Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   37 / 38

108K to 111K   out of 113.7K words

subscribe my YouTube channel please 🤲)*


*46*




Tana shiga Mamah ta kalleta, harta zauna taji tace da ita.

"Ga abinci can na shirya a tray, yana kitchen sai ki kaiwa mijinki can ɗakinsa." Iman ta shiga sosa kunne da ƙaramin ɗan yatsanta, sam bata san zuwa wajan shi sai dai babu yadda zata yi.

Tashi tayi ta fice zuwa kitchen, zagaye ta shiga yi tana neman hanyar da zata hanata zuwa gurin shi ba tare da Mamah ta sani ba. Ba zato taji muryar Mamah a ƙofar shigowa kitchen ɗin tana cewa.

"Ki kai masa sai kije ki ɗauki Daddy ya ganshi dan tunda ya shiga ɗakina naga yana son daukarsa." Iman ta lumshe idanu, shikenan tama san dole sai taje ɗakin. Tray ɗin ta ɗauka ta fice tana faman kumbura fuska. Sallama tayi a can kasan maƙoshinta, kafin ta shiga ciki. Tsaye ta ganshi wajan gado rike da waya a kunnansa, ganinta ya sashi cewa.

"Zan kiraki anjima please."

Ai Iman naji gabanta ya sara tayi saurin kallon Areef wanda ya zare wayar daga kunnansa yana kare mata kallo. Wani irin zafi taji a tsakiyar zuciyarta tana jin wani tururi na tasowa daga ciki, bakinta ya shiga rawa alamar tana san yin magana amman ta kasa saboda kishi. Cikin sauri taje ta ajiye tray ɗin ta juya zata bar ɗakin taga bece da ita kanzil ba. Haushi ya kuma kamata ta sake yin gaba zata fita sai kuma ta juyo tana kallansa rai a matuƙar ɓace tace.

"Wallahi kaji tsoran Allah, ka tuna cewa duk abinda kai za'a yi maka, mai kyau ko akasin haka. Kuma kasan dai yanzu ka fara ajiye ƴaƴa, ya rage naka wajan zamowa yaranka uba nagari abin nunawa duniya. Ya kuma rage naka wajan bin ruɗin duniya, muna zaune a gida mun killace muku kanmu, amman ku kuna can kuna nuna mu ba komai bane face ajiyayyu a gida. Hmmm." Ta faɗa tare da ficewa daga cikin ɗakin nasa.

A lokacin ne taji sallamar bakuwarta, tun daga ƙofar ɗakin nashi ta ruga da gudu tana furta.

"Oyo-yo Habibty." Areef dake cikin daki yayi saurin fitowa, ganin bakuwar so nice yasa gabansa kuma yin wani irin bugu.

"Taho mu shiga ciki." Yaji Iman ɗin ta faɗa tana jan hannunta. Kamar zai yi magana sai kuma ya koma ciki yana huci. Tunanin hanyar da zaici uban baƙuwar ya shiga yi yana zagaye ɗakin.

Sai da suka fara zuwa ta gaishe da Mamah kafin ta jasu suka tafi ɗakin Ikram inda anan itama Iman ɗin take zaune. Cikin lokaci kankani ta cika su da kayan ƙwalam da maƙulashe, suka fara hira cikin nishaɗi kafin Iman tace.

"Jasmine kince kina cikin danger, Toh ke wayafi kwanta miki a cikin Ahsan da kuma Safwan?" Jasmine tayi murmushi tana kallon sister Layla. Cikin dariya Layla tace.

"Dukkansu ba baya ba, Ahsan ɗan gidan prisdent ne, while Safwan ɗan gidan babban attajirin ɗan kasuwar nan ne. Matsalar Ahsan tsantsar kishi, Safwan kuma tsantsar rainin hankali, kumafa duk masifar sonta suke."

"Wow-wow-wow! Kaji soyayya m...." Bata ƙarasa ba taji an fisgota, Areef ne ya shiga janta da karfi tana tirjewa yaki sakinta. Janta kawai yake yi Mamah da taji ihun Iman ta fito lokacin har Areef ya kusa fitar da ita yaji Mamah tace.

"Idan ka sake yarinyar nan tasa kafa a waje sai ranka yayi mugun ɓaci." Cak ya tsaya har zai fice sai kuma ya juyo cikin rufewar ido ya shiga magana.

"Haba Mamah, haba dan Allah. HUhm! Ya Iman take so nayi ne? Na bata hakuri nace mata na rabu da Feenah tana can gidan ta cikin kwanciyar hankali amma ni Iman ta hanani zaman lafiya why? Ina ce Feenah ce matsalar ko? Toh mun rabu tun tuni me yasa Iman ba zata yarda dani ba Mamah? Toh shikenan idan tana ganin ta gaji dani sai ta gaya min ni nagaji da wannan masifar, kafin taje ta shiga halaka ta gaya min idan bata sona." Ya ƙarasa yana huci.

"Eh ɗin bata sonka, dama ai ba ita tace tana sanka ba Abban ku ne yayi wannan hadin. Shikenan kuma haka ake yi yarinya tayi baki kaje ka wulakantata a gabansu? Sannu miji, nace sannu miji da aikata wannan ɗanyen aiki. Wai Areef ina zaka kai zafin kai ne iyeee? Shikenan kai ba zaka iya controlling zuciyarka ba sai ka dinga bari tana ingizata akan raayinta? Toh ya isheka, wallahi tallahi ya isheka bana san fitina." Kamar ya fashe da kuka yace.

"Mamah ba mutunan arziki bane wallahi, ƴan iska ne kawai sune suke zugata. Mamah neman ju..ju..ju..." Ya kasa ƙarasawa sai kawai ya fice daga cikin gidan zuciyar shi tana ƙuna.

Ƙarasa sakkowa kasa Mamah tayi tare da taimakawa Iman ta tashi tana kuka suka hau sama.

"Kiyi hakuri ki Iman but Areef idanunsa a rufe suke. Yana sanki amman ya kasa gane yadda zai zauna dake. Amman dai yanzu kiyi hakuri idan bakin ki sun tafi kizo muyi magana." Iman na hawaye Mamah na share mata har sai da ta yi shiru sannan ta raka ta wajan su Jasmine suka ci gaba da hira. Sun jima tare kafin su tafi sannan ita kuma ta tafi gurin Mamah.
______________

Bayan Iman ta gama bawa Daddy nono Mamah ta kira Ikram ta ɗauke shi ta goya shi suka tafi gidan Hajiya. Zama suka yi a ɗaki Iman tana zaune akan bedside drower yayin da Mamah ke zaune a bakin gado, numfashi taja ta ɗan kalli Iman tare da cewa.

"Dukkanku keda Areef ɗaya kuke a wajena babu bambanci, tarbiya iri ɗaya na baku, babu wanda nakejin haushi ko nake ki a cikin ku, duk daya na ɗauke ku Allah shine shaida. Iman kina son Areef? Karki ɓoye min duk abinda kikeji a tattare dashi, ki gaya min idan har kika ɓoye min keda Allah, shin kina san Areef?!"

Hawaye ya cika idanun Iman ranta na zafi, me zata ce banda ta faɗi gaskiyar abinda yake ranta, ɓoyewar bashi da wani amfani, zata faɗa koda ba haka Mamah taso ji ba, zata faɗi abinda zuciyar ta ke kudirta mata koda kuwa hakan shine zai yi silar barinta duniya. Cikin zubar hawaye tace.

"Mamah daman haka maza suke dama? Ko kuma nawa mijin ne a haka? Ina son Yaya Areef Mamah, ina san shi har cikin raina. 😭sai dai kuma Mamah ni ba kalar matan da yake so bane, Yaya Areef yana san mata masu jiki, ba wai jiki sosai ba, yana son a ƙalla kamar yadda na ɗan yi Kumari lokacin dana haihu. Mamah Yaya Areef yana da ƴan mata, zawarawa, harda masu aure wadanda suke son shi, suke kuma harinsa. Wadanda suka fini komai a halitta. Bare kuma yanzu da na kuma samun wata tawayar, tabbas wannan matsalar ta ƙanƙancewar nono guda ɗaya tana damuna Mamah, gashi kina gani munje asibitoci da dama duk maganar su ɗaya ce lafiya ta ƙalau. Duk wani garin kunun da za'a ce a haɗa asha nasha Mamah kina gani amman duk a banza. Taya zan samu zuciyar Yaya Areef Mamah? Idan bayan ne shima bani dashi Mamah😭 taya zai soni ni kadai ba tare da idanunsa sun kai gurin wata ya macen ba. Mamah ina jin wani irin zafi har a cikin zuciyata. Ko kuma wani laifi na yiwa ubangiji na ya kaddara min wannan kaddarar??"

Ta faɗa tana mai rushewa da kuka tamkar ranta zai fice. Jikin Mamah yai matuƙar yin sanyi, ta matsa gurinta tare da janyo ta jikinta tana bubuga bayanta, cikin kwantar da murya ta shiga yi mata magana.

"Kiyi shiru Khadijatul Iman, shin kin yarda da Allah?"

"Kwarai da gaske Mamah, na yarda cewa shi kadai ne bashi da abokin tarayya kuma annabi Muhammad s.a.w bawansa ne kuma manzon sa ne."

"Masha Allah naji daɗi da kika san hakan Iman. Shine kuma ya yiki a haka ya yi sauran masu abinda duk kika lissafo mijinki na so a jikin mace. Toh amman abin tambayar anan shine, me yasa duk da Allah yasan Areefullah yana son mace mai irin wannan siffofin be bashi ba ya bashi ke a matsayin abokiyar rayuwa? Allah fa ya fimu sanin abinda ke zuciyoyin mu, amman sai ya hana bawa abun me Yasa Iman?" Cikin share hawaye tace.

"Zata iya kasancewa dan ya jarrabashine yaga ya zai yi. Za kuma ta iya kasancewa dan ya nuna ishararsa ne ga junan mu mutane."

"Masha Allah Iman ɗin tawa akwai tauhidi. Abinda nake so shine, karki yiwa mijinki mummunar fahimta cewa dan baki da manyan halittu a jikinki shine yasa shi kulekulan mata. A'a Iman mafi akasarin maza haka suke, kuda ace kinda duk abinda mijinki yake so hakan baya nufin cewa ba zai kalli wata ba, ko bazai yi soyayya da wata ba, ko kuma idanunsa da zuciyarsa ba zasuji cewa ina ma ace matata na da kaza ba. Duk macen da kika gani a ɗakin miji tana da nata ƙalubalen, ya rage na mata tasan yadda zata tafiyar da hanyar gidanta. Yanzu wuka da nama yana hannunki Iman, wajan ganin kin mallaki zuciyar mijinki ba tare da boka ko malam ba. Kiyi masa komai gwargwadon iyawarki, komai kiyi masa saboda Allah, kinsan Allah duk iskancinsa ba zai iya yin wani abun a gabanki ba. Areef yana sanki kece kika hana idanunki da zuciyarki yadda da kuma amincewa da hakan, saboda kinga yana kula wata ko wasu. Ina so ki tattara duk wata ƴa mace da kika san tana bibiyar rayuwar mijinki. Do what ever you want to do wajan kuɓutar dashi daga fadawa halaka, kiyi mishi addu'a Allah ya kareshi daga fadawa cikin zina domin mata da yawa ashararai suna nan suna yawo suna neman mazaje ido rufe. Duk wacce tayi wasarairai da nata sai su kwace shi."

Numfashi Iman taja tare da kwantar da kai gefen kafadar Mamah tana lumshe ido.

"Irin mijinki sai an tashi tsaye Iman, domin yana da rawar kai, sannan kuma yana da saurin yadda. Ga kuruciya yanzu gashi babanki ya sake shagwaɓa shi, ya sakar masa bakin aljihu sai antayawa yake yadda yaga dama. Kiyi addu'a Allah ya tsare miki shi, ya mallaka miki shi, yasa yaji tausayinki da soyayyarki da jin daɗinki. Karki sake wata kawa ko ƴar uwa tace zata kai ki wajan boka, addu'a itace makamin mumini ki dage kinji ko?"

Share hawayenta tayi tare da tashi zaune tana wasa da yatsun hannunta, cike da jin nauyin tambayar da zatayi tace.

"Amma wane hanyoyi kika har yanzu Abba be miki kishiya ba? Wallahi Mamah nima ina son naga na rayuwa ni kadai tare da miji na da yara na." Dariya ce ta kwacewa Mamah, ta ɗora hannunta saman cinyar Iman tana fadin.

"Ko kusa, ko alama ban taɓa bin wata mummunar hanya ba wajan hana mijina yin wani auran. Allah ne kadai be ƙadarta za'a yi ba har yanzu. Kin ganni nan? Har yau ban taɓa jin cewa wai Abban ku bazai min abokiyar zama ba, saboda namiji bashi da tabbas, sannan shi karin aure indai kaddarar mutum ne tofa ko ta wace irin hali sai anyi. Addu'a ɗaya ce da mutum zai yi Allah ya sadamu da alkairi shikenan." Iman ta kalli Mamah tare da yin murmushi tana cewa.

"Wallahi Mamah kin chaɓa. Allah ya samu a danshinku." Dariya ce ta sa Mamah tashi tsaye tana cewa.

"Iman... Iman ya kamata ki sassautawa zuciyar, kishi wahala yake sanya mace."

"Yanzu Mamah wannan maganar ma da nayi duk kishine?" 😒 Tace,

"Eh mana."

"Toh Allah ya yaye min, Allah ya rabamu da kishiya."

"Amin Iman." Mamah ta faɗa cike da murmushi tana matuƙar tausayin yarinyar ganin yadda take matuƙar son gudan jinin ɗanta. Shigowar Ikram ɗakin cikin firgici yasa su kallonta da tambayar.

"Lafiya?"

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun Mamah Yaya Areef."

"Me ya faru dashi?" Mamah ta tambaya tana karɓar Daddy.

"Mashin ne ya bugeshi bakiga jini ba wallahi."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun." Iman ta faɗa tana zaro idanuwa hannunta dafe saman kirji......

*ZO GARENI na kuɗi ne, idan kina so ki tuntubi 0706 528 3730 dan samun damar karantawa.*










*HAJJA CE 👈*
4/1/22, 13:25 - Buhainat: *ZO GARENI*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

ƘARSHEN LABARIN.


*****Gabaki ɗaya suka gigice Mamah ta kalli Ikram dan jin karin bayani amman Ikram ta kasa saboda kuka da takeyi, babban tashin hankalinta shine a ce Areef ya mutu, saboda yadda taga an ɗagoshi ko motsi bayayi. Tana jin wasu matasa suna cewa Allah sarki ɗazu yazo garin ashe harda tsautsayin da zai same shi duk a yau ɗin.

"Ikram yi min bayani yana ina yanzu?" Cikin kuka tace.

"An tafi kaishi asibiti." Mamah ba ta sake cewa komai ba hijab kawai ta ɗauka tayi waje.

Iman kuwa zuwa tai ta kamo Ikram tana girgizawa, cikin firgici take cewa.

"Garin ya hakan ta faru Yaya Iki? Mashin ɗin waye?"

"Wallahi ban sani ba, amman kamar wucewa yazo yi kawai ya bugeshi."

Tuni Mamah ta dauki mota ta fice, a ƙofar gida ta tambaya aka sanar da ita asibitin da aka kaishi. Suma su Iman shiryawa sukai suka tafi lokacin tuni su Aslam sunje suna reception sai faman zagaye suke yi.

"Ya ake ciki Aslam?" Mamah ta tambaya jikinta a sanyaye.

"Har yanzu likita bai zo ba Mamah, but nurses suna ciki tare dashi."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, yana gidafa, nasan fushi ne yasa shi wani halin gashi abinda ya faru."

Suka yi shiru suma suna jimama, ƙarasawar su Iman ne ya hargitsa asibitin saboda kuka. Ganin sun daɗe likita be zoba yasa ta kira Babanta jin tana kuka ya tayar masa da hankali, yana jin abinda yake faruwa ya ruɗe, nan da nan ya fara faɗa tare da cewa a bawa Mamah wayar, ta karɓa tasa a kunne, ko gaisawa babu ya hau faɗa.

"Taya za'a bar mai accident a cikin asibitin da babu likita? Wannan wane irin shirme ne? Yanzu zan sa azo a dauko min shi, dama Kano ina suka ga wasu ƙwararron likitoci." Mamah taja numfashi.

"Ranka ya daɗe ai private muka zo, kuma liki..."

"Hajiya ya isa kawai a kawo min yaro nan inda za'a bashi kulawa ta musamman." Katsewa yayi Mamah tabi wayar da kallo. Uncle Imran da yazo lokacin tana wayar yace.

"Me yace?" Tace.

"Tace zai turo yanzu a daukeshi, wai a nan Kano babu ƙwararron likitocin da zasu iya duba masa ɗa." Iman ya sauke numfashi tare da cewa.

"Kinsan masu kuɗin nan, yanzu ko Abuja ya ajiye shi anjima haka zai ce basu san aikin su fitar dashi zai yi."

"Wallahi kuwa Imran, sai ma kaji yadda yake ta faɗa."

"Sai muyi addu'a Allah ya bashi lafiya."

"Amin uncle."

Suna zaune kuwa sai ga likitan cikin sauri, be tsaya ba ya wuce ciki gurin mara lafiyan. Abba shima ya ƙaraso cike da tashin hankali wanda har lokacin Iman ba ta dena kuka ba. Cikin yan a wani sai ga private plane daga Sen Muhammad, duk iya lallashi da likitan ya yi akan cewar su bari Areef zai warke a gurinsu sai da suka dauke shi, aka tafi da Iman da Abba sai Aslam su Mamah kuma suka koma gida.
_______________

Babban asibiti dake Abuja Sen Muhammad ya kaishi aka fara dubashi. Iman kuwa ta kasa dena kuka saboda gani takeyi itace sila itace ta sashi cikin halin da yake a yanzu. Hajja Samira cike da bakin ciki ta fara yiwa Sen Muhammad korafi ganin shima duk ya wani gigice ya fita hayyacinsa tamkar Iman ɗin ya rasa.

"Alhaji gaskiya ka damu da yaron nan fiye da su Abbas (yaran ƴan uwansa) dubi yadda duk ka firgice tamkar ance Iman ce a cikin condition ɗin. Gaskiya soyayyar da kake yi masa tayi yawa, bana jin koni kana yiwa irin ta." Sen yaja numfashi yana tare da ajiye tea ɗin hannunsa ya kalli Hajja Samira sosai tare da cewa.

"Ina son kisan wani abu ɗaya Hajiya Samira. Al-Mustapha wani ɓangare ne a jikin Khadija, ita kuma jini na ce da bani da tamkar ta duk duniyar nan. Toh me yasa bazan so abinda take so ba? Me yasa bazanji ciwon halin da mijinta ya shiga ba? Dan me yasa kike ganin laifi na Hajiya Samira? Please idan har ba zaki nuna min hanyar da zan bawa yata farin ciki ba, ina rokonki da karki sanya min baki, wannan shine abinda zan gaya miki."

Yana kaiwa nan ya janyo babbar riga yasa ba tare da ya yi mata sallama ba ya fice. Wasu matan ma dai ka rasa gane inda hankalinsu yake. Haka ya dinga jin bacin rai har ya ƙarasa asibitin.
_____________

Tana zaune a reception tana danna waya, kusa da ita Hajiya sama ce zaune a gefenta tana faman jan carbi gefen su hagu da dama securities ne dake tsaronsu. Aslam ya fito daga ɗakin da aka kwantar da Areef yana gyara hannun rigarsa, kallon Iman yai wacce ta dago ta zuba masa ido yace.

"Mijinki na kiranki." Cikin sauri ta miƙe cike da mamaki tana cewa.

"Da gaske? Ya farka? Yayi magana? Kuma ni ya kira?"

"Kwarai ma kuwa, guy ɗin nan be manta dake ba." Kasan cewar tunda aka kawo shi beyi magana ba sai yau tsawon kwanaki goma.

Tana shiga taga idanunsa kyar akan ƙofar shigowa, kallansa ta shiga yi cike da tsantsar kauna kafin ta ruga tare da zuwa ta rungume shi tana sakin kuka.

Haɓarsa ya shiga gogawa a kanta alamar tayi shiru dan har cikin ransa yake jin kukan nata, ganin ta kasa dena kukan ne yasa shi buɗe baki da kyar yana magana.

"Sorry sweetheart."

Cikin sauri ta dago ta kalleshi suka haɗa ido, duk da ganin yanayin da yake ciki hakan be hana Iman nuna masa ɓacin ranta ba, cikin jan majina irin na wanda yake kuka tace.

"Ni karka sake ce min sweetheart bana so, karka sake kirana da sunan da kake kiran wata sakarya."

Areef ya sauke numfashi har yanzu dai yana kwancen ma ba za'a dena yi masa mita ba.

"Na dena my dear, da na mutu nasan zaki huta da takaicin da nake sanyaki kullum." Harararsa tayi tana cewa.

"Kadena yi min maganar mutuwa bana so."

"Ina gaf da ita ne dear please ki yafe min, wallahi na kasa samun nutsuwa ganin zanyi sanadin jefaki cikin halaka."

Dagowa tayi daga kwantar da kai da tayi akansa, ta janyo kujera ta zauna hannunta a saman kanshi tana shafawa. Har zata sanar dashi gaskiya cewa ba dagaske take masa ba akan harkar da tace zata shi. Sai kuma taja baki tayi shi ta bar hakan a matsayin makami duk lokacin da taga zai tayar mata da hankali

37 / 38