Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   24 / 38

69K to 72K   out of 113.7K words

shiga falo ta tarar da Mamah suna hira da Jamil. Ta ƙarasa cikin falon tana ɗan yatsina fuska ta gaishe dashi ya amsa murmushi fadade a fuskarsa ganin yadda uniform ɗin jikinta suka yi mata matuƙar kyau.

Yasha mamaki ganin yadda sabon shirinsa yaki yin tasiri akanta, gashi boka ya tabbatar masa da cewa wannan karon idan yaje suka haɗa ido zata sake rikicewa kamar farko tunda an riga an tarwatsa musu shirin da suka zo dashi na matsayin Jabir. Haka suka dinga haɗa ido amman Jamil baiga tayi ko gezau ba sai ma tashi tayi ta shiga ɗaki yana ji yana gani. Ya daɗe a gidan amman taki fitowa, besan ma kwanciya tayi ba har bacci yai gaba da ita, dole ya yiwa Mamah sallama ya bar gidan.

Gaba ɗaya abubuwan sun fara dagule masa, yana murna zai samu Iman cikin sauki sai gashi lokaci kankani komai ya ruguje, shine yasa bokansa ya bincika masa inda dangin Iman suke, ya biya uban kuɗi aka sa kafiran aljanu sukaje suka tone duk wani asiri da aka yi na raba tsakaninsu. Gashi sun bayyana shi kuma an ruguza masa tsarinsa. Shine yasa aka dinga yiwa Areef gezo ana nuna masa suffar mutum ya fito daga wanka tare da Iman, da kuma lokacin da yaga saurayin ya fito daga gidan, yaji matuƙar daɗi da yaga Areef ya saketa.

Yanzu kam ya rasa madafa, ya kasa kwantar da hankalinsa gashi baya so ya rasa yarinyar dan a yanzu ne ma da take shirin zama ma'aikaciyar lafiya yaji wata irin zazzafar soyayyarta cikin zuciyar shi. Ga Salima matarsa ta fara butsare masa tana bibiyar al'amuransa, bincikenta ya fara yawa akansa, har faɗa suka yi da ita ya kusa sakinta. Duniya ta fara yi masa zafi gashi daman saboda shiriritarsa yasa kwazon da yake dashi na harkar aikinsa ya fara yin sanyi, da wahala ya yiwa wani aiki a samu nasara, asibitoci da yawa sun dena kiransa.

Ya cije yatsa tare da cewa "Ko zanyi yawo tsirara bazan bar wani ya mallakeki ba Iman. Ke ɗin mallaki nace kuma dole ki ZO GARENI."
______________

Su Iman suna fara jarabawa komai nata ya tsaya cak, bata komai sai karatu da yawan bincike-bincike. Kasancewar yau weekend ne Islam ta haihu ranar ake suna, tana son zuwa tana kuma so ta duba lecture note ɗinta da zasu yi exam ranar Monday. Ganin su Ikram suna ta shiryawa yasa itama ta hakura da karatun taje tayi wanka ta shirya cikin wata ash ɗin shadda da aka yi mata riga da skirt, aikin da aka yiwa shaddar baki ne hakan yasa tayi amfani da bakin mayafi da takalmi, daman tunda ta fara karatu take sanya farin glasses a idanunta wanda yake ƙarawa kyawunta kyau na musamman.

Tunda yai parking motar a ƙofar gidan yake fargabar shiga, besan ta yadda zasu karɓeshi ba bare ya wanke kansa, yana sanye cikin wani maroon ɗin yadi wanda aka yiwa kananun ɗinki, ya yi kyau wata irin haiba da kamala sun sauka gareshi. Lokaci guda ya zama wani irin cikakken saurayi mai kyau da haiba, idan ka kallesa sau ɗaya dole ka ƙara saboda yadda tsarin halittarsa ta cika. Ya daure ya fito kansa a ƙasa tamkar wata sabuwar amarya.

Ya kama handle ɗin falo zai buɗe ya shigo, itama Iman a lokacin ta kama zata buɗe ta fita zuwa cikin motar Mamah ta ɗakko mata tissue, a tare suka murda taja shi kuma ya turo suka yiwa junansu kallo na farar ɗaya, a take dukan su sukaji wani irin faɗuwar gaba. Duk sun gane juna, sai dai kowanne daga cikin su yasan cewa ɗan uwansa ya canza daga yadda aka san juna. Mata iyayen shariya, duk da cewa tana son kuma kallon shi sai ta share ta raɓa zata wuce yai saurin sanya tattausan hannunsa ya riƙe nata.

Dukkansu sai da sukaji wani irin shock a tare dasu, kafin Areef ya ɗan koma baya still hannunsa ya riƙe nata yana kokarin sanya idanunsa cikin nata amman ta hana hakan faruwa.

"Malam meye haka?" Ta faɗa cikin tsiwar da bata san ma zata iya yi masa ba idan sun hadu.

"Can't you see me?" Ya faɗa da wata murya wacce tasa Iman dagowa ta kalleshi.

"Yeah nine dai ba wani ba, zaki wuce Iman ba tare da kin tsaya na bar gurin ƙofar ba?"

"Sakar min hannuna." Tayi magana tana turo baki fuskarta cike da fushi.

"Kina da karfi ai ko? Oya kwaci kanki in zaki iya." Ta zabga masa harara daidai lokacin Mamah ta fito ta tsaya tana kallon ikon Allah.

Wa take gani kamar Areef? Ta sake leƙawa tabbas shine, Toh me suke yi a haka? Cikin kakkausar murya sukaji tace.

"Sakar min hannun ƴa taje aiken da nayi mata." Areef najin muryar Mamah yai saurin sakin hannun Iman, suka kalli juna ta sake zabga masa harara tare da barin gurin, shi kuma ya juyo ya ƙarasa shiga cikin falon bakinsa da sallama yayin da kansa yake a ƙasa kamar wani mace.

"Me kazo yi mana cikin gida? Ashe har kana da kunyar da zaka iya zuwa da ita gaban mu?"

Taja tsaki tare da komawa cikin ɗakinta. Hanan da Ikram suka fito da sauri jin yadda Mamah ke faɗa sun san dole wani ne yazo gidan. Suka yi turus ganin Yaya Areef, mamaki tsababa a fuskarsu saboda basu zato ko tsammanin ganinsa ba. Ya kallesu yafa sun kura masa ido kamar sunga ɓarawo, a lokacin Iman ta dawo da tissue a hannunta taji yana ce musu.

"Menene kuka zura ido kuna kallona?"

"So mamakious Yaya Areef kai ne?" Cewar Ikram cike da mamaki.

Cikin takaici yace. "A'a aljani ne." Suka zabura suna riƙe juna, Iman da ta ɗan gotashi tana tafiya tace.

"Toh ai ba abin mamaki bane idan mun ganka a suffar aljani, nida nake da saurayi aljani har wani tsorata mu zaka yi? Zata iya kasancewa ma aljanin ne amman ni yanzu bana tsoran su wallahi." Tana gama magana ta waigo tare da murguda masa ɗan ƙaramin kugunta ta shige ɗakin Mamah.

Baki buɗe Areef yake kallonta harta shige, ya shiga cizon leɓe lallai yarinyar nan tazo da sabon abu, Yaja ɗan ƙaramin tsaki tare da shiga ɗakin Mamah ya tarar tana yafa mayafi, Iman kuma tana goge mata fuska inda kwalli ya ɓata mata.

"Ke ɗan fita ki bamu guri." Ya faɗa yana kawar da fuska.

"Wace zata fita? Babu inda zata saboda tare kazo ka tarar damu, kai nema zaka fita domin babu abinda zaka gaya min na yadda dashi. Kai da ace bani na haifeka zan iya cewa canza min akai yi."

Yayi shiru ko motsin kirki ya kasa yi, ya kalli inda Iman take tsaye yaga sai faman murmushi take yi wanda shi bega abinda akai na murmushi ba. Babu yadda zai yi tunda ta hanata fita gashi yaga kamar unguwa zasuje, dan haka ya shiga bawa Mamah hakuri Amman tayi masa banza, yaji kamar zai fashe da kuka saboda Iman a gurin gasu Ikram da suka shigo yasa shi jan baki bai kuma cewa komai ba.

"Ku wuce mutafi." Yaji Mamah ta musu magana, da sauri ya ɗauke mukullin motar ta da ya gani a kusa dashi yana cewa.

"Muje na kaiku Inda zakuje."

"Bama so kasha zamanka." Cewar Mamah.

Suka fita yabi bayansu shima. Da sauri yaje ya buɗe motar Mamah ta kalleshi tana tabe baki tace dasu Ikram.

"Ku wuce muje, yayi tunanin a mota zamuje ina ganinsa ya ɗauke mukullin motar." Suka saki dariya, yaga sunyi hanyar waje shima ya fito da sauri yabi su.

Motar da suka gani a ƙofar gidan bata basu mamaki ba, kowa yasan shi yazo da ita ganin yadda a kaita gaf da jikin gate. Babu wanda ya yi masa magana sai Ikram ce tace masa.

"Yaya ka koma gida kaci abinci ka huta, gidan kawu Sagir zamuje suna." Da mamaki tsantsa a fuskarsa yace.

"Waye ya haihu?" Tace,

"Islam ce, kaga kuma da yanzu muna shirin shan sunan yarku ko danku kaida Iman." Bata ankara ba taji yasa hannu ya bugi bakinta, cak kuma ya tsaya ta juyo tana kallansa.

"Kai Yaya Areef dan Allah menayi? Ya ka tsaya anan?" Yace.

"Kuje ku dawo."

"Dan Allah kazo muje."

"No bazanje ba."

Ya juya ma ya koma ita kuma lokacin su Mamah har sun sha kwana dan basu wani tsaya ta ba. Tunda sukaje Iman ta kagara su koma gida, ba ƙaramin daɗi taji ba na dawowar Areef duk da cewa itama yanzu jin kanta take tamkar wata babba. Wata irin izza takeji saboda tasan yanzu tafi karfin yayi mata gorin ta yadda aka sameta. Har yamma suna can tana ta faman su taho a koma gida amman sunki, gashi tana son zuwa tayi karatu sai kawai Mamah tace ta koma gida sai sun taho. Ba haka taso ba amman babu yadda zata yi dole tayi gaba ita kadai ta barsu akan cewa sai anyi sallar isha'i sannan zasu taho.

Cikin ƴar waƙarta ta Dil Toh phagal hai ta shiga falon tana zare mayafinta. Areef ta gani yana sallah daga can gefe saboda ɗakinsa a kulle yake mukullin kuma yana gurin Mamah. Ta zaro wayarta daga cikin jaka ta shiga yi masa hotuna ba tare da ya sani ba. Ɗaki ta wuce cike da nishaɗi ta ɗakko abin karatu ta fara saboda bata sallah tana period. Sam bataji takunsa sai kawai ganinshi tayi a cikin ɗakin, ta kallesa taga ita yake kallo, batace masa komai ba taci gaba da abinda takeyi. Ji tayi yace.

"Akwai abinci?" Tayi masa banza tana karkaɗa biron hannunta, ya sake cewa......

https://youtu.be/qR81anYaPdQ SUBSCRIBE please
*Top 10 Takun haske batch A, in kina son karantawa ki tuntubi wannan numbers ɗin. 0706 528 3730 or +447894142004 for more information.*











*HAJJA CE 👈*
3/12/22, 17:43 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*


*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣?*
*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️*
*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA🗣️🗣️🗣?*

*NUCEEYLUV😘 NA MUKU ALBISHIR DA DATA DINTA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA, MAZA KU GARZAYO SAUKI DATA A CANCARE KU DA DATA A BAGAS🤸🏻‍♀?, TURAWA BABU BATA LOKACI 📤👌🏻*

*MTN*
50mb-50
150mb-100
500mb-200
1GB-300
2GB-600
3GB-900
5GB-1500
10GB-3k
20GB-5k

*Codes for check balance, *131*4#*
*1MONTH VALIDITY*

*AIRTEL*

100mb-150
300mb-250
500mb-300
1GB-600
2GB-1200
5GB-3k
11GB-4500

*Codes for check balance, *140#*
*1MONTH VALIDITY*

*GLO*
1.35GB-550
2.9GB-1200
4.1GB-1600
5.8GB-2200
7.7GB-2600
10GB-3200
14GB-4k

*Codes for check balance, *127*0#*
*1MONTH VALIDITY*

*9MOBILE*
1.5GB-1200
2GB-1500
3GB-2k
11GB-4k

*Codes for check balance, *228#*
*1MONTH VALIDITY*

CALL 09039118754 OR CHAT ME PRIVATE 09039118754?

*YADDA ZAKI BIYA, ZAKI TURO KUDI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 1445626295. NUSAIBA MUSTAPHA ACCESS BANK*

*IYA KUDIN SIYEN DATA IYA SHAGALIN KU🤸🏻‍♀? BANA AMSAR KATI PLS😁👌🏻, KADA KU BARI AYI BA KU WANNAN GARABASAR😍, ZAKU IYA SAVING NUMBER NAN 09039118754 DOMIN SIYEN DATA KAI TSAYE BABU BATA LOKACI KO BANA ONLINE KU KIRA KAWAI MASOYA💃🏻*



*30*


"Akwai abinci nace?" Iman ta yatsina fuska tare da cewa.

"Oho." Ta cigaba da karatunta, yaja numfashi tare da cewa.

"Koda ace zaki min rashin kunya ki dinga tunawa ni mijinki ne, idan kuma ba haka ba zaki jefa kanki cikin wuta." Ta kalleshi a mamakance tare da sanya biro cikin bakinta tana murza ƙasan.

"Ka ce menene?" Dariya ta kwace mata tace.

"Mijifa kace? Tab dai Yaya Areef! Bakada labarin kuɗin auran wani dake kaina hala? Ai kariga ka bar damar da Allah ya baka na aurena, kayi irin sakin da ake cewa sakin wawa, gashi tun da na fito daga cikin gidanka zuwa bakin titi nayi katari da wani sabon miji mai jini a jiki, ɗan kwalisa kuma jarumi jajirtacce. Soon zamu yi aure muje mu more rayuwar mu a ɗakin mu na sunnah, sannan shi a haka yaga farantin selver yake kuma matuƙar so."

Kalamanta sun matuƙar ɓata mishi rai, ya saki tsaki tare da juyawa zai fita, kome ya tuna oho ya dawo tare da janyota ba tare da tayi tsammani ba. Jikinsa har kyarma yake saboda ɓacin rai, ya haɗata da jikin ƙofa yana ƙare mata kallon tsan. Ita kuwa duk ta firgita ganin yadda ya janyota ya manna jikin ƙofa, ta rintsa idanuwa kirjinta na wani irin bugawa da sauri da sauri. Shiru bataji komai ba daga gareshi ba, hakan yasa ta ɗan buɗe ido kaɗan, samun shi tayi yana ta kallon fuskarta tamkar yau ya taɓa ganinta, ta shammaceshi da karfi ta hankaɗeshi yayi baya kamar zai faɗi.

"Wai meye haka Yaya Areef? Karatu fa nake yi amman kazo ka fizgeni sai kace wata kaya."

Sai da ya daidaita kansa ya tsaya da kafafuwansa sosai kafin ya dosheta, ganin yana nufowa inda take ne yasa ta ɗaga skirt zata ruga yai saurin riƙota, samun kanshi yai da mannata a kirjinsa, kansa ya zura ta gefen wuyanta yana kallonta. Jikin Iman yai wani irin laushi sakamakon jinta a jikinsa ya manneta. Ƙamshi turaran body oil na alharameen dake jikinsa ya mamaye duk ilahirin hancinta. Kwakwalwarta ce ta tuno mata da Feenah ta sanar mata cewa yana yiwa Feenah fiye da irin wannan riƙon da yai miki, cikin sauri ta shiga son kwace jikinta amman ta kasa dan ba ƙaramin riƙo yai mata ba.

"Wai menene haka?."

Yasa bakinsa cikin kunnanta yana hura iska mai matuƙar ɗumi, wacce tasa Iman sulalewa zatai ƙasa Areef yai saurin riƙota da azama. Iman kuwa ji tayi yana neman jefata inda bata san ma wani bawa yana zuwa ba cikin hankalinsa, me hakan yake nufi? Gaba ɗaya taji wani irin yarari tamkar na tsutsa yana bin gaɓoɓinta. Ko hakan shine SO? Ta shiga tambayar zuciyarta wacce ta sake kaita ga wani tunanin cewa. A'a ba SO bane yarinya, wannan sha'awa ce. Ai a zabure ta dawo cikin hayyacinta, kur ta ɗora idanunta saman fuskarsa.

Kenan wannan abubuwan yake yiwa Feenah lokacin da suke tare? Itafa ji tayi tamkar an sakata a wani ni'imataccen lambu tana tsinkar fure yadda take so. Ganin yadda ya kafeta da ido ne yasa ta fara ƙoƙarin kwace kanta amman ta kasa, sallamar Mamah yayi daidai da dauƙe wutar nepa gidan yai dinɗim dashi, ko hannu ba zaka iya gani ba saboda duhu. Areef yaja numfashi tare da janta, kawai Iman taji su akan gado saman littattafanta da take karatu.

"Iman kina ina ne?" Sukaji muryar Mamah a falo, da alama haske take buƙatar a kawo mata.

"Na'aaa...."

Yaki bari ta ƙarasa ta hanyar toshe mata baki da hannu, ya kuma kwanta a saman cikinta, ya ɗora kai saman dirarrun ƴan fitilunta guda biya da suke tsaya ƙam dasu.

Ta shiga tutture shi amman yaki ɗagata, sai da ya tabbatar Mamah ta hakura da kiran Iman ɗin sannan ya dago kai tare da sa hannu cikin aljihu ya ciro wayarsa. Haska fuskarta yai ta buɗe ido still hannunsa yana toshe da bakinta ta kasa ture shi daga jikinta. Ya kuma yin ƙasa da murya yana cewa.

"Kina yin magana taji ina cikin ɗakin zatace kina sane kika dawo dan ki ganni." Ya sakar mata baki tare da kashe mata ido ɗaya.

"Ɗaga ni dan Allah, ko baka san akwai sa ranar auren wani a kaina ba?" Areef ya zuba mata wani mugun kallo mai tattare da warning, ya cije leɓansa na ƙasa yana cewa.

"Wallahi na kara jin kince akwai kuɗin auran wani a kanki sai na fasaki ƴar rainin hankali kawai. Zakice bakya sona ne? Kinibabbiya." Mamaki ya kamata baki buɗe take kallinsa, ya kawar da kai yana fadin.

"Bana son yawan kallo."

"Ka ɗagani toh."

"Anki ɗin."

Gabaki ɗaya basuji motsi ba, gashi an dawo da nepa sai ga idanun Iman cikin nasu Hanan. Cikin karfi ta dinga ture shi amman yaki ɗagata sai ma ƙoƙarin janyota da yake yi, kawai yaji muryar Mamah a bayansa, wacce ta hango su Ikram sun tsaya bakin ƙofar kowacce ta riƙe baki shine ta ƙaraso dan ganin abinda ya hanasu shiga.

"Laaaahhh menene haka?" Ai Areef besan lokacin da ya miƙe tsaye ba, ya juyo ya kalli bakin ƙofar a tsorace.

"Ehhhh lallai yaron nan baka da kunya, uban me ka shigo yi a ɗakin? Koda yake ba sai ka faɗa ba na gani da idona, zoka fita kona fasa maka kai." Ta ƙarasa maganar tana bashi hanya.

Cike da jin kunya ya fice, Iman kuwa tashi tayi tana turo baki ta nufi gurin Mamah cike da borin kunya tana cewa.

"Wallahi Mamah kawai ina karatu ya shigo, ni banma kulashi ba kina kirana shine ya makure ni wai bazan amsa kiran ba dan karki san ya shigo."

"Na gani ai, banda ya raina mana hankali yasan yana son kasancewa dake ya rufe ido ya sakeki? Kuma tsawon lokaci kin manta da zamaninsa shine zai zo ya dinga zage jiki yana jibga miki. Rab....." Bata ƙarasa ba sukaji yana cewa.

"Nifa ban saketa ba, yaushe na sake?"

"Okay tambaya ma kakeyi? Nace mu kake tambaya yaushe ka saketa? Ka manta kenan? Toh tun ranar daka dena ganinta a gabanka tun a sannan ka yi sakin. Shine yanzu zaka zo ka raina mana hankali ko?" Shima cikin turo bakin yace.

"Wallahi Allah Mamah ban saketa ba, ni koda nayi ma ai da daddare dana koma gidan nace na dawo da auran."

"Ubanwa ka sanarwa cewa ka maida ita? Kana nufin kace auranku yana nan saboda a garin gaɓa-gaɓa aka haifeka?" Areef ya sake marairaice fuska yace.

"Wallahi Allah Mamah na dawo da ita tun a ranar, kawai ni tsoron kiranku nayi ina gudun faɗan da zaku yi min. Kuma Mamah tare da wani kato fa naga sun fito daga wanka, kuma still bayan na fita nayo sallah zan dawo naganshi ya sake fitowa daga gidan yana ta murmushi, ganin ta maida ni bansan abinda nake yi ba yasa bakin ciki kawai nace na saketa saki ɗaya. Da daddare dana koma gida na tabbatar da cewa bata nan hankalina ya tashi dan bansan inda ta tafi ba, sai a raina nace na dawo da auren. Banyi zaton gida ta dawo ba shi yasa na kasa zuwa dan bansan abinda zan gaya muku ba." Kamar jira take yi ya kai karshe, tace masa.

"Karya ne, ka dawo kaga yarinya ta samu kwanciyar hankali, karatu ya fara ratsata shine zaka fake da cewa ka maida ita. Toh bari kaji na gaya maka banda an ɗan samu matsala da tuni Iman ta kusa zama matar wani. Kuma yanzun ma ai mu muka baka ko? Toh mun kwace kayarmu kaji na gaya maka." Tana gamawa taja hannun Iman suka wuce ɗaki tare da rufewa.

Kaɗan ya ragewa Areef fashewa da kuka, ganin su Ikram ne yasa shi kasa yin koda motsi. Sai dai fa wannan abun da ya faru yanzu yasa shi cikin tashin hankali, bema taɓa sanin

24 / 38