ai ni yanzu bazan iya auran mijin wata ba. Dan haka karki sawa ranki cewar zan iya auran miki miji."
"Yana sanki fa, ni kuma ina san duk wani abu da miji na yake so. Dan haka ina muku fatan alkairi." Cewar Iman tana murmushi.
Shiru bata ga reply ba, tana ta jira ta dai tabbatar da cewa Feenah ta sauka daga online. Sai kawai ta tashi ta fito zuwa kitchen dan samun abinda zataci. Tana tsaye wajan fridge tana zuba madara a cikin kofi taji shigowarsa amman bata juya ba. Sai da ta gama ta rufe fridge ɗin sannan ta ɗan kalleshi sai taga yana murmushi tare da ƙarasawa gurinta. Kamo mata kugu yayi tare da rungumeta ta baya, wani irin kululun abu ya tokare mata a wuya, ji take tamkar ta hankaɗeshi, amman ta daure taci gaba da kurɓar madarar.
"My dear wife, na tashi." Yayi maganar yana sumbatar gefen wuyanta.
"Eh nagani ai." Ta faɗa cike da rashin damuwa.
"Waye ya canza kujerun falo daga yadda suke? Kadai kice min kece bayan kinsan halin da kike ciki?" Takaici yasa ta yatsina fuska, batace komai ba.
"Kina Jina kuwa?" Tace,
"Naji, yi nayi saboda ina son hakan."
"Uhmmm anya wannan dear ɗin tawance kuwa?"
Ya faɗa yana murmushi. Still bata bashi amsaba sai kokarin zare jikinta daga nashi take amman ya matseta duk da cewa bata nuna masa tana cikin fushi dashi ba. Ya janyota suka fito, kai tsaye ɗakinsa suka koma ya zaunar da ita a bakin gado. Yace ta jirashi ya shiga bandaki. Yana shiga ta ɗakko wayar, abin mamaki harya canza password. Tayi dariya, kenan Feenah ta kirashi tayi masa magana cewa ta mata magana ta WhatsApp, shinkum shine ya canza password ɗin wayar.
Ajiye Masa wayar tayi har ya fito daga bandakin, ta kalleshi suka hada ido yace.
"My Dear kenan."
"Da tayi mene.?"
"Babu komai, na Faɗa ne kawai just for nishaɗi."
Miƙewa tayi zata bar gurin yai saurin riƙeta, Iman ta rintsa ido saboda wani irin azababban haushinsa takeji. Ya sake janyota tare da zaunar da ita saman cinyarsa yace.
"Gaskiya akwai dalilin wannan sharewar da kike min, shin menene matsalar?" Ta zabga masa uwar harara tare da cewa.........
*HAJJA CE 👈*
3/26/22, 17:01 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲*
*40*
"Bakasan abinda ya faru ba?" Ya sake janyota zuwa jikinsa tare da kwantar da kansa a kafaɗarta yana cewa.
"Shi yasa nake tambayarki." Haushi yasa ta fizgewa daga jikinsa tare da bar masa ɗakin.
Da kallo ya bita tana barin ɗakin ya dafe kai tare da rintsa ido. Wayar ya janyo ya kunna WhatsApp tare da shiga cikin content ɗin Feenah yaga tayi masa magana. Kwanciya yayi suka ci gaba da chatting ɗin su inda yake tabbatar mata da cewa zai goge lambarta daga cikin wayar Feenah yadda bazata kuma samun access da ita ba.
"Ina takwara na?" Ya tambaya yana sake yin juyi akan gado.
"Gashi yana ta bacci, yana ta so ya ganka saboda nace masa akwai daddyn sa mai irin sunansa." Murmushi yayi yana sake maƙale wayar a kunnensa yace.
"Ai ina son zuwa dubashi, kawai bana so mu hadu da Babansa a asibitin."
"Dan Allah kazo yau."
"A'a bana son fitina, kinga dai duk da bakwa tare da juna gani na tare da ke zai sa shi jin babu daɗi, musamman idan yasan cewa nine wannan the one you love, Allah kila muyi danbe a gurin." Feenah ta ɗan ja tsaki cikin yatsina fuska tace.
"Dan Allah ka dena faɗar haka. Nifa dashi da babu duk ɗaya suke a guri na." Areef ya yi murmushi.
"A'a duk da haka ai Kinga tare kuke." Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin.
"Babu komai a tsakanin mu sai albarkacin Areef, banda haka da babu komai tsakanina da Sultan. Ka sani cewa duk duniya babu ɗa namijin da nake so sama da kai, da soysyyarka aka halicce ni, da ita na rayuwa gashi ina ji a jikina cewar da ita zan mutu. Dan Allah dan Annabi ka ZO GARENI ko idanuwa na zasu yi farin gani, zuciyata tayi haske."
"Shikenan zan zo da anjima."
"Yeehhh thank you so much my baby, I love you and I can't do without you. Wallahi soyayyarka tayi min ila a cikin zuciyata, komai naka yana burgeni."
"Nima haka kema kuma kinsan da hakan sweetheart. Ki tanadar min somethings special."
"As you wish my babylove." Ta turo maganar cikin haɗa masa da alamar🤩
Sauka yayi daga online ɗin ya ajiye wayar a karkashin filo. Tashi ya yi ya fito falo Iman bata nan, yaje kitchen nan ma bata ciki sai ya shiga ɗaki. Tana zaune tana ninke kayanta, ko dagowa batayi ba bare har yasamu ganin murmushin da a kullum idan basu tare da juna tana ganinsa shi take fara aika masa kafin kyakkyawar runguma ta biyo baya. Yayi murmushi tare da ƙarasawa har inda take ya zauna. Sumbatar gefen fuskarta yayi tare da karɓar underwear ɗin da ta ɗauka, bata kulashi ba taci gaba da harkarta, muryarsa a sanyaye yace.
"Wai dear ba zaki sanar dani laifin da nayi miki ba? Feel free ni mijinki ne duk duniya baki da wanda ya fini a yanzu."
Kalamansa suka bata mamaki, hakan yasa ta juya ta ɗan kalleshi cike da takaici tace.
"Waye ya gaya maka hakan? Taya zaka faɗi haka cewar duk duniya bani da wanda ya fika?" Ya zaro ido tare da juyo da ita gabansa yana kare mata kallo.
"Au kina da waɗanda suka fini ne?" Iman ta kawar da fuska tare da cewa.
"Tab..." Mamaki ya kamashi.
"Dear kina nufin kice min bani ba gaskiya na faɗa ba? Ashe har akwai wanda ya fini matsayi a gurinki?" Iman ta taɓe baki tare da cewa.
"Ni dai ban faɗa ba, abu ɗaga kawai zan gaya maka shine. Duk yadda kasan matsayi na a cikin zuciyarka, ina nufin duk yadda kakejina a ranka toh kwatanƙwacin haka nake jinka kaima. Babu cuta babu cutarwa ahhh Tohhhh." Tana kaiwa nan ta fizge skirt ɗin daga hannunshi taci gaba da aikinta ranta yana zafi.
"Ohhh tohh masha Allahu, ni yadda kike a cikin zuciyar nan tawa ai baki bazai iya furtawa ba." Ya kuma janyota jikinsa ta shiga tutture shi ganin yasa mata karfi yasa ta kyaleshi, hannunsa a saman cikinta yana shafawa yace.
"Kinsan matsayi da girman matar farko kuwa? Haba dear we are together fa, babu wacce zata samu irin matsayinki a zuciya ta." Maganganunsa suka tunzura ta, rai a bace tace dashi.
"Ohhh! Naga alama ai, shi yasa kaje kana cewa wata har yanzu kana mutuwar sonta ko? Wai tsaya in tambayeka." Ya kwantar da kai a saman bayanta tare da fadin.
"A zaune ma nake dear, gaya min ina jinki."
"Ku maza bakwai jin kunyar zabgo karya ne? Kai yanzu har kana da abinda zaka ce min? Wallahi ka bani mamaki, har wata tazo tace dakai wai bata jin daɗin sunnah da mijinta sai ta hasaso tamkar tare kuke sannan take jin daɗi. A haka kake tunanin cewar mutuniyar kirki ce ko? Toh duk rashin ilimi na bazan iya furtawa saurayi na haka ba koda kuwa ace da gaske ne. Amma kaibi duk ka ɗaukaki abin saboda salon iskanci. Mtww." Taja tsaki tare da fincikewa ta shige toilet.
Zama tayi akan toilet seat tare da dafe kai, kirjinta banda harbawa babu abinda yake. Da kyar ta iya miƙewa, alwala ta ɗauro ta fito, baya cikin ɗakin abin ya sake kona mata rai ta janyo sallaya ta hau tare da tada iƙama. Shi kuwa ganin ta shige banɗaki yasa shi jan numfashi, kallon toilet ɗin yayi tare da furta.
"Mata! Mata!! Halinku sai ku."
Ya ɗakko wayarta tas ya goge numbern Feenah daga cikin wayar. Daga haka yabar ɗakin ya koma nashi. Yana shiga ya tarar wayarsa ana ta kira, ya duba yaga 'S.H' Wato Feenah da ya canza sunan na sweetheart dan kar Iman ta sake gani. Sai da ya koma ya rufe ƙofar kafin ya kara a kunnansa.
"Gani nayi chat ba zai sanyaya min rai ba, saboda shi rubutu ne kawai. Ni kuma ina son jin muryarka mai sanyaya nutsuwa da kwanciyar hankali a gareni." Ya zauna a bakin gado yana shafa fuska, cike da nishaɗi yake cewa.
"Gaskiya kin mana illa da har kika yadda da komawa gidan tsohon mijinki. Meyasa baki jajirce wajan ganin kin nemoni ba a lokacin? Yanzu gashi nan duk munzo mun rasa yadda zamu sai dai hakuri." Feenah ta fashe masa da kuka nan da nan kuwa ta tashi hankalinsa, sai faman cewa take.
"Babu yadda zanyi babylove, Sultan shine wanda yaje ya tsammani daga cikin uƙubar da daddy ya sani. Saboda soyayyar da suka ga ina yi maka, wallahi baby inda aka kaini har tare da almajirai naci tuwo. But Sultan yana min wani irin so, wanda yasa har sai da ya dawo ya nemo ni yace zai maida auran mu. I have no way da zan iya kuɓutar da kaina bayaga na yadda na koma. Am telling you the truth saboda na nemoka yasa ni fitowa daga gidan sa. Sultan yaki ya rabu dani baby ya hanani sukunin rayuwa dan Allah kazo na ganka."
"Zanzo bari nayi wanka."
"A'a ni ka taho a haka." Ya ɗan zaro ido tamkar suna tare.
"Kinsan a yadda nake kuwa? Ayi min hakuri nidai."
"Shikenan five minutes." Katsewa tayi shima ya ajiye wayar.
Tsab ya shirya cikin kananun kaya, kai banda ma dai itama Iman ɗin sai da Allah ya gama tsarata a hallita, jiki ne kawai batadashi. Amman kam da ta shiga uku, Areefullah ɗin bada baya ba, kayan sun zauna a jikinsa ya yi bala'in kyau ta yadda babu maccen da zata ɗora ido akansa, bataƙi sake kallansa ba. Yaron ya hadu Tubarkallah masha Allah dole ne yanzu in Feenah ta ganshi sai ta sake ruɗewa.
Haka ya fito cikin shirinsa, har zata fito ta hagoshi gabanta ya faɗi ras! Da sauri ta juya tare da zura doguwar riga purple tana cikin yane kanta da mayafi ya shigo, kallonta yayi da tsantsar mamaki. Sai dai be nuna cewar ko fita zata yi ba yace.
"Dear bari naje na dawo." Ta juyo a hankali tana kallonsa, batace komai ba sai da ta juya taci gaba da gyarawa tace.
"Ka fita ko mu fita? Dama yanzu nake shirin zuwa nace ka fito muje yunwa nakeji, and nagaji da zaman gidan wallahi."
Areef ya shiga shafa gashin bakinsa yana kara kallon Iman, gani yake tamkar ta gano inda zashi, amman kuma ai ba'a gabanta yayi wayar ba bare yaci tana sane zata masa haka. Kuma yanzu ba zai iya rejecting fitar da ita ba, saboda matsayin nata ne. Dan haka ya ƙarasa gurinta tare da jin gina bayansa a jikin bango yace.
"Toh my dear yadda kika ce haka za'a yi." Ya faɗa tare da harɗe hannayensa a kirji. Tana gamawa ta kalleshi tare da zuwa ta ɗakko jakarta ta rataya, zuwa tayi ta sargafa hannunta jikin nashi tare da cewa.
"Muje." Suka fita tare da rufe gidan.
Sai da sukaje sukaci abinci sukai yawo karshe suka zauna a wajan shaƙatawa. Suna zaune yace bari yaje banɗaki, tace toh. A ranta take cewa. 'Sai dai kai ta yi amman wallahi bazan bari kaje ko'ina ba.' Ta juya ta kishingiɗa tana turo baki.
Iman bata dan duk wannan abin a banza ba, sun riga sunyi magana cewar tazo gurin su hadu. Dan haka yana ce mata zaije toilet ya sulale ta baya ya shiga inda Feenah tace masa tana jiranshi. Yana shiga daman guri ne na musamman da aka ɗan keɓance, shigarshi tun daga bakin ƙofa yasan cewa tana nan a ciki saboda wannan fitinanniyar khumran da take amfani dasu, ga ƙamshin turare mai sanya muguwar kasala.
Ya shiga ciki yana lasar lips tare da baza ido yana nemanta. Juyowa tayi kawai ta hangoshi, cikin sauri ta miƙe tsaye, shi kuwa be gane ta ba sai da tazo gabansa saboda tayi ƴar ƙiba ga wani fari da ta sake yi, tayi luf-luf tamkar ba Feenah da ya sani ba. Kamanninta suna nan, ya saki murmushi tare da cewa.
"Lallai idan na ganki a hanya bazan iya ganeki ba, haka kika zama big girl?"
Kawar da fuska tayi tare da nuna masa kujera, kallon hanyar shigowa yayi saboda hankalinsa duk yana wajan Iman, gani yake tamkar zata iya biyoshi. Ya kalleta yana karewa hannunta da yasha jan lalle kyau, Ya girgiza kai tare da yin murmushi yana zuba hannuwa cikin jeans ɗin dake jikinshi.
"Kinsan tare muke da ita, dole bazan daɗe ba." Feenah ta shagwaɓa fuska tare da turo baki tayi kamar zatai fushi tace.
"Meyasa kazo da ita bayan ba haka mukai da kai ba? Baka son muyi hira? I have a lot of something to say babylove, ina buƙatar nida kai muyi magana."
"Zan kuma samun time nazo, but yanzu kam akwai problem sweetheart." Juyawa tayi ta koma gurin da ta taso, sai faman juya jiki take yi, yai saurin kawar da fuska kafin shima ya ƙarasa gurin. Jakarta dake kan table ya ɗauka tare da zugewa yana fadin.
"Mekika kawo min?" Ta jingina bayanta jikin kujera tana cewa.
"Ni ba komai, daman banzo ba wallahi."
Turare ya hango a cikin jakar, ya fito dashi yana jujuyawa.
"No gwara da kikazo, yanzu bagashi munga juna ba? Wannan turaren zan ɗaukeshi just to remember you. Bari na koma kar taga na daɗe." Ai Feenah najin abinda yace wato tafiya kenan zai yi ya barta ba tare da sunyi hira ba tace fashe masa da kuka.
Hankalin Areef ya tashi, besan lokacin da yaja kujera ya zauna ba, hakuri ya shiga bata duk hankalinsa a tashi, shi kuma ya ƙagu ya tafi ne sakamakon wani irin yanayi da yaji ya shiga, ƙamshin ta gaba ɗaya ya tayar masa da hankali, ya kasa sukuni. Gashi yanzu ta saki kuka kuma shi kansa yasan beyi mata adalci ba tunda be daɗe ba a gurinta yake cewa zai tafi. Cike da damuwa tare da kwantar da kai yake ce mata.
"Dan Allah dan Annabi kidena wannan kukan, wallahi bakiji zuciya ta ba yadda take min zafi da zugi. Zan tafi ne badan kin gundireni ba, kinsan tare muke da Iman, kuma yanayinta a yanzu baya buƙatar duk wani tension, yanzu idan wani abun ya faru da ita na shiga uku." Ya faɗa iya gaskiyarshi, Feenah ta shiga kallonsa da mamaki rai a bace ta miƙe tana cewa.
"Na sani, tabbas nasan yanzu dole kafifita matarka fiye da yadda zaka yiwa kowa. Nasan dole yanzu ka dinga gudun fuahin matarka tunda yanzu tare kuke. Ni ina son ma naji ta ya akai kukai aure da ita bayan baka taɓa sanar dani cewa akwai aure a tsakanin ku ba? Babu komai nasan yanzu baka sona Allah ya bani hakurin jure rashinka my baby. But nasan dai tabbas zuciya ta tana yi maka soyayyar da har gobe ba zataiwa wani ba." Ta dauki jakarta tana zugewa. Wayarsa ya ɗakko ya shiga yi mata video tana kakkare fuskarta.
"Kiyi hakuri duk ba wannan bane, kuma zan baki labarin duk abinda yake faruwa har na auri Iman. Kawai ni yanzu ki dena yi min asarar hawayenki, har cikin zuciyata nakejin kukan nan. Zan samu nazo kafin kubar ƙasar nan."
Feenah tasa hannu tana share hawayen, ya yi murmushi wanda yasa Feenah saurin kawar da kai dan ji take tamkar taje ta faɗa saman kirjinsa ko zataji saukin sassaucin wutar azalzalar soyayyar sa da take mata zafi cikin zuciyarta. Sai dai duk da haka sai da ta kamo hannunsa ba zato bare tsammani yaji ta ɗora a saman kirjinta, ya zaro ido cike da mamaki, ita kuma ta langaɓe kai tare da cewa.
"Kaji yadda kake a cikin rai na. Ya rage naka ka ceci rayuwata ta hanyar kasancewa tare dakai a koda yaushe, ko kuma ka barni cikin masifa har soyayyarka ta kasheni."
Gaba ɗaya ta kusa yi masa formating cikin kwakwalwarsa saboda kusancin da suka yi da juna, ga kuma hannunsa a saman fitilunta da suke manya. Ya zare hannunsa a kasalance yana jin wani irin abu a jikinsa na tsantsar son kasancewa da ita a dai dai wannan lokacin. Cikin dauriya ya fara addu'ar neman tsari daga shaidaniyar zuciyarshi wacce ke zugashi ga son aikata abinda zai janyo mishi bala'i.
"Karki damu Sweetheart, zanzo zamu daɗe kuma, yanzu dai kiyi min alfarmar tafiya kar taga na daɗe please."
"Ya zanyi idan ban barka ka tafi ba? Dole na kyaleka kaje gurinta tunda a karkashin ikonka take, shikenan sai ka kuma zuwa kaje kawai." Tayi maganar tana saurin ficewa ta barshi a gurin.
Shima babu yadda zai yi dole ne ya kyaleta ya tafi gurin Iman saboda a yanzu tafi kowa kusanci dashi. Ya sake ware hanci yana shaƙar ƙamshin turarenta da har yanzu yana nan a gurin. Ya zura wanda ya ɗauka a cikin aljihu kafin shima ya fito ya nufi gurin Iman. Yana zuwa ya tarar da ita tana faman gyangaɗi, ya saki ajiyar zuciya tare da ware hannuwa yana niyar ɗaukarta ta buɗe ido. Murmushi yayi mata yana sakinta dan ta samu damar tashi tsaye yace.
"My dear a haka kamar ba zaki nauyi ba, amman kinji ki kuwa?" Iman ta bugi kafadarshi cikin shagwaɓa tace.
"Wallahi banida wani nauyi, kawai kune ragwaye. Khajol tafini sosai amman kaga yadda Sharukhan yake juyi da ita tamkar wata ƴar bebi." Ya kamota zuwa gefensa suka fara tafiya yana cewa.
"Yoo ai koni zan iya ɗaukarta nayi harda gudu ban gaji ba, kinsan dalili?" Iman ta turo baki tare da girgiza kai.
"Saboda su basu cin carbohydrate, abincin su marar nauyi ne. Ku kuma tun asali su Mamah sun ɓata ku da su tuwo, shinkafa habba malam, irin waɗannan." Ya shiga nuna mata turawan da suke wucewa yana fadin.
"Duk basu da nauyi, saboda salad shine abincinsu."
"Naji toh abar maganar. Ni wallahi ɗan baccin nan ma da na farayi har mafarki nayi." Tayi maganar cike da shagwaɓa tana sake kwantar da kai a kirjinsa.
"Mafarki? Kice bacci yayi dadi shi yasa kikai mafarki, na meye?"
"Wai kun hadu da shegiyar matar nan." Ya zaro ido.
"Ni kuma? Wace mata?"
"Banzar Feenahr nan mana." Ras! Yaji kirjinsa ya yi wani irin bugu.
'Kodai ganinsu tayi? Yasan halin Iman sarai da iya shariya idan taga abu. Sai dai zatai ta dasa maka magana idan kuna hira har sai ka gano cewa tafa san wani abun.'
"Subahanallahi dear tsabar kinsata a ranki ne fa. Ke da mijinta fa amman duk kinbi kin takurawa zuciyarki akanta."
"Ba takurawa nayi ba, abinda