Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   26 / 38

75K to 78K   out of 113.7K words

wallahi. Ki kawo min abinci zanci." Ya faɗa tare da shigewa nasa ɗakin yana dariya.

Mamah tabi Abba da kallo ganin tamkar be damu da abinda take son ya gane ba, sai gani ma tayi kamar yana murna da hakan. Hannu tasa da bugi cinyar Iman ɗin tare da cewa.

"Ja'irai kawai, tashi ki koma ɗaki kafin na tumurmushe ki a gurin nan." Ikram ta kwashe da dariya, yayin da Iman ta miƙe da gudu ta shige ɗaki.

Mamah ta wuce kitchen dan haɗawa Abba abincinsa tana ta jinjina abin a zuciyarta. Ikram kam da gudu ta shiga inda ta tarar da Hanan na waya ita kuma Iman tana bandaki, dariya sai cin Ikram take ta kalli Hanan a hankali tace.

"Kina nan kina waya, ashe su Yaya Areef an kashe arna shida mutuniyar." Cikin sauri Hanan ta zaro ido tare da katse wayar a ruɗe.

"Ke baki san waya nake ba kike min wannan hirar?"

"Dalla can dan ma ana baki labari."

"Shine bazaki jira na gama wayar ba?"

"Wayasan lokacin gamawarku? Kuda idan kuna waya kamar marasa aikin yi. Uhmmm ke bakiga show ba wallahi, yadda kika san a India haka yaya ya ɗakko Iman a hannu ya dire a kusa da Mamah." Ta kuma tuntsirewa da dariya tana cewa.

"Kai yau naci dariya wallahi." Kiran da ya sake shigowa cikin wayar Hanan shine ya dakatar da Ikram daga ɗan banzan surutun da takeyi.

Hanan ta tashi daga gurin ta gudu falo dan idan ta zauna tabbas Ikram ce zata isheta. Iman ce ta fito daga bandakin ta shiga ɗakko abubuwan karatunta da aka ajiye a gefe. Ikram ta matso cike da son jin gulma, ganin haka yasa Iman tuntsirewa da dariya tana cewa.

"Kai.. Kai innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me kuma kike son kiji ne?"

"Dalla can ni ba wani abun bane, so nake inji ina kukaje, wallahi ba wanda zan gayawa dagani sai ke."

"Babu inda mukaje wallahi muna gidan nan." Ta sake matsawa kusa da Iman.

"Toh meye faru ya ɗakko ki?"

"Ba abinda ya faru, cewa kawai yayi bani da takalmi a kafata bari ya kai ni ciki." Uwar harara Ikram ta yiwa Iman tare da cewa.

"Karya ne."

"Toh shikenan tunda baki yadda ba."

Ta juya tare da hayewa kan gado ta kwanta, karatu take son yi amman ta kasa saboda tunanin yadda suka kasance ɗazu ita da Areef. Ta rintsa ido tare da kawar da fuska tana matse cinyoyi lokacin da ta tuno ya kwanta tare da janyota jikinsa murya a matuƙar sanyaye yace da ita. 'Please Iman inyi? Wallahi muna da aure kuma ina cikin bukata, ki bani please...' bata san lokacin ta da kama hannunsa ta ɗora akan pad ɗin dake jikinta ba, sai ji kawai tayi ya mata wata muguwar runguma, da alamar kwalamarsa ya mayar.

Tabbas tana san Areef dan batama san cewa tana san sa ba sai yau da suka kebe. Ta sake rintsa ido tana cizon leɓe ita kadai tasan abinda takeji game dashi, dan haka batajin zata iya kin amince masa a duk lokacin da ya buƙaci soyayyarta.
_____________________

Yana dawowa daga gidan su Aslam ya buɗe zai tura gate ya shiga da motarsa ya hango Abba ya fito zai kulle gidan, ya ƙarasa wajan shi abin mamaki sai yaga ransa a matuƙar bace, fuska babu annuri babu walwala bare yasa ran jin magana mai daɗi, hakan nan dai ya daure yaje gurin da yake tsaye, har ƙasa ya durkusa ya gaidashi.

"Barka da dare Abba."

"Me kazo yi min a gida?" Areef yaji maganar a wani birkice, ya ɗan kalli inda Abban yake tsaye.

"Eh kallanni da kyau ai gidana ne ni na gina abuna shi yasa nake tambayarka mekazo yi?"

"Dan Allah dan Annabi Abba kayi hakuri, nasan nayi laifi. Abinda ya hanani zuwa tuntuni ban san da wane ido zan kalleku ba."

"Oho yanzu ka samo idanun kallon mu ko? Gaya min me kazo yi gurin mu bayan ka kewaye mana baya?"

Areef yayi shiru bashi da wani abun cewa har sai da Abba ya koma ciki sannan ya samu damar miƙewa ya shigo da motar. Ya daɗe a bakin ƙofar falo kafin ya samu ya shiga. Babu kowa hakan ya sanyaya masa rai ya samu kujera ya kwanta tunda an hanashi mukullin ɗakin da zai shiga.

Washe gari da sassafe ya fice ya dauki Aslam suka tafi kauyen su Iman, ita kanta bata taɓa zuwa ba saboda sai sun gama exam Abba yace zasuje, shine kawai yaje ya gano inda suke sai kuma yanzu da Areef zaije. Ko a wane matsayi zaije musu oho? 😂










*HAJJA CE 👈*
3/16/22, 20:38 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please*


*32*



Suna tafiya cike da nutsuwa suna ƴar hirarsu har suka yi nisa da cikin gari, Areef ne yake tukin hankali a kwance, babban burinsa shine ya isa ga asalin iyayen Iman, ya riga ya gama shirya abinda zai sanar dasu har su goya masa baya Suyi masa jagoranci wajan ƙwato masa matarsa. Sai da sukazo daidai wani daji suka ga wani Dattijon mutum a tsakiyar titi, sam basu ga ta inda ya fito ba sai kawai ganinshi suka yi a gabansu, kaɗan ya rage suyi ciki dashi Allah ya taimaka Areef yaja wani mugun burki wanda yasa suka kusa hantsilawa.

"Dan Allah ji wannan tsohon, banda Allah ya kare me kake tsammanin zai faru? Kawai zai janyowa mutane yin azumi ba tare da an shirya ba." Cewar Aslam cike da fushi.

"Wallahi ban ganshi ba sai da mukazo gab dashi." Areef ya faɗa yana mai buɗe motar ya fito. Shima Aslam fitowa yai yana jan tsaki suka ƙarasa inda tsohon ya zube saboda tsoro.

"Sannu bakaji ciwo ba ko?" Areef ya tambayeshi yana kokarin kamo hannunsa dan subar tsakiyar titin.

Dattijon nan ya yiwa Areef wani mugun kallo, jikinsa har kyarma yake yi saboda tsabar haushinsa da yake ji. Areef ya sake kamo hannun tsohon yana cewa.

"Taso daga nan kar wata motar ta taho."

Cikin sauri tsohon ya fisge hannunsa tare da miƙewa da kyar yana ɗaukar ledarsa mai dauke da goro yace.

"Kai daman tun lokacin da na fara ganinka nasan cewar bakada mutunci. Haka kurum iyayenku sun sakar muku kan motoci sai ku hau manyan titi kuna tsola iskancin da kukaga dama. Wallahi da jini ya fito daga jikina sai ka gane kuranka" Tsohon nan yana magana yana nuna Areef da yatse yana cewa.

"Abinda ka fito nema kuma ba zaka samu ba sai dai kai ta wahala kana kara ɓatawa kanka lokaci. Sakarai shasha zanyi maganinka..."

Yana kaiwa nan tinkis-yinkis ya fara tafiya yana ɗingisa ƙafa, ko kafin su yi wani yunkurin sun nemi tsoho sama ko ƙasa sun rasa. Gaba ɗaya suka shiga zaro ido, kafin Areef ya shiga waige-waige yana cewa.

"Aljani ne wannan ba mutum ba, Aslam wallahi wannan ba mutum bane ta iya yiwuwa yana cikin makiran da basu so kowa ya rabi jikin Iman. Ni kuma da izinin Allah sai na mallaketa mallaka irin wacce basu taɓa tunanin ba, Allah yafi su da shi kuma muka dogara Insha Allahu mune da galaba."

Sam Aslam ya gaza gane inda maganganun Areef suka nufa, sai da suka koma cikin mota wannan karan Aslam ne ya karɓi tukin dan gabaki ɗaya idanun Areef sun rufe banda masifa da bala'i babu abinda yake yi. A sannan ne ya bashi duk labarin abinda yake faruwa, har sanadin da yasa ya saki Iman. Aslam ya jinjina lamarin yana kuma bawa Areef ɗin hakuri akan cewa sune da nasara tunda akwai Allah a lamarin su.

Suna zuwa kauyen yara suka dinga gudu ganin motar ƴan birni, sai tsalle suke suna son zuwa isar da sakon anyi baƙi. Su Areef Suka tambayi gidan mai unguwa, wani yaro yai musu jagoranci har ƙofar gidan. Areef ya dinga mamakin taya za'a ce a wannan kauyen aka samu Iman? A cikin wannan kauyan iyayenta suke? Allah kenan babu ruwanshi ikonsa kuma yawa gare shi.

"Wai ance kuhigo." Cewar yaron da ya isar da zuwan su gurin mai unguwa.

Da sallama suka shiga aka nuna musu gurin zama suka zauna, aka kayo musu ruwa a cikin kwanon sha irin wanda ake kurɓi ka bani ɗin nan. Gaishe da mai unguwa ya amsa tare da tambayar daga inda suke. Wannan ya kalli wannan haka suka dinga yi kafin Aslam ya ɗan muskuta ya fara bayani.

"Daga Kano can gidan Alhaji Ahmad mariƙin Khadija."

Ai nan da nan ya gane inda suke nufi, cikin ɗaga murya mai unguwa ya shiga kiran matan gidan, sai gasu kuwa yara da manya yace dasu.

"Daga gidan mariƙan Khadija ne gasu nan, ina Habi?" Ya faɗa ganin bega mahaifiyar Iman ɗin a gurin ba.

"Tana can rufa tana yiwa INdo kitso."

"Aje a kirawota." Wata yarinya ta fita da gudu tana kwaɗa kiran Inna Habiba.

Ƴan matan gurin sai kallonsu Areefullah suke shima yana binsu da kallo, banda murna da farin ciki matarsa ba anan ta taso ba babu abinda yake yi, domin kuwa Areef mutum ne mai matuƙar son wayayyar mace, hakan ne yasa Feenah take rinjayar zuciyarshi. Maida kallonsa yayi gurin Aslam da yaji yana cewa mai unguwa.

"Wannan shine mijin Khadijan." Gabaki ɗaya ƴan matan gurin suka ware ido wata ma harda dafa kirji, suda suke jira suji an ƙyasasu ya zasuji ana cewa suna da aure? Murmushi ya subucewa Areef kyawunsa ya sake tsatsowa, aji da kamalarsa suka kuma bayyana, kansa a ƙasa har Inna Habiba ta shigo ɗakin.

"Habiba ga surukinki yazo." Tayi saurin sunkuyar da kai tana murmushi batace komai ba.

"Sabon manemi ne ko kuwa wanda Baba Sunusi ya gano cewar azzalumi ne?" Cikin sauri Aslam yace.

"A'ahh wannan shine asalin mijinta da auran su har yanzu." Nan ya kwashe labarin da Areef ya gaya masa suma ya sanar dasu. Ya kuma basu tabbacin cewa Areef ɗah ne a gurin mariƙan Khadijansu.

Inna Habi ta sake satar kallon Areef, ta kuma maida kanta ƙasa ganin sun haɗa ido. Shi Areef kallonta yake yana mamakin yadda aka ce itace ta haifi Iman, akwai kama sai dai wannan ɗin tifical ƴar kauye ce wacce wahala yasa duk ta yi wani iri. Nan aka bar su kowa ya fita sai su kawu Sule da malam Bello mijin Inna Habiba sai Baba Sunusi. Ta kowane ɓangare sai da aka shigo musu da abinci, kowa so yake yayi gwaninta a gurinsu.

"Kunga kuwa jiya-jiyan nan akai waya da mahaifin Khadija, tunda aka tabbatar tana raye bayan munje mun ganota sai aka tura masa sako, Toh da yake abin ne sai addu'a yana cikin ƙangin asiri shi yasa be samu damar yin magana ba sai jiya, yace kuma Insha Allahu zai zo a nuna masa gudar jininsa tunda har zuwa wannan lokacin be kuma samun haihuwa ba."

Jikin su Areef yai mugun sanyi, wato akwai mugayen mutane da basu tsoran Allah bare suji tsoran cewa idan aka mutu ba'a dawowa. Sun daɗe a kauyen, sun kuma sha hotuna da yara da manya. Sosai Areef ya saki jiki dasu duk kuwa da cewar yana ɗan kyankyamin masu majina a hanci. Kayan abincin dake baya cikin booth wanda ya siyo zai kaiwa su Abba sai kawai ya sauke musu yace a rarraba. Sunyi murna sunyi farin ciki sosai sannan suka juyo zuwa gida bayan Baba Sunusi ya bawa Areef wasu layu guda biyu yace shi ɗaya Iman ɗaya, tasa a tsakiyar kanta shi kuma ya daura a ƙugunsa.

Zuciyarshi shar suka dawo gida cike da farin ciki. Mamah na zaune a falo tana kallo yai sallama ta amsa ba tare da ta ɗaga kai ta kalleshi ba. Yaje kusa da kafafunta ya zauna tare da kwantar da kai gefen kujerar da take a zaune yace.

"Mamah kina fushi dani bayan kinsan illarsa a gareni? Wallahi yau Allah ne ya rufa min asiri ba'a kasheni ba." Cikin gigicewa Mamah ya dago tana kallasa da mamaki tace.

"Waye zai kashe ka?" Ganin ta ruɗe yasa shi fashewa da kuka yana cewa.

"Muna cikin tafiya a mota nida Aslam kawai muka kusa bige wani Dattijo, bamu ga daga inda ya fito ba, kawai ganinsa mukai tsakiyar titi. Na fita dan mu duba shi shine yake nunani yana cewa shine ajalina wai bazai kyalini ba sai yaga bayana tunda naki barin auran Iman." Areef ya sake zubar da hawaye yana cewa.

"Tunda dama kema yanzu baki son auran namu shikenan zan ƙarasa igiyoyin kowama ya huta."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, toh waye wannan? Koma waye shida Allah kuma ni da wasa ma nake yi, ya za'a yi naso rabuwarku Areef? Kawai dai raina ne ya ɓaci shi yasa." Da sauri ya kalleta.

"Kin yafe min.?" Tace.

"Tun yaushe? Nifa daman ban tsine maka ba ban yi komai ba, kawai dai fushi nayi da abinda ka aikata." Ya saki ajiyar zuciya tare da yi mata godiya, dai dai lokacin Iman ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama.

Kallon juna suka yi ta ɗauke kai, ba karamin kyau yaga tayi ba cikin fararan kayan jikinta riga da wando da hijabi ga farin glasses tasha, wanda ya zauna ɗas a kan ɗan siririn karan hancinta. Wayyo Allah na, sai wanda ya ganta, kyau iya kyau babu wani kwalliya sai tsagwaran halittar da Allah ya tsara mata.

"Mamah I'm back."

"Welcome Auta an dawo lafiya?"

"Alhamdulillahi Mamah bari naje nai wanka." Ta faɗa tana tafiya ba tare da ta sake kallon Areef ba. Ganin haka yasa shi saurin cewa.

"Zoki ga wani abu." Iman ta tsaya cak tare da juyowa a hankali tana kallonsa.

Wayarsa ya ciro daga cikin aljihu yana dannawa, ganin bata dawo ba ta tsaya a inda take yasa shi cewa.

"Kizo aka ce."

Yayi mata maganar cikin bada umarni tunda yaga na farkon ta wani ja ta tsaya guri guda. Sai da ta kalli inda Mamah take ko zatace kartaje, sai taga hankalinta yana wajan kallon tv, ta yatsina fuska tana duba agogon dake daure a hannunta.

"Yaya bana son magariba tayi banyi wankan nan ba." Ya kalleta da sauri, cikin zuciyar shi yana tunanin 'Ko wankan tsarki zatayi? Murmushi ya saki cikin zuciyarshi tare da cewa.

"Okay jeki, idan kina buƙatar ganin komeye kya nemeni." Ya sake kallonta ganin bata tafi ba ya maida kansa gurin wayar yana cewa.

"Mamah kinga inda mukaje yau. Nida Aslam mukaje family ɗin Iman." Har ta juya fa zata tafi taji abinda ya ce, da sauri ta isa gurin tana murna tace.

"Dan Allah?" Ɓoye wayar yayi a bayansa tare da cewa.

"Kije anjima kya gani."

"Dan Allah Yaya ka nuna min dan Allah." Ya sake ɓoye wayar a bayansa yana cewa.

"Kije kiyi wankanki idan anyi sallah kya gani." Ta shiga bubbuga ƙafa a ƙasa tana marairaicewa tace.

"Dan Allah ka nuna min na fasa yin wankan yanzu." Ta faɗa tana zama a kusa dashi. Sosai take son ganin abinda ya ɗakko a can, tana so taga komeye saboda an ambaci mahaifiyarta. Areef ya rintsa ido jin yadda ta gogi kafaɗarsa, wani irin abu ya taso masa gashi sai kuma naniƙe masa takeyi, sai da Mamah tace.

"Kije kiyi wankanki sanda yaga dama ya nuna miki."

"Dan Allah ka nuna min Yaya Areef." Ya juya inda take suka yi ido huɗu ya turo bakinsa yana mata alama da tai masa kiss😘 Iman ta ware ido tare da miƙewa da sauri tabar gurin.

Murmushi yai sai da yaga ta shige sannan ya dakko wayar yana nunawa Mamah videos ɗin da hotunan, tasha mamaki.

"Toh kai ya akai ka san da maganar su?" Yai dariya wacce iyakarta saman leɓensa yace.

"Aslam ne ya gaya min, kuma yace yasan kauyen shine mukaje."

"Lallai ko ita Iman ɗin bata taɓa zuwa ba, amman ku iyayen sauri har kunje." Areef dariya yayi yaci gaba da kallon pic's ɗin har zuwa lokacin da aka kira sallar magariba yaje yayi ya dawo.

Koda ya dawo Iman tace ya nuna mata cewa yai sai anyi isha'i, yana sane kuma baya so ya nuna mata ne sai suna su biyu ta yadda zai kasance tare da ita.
______________________

Jamil kuwa gabaki ɗaya a hargitse yake, babu wani abu da yake zuwa masa cikin jin daɗi. Sosai hankalinsa ya tashi lokacin da yasan tabbas auran Iman sa Areef yana nan be mutu ba. Duk ya rasa wane irin aiki zai yi a mallaka masa Iman hankali kwance. Duk ya kasa maida hankali akan harkokinsa, waɗanda dama can ba ta hanyar Allah da ma'aiki yake yin su ba.

Iyalinsa sun rasa samun nutsuwa dashi, sam bashi da lokacin su kullum yana hanyar Niger to Kano, uban kuɗin da yake dasu duk sun fara karewa ya kasa gane cewa Iman ba tashi bace ba, yaki hakura yasan cewar Areef Allah ya tanadarwa ita. Ya bugi sitiyarin mota ta dinga bada horn babu kakkautawa. Murza mukulli yayi tare da jan numfashi yaja motar ya nufi hotel ɗin da yake kwana, tare da ɗaukar aniyar ba zai bar kano ba sai da Iman a matsayin matarsa.

Yaji haushi matuƙa da yaga Areef yaje dangin Iman har sunyi murna da farin cikin ganinsa a matsayin suruki. Koda bokansa ya mai aikin da yasa ya zama tsoho lokacin da su Areef zasu wuce, ba ƙaramin kuɗi ya bada ba, amman still babu nasara, takai ta kawo ma yanzu tsoron haduwa yake da Areef ɗin saboda layar cikin aljihunsa.
_____________________

Yana dawowa daga masallaci yaje ya samu Mamah a ɗaki tana sallah, sai da ya jira har ta idar kafin yace.

"Mamah zan samu key ɗin ɗakina?" Ba tare da tayi masa magana ba ta miƙe ta buɗe wata jaka ta ɗakko tare da miƙa mishi ya karɓa.

Sai da ya fara biyawa ɗakin su Ikram ya same su zauna akan gado suna cikin awara ya kalli inda Iman ke zaune, taki kallansa saboda daga ita sai vest kanta ko ɗan kwali babu yace.

"Ku shirya mu fita."

"Ina?" Cewar Ikram tana dangwalar yaji.

"Sai kunji sannan zakuje?" Ya tambaya still idanunsa suna kan Iman wacce ta janyo ɗankwalinta dake gefenta tayi mayafi dashi.

"Wai musan irin shigar da zamu yi." Ikram ta bashi amsa.

"Kuyi wacce kukaga dama." Yana kaiwa nan yabar wajan.

Sai da ya fara zuwa mota ya dakko jakar kayansa sannan ya shiga ɗakin. Wanka ya shiga yayi yana cikin shafa mai yaji muryar Mamah a bakin ƙofar tana cewa.

"Kace su shirya ku fita.?" Areef yace,

"Eh Mamah."

"Ina zaku?" Yace.

"Ice cream zamuje siyowa." Ta kaleshi tare da cewa.

"Toh wallahi da kunsiyo ka dawo min da yara gida, bance ka kai su gidan kowa ba." Mamaki ya kamashi jin yadda take maganar cike da faɗa. Dan karya tofa wani abun yajawa kansa yasa shi cewa.

"Toh

26 / 38