjaju?" Iman ta yatsina fuska tare da cewa.

"Musamman idan kasan muna tare, ai sai ka dinga janyo min raini. Kasan mata isan sunga namiji mai aure yana tare dasu sai duk su ɗauka cewa ta gida ta gaza ne. Toh gaskiya ni bana so idan kana son zaman lafiya ka dena tozartani." Ya kalleta yana lumshe ido tare da cewa.

"ZO GARENI my dear." Ta ɗan matsa ya rungumeta yana cewa.

"Anta wahid dear wife, kin riga kin kamani da yawa wallahi. Tashi mu shiga ciki kafin Hajiyan sama ta fara wani tunanin." Daga haka suka fito suna rike da hannusu har cikin falo.
______________

Rayuwa a koda yaushe tafiya gaba take ba baya ba, a gurin su Iman da Areefullah rayuwa suke mai cike da jin daɗi da annashuwa. Koda dai ba kullum suke riskar daɗin ba, amman a ɓangaren kowa a cikin su yasan abinda ɗan uwansa yake so da wanda baya so. Iman ta riga ta gama gano cewa mijin nata akwai farin jini ta yadda yake shan gwagwarmaya da mata, hakan yasa kullum addu'ar ta Allah ya tsare mata shi badan halinta ba.

Sun sha bikin Aslam, bayan nashi suka sha sunan ɗan Hanan wacce a yanzu ƴaƴanta uku itama, Ikram ce har yanzu Allah be kawo mijin ba. Yaya Haneef yazo yaji labarai na abubuwan da suka faffaru, yayi mamaki matuƙa jin abin da Jamil yayi masa ya kuma sanya a ranshi ba zai kuma yadda da aboki ba, a nashi ɓangaren dama babu maganar wani aure dan baya zama. Iman tana matuƙar kulawa da mahaifiyarta, duk abinda zata yiwa Mamah sai ta haɗa da inna Habiba bata bambanta su kamar yadda shima Areefullah baya nuna banbanci.

*****Dawowarta daga asibiti kenan, duk ta gaji yau tasha aikin bada magunguna har kanta ya fara ciwo. Farin hijab ɗin dake jikinta ta cire tare da faɗawa kan gado tana sauke numfashin gajiya. Kwata kwata bata san Areefullah yana cikin gidan ba domin ko motarsa bata gani ba, muryarshi ta jiyo yana cewa.

"Habibty ZO GARENI." Tayi saurin kallon bakin kofa taga babu kowa, sai ta kuma jin ya kirata.

"Ki ZO GARENI please I need you here." Da sauri ta miƙe zaune tana kallon ƙofar shiga banɗaki, shi ta gani a tsaye ya ware hannuwa alamar yana jira taje, ta rufe ido tana cewa.

"Na shiga uku idan yaran nan suka shigo fa.?"

"Idan baki ZO GARENI ba Allah bazan koma ciki ba." Ai tana jin haka tayi saurin tashi taje ta rufe ƙofar ɗakin, tana dariya sannan ta ruga tare da shigewa jikinsa ya maida hannu ya matse ta yana sumbatar goshinta yace.

"Farin cikina ZO GARENI mana, ko so kike na shiga wani yanayin? Saboda na kasance dake na tahu gida wallahi."

Daga haka ya taya ta rage kayan jikinta suka shige cikin jacuzzi tub suna ƴar watsawa juna ruwa sai dariya suke yi......🤸‍♀?


ALHAMDULILLAHI³ ALLAH SHINE ABIN GODIYA. DA ƊAUKAKARSA DA KUDURARSA NA SAMU DAMAR FARAWA DA GAMAWA.

FAƊAKARWAR DAKE CIKI ALLAH UBANGIJI YASA MUYI AMFANI DA ITA. KURA-KURAN CIKI ALLAH YA YAFE MANA GABAKI ƊAYA.

WATAN AZUMIN RAMADAN DA ZAMU SHIGA UBANGIJI YA DUBE MU YA RANGWANTA MANA HALIN DA MUKE CIKI, ALLAH YASA MU YI AZUMI LAFIYA MU GAMA LAFIYA. YA AMSA IBADARMU YA KAWO MANA KARSHEN MASIFUN DA MUKE CIKI.

ALLAH KASA FARIN CIKI A ZUKATAN MASU AZUMI. ALLAH KA CIRE KUNCI, DAMUWA, BAKIN CIKI A CIKIN ZUCIYAR MAI AZUMI. ALLAH KARKA BAMU DAMA DA IKON CIN HAKKIN WASU KO YA YANE. ALHAMDULILLAHI. KARKU MANTA NI ƳAR ADAMA CE, ABINDA NAYI KUSKURAN RUBUTAWA INA ROKON ALLAH KARYA TASHE NI RANAR TSAIWA.

WATTPAD:- Hajjac
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022
SUBSCRIBE MY YOUTUBE CHANNEL https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g STYLISH TV.











*HAJJA CE 👈*

38 / 38