Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   27 / 38

78K to 81K   out of 113.7K words

Mamah." Ficewa tayi ta koma falo ta zauna.

Dukkansu shiryawa sukai kowanne yayi kyau sosai, Iman tasa riga da skirt na atamfa dark blue da ratsin fari a jiki, ɗinkin ya yi mata ɗas a jikinta, ta zaro farin mayafi bata yafa ba sai riƙowa da tayi a hannu ta fito tana selfy. Dai-dai lokacin shima Areef ya fito sanye cikin blue jeans da white t-shirt, ya yi masifar yin kyau, kai daga ganinsa kasan cewar yaro ne mai ji da kwalisa, yarinta da kuma gayu. Tunda ya kalleta yaji ya kasa ɗauke idanunsa akanta, shi gaba ɗaya da besan abinda ya toshe masa kwakwalwaba har ya kasa fahimtar akwai soyayya a tsakanin su ba sai yanzu.

Iman kuwa wani abu ne ya tokare mata wuya taji tana bakin cikin wata ɗiya mace ta kaleshi, ya karsa fitowa falon yana yana kallon Mamah yace.

"Zamu tafi, me zan siyo miki?" Tace.

"Duk abinda kuka ciwo."

"A'a gaskiya Mamah banda kayan sanyi saboda haƙorin ki. Kayan zaki ma babuke a ciki sai dai masu gishiri-gishiri zamu siyo miki." Cewar Hanan tana murmushi.

"Oho muku dai, koma meye a siyo min." Ta basu amsa tana kallon inda Iman take. Wacce tun da Areef ya fito ta kasa ɗauke fuskarta daga gareshi.

"Kuzo mu tafi." Yai maganar yana yin hanyar fita.

"Ke kuma ya kika tsaya a nan?" Iman tai saurin turo baki, ji take tamkar tace a fasa zuwa, sai dai bata sa reason tunda har ta shirya, dama tun farko ne da tace karatu zatayi.

Hakan nan ta hakura tabi bayansu, Ikram da Hanan sune a baya sai Iman ta shiga gaba wanda hakan ne ya sanyaya mata rai ya mantar da ita haushin da takeji. Shi kam sai da yaje ya buɗe gate sannan yazo ya fitar da motar ya sake fitowa ya rufe gate ɗin sannan ya shiga mota yaja suka bar unguwar.....
(Areef an tafi chilling 🤪Allah yasa karya wuce hotel da amarya🚶🏻‍♀?)


*Littafin kuɗi ne, idan kina so ki tuntubi 0706 528 3730 or +447894142004*







*HAJJA CE 👈*
3/16/22, 20:38 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲*

*33*



Suna hawa babban titi Iman ta kalleshi kallo irin na soyayya da batama san tayi shi ba, ya juya shima ya ɗan kalleta ya maida ido kan titi yana murmushi. Gabaki ɗaya sun canzawa juna sun koma masoyan karfi da yaji, idan ka kallesu sai ka rantse cewa sun daɗe a cikin soyayya. Ya kamo hannunta yana tuki da guda ɗaya yace.

"Ya akai?" Ta narke fuska.

"Wayarka zaka bani." Matse mata hannu taji yayi ta saki ƴar kara.

Su Hanan na baya suna kallonsu, sosai yanayinsu yake burge Hanan, Ikram kuwa banda dariya babu abinda takeyi. Ya sakar mata hannun tare da ci gaba da tuki yana cewa.

"Zan baki amman ba yanzu ba sai mun koma gida."

"Kai Yaya Allah sai ka gama wahalar dani zaka nuna min?" Ta faɗa tana turo baki gaba.

"A'a ni cikin sauki nake son baki." Juyawa tayi alamar fushi tana kallon glass, ya ɗan kalleta tare da rage gudun da yake yi yace.

"Kinyi fushi? Toh mu juya gida mun fasa zuwa." Yayi kamar zai juya tai saurin cewa.

"Nifa ba fushi nayi ba." Dariya yayi tare da cewa.

"Okay tom ki saki ranki." Ta ɗan saki sukaci gaba da hira.

Wani kayataccen mall ya kaisu yace suje su siyo abinda suke so na iya karfin aljihunsa dan kar wata taje ta zake musamman Ikram da Iman. Ya samu guri kusa da inda ake payment ya zauna yana jiran fitowarsu, wayarsa ya ciro yana dannawa, jefi-jefi yakan dago kai yaga ko zai hango su sun taho. Sun jima a cikin mall ɗin har ya fara tunanin ko kayan ciki zasu kwaso dan ba hankali gare su sosai ba. Kamar ance ya ɗago can ya hango wani Alhaji ya tsaida Iman suna mana, kirjinsa ya bada wani irin ras, zuciyarsa ta hasala, wani irin abu ya taso masa daga can kasan kirjinsa, su Hanan kuma suna gurin ɗakko ice cream alamar sun gama zabo abinda suke so daga ciki shi kawai ya rage su ɗauka.

Areefullah ya miƙe jikinsa har wani tsoma yake ya nufi gurin. Yana zuwa bece komai ba ya kamo hannunta suka bar gurin Alhaji, sai da sukaje kusa da kujerar da ya taso ya tsaya tare da fisge mayafin da Iman ta yafa a kafaɗa ya warware shi tare da ɗora mata shi a saman ka ya lulluɓe mata yadda matan aure keyi. Ya zabga mata harara tare da jan ɗan ƙaramin tsaki be ce mata komai ba ya koma ya zauna sai kallon inda Alhajin yake yana hararasa shima. Su Ikram na ƙarasowa ba ɓata lokaci ya miƙa ATM card ɗinsa aka lissafa kayan suka dauki kuɗinsu tare da miƙa mishi katin da takardar.

Yana riƙe da hannunta har suka buɗe mota Ikram da Hanan suka shiga gurinsa da ledojin, itama Iman ɓangarenta ta buɗe ta zauna, Areef yaji ana ƙwanƙwasa glass ɗin gefenshi, mamaki ya kusa kasheshi ganin mutumin ya biyo su. Zogewa yai yana masa wani irin kallo ba tare yace komai ba.

"Assalamu alaikum ɗana barka da dare." Areef ya kasa amsawa saboda haushi, mutumin be damu ba yace.

"Naga kayi fushi kaja hannun ƙanwarka, ayi hakuri idan laifi nayi, naganta ne naji ina son mu haɗa zumunci, indai babu matsala a bani address zanzo har gida."

Areefullah yaja wani dogon tsaki yana murza mukulli, ke Ikram da Shegen surutu ta leka tagar kusa da ita tana cewa mutumin.

"Matarsa ce fa." Ko jiran abinda zai ce Areef beyi ba ya figi motar suka bar wajan.

Tunda suka tafi yaki yin magana duk kuwa da hirartasu tana magana ne akan yadda in suka fito sai wani a cikin su yayi kasuwar saurayi. Sai da ya tsaya ya siyo gasassun kaji saboda su Mamah da Abba ya siyo harda lemuka sannan suka nufi gida, sam fitar bata yi masa wani daɗi ba sai ɓacin rai. A falo suka baje aka zubo abinci shi kuwa ɗaki ya wuce ya canza kaya zuwa marasa nauyi, be fito ba sakamakon waya da yake da abokan aikinsa yana tabbatar musu da cewa zai dawo jibi.

"Kome yaya yake yi a ɗaki be fito yaci abinci ba?" Cewar Hanan ganin su har sun kusa kammalaci.

"Ikram jeki kirawo shi." Mamah ta bata umarni, Iman kuwa kallon hanyar ɗakin nashi tai tayi har Ikram ta shige.

"Yaya Mamah tace ka fito kaci abinci." Ba tare da ya kalleta ba ya girgiza kai alamar bayaci.

Ta fito ta sanar da Mamah abinda yace, bayan kuma da zasu fita cewa yayi yana jin yunwa amman yanzu yace ya koshi. Shigowar Abba yasa hankalin Mamah komawa gurinsa, hakan ya bawa Iman damar tashi taje ta shiryo masa abinci tazo ta dauki kazar shi da aka ware masa ta ɗora a saman tray ɗin. Koda ta shiga ɗakin babu kowa tana cikin ajiyewa taji ya buɗe banɗaki ya fito, suka kalli juna yai saurin ɗauke kai daga kallonta, ganin haka yasa itama tayi hanyar ficewa yai saurin riƙe mata hannu.

"Baki iya bada hakuri bako?" Mamaki ya kamata, amman da yake tana son ganin hotuna sai tace.

"Kayi hakuri duk da ban san nayi wani laifi ba."

"Haka kikace?" Ya tambaya yana kuma janyota kusa da shi.

"Ga abinci nan saboda naji da zamu fita kace kana bukata. Sakarni naje karatu zanyi."

"Wato daman haka ake yiwa miji ko? Haka kikaga Mamah na yiwa Abbah?"

Iman ta turo baki tana motsi da saman lips ɗinta da alama magana take son yi amman ta kasa, ya sakar mata hannu tare da komawa ya dauki wayarsa yana cewa.

"Idan bazaki lallaɓani naci ba ki ɗauke ki fitar dashi, kuma zan goge pictures ɗin da nayo, ba kuma zan sake roƙon komai ba tunda daman har yanzu kina yin sabbin samari."

Ya haye kan gado tare da juya baya yaci gaba da danna wayarsa harda saka videon da yaran suka dinga ihu suna cewa a gaida mutanan birni. Kamar ta fice dan har ta fara janyo masa ƙofa yaji wani dumm a zaton shi harma ta fice, sai kuma yaga ta janyo tray ɗin zuwa kusa dashi tana ɓata fuska tace.

"Tashi kaci." Kamar ya yi dariya saboda yadda tai maganar, sai kuma ya kalleta yana daga kwancen yace.

"Mezanci?" Abincin ta kalla shi kuma yaki ya kalleta bare ya nuna mata ya gane me take nufi.

"Yaya Areef karatufa zanyi."

"Kije ki dakko kayan karatun naki kizo nan, kina bani abincin kina yin karatun ai nawa da zaki yi shine mai lada ba wancan da kike tunani ba."

Habawa kamar ta fashe haka ta saka hannu ta yago kazar nan tare da miƙa hannu ta danna masa tsoka cikin bakinsa. Yayi saurin riƙe mata hannu yana zaro ido ya ciro naman daga cikin bakin yana cewa.

"Bafa cewa nayi ki min ɗora ba madam."

Ta faki idanunsa ta warce wayar hannunsa, sai dai kafin ta tashi ta gudu ya riƙota ta faɗo jikinsa. Sama ta dinga yi da wayar alamar ba zata bashi ba, ganin haka yasa shi zura hannunsa kasa yaji babu Pad a jikinta, ya miƙe da ita rungume a jikinsa har zuwa bakin ƙofa yasa ƙafa ya rufe tare da sa hannu ya murza key a jiki.

"Yau zanyi maganinki."

Cikin sauri ta shiga miƙa masa wayar a tunaninta itace matsalar da zata sashi yi mata wani abun Amman Areef yaki karɓa. Zare mukulli yayi sannan ya ja ta tana tirjewa har gurin abincin yace.

"Oya zauna muci tare idan ba haka ba kuma yau sai na nuna miki matsayi na a gurinki."

"Wallahi Yaya naci nawa, dan Allah ka barni na tafi ga wayarka nan." Ya maƙe kafaɗa ɗaya.

"Ki riƙe ki kalli abinda kike so." Ya janyo tray ɗin ya faraci yana murmushi kona meye oho. Ita dai Iman banda turo baki da ɓata fuska babu abinda take yi.

Har ya gamaci tana ta magiya yaki buɗe mata, yaje yayo brush ya dawo lokacin ta gama tattare gurin ta dauki tray ɗin, yana fitowa daga banɗakin tace.

"Toh buɗe naje nakai." Dariya yayi irin ta saman leɓen nan yace.

"Idanma zaki saki jiki ki saki su Mamah sun riga sun san kina wajan mijinki yarinya."

"Wayyo Allahna na shiga uku na, dan Allah yaya ka rufa min asiri ka barni naje nayi karatuna." Sai da yaje gab da ita sannan yace mata.

"Dan Allah nima ki barni mu kwana tare a nan ɗakin, haka nake so, haka kuma nake muradi, ki barni tun kafin wani bakin aljanin ya shiga tsakanin mu."

"Dama ban kawo abincin ba." Ta faɗa kamar zata rushe da kuka. Yace.

"Ai ba yiwa Allah dabara, idan ya kaddara abu ya kasance sai yace Kun fayakun, ba tare da mutum ya sani ba sai yaga abu ya kasance."

Jikinta yai mugun sanyi ta gano cewa yau mai rabata da gayen nan sai lillahi dan bataga alamar zai rabu da ita ba. Gani kawai tayi ya karɓi tray ɗin yaje ya diri a bakin ƙofar ya dawo tare da janyo mata hannuwa yana kallon fuskarta. Ɗan bakin da take tsotse lips ɗinta da yawu shi yabi da kallo kafin ya manna bayanta a jikin wardrobe. Murya a sanyaye taji yana mata magana cewa.

"I love the way you look at me. My one and only wife. Ina sanki, ki manta da duk wasu abubuwa da suka faru a baya, ki yarda dani ki soni kema da zuciya ɗaya please Imani, Insha Allahu na miki alkairin baki kulawa ta musamman, zan nuna miki soyayyar da ba kowace mace ke samu a gurin mijinta ba. Love me as I love you ❤️ ta yadda iyayen mu zasu kumajin daɗin ganin mu."

Jikinta duk ya mutu, wata irin azababbiyar sha'awa ta kamata, ita kanta tasan tana da ita, kuma bata tashi ganewa sai wani abun makamancin yadda suke a yanzu dashi ya shiga tsakanin su. Nan da nan taji ta fara jiƙewa, jikinta ya shiga rawa ta kasa yi masa magana. Ganin haka shi kuma ya janyota jikinsa ya manneta yana kissing ɗinta, Iman ta kuma ruɗewa ganin yana zuge mata zip ɗin skirt yasa ta yin sauri ta riƙe mishi hannu, ido a lumshe cikin wani irin yanayi tace.

"Please Yaya stop." Shima cikin tsuma saboda a wannan lokacin da yaga yanayinta ya kuma jefashi cikin tsananin buƙatarta gashi kuma tana neman kawo masa cikas.

"Mamah Yaya Areef, Abba ma yana nan dan Allah ka barni in koma ɗaki, su Ikram duk suna gidan nan please Mamah zata min faɗa wallahi."

Ya sake matseta a jikinsa tare da ɗora fuskarshi a saman kirjinta ya shiga gogawa kamar wanda yana ta rufewa fuska. Wani irin riƙo tayi mishi saboda yadda taji yana neman sumar da ita. Ya ɗan sassauta mata suka saki juna, ya juya zai tafi daga gurin yaji ta riƙo masa hannu, sai dai ta kawar da fuska, ji take kamar ta sakar mishi ganin yadda jikinsa yayi dumi, sai kuma ta sakeshi tare da tugawa da gudu ta nufi ƙofa. Murya na rawa tace masa.

"Zoka buɗe min Yaya."

Babu musu ya zaro mukullin yaje ya buɗe mata, da sauri ta fice yabi bayanta da kallo kamar yayi hauka.

Sai da yaga shigewarta cikin ɗakinsu sannan ya juya ya koma ciki, ƙafa yasa ya naushi katakon gado, zafin da yaji a ƙafar ne yasa shi dafe goshi tare da furta.

"Occh!"

Yaja kafar a hankali ya ƙarasa kan gado. Juyi ya shiga yi yana jan numfashi tare da saukewa a hankali har sai da yaji ya dawo normal sannan ya gyara kwanciyarsa. Da kyar ya samu damar yin bacci daman da gajiyar da ya kwaso daga Abuja zuwa kano, ya sake ɗaukar hanya sukaje kayan nan, shi yasa baccin yazo masa banda haka yadda yake cikin yanayin nan zai yi wahala ya yi bacci.
______________

Ganinta a firgice yasa Ikram tuntsirewa da dariya, Iman ta kalleta cike da mamaki tana cewa.

"Lafiya?"

"Ƙalau, kawai sha'aninku keda Yaya Areef yake bani dariya." Iman ta taɓe baki tana hayewa gado tace.

"Koba sha'ani ba?" Ikram ta sake tuntsirewa da dariya tana cewa.

"Eh shi nake nufi, ku yanzu bazaku iya hakura a sake kaiku gidanku ba, kema fa naga alama yanzu kina son ɗan gayen can."

Iman ta kalleta suka haɗa ido, kamar wasu taɓaɓɓu suka saki dariya a tare Hanan tana kallonsu sai girgiza kai take cikin ranta tana Allah ya shirya. Koda ta kwantama kasa yin karatun tayi, da ta rintsa ido zata hango yadda Areefullah yake kissing ɗinta tamkar yadda Sharukan yake yiwa khajol a cikin wata waƙa ta film ɗin khabi kushi khabi gham😜. Littafin hannunta ta kifa a saman fuskarta tana murmushi, tunani take me yasa bata tsaya ba? Anya tayi daidai kuwa? Ta sake yin juyi har tana buge Hanan dake kwance a kusa da ita.

"Kewai meke damunki ne duk kin kasa kwanciya guri guda?" Caraf Ikram ta karɓe zancen.

"Shauƙi ne yake ɗibarta, hmmm Allah kadai yasan me suka yi a ɗakin."

"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, me muka yi kuwa? Ba ruwa na wallahi Allah yasa yaji ku." Iman ta faɗa tana sake rufe fuska da book ɗin hannunta.

A ranar dai Iman bata iya karanta komai ba sai da asuba ta dakko ta dudduba kafin ta tashi ta shirya. Dama set huɗu gareta na uniform saboda idan bata samu damar wanke wani ba ta zamana tana da na sawa wankake gogagge idan ta tashi kawai dauka zatai tasaka. Suwaga bag ɗinta ta rataya a kafaɗa ta sanya farin glasses ɗin idanunta tare da daura agogo ta fito zuwa falo.

Areef da yazo fitowa ya hangota cikin shirin makaranta, saurin komawa yayi ciki ya saka kayansa tare da ɗakko car key ɗinsa da wayarsa ya fito. Ganin tana shan tea a tsaitsaye yasa shi kallonta, tayi saurin kawar da ita taji yana cewa.

"Muje na rage miki hanya." Tayi murmushin jin daɗi tare da ajiye cup ɗin dama ta gama sha.

Sai da ya koma ɗaki ya dakko layar da aka ce asa mata akanta, ya fito tayiwa Mamah sallama suka tafi, a hanya ya bata layar yace ta sanya akanta, ta cire ɗan ƙaramin hijab ɗin dake jikinta, lallausan bakin gashinta ya bayyana wanda yasha kananun kitson shuku. A tsakiyar kanta tasa sannan ta maida hijab ɗin. Har ƙofar gate ɗin makarantar ya kaita, cike da murna tayi masa godiya sannan ta fito, shima fitowa yayi ya rakata har kusa da ƙofar shiga school ɗin.

"Khadija Ahmad kin ƙaraso?"

Cewar wata yar ajinsu, ta gaishe da Areef sannan suka kama hannu suka wuce. Yana ji ƙawar Iman ɗin na tambayarta waye shi, besan wannan karon abinda zata gayawa wannan ba, tunda kwanaki cewa tayi driver ne. Juyawa yayi ya koma gida yai breakfast daga nan yayi wanka sai ga su Aslam da Irfan sai kuma Sudais, nan suka hadu sukai ta hirar yaushe gamo irin tasu ta abokai.........
(Soyayya ruwan zuma😍Arim ana buga wasa🤸‍♀?, kowa zai ci kwallon?)


*Littafin kuɗi ne, idan kina son shi ki tuntubi wannan lambar 0706 528 3730 or +447894142004 top 10*










*HAJJA CE 👈*
3/19/22, 08:16 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*

*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲*


*34*



A ranar da Areef zai koma Abuja ranar ne su Iman zasu kammala jarabawa, shi ya kaita makarantar da kansa yace idan an tashi ta kirashi zai zo ya ɗauketa, murna fal cikin zuciyar ta. Bayan ya kaita ya dawo ya shirya kayansa ya kai booth, cin-cin da dambun naman da Mamah tayi masa duk yaje ya kai mota ya ajiye ya zauna suna ta hira da Mamah, daman ya gaya mata ba da wuri zai tafi ba. Iman ana fitowa daga exam tayi masa waya, ya tashi yaje ya ɗakko ta. Ya ɗan kalleta lokacin da ya ɗauke kan motar daga barin titin da zai kaisu gida yana cewa.

"Rakani zaki." Cike da mamaki tace.

"Ina?" Ya kamo hannunta da hannu daya ɗayan kuma yana tuki dashi yace.

"Gidan wata mata." Gaban Iman ya faɗi, wacece wannan? Kodai budurwarsa ce? Da sauri kuma ta girgiza kai tana so ta karyata abinda zuciyarta ke shirin kitsa mata.

Daidai wani ɗan madaidaicin gida suka yi parking ya kalleta yana murmushi yace.

"Kisaki jikinki fa, kar a ɗauka bama mutunci dake." Iman ta ɗan yi murmushi sannan ta buɗe ƙofar ta fito shima ya fito tare da kulle motar da key.

Yana riƙe da hannunta suka shiga, ganin sun kusa zuwa tsakar gidan yasa ta fara kokarin kwace hannunta amman yaki saki. Sallama

27 / 38