dai yasan ko yana shan wiwi ba zai iya kira ya tambayeta ba, dan haka ya hakura da kira yana maida wayar cikin aljihu. Jiyayi tamkar an fizgar masa sitiyarin motar ana kara masa karfin gudunta. Ya shiga ƙoƙarin tsayawa amman abu ya gagara, ga duhun dare fitilar motar ma daukewa takeyi sai yazo gaf da wata motar sai yaga ta kunna kanta. 'Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun' Ita ya dinga yi yana kuma ƙoƙarin hana jansa da ake yi. Areef ya shiga cikin tashin hankali wanda be taɓa tsammanin zai shiga ba. Ƴar ƙaramar layarsa da aka basu shida Iman ya dinga lalubawa be jita a jikinsa ba, ya tuna cewa be taho da itaba tana kan wardrobe ɗinsa.
Duk iya kokarinsa da dabararsa na son ganin motar ta tsaya amman ya kasa, sai kawai ya shiga yin addu'o'i babu ƙaƙƙautawa. Can yaji tamkar anyi sama da motar tashi, hasken fitilar motar ya dallare wata bishiyar kuka, yaji an nufeshi da ita gadan-gadan. 'Walayauduhu hibzihuma wahuwal aliyul azeem.' Ita ya yi a karshe tare da rintsa ido. Motar ta bugu da bishiyar wanda yayi sanadin tsayawarta a gurin cak. Kansa ne yayi wani irin sarawa, jiki na rawa ya shiga neman wayarsa dan ɗazu kasa shiga aljihu tayi sai zirarewa ƙasa.
Da kyar ya iya zarota ƙarƙashin kujera, ya shiga neman lambar Aslam, tana ta ringing ba'a ɗaga ba, sai da ya kirashi kusan sau biyar kafin ya ɗauka.
"Daka kira kaji ban ɗauka ba bazaka kyaleni ba, toh bana ɗakin sai yanzu na shigo."
"Ina cikin tashin hankali Aslam."
"Subahanallahi, tashin hankalin me? Hanaka Iman ɗin tayi?" Areef yaja tsaki, tsiyar kayi irin wannan shawarar da abokai kenan suyi ta kallanku a tsaitsaye.
"Malam ba wannan maganar ba, na taho Abuja yanzu haka ina Kaduna cikin wani daji, ina tafiya a motar naji an kwace sitiyarin ana sarrafa min shi. Aslam ina cikin daji yanzu haka babu kowa kusa dani."
"Guy kana cikin tashin hankali kam, Toh yanzu ya za'a yi?"
"Shine dalilin kiran da nayi maka."
"Kajika da wata magana, toh ni yanzu me zan maka."
"Eh wallahi ni ban ma san dalilin da yasa na kiraka ba. Duk da haka dai me kake tunanin zanyi?" Cewar Areefullah yana sake kunna motar amman taki tashi.
"Wai taya za'ai ka ce ana sarrafa maka tuki, kaida waye a cikin motar?" Aslam ya tambayeshi saboda yaji kamar almara.
"Ni kadai ne a ciki wallahi."
"Kam bala'i! Gaskiya kila akwai mutanan ɓoye, ta yiyu ma na Iman ne suke binka. Ɗazu ka mallaketa ne?" Tambayar ta yiwa Areef wani gingiringim ya kasa sanarwa Abokin nashi, sai kawai yace.
"Tabbas zata iya yiwuwa sune, yanzu ya zanyi?"
"Uhmmm Toh! yauwa bari na kira maka wannan mutumin na kauyen su Iman, kasan mun karɓi lambar junan mu da tashi da mai unguwa, kaima sai da nace ka karɓa ka wani ce baka buƙata gashi yanzu zatai maka amfani." Cikin sauri Areef yace.
"Turo min kawai." Aslam yai dariya.
"Wallahi zan barka ka kwana a da jin nan, ai kai namiji ne."
"Baka sona dama ni na daɗe da sanin haka."
Areef ya faɗa cikin jin haushinsa. Katsewa yayi tare da dafe kai, motsin komai babu sai kadawar iskar bushiyu, wani ikon Allah kuma beji wani tsoro ba saboda ya riga ya barwa Allah lamarin, yasan shine zai kawo masa mafita ba wayonsa ko dabararsa ba.
Aslam be turo masa lambar ba sai da ya fara kira ya yiwa Baba Sunusi bayani cewar mijin Khadija yana cikin matsala sannan yace ya turawa Areef ɗin Suyi magana. Shi kuwa dama yana zaune zuciyarshi tana wajan Mamah da Iman, bashi da wata damuwa dan yana zaune cikin dajin nan, yana ta kokarin kiran Mamah sai yaji ya kasa dan bema san abinda zai faɗa ba. Ganin abin yana damunsa yasa shi rufe ido kawai ya kirata, bugu biyu ta ɗauka, samun kanshi yayi cikin yin alamu na tashin hankali yana cewa.
"Mamah ki min addu'a ina halin rayuwa ko mutuwa."
"Ban gane ba, kana ina yanzu?"
"Ina cikin daji Mamah bansan ko ina bane."
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun na shiga uku, to kai ina ka fita?." Yace,
"Na taho Abuja har na shigo Kaduna ma, daga nan ne naji ana sarrafa min motar. Yanzu haka ina cikin daji bansan a wane hannu nake ba dama ko hagu." Cikin zabura Mamah ta miƙe tana dafe kirji.
"Kai waye yace ka tafi da yamman nan.?" Yayi shiru ya kasa magana.
"Yanzu a wane hali kake ciki? Ina nufin meya sameka?"
"Babu komai Mamah, motar ce dai taki tashi."
"Bari na kira Abban ku naji yadda za'a yi." Ta katse cike da tashin hankali ba tare da tajira yace wani abu ba. A lokacin ne yaga sakon Aslam ya turo masa lambar Baba Sunusi.
Sai da ya fara shigar da ita cikin contect ɗinsa kafin ya kira shi. Bayan sun gaisa ne yake tambayarshi duk yadda aka yi, Areef ya sanar dashi sannan yace ya jira zai kirashi nan da ƴan mintyna. Kiran Abba ya shigo wayarsa Areef ya ɗauka cike da girmamawa Abba ya tambaye shi halin da ake ciki, sanar dashi komai Areef yayi ya kara da cewa.
"Munyi magana da kawun Iman yace na jirashi zai sake kirana." Da mamaki Abba yace.
"Daman kuna waya dashi ne?" Areef yace,
"A'a Abba yanzu Aslam ya turo min da lambar, lokacin da mukaje duk ya karɓi lambar tasu."
"Toh shikenan nima bari naje nakai report wajan ƴan sanda ko akwai abin da zasu iya yi mana."
Godiya Areef ya yi daga nan ya zare wayar daga jikin kunnansa. Tsawon lokaci har ya fitar da ran kiran Baba Sunusi sai gashi ya kirashi, ji yayi yana tambayarsa cewa.
"Waye Jamilu?" Da mamaki Areefullah yace.
"Jamilu kuma? A ina?" Kafin a bashi amsa yaji an bugi bayan motarsa, Areef ya zabura tare da waigawa, duhun gurin yasa shi kasa ganin komai. Muryar Baba Sunusi ce ta sake dawo dashi cikin hayyacinsa, inda yaji yana ce masa.
"Duk abinda zakaji kada ka waiga, ka riga ka ajiye layar da na baka a gida. Yanzu bazaka tuna da wani Jamilu ko aboki ko a cikin ƴan uwa wanda yake kusanci a gare ku ba.?" Nan da nan kwakwalwar Areefullah ta shiga yin nazari da tunani, har yace a cikin zuciyar shi. 'Jamil' muryar Baba Sunusi ta sake katse masa zancen zuci inda yake cewa.
"Kasan shine?" Areef da mamaki yace.
"Waɗin?" Baba Sunusi yace.
"Jamil ɗin." Areef yace.
"Guda ɗaya na sani kuma best friend ɗin Yaya Haneef ne." Murmushi Baba Sunusi yayi tare da faɗin.
"Idan nace maka yana da sa hannu cikin duk wata kullalliya da ake muku kai da Khadija zaka yadda?"
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun Jamil ɗin? How? Aminin Yaya na ne fa, iyayena sun amince dashi sosai, ya za'a ce shine yake aikin nan."
"Yau wani abu ya haɗaka da Khadija ko?" Areef yaji Baba Sunusi ya tambaye shi, kunya ta kamashi yaki cewa komai.
"Allah ne ya taimakeku ana gano komai naku cikin sauki, idan ka duba kullin da aka yiwa Habiba da mijinta, (Iyayen Iman) duk iya kokarin mu na son warwarewa kasawa mukai, da yake Allah beso ba a lokutan, har sai da ya bayyana wannan bawan nasa gashi mijinta ya dawo cikin nutsuwarsa, ƴarsu tana raye cikin koshin lafiya. Ku kam sai ku godewa Allah abubuwan basu yi tsaho kamar nasu ba, kuci gaba da dagewa da addu'a saboda takobice a gurin duk wani mumini."
"Toh me muka yi masa yake bin mu da wannan sharrin? Ko wani abu ne tsakanin shi da Yaya Haneef yasa shi ramawa akan mu?" Baba Sunusi ya shiga girgiza kai tamkar yana tare dashi.
"Daman can mushiriki ne ba tare da Yayan naku ya sani ba. Ya kuma fara shiga cikin rayuwarku ne tun a lokacin da idanunsa ya sauka akan Khadija, yana gab da bayyana mata soyayyarsa gareta yaji an mallaka maka ita a matsayin mata. Wannan shine dalilin da yasa ya shiga rayuwarku yake takura muku ba tare da kun sani ba."
Gabaki ɗaya jikin Areef yayi sanyi, tabbas mutum mugune, zama da munafuki kuma gaskiya ne domin ma'aiki ma ya zauna dasu sai dai shi Allah ya bayyana masa ko suwaye amman kuma yasan ta yadda zai yi mu'amala dasu cikin aminci da salama.
"Yanzu za'a yi wani aiki idan ka tashi ka dawo gida karka tafi gurin aikinka, tafiya tare da matarka shine hanyar da zai kuma warware musu duk wani kulli da suka yi."
Areef ya rasa me zai yi murna ko bakin cikin abinda Jamil ya yi musu? Ba shakka sai yanzu ya tuna lokacin da Iman take ɓuya a bayan Jamil tana cewa shi zata aura, ya tuna lokacin da ta makure shi tana niyar kasheshi. Ya tuna lokacin da Jamil ɗin suka tafi shida Haneef amman ya dawo yace zai dauki takardu. Yanzu ashe duk shine ya sanya su Kawu Balarabe da liman cikin tsananin wahala? Idan ka ganshi a zahiri ba zaka taɓa yi masa kallon mugu ba, ashe Musa ne a fuska fir'auna a zuci.
Abba ya kira ya sanarwa da komai, hankalinsu ya matuƙar tashi a lokacin yaje ya sanar da dpo halin da Areef ɗin yake ciki, shi kuma ya yi waya da station ɗin Kaduna ya sanar har sun fara aikin neman motar Areefullah ɗin. Yayin da a can kauye Baba Sunusi ya sanarwa da mai unguwa da kowa halin da ake ciki. Nan da nan akai da'ira ta saukar al qurani mai girma. Mamah kuwa da su Ikram hatta ita kanta Iman dake kwance tana jinya sai da lamarin Jamil ya girgiza su. Suma hardasu a cikin saukar kowa ya dauki inda zai karanta.
Sai wajan karfe uku na dare ƴan sandan Kaduna suka isa inda Areef yake maƙale, da taimakon Allah da bincike irin nasu na sirri. Yana zaune cikin mota yana fatan Allah ya haɗashi da Jamil ido biyu sai ya masa rashin kunyar da bai taɓa zato ko tsammanin za'a yi masa ita ba. Suka ɗakko shi suka dawo dashi cikin motarsu, tashi kuma aka janyota. Suna shiga station ɗin ya tuna masa da daddyn Feenah lokacin daya tunkuɗeshi. Cikin ransa yace 'rayuwa kenan.' Amman a zahiri gurin da suka bashi dan ya huta ya kwanta ya nufa.
_______________
Washe gari tunda safe Areef ya dawo gida, babu abinda ya tsaya yi ya shiga wanka saboda jiya daman a haka ya tafi be kuma yi ba, sallolima sai taimama yayi. Sai da ya shirya tsab sannan ya fito cikin shadda milk wacce tayiwa fatar jikinsa kyau. Zagayeyyen gashin bakinsa baki wuluk ya kwanta tamkar wanda ake yiwa relaxer. Falo ya fito ya tarar dasu duk a shirye, cike da mamaki ya kalli su ikramy, Iman ce kawai babu a gurin tana ɗaki taki fitowa saboda raki take yi har yanzu.
"Yaya kai da zamu gani wurjanjan sai kawai mu ganka tamkar kaje wani gurin hutawa?" Ikram ta faɗa tana dariya.
"Ya ranki? Keda Aslam mugayene wallahi." Ya faɗa yana gyara links ɗin rigar shi.
"Wai ina zakuji haka?." Yana magana idanunsa suna kan links dan tunda ya shigo gidan yaki bari su hada ido da Mamah, kunyarta yakeji matuƙa.
"Gidan su Iman." Still yaki ɗago kai yace.
"Wow masha Allah."
"Dama kai muke jira ai, sai ku tashi mu tafi." Areef ya dago a hankali yana kallon Abba.
"Ni Abba? Naje fa."
"Wallahi nima naje Areef, amman wannan tafiyar ta dukkan muce tare zamuje, kayiwa ƴan gurin aikin naku magana cewa Suyi maka uzuri."
Areef yai murmushi jin Abba harda rantsewa, Mamah ta kawo masa breakfast da kanta, har kusa dashi taje ta ajiye. Kamar ya nutse saboda tsabar jin kunya, murya a hankali yace mata.
"Thank you Mamah." Itama murmushin tayi taje ta zauna, jefi-jefi tana kallansa har ya kammalaci.
Gabaki ɗaya suka tashi Mamah ta shiga ɗaki ta fito da Iman. Suna fitowa Areef ya kalli hanyar, idanunsa caraf cikin na mutuniyar tashi wacce ke sanye cikin doguwar rigar shadda maroon, farin mayafi ta yafa sai farin flat shoe. Iman ta turo baki tare da sake riƙe hannun Mamah wacce ki janyo ƙofar ɗakin ta rufe.
"Muje toh auta." Iman ta kawar da kai gefe suka fara tafiya. Areef ya saki ƴar dariya, farin ciki lullube a zuciyar shi ganin ƴar matar tasa kyakkyawa ce ta nunawa sa'a. Yana so ya yi mata magana nauyin Mamah ya hanashi, dole ya hakura suka tafi gurin mota.
Abba ne ya zauna gurin driver, da sauri Areef yaje zai karɓa Abban yace a'a ya barshi. Mamah ta zauna a gefen Abban hakan ya tabbatar musu da cewa baya Areefullah zai zauna. Hanan da Ikram sukai saurin shiga tsakiya, cike da mugunta Ikram tace.
"Yaya sai ku shiga can baya kai da Madam ɗinka." Cikin sauri sukaji Iman tace.
"Wallahi ni dai a'a." Abba ne yace.
"Yi hakuri ki shiga mu tafi, rabu dasu manyan banza kawai."
Wayyo Allah kamar ta fashe haka ta shiga bayan tana faman hararar su Ikram. Ta hakince a tsakiya ta yadda idan ya zauna a inda ta bar masa zai matsu. Areef yaki kulata ya zauna a inda ta bar masa suka fara tafiya. Murmushi yayi yana cizon ƙasan lips ɗinsa saboda shi kadai yasan irin abinda ya shiryawa ransa da zai mata in har bata matsa mai ya zauna sosai ba. Ba zato babu tsammani taji hannunsa a kan ƴan fitilunta, cikin razana ta kalleshi tare da yin gefe sai faman turo baki take yi. Areef yai dariya yana kallonta.
Matsawa yayi kusa da ita ta makure a jikin motar idanunta a rintse, ya kai baki wajan kunnanta yana cewa.
"Ya jikin naki?"
"Ba'a sani ba." Tai maganar cikin jin haushi.
"Sorry my dear, ba gashi ba mun gano tsinannan mutumin nan Jamil, da munyi sanya ai da har yanzu muna cikin tashin hankali. Shege kawai idona idonsa sai na masa rashin kunya." Ɗan kallansa tayi da sauri ta janye idanun saboda wani abu da taji ya soki cikin kirjinta.
"Kinji daɗi kuwa?" A shagwaɓe tace masa.
"Wallahi zan gayawa Mamah ka dameni." Yace,
"Wayace miki ana yawan kai miji kara? Toh kima dena dan zasuce bakida riƙe sirri."
Iman ta shiga yin tunani, anan kam tabbas ya faɗi gaskiya, kuma abin haushin ma iyayena ne ba nata ba. Taja baki tayi shiru, shi kuma sai ya samu damar takura mata sosai.
"Ya warke gurin?" Cikin takaici tace.
"Wai ina tuwanka ne Yaya Areef.? Ni ka rabu dani wallahi bana son yawan magana."
Bakinsa yaja yayi tsit yana murmushi, wayarsa da aka kira ya dauka yana amsawa, daga can wajan aiki ne anjishi shiru bezo ba, ya sanar dasu halin da yake ciki. Da yake babban uzuri ne sai basu yi korafi ba sai kara masa kwanaki ma da suka yi cewa yabi komai a hankali.
Sun isa kauyen lafiya lau, sun kuma samu kyakkyawar tarba daga mutanen ciki. Duk inda sukai binsu ake yi. Farin ciki ya cika zuciyar Iman, bata kyamaci kowa ba duk wanda yazo gareta rungume shi take yi tana jinsa har cikin jikinta.
Areef kuwa mota ya koma yai zamansa saboda matan garin sun uzzara masa da kallo tamkar zasu cinye shi. Abinci ma da aka ce yaje yaci cewa yayi ya koshi fura da nono damammiya kawai ya sha itama ba wani sosai ba. Sunci sun sha sun zazzaga ko'ina a kauyan, karshe suka yada zango a gurin Baba Sunusi inda yayi musu bayani akan mutane irin su Jamil, basu yi mamaki ba duba da yadda ya ringa zuwa yana nuna damuwarsa akan halin da Iman take shiga, ashe duk na munafunci ne, lallai dole su sanar da Haneef dan yasan da wa yake tare.
Har yamma suna can kauyen kuma a can zasu baro Iman dan tayi musu kwana biyu taga ƴan uwa. Areef dake murna zai koma da matarsa Abuja murna ta koma ciki, gashi tunda sukaje taki bari su hadu har suka taho, daman da kayanta Mamah ta ɗiba ba tare da su sun san da manufar barinta a can ba. Sosai Areefullah yaji babu daɗi dan yaso ace sun dawo tare an danƙa masa ita su tafi gidan su.
*Wannan littafin na kuɗi ne, idan kina bukatarshi sai ki tuntubi wannan lambar 0706 528 3730 or +447894142004 dan mallakar naki.*
*HAJJA CE 👈*
3/21/22, 09:21 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲*
*36*
Tunda yaji abinda ya shiga tsakanin Iman ɗinsa da Areefullah yaji duniya tayi masa baƙiƙƙirin, banda tafasa babu abinda zuciyarshi keyi. Tunda yake komai yasa a gaba sai ya samu, amman tunda ya hadu da Iman ya garara samun nasara a cikin lamuransa. Komai ya dena zuwa masa cikin sauki da jin daɗi kamar da. Menene yasa hakan? Ya akai ya gagara mallakar wannan ƴar tatsitsiyar yarinyar da batafi loma bakwai ba? Hakan ma dan dai tana da tsaho ne shi yasa takai loma bakwai.
Wata irin zufa yakeji duk da cewa cikin office ɗin akwai sanyin a.c. Tunda malaminsa ya shaida masa an karɓi ƴan matancin Iman yaji komai nasa baya aiki dai dai. Gashi har zuwa wannan lokacin beji ya dena san Iman ɗin ba, banda kara masa wutar soyayyarta babu abinda ake kunsa masa a zuciya. Shawarar da malaminsa ya bashi ta ƙarshe wacce idan anyi dole akwai nasara a ciki shine yake damun zuciyarsa. Ya bada rayuwar yarsa saboda ya mallaki Iman amman a banza, yanzu bokansa ya tabbatar masa indai yana so asirinsa ya rufa a idanun kowa sai ya bada rayuwar matarsa ko mahaifiyarsa, shin a ciki wa zai bayar?
Yaja numfashi zuciyarsa na azalzalarsa akan ya bada wacce take ganin ba wani amfanin da zata yi masa sosai. Tashi yayi da sauri, mukullinsa ya ɗauka ya fice daga cikin office ɗin, gida ya nufa yana jin wani iri a tsakiyar wuyansa. Tun a mota ya sanarwa malamin wacce za'a ɗauka ayi masa toshiyar bakin da ita. Ko gama parking beyi ba Salima ta fito a gigice tana kiran sunanshi. Cikin kiɗima shima ya fito yana tambayarta.
"Lafiya..?"
"Umma Jamil, Umma ciwon ciki." Yana jin haka ya ture ta gefe ya shiga.
Yana zuwa ya tarar da ita sai faman juyi takeyi, ya rungumeta a jikinsa yana mata sannu. Wani kallo Jamil yaga Umman nayi masa, nan da nan sai yaji ya tsargu, ya fara tunanin ko tasan abinda yake faruwa? Murya a raunane yake cewa.
"Sannu Umma."
Ta kasa cewa komai banda hailala babu abinda take yi, ya tashi da sauri ya shiga ɓangaren su, ɗakinsa ya nufa yaje ya dakko abin