ba haka bane. Kuma wannan kadai yasa ku gane cewa ba'a yiwa Allah dabara. Yarki Meenal Jamil ne ya bada ita ga sarkin aljanu dan ayi masa asirin da zai sa ya auri wata yarinya. Da hakan beyiyu ba, kuma asirinsa zai iya tunawa aka ce za'a rufe bakin mutane dan kar wani yasan irin aikin da yake aikatawa, sai aka ce ya bada rayuwarki kota mahaifiyarsa, shine ya bada ta Umma, bayan yayi ayyukan da in kukaji sai kun tabbatar wannan ba abin tausayi bane."
Tunda tayi maganar cewa Jamil ne silar mutuwar Umma da Meenal, kowa na cikin ɗakin ya kasa motsi. Salima kuwa kai ta riƙe wanda taji yana barazanar cirewa daga inda yake.
"Karya ne, karya kike yi, idan har da gaske kike meyasa zaki tarwatsa mana rayuwa, me yasa tuntuni baki gaya mana ba sai yanzu da kika ga ya shiga cikin wannan halin? Police...!" Ta shiga kiran ƴan sanda tana kuka tamkar wata zararriya. Kafin ƙifta ido sun nemi tsohuwar nan sun rasa, babu kuma wanda yaga ficewarta hatta ɗansanda dake bakin ƙofa.
"Karya ne, wannan daga ji sharri ne ake son yi masa wallahi, tayaya Jamil zai iya aikata duk wadannan aikin? Sharri ne kawai na rantse da Allah..."
"Ya isheki Salima, wannan rantsa-rantsen ba sune abin yi ba. Ki gaya mana gaskiya da gaske mahaifa kika cire?" kawu Bala ya tambayeta cikin fushi. Salima ta fashe da kuka, ganin duk ita ake saurara yasa tace.
"Kawu baya son haihuwa da yawa, wannan dalilin ne yasa ina haihuwar Meenal yaje ya cire min mahaifa bayan yace min ni kadai ce, ba zai min kishiya ba. Wallahi kawu nayi nadamar haka tun lokacin da naga na rasa Meenal."
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, wanda yai miki wannan abin taya zaki zauna karyata waɗancen laifukan da aka ce yayi? Gashi nan kinaji tace wata yarinya yake so zai aura, ta iya yiyuwa bata son shi shine yaje yana aikata wannan ɗanyan ai..." Ko ƙarasawa beyi ba Salima ta sake fashewa da kuka tana cewa.
"Wayyo Allah na shiga uku..."
"Kin shiga uku ko mun shiga uku." Ma'u kanwarsa ta faɗa tana sakin kuka.
"Yanzu Yaya dama duk wannan tashin hankalin kaine silar sanya mu ciki? Kaine silar mutuwar Umma yaya? Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, wai ashe kaine silar mutuwar Meenal? Da Allah ya barka da lafiya kila harmu bazaka ƙyale ba sai kaga bayan mu saboda kawai mace, tunda nake ban taɓajin namiji da asiri ba sai akan ka Yaya Jamilu. Wannan hatsarin da kai alhaki ne ya fara bibiyarka. Wallahi gaura mutuwarka da wannan raɗaɗin azabar da kake kwasa, kaima gashi nan zakaje inda kayi sanadin zuwan su Umma. Kaico.. Kaico da wannan masifar da ka janyo mana."
"Ya isa haka Ma'u, ku tashi muje daga waje." Kawu Bala ya faɗa yana korasu.
Tabbas kamar yadda Ma'u ta faɗa ne gwara mutuwar farar ɗaya ga Jamil, akan yadda yake yanzu yana jin jiki. Haka duk suka fita suna kukan bakin ciki, wasu daga cikin su ma tafiyarsu suka yi a cewar su bashi da wani amfani, babu kuma abinda zasu yi masa. Salima kuwa sai da aka bata gado a asibitin, gwajin farko da akai mata ya tabbatar da tana dauke da ciwon zuciya. Tayi kuka tayi bakin ciki tayi nadamar kasancewarta karkashin ikon Jamil, lallai mutum mugu ne, ba zaka taɓa yadda cewa Jamil zai iya cutar da ɗan adama irin haka ba, sai gashi ba kama.
Haka yake a gurin mu mata muyi ta wahalar da kanmu gurin ɗa namiji, mu dinga kishi tamkar ba zamu mutu ba. Mu fifita kalamansu akan faɗar ubangiji, karshe ko Allah be nuna miki karshen abin ba kinsan tabbas akwai mutuwa saboda duk wanda yazo duniya wata rana zai tafi ko ya shirya tafiya ko bai shirya ba, zai koma ga Allah, mutuwa batada dangi amma tafi kowa zumunci, idan yau tazo min gobe kai zata jewa. ya Allah kasa duk randa zata zo mana kasa mucika da kyau da Imani amin.
Gabaki ɗaya suka tattara suka bar shi a asibitin ba uwa ba uba babu wani da zai yi jinyarsa. Suma ƴan asibitin suka bazama neman inda zasu kaishi saboda duk iya kokarin su na son ganin ya samu sauki abin ya cutura. Da yake na gwamnati ne asibitin sai suka kaishi wani keɓantaccen waje suka direshi a gurin, babu kulawa babu magani bare asan halin da yake ciki. Yau babu tsimakon boka, babu kuɗi da izzar da yake da ita, a halin da yake ciki shi da kansa yafi son mutuwa. Wannan azabar fa iya ta duniya ce, ciwon kai kadai bawa zai yi ya shiga cikin damuwa da ɗimauta, ina ga ka rasa duk wani mahadi dake jikinka? Kuma still kana shaƙar numfashi?
Kawu Bala ne ya kasa jurewa dole ya dawo asibitin sai dai be tarar dashi a ɗakin da yasan an kwantar dashi ba. Sai da ya tambaya sannan aka kaishi inda yake. Ƙiris ya rage kawu Bala ya fashe da kuka saboda yadda yaga Jamil ya sake komawa. Ya tuna waye Jamil, cikakken namiji ɗan kwalisa mai ji da kuɗi da gayu, yau gashi cikin kashi da fitsari, babu kafafuwa ba hannu ɗaya, ba idon ganin duniya da abinda yake cikinta. Bakin ma da aka bar mishi baya iya magana sai dai kaga yana zubar da yawu.
"Jamilu yanzu babu abinda ya rage maka a duniya, sai dai ka zauna kai ta innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Kayi ta faɗa Jamil."
Ina kawu Bala ya gaza gane cewa kalmar ta yiwa zuciyar shi nisa, Allah ya hana ikon bashi damar furtawa sai dai kuka kawai. Ƙiri-ƙiri zuciyar shi ta kasa ɗaukar kalmar ballanta ya samu bakinsa ya furta. Har kawu ya tafi dan shi kansa duk imaninshi kasa taimakawa yayi wajan gyara Jamil, saboda ba karamin dagadaga jikinsa yayi ba, ya ƙone sosai ta yadda naman jikinsa yake salewa da kanshi. Cikin dare yace ga garinku nan, dama almajirai sun ɗan fara jin cikakken labarin marar lafiyar, suna zuwa gurin da asuba suka saka mishi wuta.
A lokacin da su Salima sukaji labarin tayi kuka ta yi shi sosai saboda a yanzu ya bar bayanta cikin tashin hankali. Khaleel ne kadai take gani taji daɗi, shima kuma kullum cikin fargaba take, sai taga kamar za'a kawo mata sakon mutuwarsa idan ya bar gabata. Jamil ya cuce ta har ta rasa wane kalar Allah ya isa zata yi masa. Allah ka yafe mana amin.......
(😭Duniya kibar jan mu cikin halin ruɗani, Allah kasa mu mutu muna masu tsoranka. Allah kasa kalmar shahada ta zama karshen furucin mu amin.)
*ZO GARENI na kuɗi ne, please idan kina so ki kira 0706 528 3730*
*HAJJA CE 👈*
3/24/22, 18:00 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲)*
*39*
****** Cikin kankanin lokaci Areefullah da Iman sunyi wata irin muguwar shaƙuwa, soyayya da nuna ƙauna wajan kowanne babu sauki. Sen. Muhammad kuwa ya sakar musu bakin aljihu ta yadda ko sati cikakke basa iya yi a ƙasar Nigeria, kullum da inda zasu tafi har aka yi cuku-cukun tafiyarsu karatu zuwa UK. Ko bikin Hanan basu samu damar zuwa ba. Itama anyi bikinta danƙareren gidan da Sen. Muhammad ya ruguje nasu yayi musu shi ya koma na zamani da abubuwan more rayuwa da rage daga Mamah sai Ikram.
Kwance yake akan doguwar kujera yana bacci, tunda ya dawo daga lecture ya kwanta a gurin bacci ya ɗauke shi. Tana shigowa har zata wuce sai kuma ta hangoshi a kwance, murmushi tayi tare da yowa baya ta ƙarasa inda yake, a tunaninta ma yana jinta yayi baccin karya. Swagger bag ɗin dake rataye a ƙafaɗarta ta ajiye a gefe tare da kwanciya a saman cikinsa. Shi kuma jin nauyi yasa shi buɗe ido da kyar ya kalleta tare da sanya hannu ya rungumeta. Cikin sanyin murya yake cewa.
"Welcome back my dear." Iman ta ɗan ɗago kai tana kallansa, still idanunsa a lumshe suke, ta sa hannu tana wasa da zagayeyyen gashin bakinsa da yake ƙara masa kyau tace.
"Hutawa kake yi ne?"
"Uhmmm tun ɗazu kai na ke ciwo." Ta zaro ido.
"Ciwon kai? Kasha magani? Ko asibiti zamuje?" Gaba ɗaya ta rikice masa, shi yasa indai yana jin ciwo a jikinsa baya gaya mata saboda sai ta fishi shiga damuwa da lamarin.
"Na warke fa." Ya faɗa yana kokarin tayar dasu zaune.
"Nidai gaskiya muje asibiti." Ta dage sai sunje, babu yadda beyi da ita ba akan cewa yanzu ya dena ji amman taki yadda har sai da suka tafi.
Baiwar Allah ko hutawa batayi ba, sukaje asibitin da take attachment, da yake sun sanda a gurin yasa babu ɓata lokaci suka duba shi. Taje pharmacy ta karbo magungunan sannan suka koma gida. Sai da ta fara dafa musu indomie wacce tasha kifin gwangwani da kayan lambu, ta kawo ta ajiye, lemo da ruwa duk ta ɗakko ta ajiye yana daga kwance.
"Sugerpie taso kaci abinci, sai kasha maganin." Areef ya dafe kai saboda yadda yake masa ciwo.
Ko yunwa bayaji, amman dan karta kuma shiga cikin damuwa yasa shi daurewa ya zauna. Iman ta shiga bashi a baki tamkar wani jariri, sai da taga yaci sosai kafin ta kyaleshi, yasha maganin ya sake kwanciya sai bacci. Itama taci nata sannan ta miƙe ta shiga bedroom ɗin ta. Wanka tayi ta fito tare da shiryawa cikin have vest pink da ɗan gajeran wandonta, tayi parking sumar kanta a gefe, tayi kyau ainun sannan ta fito da kayan karatun ta zuwa falo. Kusa dashi ta zaune jefi jefi tana juyawa ta kalle, kaunarsa na kuma shigarta, musamman yanzu ya ƙara girma ya yi fresh dashi, hutu da jin dadi sun samu guri a jikinsa.
Tana ta aikinta har ya farka yaga magariba ta kusa. Bata san ya buɗe ido ba sai kawai ji tayi an saƙalo hannu ta bayanta an ɗora saman kirjinta. Murmushi tayi sannan ta juya suka haɗa idanuwa, tasa yatsanta a saman gashin girarsa tana shafawa.
"Sugarpie ya jikin?" Sai da ya ɗan janyota zuwa wajan cikinsa, bayanta yana shafarsa kafin yace.
"Da sauki." Yana kuma janyota.
"Mezan samu.?" Tayi murmushi tare da kai lips ɗinta saman nashi ta bashi zazzafar sumbata.
"Shikenan?" Ya tambaya yana sake lumshe ido.
"Toh kana bukatar wani abun ne?" Iman ta faɗa tana kwantar da kai saman jikinshi.
"Uhmmm, idan har za'a bani."
"Okay nasan ko menene bari naje na ɗakko maka." Yayi saurin dawo da ita jikinsa yana cewa.
"Yo me zaki ɗakko bawan yana gurinki a yanzu haka." Tayi dariya tana ture masa hannu daga inda ya ɗora.
"Kaida bakajin daɗi, please kayi kwanciyarka." Ta shiga kokarin tashi amman ya hana hakan faruwa.
"Idan har kina son kiga na dawo normal sai fa kin bani. Naga kwana biyun nan wallahi bakya son al'amuran nan, ko bakya jin daɗi?"
Iman tayi murmushi tare da ja masa hanci a hankali, cikin ranta tana tunanin ya za'ai ta nuna masa rashin marmarin abin da batayi a kwanakin nan? Dan ita a yanzu bataki su yi sati ko watanni ba tare da sun kusanci juna ba. Ta rasa dalilin da yasa takijin haka, kuma cikin ƴan kwanakin nan abin ya fara mata. Sai dai duk da haka yanzu ma bata nuna so ne bata yi ba, ta kwantar da kai wajan kafadarsa tana cewa.
"Ni babu abinda yake damuna, Kaine kawai baka nema ba."
"Gashi na nema yanzu dear, hope dai za'a biye min?"
Iman tayi dariya cike da jin kunyarsa ta shiga yi masa duk wani abu da tasan yana so, daga nan kuwa komai ya canza suka shiga bawa juna kulawa. Rayuwar su abin sha'awa da burgewa, da yawa suna bawa mutane sha'awa ba kadan ba. Cikin haka ne ta fara ƴan ƙwaɗayi musamman na manja da yaji, kome zataci tafi son asa mata manja, ga yawan yin bacci, suna hira zata bingire, ko idan suka fita shan iska zata azalzalesa su koma gida, har dai suka gano cikin dake jikinta. Wowwww! Sen Muhammad kamar zai yi hauka saboda tsananin murna da farin cikin zai samu jika, zai kuma samun wani ɗan na jininsa ba aro ba. Na ya sake shagwaɓa Iman, gasu Mamah ma sun dage wajan kara mai da ita tamkar yarinyar gobe.
________________
Ƴan kwanakin nan gabaki ɗaya Areefullah yana matuƙar bawa wayarsa muhimmanci. A da idan suna tare da Iman in har ya dauki waya yana chatting to baya daɗewa a kai zai sauka. Yanzu kam baya minti biyar be janyo wayarsa ya shiga WhatsApp ba, idan da daddare ne sai yakai har kusan karfe ɗaya yana online. Iman takan farka shan ruwa ko fitsari ko kuma taci wani abun saboda yanayin da take ciki.
Idan ta ganshi beyi bacci ba takan tambaya sugarpie lafiya? Ya kalleta tare da janyota jikinsa, rintsa ido yake yana girgiza kai zai tabbatar mata da cewa. Project ke bashi ciwon kai, yana son yaga ya kammala shi yazo ya huta da wannan research ɗin da yake faman yi kullu'yaumi. Cike da tausayinsa zatai ta kwantar masa da hankali tace yayi addu'a Insha Allahu komai zai zo da sauki. Kullum haka ne yake faruwa, Iman ta yarda dashi ɗari bisa ɗari ta yadda komai zai gaya mata yarda takeyi.
Yana kwance yana ta faman bacci sakamakon rashin kwanciyar da beyi ba da wuri. Iman tayo wanka ta shirya cikin wata ƴar yaloluwar riga ta shan iska, cikin jikinta ɗan watanni bakwai tamkar ɗan wata uku saboda rashin girma, sai dai tana jin nauyinsa sosai. Zuwa tayi ta kwanta a kusa dashi tana faman shafar cikinta murmushi kwance a fuskarta, ita kanta ta kagara ta haihu taga tana shayar da babyn, abin yana matuƙar burgeta. Wayar Areefullah dake gefe a ajiye ta janyo tare da buɗewa kasancewar tasan password ɗin, kai tsaye ta shiga WhatsApp contect ɗin farko da ta gani shiya firgitata inda taga sunan Sweetheart, da sauri ta juya ta kalleshi bacci yake hankali kwance, tayi saurin shiga dan ganin ko wacece.
Scrolling tayin har sai da taje farkon hirar inda taga anyi masa sallama, ga yanayin yadda chatting ɗin nasu ya kasance duk da cewar bawai a nutse take dubawa ba.
"Assalamu alaikum."
"Wslm."
"Ya gida da yara?"
"Lfy alhmdll."
Aka yi shiru ba'a sake turo komai ba, sannan ita da take dubawar bata tsaya taji me aka faɗa fa taci gaba da dubawa inda taga ana cewa.
"Kasan dai ina sanka, kawai babu yadda zanyi ne tunda kaga yadda abubuwa suka faru." Yace.
"Nasani kuma nima kinsan ina sanki, daman nasan karfin hali akai wajan rabamu da tuni yanzu muna tare." Tace dashi.
"Haka ne, kuma ni wallahi tunda na aureshi bana jin daɗin mu'amalar aure dashi sai na tunoka sannan." Yace.
"Toh ke me yasa tun a lokacin baki yi duk yadda zaki yi ba wajan ganin mun auri juna ba?" Tace.
"Kasan dai yadda abubuwa sukai ta faruwa, kasan ba yadda zanyi tunda anfi karfina. Kasan kuma ina mutuwar sonka" Ya tura mata murmushi tare da cewa.
"Nima ina sonki ke kanki kin sani."
Gabaki ɗaya tashin hankali ya hana Iman tsayawa ta duba chats ɗin duka. Cikin rawar jiki ta fita daga WhatsApp ɗin ta duba wajan calls, 'Sweetheart' ta kuma gani alamar itace karshen wayarsa a daran jiya. Ta kuka fita ta koma SMS inda taga sakwannin su harma yana cewa dan Allah ta sake turo masa hotan be gani ba ta goge, ita kuma tana cewa a'a gaskiya gwara yazo su hadu face to face tunda itama tana US ɗin.
Tashi tayi da sauri taje ta ɗakko wayar ta, number ɗin ta ɗauka sannan ta ajiye masa wayar a inda ta ganta. Kallonshi ta shiga yi yana ta bacci hankali kwance, da sauri ta fice daga cikin ɗakinsa ta nufi nata wanda tunda suka zo cikin gidan bata taɓa kwana a ciki ba, kullum suna tare dashi a ɗakinsa. Ta kwanta akan gado tare da rintsa idanuwa, ko rantsuwa tayi ba zatai kaffara ba wannan Feenah ce, Feenah ce ta dawo cikin rayuwar Areefullah, wacce da alama rabuwa sukai da mijin nata.
Gaba ɗaya Iman ta rasa sukuni, banda mamaki babu abinda take yi, wai Areefullah ne yake cewa wata yana mutuwar sonta? Kenan duk kalaman da yake zuba mata karya yake yi? Kenan da yace mata babu wata mace a ransa sai ita wannan duk karya ce? Yanzu da ita da Feenah wacece Annurin zuciyar shi? Haƙika ta girgiza ta kuma gane cewa namiji munafuki ne. Wayarta ta ɗauka ta yi mata sallama ta WhatsApp. Bata online hakan yasa ba'a bata reply ba. Sauka tayi daga online ɗin ta fito zuwa falo, aikin da be kamata tayi ba a cikin yanayin ta shi ta dinga yi. Can ta kuma kunna data cikin sa'a taga an amsa mata kuma tana online itama.
"Ya gida?" Cewar Iman.
"Lfy lau, ban gane mai magana ba."
"Sunana Khadija, ina son mu zama friends, Allah yasa dai zan samu karɓuwa." Iman ta tura mata tana ɗan cije leɓe.
"Ayya Toh ba komai, but Khadija daga ina."
"A Kano nake, yanzu dai ina UK ina karatu." Cewar Iman.
"Wow masha Allahu, nima ƴar Kano ce, nazo UK yaro na bashi da lafiya."
Iman ta riƙe haɓa, kenan har ta haihu? Ikon Allah amman da wulakanci tazo tana cewa wani kato wai tana tuno shi idan suna sunnah da uban ɗan, lallai mata akwai abin takaici.
"Ayya, Allah ya bashi lafiya." Iman ta faɗa tana lasar leɓenta na ƙasa.
"Amman dan Allah a ina kika samu number na?" Iman ta cije baki tare da cewa.
"A gurin wani."
"Waye shi please."
Kamar zata ɓoye mata wajan wanda ta karɓi wayar, sai kuma taga meye na ɓoyewa, ai gwara kawai ayi ta yanzu tasan cewar tasan komai game da su. Dan haka kawai tayi kundin bala wajan cewa.
"A wajan mijina." Cike da turo kan ɗan emoji mai zaro ido tace.
"Mijinki kuma? Waye mijinki?" Kai tsaye babu wani kwana-kwana tace da ita.
"Mijina Al-Mustapha Ahmad." Nan da nan taji tace mata.
"Au Iman ce? Subahanallahi, kiyi hakuri nasan kila chatting ɗin mu kika gani. Dan Allah karki dauki wani abun ne, kawai hira ce please." Murmushi Iman tayi ganin ana neman raina mata hankali bayan kuma da wayonta, dan haka tace mata.
"Nooo.. No.. No karki damu, ai shi ɗin mijin mace huɗu ne, kuma ai nasan irin yadda soyayyarku take, ni dai kawai na miki magana ne dan mu sake shaƙuwa kafin ki shigo daga ciki." Tana tura mata Feenah tai saurin cewa.
"A'a wallahi