Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   5 / 38

12K to 15K   out of 113.7K words

yasa idan aka yiwa yarinya aure da wanda ba ita ta nuna ra'ayi akan shi ba, sai taga kamar iyayenta basu iya komai ba. Ko kuma basu san ta. Kuci gaba da yi mata addu'a don itace a tsakanin ku. Ragowar yaranka kuma da kake damuwa akan rashin auren su, wannan duk da sanin ubangiji yasan dasu, fatan mu kawai Allah yasa jinkiran ya zamar musu alkairi.?

“Amin ya Allah malam. Amman dan Allah a taimaka a kafe min ita a gidan mijin, ta dena tunanin kashe auran ta.?

“Babu damuwa Alhaji Nura, za a yi da izinin Allah. Allah kuma ya bata hakuri tasan cewa zaman ibada take yi.? Yace,

“Amin malam, yaran ne ka rasa me suke lissafawa a kwakwalwarsu.?

Sallama suka yi da juna bayan Alhaji Nura ya yi masa ihisani ya koma gida, koda yaje babu wanda ya kula bare ya amsa sannun da suke yi masa.

____Feenah kuwa haka tasha kukanta ta gama, daman tuni Sultan ya buɗe mata ƙofa bayan ya tanadar mata abinci ya rubutu mata wata yar takarda. Sai bayan da taji yunwa na nema halaka ta ne ta fito ta tarar babu kowa a parloun, taja tsaki tare da wucewa kitchen ta tarar ya yi mata order, amman ko kallanta ba ta sake yi ba bayan gani na farko. Madarar gari ta zuba a cup tasa ruwa da sugar ta dama sannan ta bud'e fridge ta dakko cornflakes tare da komawa parloun ta zauna, a nan ne taga takarda kamar zata share taki dubawa, Sai kuma wata zuciyar tace da ita 'ki dauka kila ta rabuwarku ce' ta dauka da sauri tare da warwarewa tana dubawa.

_“Naga alamar zaki Iya kashe ni saboda kina tunanin wannan ɗan tatsitsin yaron da har yanzu ba a gama goya shi ba. Toh na bar gidan ba zaki sake gani na ba sai randa kika gane cewa ni d'in mijin ki ne da Allah ya zaɓa miki.”_

Uban tsaki ta saki tare da yin cilli da takardar taci gaba da abinda da take yi. Tana gama sha bacci ya dauke ta a gurin bata farka ba sai cikin dare shima fitsari ne ya ishe ta. Bayan ta kammala ta dawo taci gaba da baccinta har washe gari. Shiryawa ta yi tsab na tafiya makaranta cikin wando da riga, tayi haka ne kuma dan ta bawa Sultan haushi saboda bata tab'a yin sha'awar tafiya a irin wannan shigar ba. Uniform din kuma tasa su cikin school bag da nufin idan ta gama bashi haushi ta shiga school ta biya toilet tasaka. Har ta gama breakfast bataji ya fito ba, ta duba agogo taga lokacin tafiyarta ya yi idan be fito ba zata makara.

Ta nufi bedroom d'in sa taga baya nan sai tayi tunanin yana waje ta fito. Tana murd'a kofar taji ta gam a rufe, da sauri ta duba inda suke ajiye mukullaye taga babu ko ɗaya sai a sannan ne hankalinta ya yi mugun tashi. Can ta tuna da takardar jiya inda yake cewa ya bar mata gidan ashe tafiya ya yi Ya barta ita kadai ba ta sani ba. Kuka ta saki tare da durkusawa a gurin ta dora hannu a ka. Ganin babu me lallashinta yasa ta mikewa ta koma ciki, wayar ta da ta yar jiya ta dakko ta shiga kiran sa karo na farko tun had'uwar su, koda wasa bata tab'a gigin kiranshi da kanta ba sai dai shi ya kiranta in taga dama ta dauka idan bata ga dama ba taki dagawa.

Sultan yana zaune a gurin shak'atawa ya gama breakfast d'in sa yaji wayarsa na ringing, kamar ba zai daga ba saboda zuciyarsa ba a nutse take ba, sai kuma ya zaro wayar daga gefen aljihun jeans dinsa yana dubawa. 'Feenah dear' shine a jikin screen d'in wayar. Murza ido ya yi dan ya tabbarar ba gizo idanunsa suke yi masa ba. Tabbas kuwa itace ba karya, amman me yasa take kiransa da kanta? Gaba daya mantawa ya yi da cewar ya rufe ta a gida saboda mamakin wannan kira da ya gani. Da kyar ya samu bakinsa ya bud'e.

“Hello...? Abinda ya iya cewa kenan yana jiran jin ta bakin ta.

“Saboda ka maida ni dabba shine ka kulle ni??

“Opphs!.? Ya fad'a bayan ta tuna masa.

“Amman Feenah ta ya ya zan barki sakaka bayan nasan ba jin maganata kike yi ba? Karshe ma fa kashe ni kike son kiyi, kuma kin san k'asar da muke ciki. Kina kashe ni suma kashe ki zasu yi abinda ni kuma ba zan lamunta ba kenan.?

“Allah ya saka min, kuma ba zaka samu soyayya daga guri na ba har abada, kaje kayi ta kulleni kuma kasan ai ina zuwa makaranta shine zaka kulleni. A can baka barni nayi karatun ba, anan ma ka fara hanani zuwa kai da Allah.?

Rasa abinda zai ce mata ya yi, shirun da taji ya yi yasa ta ajiye wayar tare da zaman dirshan tana kuka kamar wacce zata kashe kanta. Wannan wace irin masifa ce baka son mutum ace dole sai ka zauna da shi? Ita kam ta shiga uku. Haka ta karaci kukanta ta gama, tashi tayi ta koma bedroom ta kwanta tunani kala-kala ya shiga yi mata yawo a kwakwalwarta, wanda ya kamata da wanda sam be dace ace a irin shekarunta suna yin irin shi ba.

Tsawon wanaki uku babu Sultan bare me kama dashi, sai da ta cika kwanaki hudu sannan ya dawo da daddare hannunsa rike da ledoji.

Kwance ya tarar da ita akan kujera tana kallo, saman cikin ta kuma ta d'ora boul d'in da ta zubo cornflakes tana dauka d'ay-d'ay tana cinsa a busasshen shi babu madara. Ko kallansa ba ta yi ba bare ta amsa masa Sallamar da ya yi. Mamakinta yake yi kullum saboda a ganinsa shekarunta basu ci ace tasan wannan salon iskancin ba, sai gashi yana ganin su Kala-kala kamar wata babbar mace.

“Feenah nayi sallama baki amsa ba.? Ya yi maganar yana zama akan kujerar da take kallon ta.

Amman ko kwakkwaran motsi taki yi saboda taurin rai da rashin ganin girmansa da take yi.

“Shikenan, ga shi na siyo miki ban sani ba ko zaki bukata.? Ya fad'a yana ajiye mata ledojin a kusa da ita.

Abin ka da me ciki, uwa uba mai d'an karan kwad'ayi. Kamshin kaza kawai taji miyaunta ya tsinke, nan da nan cornflakes d'in da take ci ya fita a ranta. Ta had'iyi yawu kwat tare da d'aukar remote kamar gaske ta shiga sauya tasha daga wadda take kallo zuwa wata. Shi kuma ya mike ya nufi bedroom d'in sa dan kwanciya saboda yayi matukar gajiya, ga wani bacci da yake ji. Kallon kofar ta yi taga ya rufe, ta d'an leka cikin ledar ta hango kunshin naman kaza da pizza da sauran abubuwan kwalam da makulashe. Tana son ci saboda zuciyarta ta biya, amman tana shakkar ci gudun ko ya zuba mata maganin da ya saba sawa idan yana son cinma muradinsa akan ta.

Nan da nan taji kamar zata mutu idan bataci ba, ta zaro kafa ta sauke kasa tare da bud'e ledar ta shiga ci kamar wacce ta dad'e basu hadu ba. A ranta ji take koma me ya zuba mata sai taci shi dan ya riga ya tayar mata da wata masifaffiyar son cin abubuwan da ya kawo mata. Sai da taci tayi nas da ita harda gyatsa sannan ta ture ledojin ta koma gefe tana tand'ar harshe da lebenta.

Agogo ta kalla, ganin lokacin kwanciya ya yi ta mike ta nufi d'akin ta ba tare da ta kwashe kayan ba, saboda ganda ji tayi ko tsinke ba zata iya d'aukewa ba. Tana shiga ta kulle kofarta daga ciki gudun kar Sultan ya shigo ya yi mata wani abun. Kwanciya tayi bacci ya yi awan gaba da ita. Koda Sultan ya kammala duk abinda zai yi, fitowa ya yi parloun amman be ganta ba sai dai gashi nan yaga taci abin da ya kawo mata. Yaji dadi kuwa ya nufi bedroom d'in na ta yaji sa a kulle, hakan yasa shi juyawa ya dawo gurin da ta tashi yaci gaba da kallo na d'an wani lokaci, zuciyarsa cike da tunanin yadda zai saita tunanin Feenah zuwa gare shi.

Haka suka ci gaba da rayuwa duk da cewa abubuwan sunyi sauki ta dena cewa ya sake ta amman ta nuna masa kuskuran da ya yi na raina mata wayo da ya dinga yi yana sa mata kwaya. Da ta sanar dashi cikin dake jikinta, ba karamin murna ya yi ba, sai dai ita ba ta wani son abin da ke cikin, kawai babu yadda zata yi ne shi yasa take dauke dashi a jikinta. Nan fa Sultan ya ci gaba da bata kulawa ta musamman, dan yanzu har guri guda suke Kwana, duk da cewa kafin ta yadda ya biya bukatar shi sai ya wahala, kuma idan suna yi ko ya gama ko be gama ba indai ta gaji hanashi take yi sai dai ya kwanta a haka.

Daddyn ta kam tunda yaji shiru Feenah ba ta kuma yin tashin hankali ba yasan aikin kafewar da akai mata ne. Sai a sannan hankalinsa ya kwanta yasan ko babu komai zai dinga tunawa cewa yarsa tana gidan miji, ba kamar sauran ba da suke gabansa rid'a-rid'a dasu. A haka taci gaba da yin makaranta tana kuma wayewa da sauran abubuwan rayuwa. Lokacin da haihiwarta ya yi Sultan ba karamin tada hankalinsa yai ba, saboda baya son ya rasa Feenah, kaunarta yake kamar numfashinsa.

Haihuwar kuma tazo mata da matsalar zubar jini, aka gwada nasa be yi mata ba dole ya dinga siya ana saka mata. Cikin hukuncin Allah ta haifi baby boy d'in ta jajir dashi kamar ka tab'a shi jini ya fito. Koda ta haihu ma tasha wahalar ciwoka har kusan kwanaki goma sha d'aya bata san wanda yake kanta ba.

Da taimakon Allah da ya bawa Doctor's sa'a Feenah ta samu lafiya tayi ras da ita kamar ba ita ta haihu ba. Amman fa fur taki bawa babyn nono a cewarta me zai sha. Aka ci gaba da bashi madarar yara. Gaba ɗaya Sultan shi ke kula da babyn sa mai suna Omar Farooq, sam Feenah ba ta masa kulawa daman wanka ba Iya yi masa tayi ba. Sanda suka yi arba'in da uku baby Farooq ya rasu, sai a sannan Feenah taji a jikinta ta dinga kuka da kyar makota da matan abokan Sultan suka dinga bata hakuri.

A cikin matan abokan ne jinin Feenah ya hadu da guda d'aya wato matar Saifullahi mai suna Zarah. Ita ta koya mata gyaran jiki da yadda ake kula da miji da sauran abubuwa na karuwa. Sai dai fa ace har gwara da ba a koyar da ita ba dan a lokacin ne ta kuma ƙaro wani iskanci da rashin mutunci. Jikinta ya jiko ko'ina masha Allah ta dinga gara Sultan, ta dawo da neman takardar sakin ta. Babu shiri ya shirya suka dawo gida Nigeria inda yake zaton za'a samu masalaha a lallabata taci gaba da zama dashi. Sai dai kash! ta baya ta rago, dan sai da ya gwammace suna can kasar.

Ganin anki raba su yasa Feenah yanke shawarar kai su kotu a karbo mata hakkinta. Daddyn ta da Sultan suna zaune a gidajen su suka ga takardar sammaci, abin da ya tayarwa da iyayenta hankali kenan. Tun kafin ma aje Alhaji Nura ya samu Sultan yace kawai ya sauwakewa Nafisa amman yaki shi a dole yana son kayarsa. Babu yadda aka yi dole suka tattara suka tafi kotu daman ba a gidan su take ba tana gidan Sultan d'in, shi yasa Koda suka hadu da iyayenta a kotu bata yadda sun hada ido dasu ba ko da wasa. Akai ta shari'a har dai bakin ciki yasa Sultan cewa sai ta biya shi kudin wani auran, duk da cewa ba rasawa ya yi ba, amman ya fadi haka ne dan Feenah taji tsoro tace ta fasa tunda ba ta da kudin da ya ambata.

Amman da yake zuciyarta a k'ek'eshe take sai ta amsawa da alk'ali Toh zata kawo.

Daddy da Mommyn ta harma da sauran sisters d'in ta babu wanda be mike tsaye ba dan mamakin jin yadda ta amsa cewa zata biya shi..........

_Sai fa kunyi hakuri, duk a typing babu abinda ke bani wahala irin editing. Idan anci karo da wata kalma da batai daidai ba ayi hakuri._


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR8iiiii KDAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.






*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 11:17 - Buhainat: *ZO GARE NI...*
Free page 6

NA
*HAJJA CE 👈*

Wattpad:- Hajjac

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*💡




Zufa ce ta dinga karyowa Daddy da Mommy, banda zaro idanuwa babu abinda suke yi, har alƙali ya yi rubuce-rubuce dan shi kansa yana jinjina karfin hali irin na yarinyar, hakan kuma ya sake tabbatar masa da cewa da gaske ta yi yarinyar bata son auren da aka yi mata.

“Nafisa...! A Ina kike da wannan makudan kuɗin da yace ki biya shi dan ya yi wani auran? Wallahi Nafisa ni dai ba biya miki zan yi ba, na yi iya yina a gurinki Allah yaji ya gani.?

Daddyn ta ya yi maganar yana kallonta cikin fushi, fuskarsa na nuna tsantsar ɓacin rai amman ko a jikinta dan ba tama kalli inda yake ba bare taga yanayin da yake ciki. Burinta kawai a karɓar mata hakkinta a raba auren ta da Sultan. Shekara ɗaya aka bata cewar ta kawo kuɗin lokacin ta gama iddah.

Aka sanya Sultan a gurin ba dan ya so ba ya rubutawa Feenah takardar saki d'aya, jikinsa na kyarma saboda tashin hankali dan ya gama tabbatar da cewa babu son sa a cikin zuciyar ta ko kad'an.

Lokacin da ta tabbatar da Sultan ya saketa, ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai kunshe da tsananin farin ciki, ji take kamar ta zubar da ruwa a ƙasa ta sunkuya ta shanye saboda tsananin daɗin da take ciki. Alkalin ya kuma yin ƴan rubuce-rubuce kafin ya dago kansa ya yiwa mutanan cikin kotun bayanin sakin Nafisa.

Yana gama tabbatar da cewa sakin ya yi ya buga gudumarsa mutane suka fara fita. Wasu na zagin Feenah yayin da wasu ke ganin laifin iyayen da kuma shi Sultan ɗin da ya dage wajan ganin ya aure ta duk da yasan ba son shi take yi ba.

Ba a bari ta fita ba sai da aka tabbatar da cewar iyayenta sun tafi sannan itama aka sallameta ta koma gidan Sultan d'in dan dibar kayanta. Tana cikin had'a kaya a trolley taji an banko ƙofar d'akin da take ciki, kafin ta kai da ganin ko waye taji duka babu ji ba gani. In da ta fara gane me yi mata wannan mahaukacin tukun, maganar da ake yi ba a kuma fasa tsula mata durinar ba.

“Dan ubanki mu zaki tozar ta a idanun duniya Nafisa? Irin tarbiyar da muka baki kenan marar mutuncin yarinya. A gidan ubanwa zaki samu wannan uba-uban kuɗin da yace ki biya shi? Sata ko karuwanci zaki fara yi tunda naga kin zama kwankwararriya marar ɗa'a...??

Mommy ta sake zuba mata bulalar a gadon baya, Feenah ta saki wani ihu tana son kamo bulalar ta kasa.

Shigowar Sultan da yayarsa ɗakin ne suka taimaki Feenah daga dukan da Mommynta keyi mata, duk ta yi mata jina-jina da jiki ya yi burd'un-burd'un abinka da farar fata kuma mai taushi wacce aka tarairaya cikin jin daɗi da more rayuwa.

“Mommy dan Allah ki rabu da ita, har yanzu Nafisa yarinya ce.? Cewar Sultan yana rike da bulalar hannun Mommy, tana ja yana ja kamar masu wasa.

Cikin fushi Mommy ta waigo tare da zabga masa wata uwar harara, tama manta cewa shine surukin nata tace.

“A gidan ubanwa za'a kira wannan makirar da yarinya? Toh ko ni ba zan iya irin wad'annan shaid'anun abubuwan da take aitawa ba. Ku barni na farfasa mata jiki har ta gaya min menene takamarta na cewa zata biya kud'ad'an da ka ambato mata.?

“Mommy ai ba ta haka zaku tambaye ta ba, kin san dai halin Feenah da taurin kai. Ko bata da yadda zatai ta biya ni dan na rabu da ita zata iya amsawa alƙali. Abin tsoran dai kawai shine, zata fara yin wani tunanin na daban wanda zai Iya kaita ga halaka, shi yasa har na fito daga kotun na koma na sanar da alkali cewa na yafe mata ba sai ta biyani komai ba.?

Da sauri Mommy ta kuma d'agowa ta kalli Sultan, ji take tamkar ta rungume shi dan jin irin jarumtar da ya yi, saboda gabaki ɗaya ta gama lissafa ta yadda ita kanta zata fito da million biyar bare kuma Feenah da ba wata sana'a take yi

5 / 38