Aslam and the second one is Irfan Ko?" Ganin yadda take buɗe masa kwawawan idanunta tana son nuna masa cewa tasan waɗanda zai ɗauka yasa shi hura iska a cikin su, ta lumshe su tana kawar da kai ga murmushi faɗaɗe a fuskarta.
"A'a basu bane, baki san nayi sababbin abokai ba?" Ya faɗa cikin zolaya. Ita kuma ta kasa fahimtar a wasa ya faɗa, ta kalleshi da mamaki.
"Toh ai ko baka bawa Irfan ba, yaci ace Aslam ya samu, amman idan har da gaske ba zaka bawa Aslam zan daure na tambayi Baban shi ma a haɗa dashi. Yana da kirki sosai." Areef yai murmushi tare da kwantar da kanta saman kirjinsa.
"Wasa nake yi miki ai kinsan dole shine sahun farko, Irfan ma be zama lallai ba saboda kinsan baban su bashi da lafiya, shi yake rike da gidan su. Sai dai ko Affan ko Sultan." Kanta na saman kirjinsa tayi luf da ita wani irin farin ciki yana ratsata, a hankali tace dashi.
"Toh yayi, indai akwai Aslam a cikin tafiyar shikenan."
"Yana da muhimmanci a gurinki ne?" Sai da ta ɗan dago kai suka kalli juna kafin tace.
"Yana da kirki."
"Ya kaini ko ya fini?" Ya tambaya yana ɗora lips ɗinsa a saman kanta.
Iman tayi shiru ba tare da ta bashi amsa ba, ita kawai tasan kowa da matsayinsa. Aslam ya ƙarfafa mata guiwa matuƙar a lokacin da ta baro gidan Areefullah ta dawo gida. Shine mutum na farko daya tabbatar mata da cewa Areef yana santa, sai dai shi kansa besan da hakan ba. Ko soyayyar da suke yi da Feenah ya tabbatar mata da cewa hauka kawai suke da kuma shirme, amman ainahin love ita yake yiwa. Gashi yanzu tana gani a zahiri, ta yadda da cewa Areefullah yana santa so marar gauraye.
Suna zuwa airport abinka da masu riƙe da ƙasar, ba wani ɓata lokaci suka wuce wajen shiga jirgi. Da yake wayayyu ne a cikin su babu wanda ya nuna ƙauyanci, kowa ƙoƙari yake ya nuna cewa yasan komai na shiga cikin jirgin. Guri ɗaya Sen. Muhammad ya kuma basu, suna da murmushi zuciyoyinsu shar har jirgin ya tashi ya bar birnin Kano zuwa Abuja birnin tarayya. Ya subahanallahi jama'a mulki daɗi gareshi, yadda kadai ake nan-nan dasu kai kace su kadai ne mutane a cikin duniyar nan. Maganar da take fitowa daga bakin mutane shine. Senate ya dawo tare da ƴarsa da kuma surukinsa, yan jarida ana subirbuɗa labari.
Kai tsaye katafariyar unguwar masu farcen susan cikin ƙasar nan. Tun a hanya Areef da Iman ke faman kale-kale, sai yanzu ma yasan shi be san ko'ina a garin Abuja ba. Aka yi parking a dai dai wani ƙayataccen gida, wanda alƙalami ba zai iya rubutawa ba saboda tsari da kuma ɗaukar hankali. Cike da murmushi Sen. Muhammad ya ƙarasa ya kamo hannayensu yana cewa.
"Kuzo muje, nan gidan kune yarana."
Suka shiga ciki securities da masu kula da gidan taɓangarori da dama suka dinga miƙa gaisuwa yana amsa musu cike da fara'a. Daman tun a social media sukaji labarin ya taho da ƴarsa, hankalin Hajja Samira yayi koluluwa wajan tashi, saboda sam be sanar da ita cewar anga ƴarsa ba, yasan idan har ta sani sai ta kuma yi masa kullin da zai sake nisanta shi da ita. Tun a saman tagar bene ta hangosu, ita kanta sai da kanta ya Sara, kirjinta ya buga ganin yarinyar da Sen Muhammad yake tare da ita, dole kenan sai mijinta ya mallaki magaji? Wannan wace irin masifa ce? Tabbas taso su mutu a haka tunda itama bata da rabon haihuwa a duniya, sai gashi duk irin dukiyar da ta narka dan ganin be samu haihuwa ba, gashi Allah ya kawo masa jininsa cikin koshin lafiya.
Da kyar ta iya sakkowa ƙasa jin yana ta kiranta, da gayya yake son ta fito dan taga Iman ɗin. Cikin isa da kasaita take tafiya har ta gama sakkowa ƙasan tana yatsina fuska. Duk iya kokarin ta na san ganin bata nuna halin damuwa da ganin Iman ba, kasawa tayi har sai da fuskarta ta bayyana abinda yake cikin ranta.
"Allah ya bayyana mana Khadija." Abinda Sen ya faɗa kenan yana sake rungume Iman a jikinsa.
"Masha Allah A'i tun a BBC News mukaji labari." Tana magana tana ƙarasawa wajan kujera ta zauna.
"Iman jeki gaisa da Mamanki." Iman ta nufeta, zuciyar Hajja Samira tamkar zata buga a haka Iman taje ta rungume ta.
"Ga kuma mijinta." Ya sake nunawa Hajja Samira Areef a matsayin mijin yarsa.
Wato ma har aure tayi saboda tsabar samun guri? Batace komai ba sai ɗan murmushi da tayi tana janye Iman daga jikinta.
"Bari nasa a kaisu inda zasu zauna su huta." Da sauri ta kalleshi tace.
"Au wani gurin zaka kai su?" Ba tare da ya kalleta ba yace.
"Eh akwai gidan uncle ɗin Al-Mustaphan yace can zasu je ko?" Ya faɗa yana kallon Areef. Shi kuma gabaki ɗaya mamaki ya kusa kasheshi jin abinda Sen. Muhammad ya faɗa, amman dan karya karyata shi sai yace yana ɗan murmushi.
"Eh haka ne."
"Iman taso kuje a rakaku."
Iman ta tashi gabaki ɗaya itama lamarin ya daure mata kai. Kenan mahaifinta tsoran matarsa yakeji? Idan hakane kuwa akwai matsala domin bata san irin wannan rayuwar. Ko sallama Hajja Samira batayi musu ba, kila yasan idan ya bar su a wajanta sai sun gabe kuransu dan ko abinci ba zata sa a basu ba. Dama tuni Sen. Muhammad ya gayawa driver ɗinsa inda zai kai masa yaran, tare da babban gargadi cewa karya sake ya gayawa kowa inda suke. Shima inda aka kaisu ba kananun mutane bane a unguwar, ko wane gida yana cewa bani guri. Areef da Iman suka shiga gidan harda masu aiki a ciki.
Wani ɗaki suka shiga a tare wanda ya gaji da taruwa, gadon Areefullah ya haye yana wani babbude hannuwa, cikin gajiya yace.
"Washh Allah na, ina ma zan samu mai yi min tausa da naji daɗi." Murmushi kawai Iman tayi tana sake duba yadda aka ƙawata room ɗin. Ganin bata da alamar zuwa tayi masa yasa shi kuma sauke numfashi.
"Dear zokiji." Iman tasan wayo yake mata, ta san tana zuwa riketa zai yi.
"Subahanallahi gashi nan..." Areef ya faɗa yana nuna gefen Iman, wacce a zabure tayi kansa da gudu. Ya bata wata kyakkyawar runguma yana faman dariya.
"Daman ba komai bane ko?" Ya lakuce mata hanci yana cewa.
"Yanzu ba gashi kinzo inda nake ba."
"Dabara ko?" Tayi maganar tana turo baki.
"I miss you dear." Iman ta kunshe fuska a saman kirjinsa.
"Please wannan karan dai ki daure ki amince dani ba tare da tilastawa ko na nuna fin karfi ba. Ina so ki nuna min taki kalar soyayyar."
"Yaya.." Ta faɗa da murya irin ta jin kunya.
"Yes zaki iya, karki ce min kunya ce zata cucu mu, ki ajiye ta gefe idan aka gama sai ki mayar da abarki."
Tayi lamo a jikinsa ba tace komai ba. Ganin haka yasa Areef dago mata da fuska, idanu ta lumshe hakan ya bashi damar sanya bakinsa a nata, yayi amfani da hannu ɗaya wajan zuge zip ɗin rigarta. Wayyo tayi saurin riƙe masa hannu yace.
"Karki hanani dan Allah." Babu yadda zata yi dole haka tana ji tana gani ya ƙarasa zugewa tare da zare mata rigar gabaki ɗaya. Kyawawa kuma tsayayyun fitilun kirjinta suka bayyana waɗanda suke cikin black ɗin bra. Wani irin zirrrr...! Yarrrr...!! Yammm...! jikin Iman ya yi lokacin da taji hannuwan Areef a kansu, cikin hikima Areefullah ya rabata da kayan jikinta, ya shiga aika mata da wasu saƙwanni masu rikita kwakwalwa.
A wannan rana, a daidai lokacin, a cikin shekarar da suka samu ɗin bin alkairi Areefullah ya samu amincewa ta gasken-gaske a wajan khadijatul Iman. Ta sakar masa da kanta, ta bashi amanar kanta da zuciyarta. Duk ta kuma narkewa a cikin so da wata zazzafar ƙaunar mijin nata. Shima kuma a nashi ɓangaren yaji tabbas cewa Iman itace sirrin rayuwarsa, itace farin ciki zuciyarsa, da gasken-gaske yake santa so marar gauraye marar algus. Bayan sun nutsu still Areef yana riƙe da ita yana wasa da sumar kanta, murya a hankali yace.
"My dear." A hankali tace.
"Uhmmm."
"Akwai yunwa ko?" Tayi shiru, ya sake juyo da fuskarta yana so ya kalli idanunta amman Iman ta hanashi.
"Shikenan muje muyi wanka."
"Jeka farayi." Ta faɗa tana sake ɓoye fuskarta.
"Tab! Da kenan, yau kam tare zamuyi ko bakya so mu sake shakuwa da junan mu?"
"Yaya bazan iya bafa." Maganar ta fito tamkar zatayi kuka.
"Okay naji amman gobe kisa a ranki tare zamu yi, bana son kina yin abu kamar baki waye ba." Ta turo baki jin abinda ya faɗa.
"Kodai tare zamuyi dan naga kinki ɗagani." Ai tana jin haka tai saurin ɗagashi tana murmushi.
Shima murmushin yake yi daga haka ya sauka ya shiga ƙawataccen bathroom ɗin cikin ɗakin, wanda shi kansa abin ya ɓatawa mai kallonsa lokaci ne. Da karan bani Areef ya dinga gano meye amfanin wasu abubuwan dake ciki, har ya fito jikinsa daure da farin towel. Yayi mamaki da be ganta a ɗakin ba, ya yi saurin saka kaya tare da fitowa nemanta. Kiranta yayi tayi, sai gata ta fito daga cikin wani ɗaki, da alama itama wankan tayo duba da kayan da ta canzo. Areef ya saki ajiyar zuciya tare da ƙarasawa inda take ya riko ta.
"Kawai zaki tafi ba tare da na fito ba? Naji tsoro da ban ganki ba." Ya leka fuskarta da sauri ta kawar zuwa ɗaya ɓarin.
"Wanka nayi nima." Ta faɗa murya a sanyaye.
"Yeah I see. Zo muje ga abinci a ƙasa nasan kina jin yinwa." Ya jata suka ƙarasa wajan dining. Da kanshi ya dinga bata tana kan cinyarsa, Iman ta tabbatar da lallai Areefullah ɗan soyayya ne. Yasan salo-salo na yadda zai tarairayi mace, gashi dai ba wani babba ba, amman tana da yaƙinin ko wani ƙaton ba zai nunawa mijinta iya kula da ko wacce irin mace ba.
Haka suka raya ragowar ranar da tsantsar kulawa, ko wanne kokari yake ya farantawa ɗan uwansa, har zuwa dare Sen Muhammad yazo ya duba lafiyar su, ya damƙawa Areef mukullayen gidan da kuma takardun gida sai kuma car key na danƙareriyar mota, yace yayi amfani dasu kafin wani lokacin. Aikin ma ya hanashi zuwa da kanshi yaje ya samu Alhaji Sammani suka yi magana ta fahimta, har ya yi masa nashi ihisanin sannan ya bawa Areef ɗin kuɗi isassu na amfanin yau da kullum, bayan komai an ajiye musu. 😒
Cikin kwanaki uku da suka yi ya biya musu umara su biyu yace suje suyi addu'a idan sun dawo sai su tafi honeymoon. Sunyi murna matuƙar, sun kuma ci gaba da gurzar soyayya tamkar babu wasu masoya a doran duniya......
(Hmmm ko ace Hajja shirgo mu tafi 😏 ba komai na samu nayi bacci kafin ku dawo😜)
*ZO GARENI book ɗin kuɗi ne, idan kina so sai ki tuntubi wannan labar 0706 528 3730 or +44789414004 dan samun naki cikin sauki.*
*HAJJA CE 👈*
3/23/22, 18:28 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲*
*38*
*****Jamil kuwa tunda ya dauki kan mota ya fara tuki tafiya kawai yake ba tare da sanin inda yake jefa motar ba, abinda kawai ya sani shine yana san zuwa Niger a ranar, saboda ayi masa aikin dena ganin Meenal da kuma Umma. Gabaki ɗaya tunda Umma tabar duniya yaji zuciyar shi a ƙuntace, sam bayajin daɗin komai, magani ma idan yasha mai makon yaji relief a'a sai yaji kamar ana sake takurawa zuciyar tashi. Idan yayi kamar addu'a zata zo masa zai yaji wani azababben ciwo bakinsa kuma sai yai ta rawa.
Ya kira malam yace ya taimaka yai masa aikin layar zana ta yadda kawai zai ganshi a ƙasar, amma bokan yace aiki ne mai wahala dan kamar wancen da akai na tura wani bandakin Iman sai da suka kashe jaririn aljani sannan aikin yayiwu, yanzu kuwa ba zasu iya yin wannan aikin ba saboda har yanzu akwai faɗa tsakanin uwar jaririn da kuma aljanin da yaje ya kashe mata ɗan.
Wannan dalilin ne yasa shi tilastawa ransa ganin yaje Niger ka kanshi. Irin yanayin tukin da yake yi ne yasa mutane suka dinga zaginsa suna tsine masa. Sai da yazo wajan wata mota mai ɗauke da man fetur garin yin overtaking kawai ya bugi tankin man, Allah ya taimaka hanyar babu motoci wuta ta kama, tun daga cikin motar aka finciko Jamil aka watsar gefe. Ya subahanallahi wuta ta kamashi kafafuwan sunyi ratata, hannu ɗaya ya fice daga jikinsa, gundarin jikin sai motsi yake tamka an kashe tsaka jelar na rawa.
Banda ihu da kururuwa babu abinda yakeyi, mutane suka fara tsayawa a motocinsu bayan Allah suka dinga zuwa wajan wani ɗan ƙaramin rafi suna debo ruwa da ƙasa suna watsawa motar dan wutar ta mutu. Shi kuma Jamil da kyar aka samu wasu mutane suka daukeshi zuwa asibiti yana ta ihu har ya ɓatawa masu taimakon nashi rai. Dan dai kawai sun riga sun dauki aniyar kaishi saboda Allah ne, amman jini duk ya ɓata musu mota dan ma dai ƙurƙura ce.
Koda akaje asibitin kafin a karɓeshi sai da aka ɗakko ƴan sanda, Allah kawai yayi numfashin Jamil yana da saura amman kowa ya bashi mutuwa a take. Sai dai fayakunu bata sauka ba har likitocin suka fara bashi taimakon gaggawa. Wayarsa da masu motar suka ɗakko shi, duk ta fashe aka ciro sim card ɗin wani ɗansanda ya saka a wayar keypad, neman lambar da ya kamata su kira dan a sanar da ƴan uwanshi suka shiga yi. Kawu Bala da suka gani ne yasa suka kira, bugu biyu ya ɗaga da sallama.
"Jamilu ya gida?"
"Bashi vane ɗansanda ne."
"Subahanallahi ɗansanda kuma? Toh lafiya dai ko?" Kawu Bala ya tambaya cike da fargaba.
"Me wannan lamar yayi accident akan hanyarsa ta zuwa Nassarawa, yanzu haka besan inda kanshi yake ba, yana nan general hospital."
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun. Hasbunallahu wani'imal wakil, bari naje na sanar da iyalinsa."
"Toh shikenan ya dai kamata a samu makusantanshi a kusa, saboda hatsarin yayi muni." Kawu Bala yace.
"Gamu nan Insha Allahu."
Suna yankewa ya tashi yana sanar da matansa cewa Jamil yayi hatsari yana asibiti. Daga nan ya fice ya nufi gidan, yana zuwa ya tarar da Salima tana koyawa Khaleel homework, tana jin sallamarsa dama ta tashi daga kan kujerar da take tace ya zauna. Sai da ya zauna suka gaisa kafin yaja numfashi tare da cewa.
"Tashi zaki ki shirya zamuje asibiti." Tunda taji haka gabanta ya faɗi, cikin sauri ta kalli kawu Bala tana dafe kirji tace.
"Jamil?"
"A'a ku mata kuna da matsala, ke daga cewa za'a asibiti sai ki ce wani Jamilu? Kije ki ɗakko mayafi idan munje kwaga komeye."
Jiki yana kyarma ta tashi, hijabi ta ɗakko ta fito suka tafi har da Khaleel. Sai da suka biya ta gidan ƙanwarsa suka ɗakkota kafin suka tafi, jikinsu duk a sanyaye gashi Kawu Bala yaki sanar dasu ainahin abinda yake faruwa, har suka ƙarasa asibitin lokacin anata kiraye-kirayen magariba. Tambaya sukayi, wani masinja ya rakasu har wajan dakin da aka kwantar da Jamil, suna jiyo ihunsa gaban su ya sake bugawa, wani ɗansanda ya sanar dasu abinda yake faruwa hankalinsu ya tashi. Ya sake cewa.
"Duk wata allura da take sanya bacci anyiwa bawan Allahn nan amman yaki yi, banda ihu babu abinda yake yi.
"Dan Allah ya za'a yi mu ganshi?" Salima ta tambaya jikinta a matuƙar sanyaye.
"Bamu sani ba ko zaku iya shiga, amman dai ga likita nan bari a tambaye shi."
Likita na isowa wajan suka tambayeshi, harya hana sai yaga dai sun damu sosai, dan haka yace su bishi. Ai suna shiga duk suka ruɗe da ganin Yadda Jamil ya koma yasa Salima faduwa a gurin ta sume. Da yake akwai likita a gurin hakan yasa aka yi gaggawar samun kanta da taimakon shi. Tayi kuka domin tasan shima ta rasa shi, tasan mutuwa zai yi ya barta kamar yadda take ta rasa duk wasu makusantata. Sai gashi duk da irin ratattakewar da Jamil yayi Allah be dauki rayuwarsa ba, cikin sati guda ya fara kokarin magana ba tare da ihu ba, sai dai da taimakon oxygen, kuɗi kuwa duk akanshi suka kare saboda kokarin nema masa lafiya.
Idan kaga yadda Jamil ya koma duk rashin imaninka sai ka yadda cewa Allah ɗaya ne daga shi babu ƙari, babu abin bautawa sai shi guda ɗaya. Kyawun nan duk babu, idanuwansa sun tsiyaye fuska duk tayi damege. Ranar da ya cika sati a asibiti ne duk wasu ƴan uwanshi sukaje dubashi, Salima kuwa daman tana can tun randa sukaje. Jamil ya a ta faman kuka yana kiran Umma, babu wani abu da yazo bakinsa a wannan lokacin da ƴan uwansa suke ta faman yi mishi addu'a sukaji yace cikin muryarsa da bata fita.
"Umma.. Umma..." Kawu Bala yana ta cewa.
"Ka dena surutu ka dinga yin kalmar shahada, La'ilaha il'illah Muhammad rasulillah sallahu alaihiewasallam."
Amman Jamil ya kasa yi, gashi cikin zuciyar shi tamkar ana matse masa ita. Yana so ya yi amma ya kasa. Suna cikin wannan yanayi ne wata mata ta shigo fuskarta cike da hawaye, duk basu santa ba taje har kusa da gadon Jamil, cikin bakin ciki take cewa.
"Bakaga komai ba, wannan ba komai bane sai kaje inda kayi sanadiyar zuwan ɗana da kuma mahaifiyarka. Taɓewa ta tabbata a gareka Jamilu, kuma gashi karshe baka samu yarinyar da kake san mallaka ba. Jamilu ka daɗe kana samun nasara a duk lokacin da kake son abu. Amma karka manta uwa ba abar wasa bace. Mahaifiyarka kayiwa karkayi tsammanin kayi sanadin barinta duniya a banza, wallahi sai ka dauwama a cikin Jahannama, kuma da kai da masu son duniya bazaku shiga cikin alfarmar ma'aiki ba, mugu azzalumi."
Tana kaiwa nan ta juya ta kalli Salima wacce ɓacin ran kalaman tsohuwar nan ya ɓata mata rai. Takaici ya kama tsohuwar nan taja tsaki tare da dafa kujera.
"Da kinsan waye mijinki da baki wahalar da rayuwarki kina masa kuka ba, mijinki asararre ne, ke kanki be barki haka ba sai da ya cuceki ta hanyar cire miki mahaifa." Cikin tsananin razana Salima ta miƙe tana dafe kirji, tayi mamaki da taji maganar a bakinta domin babu wanda yasan wannan sirrin daga ita sai mijinta suka yi suka binne.
"Ke waccece?" Tsohuwar nan ta kalli mutanen cikin ɗakin, can kuma ta maida dubanta wajan Salima tana cewa.
"Kamar yadda kuke tunanin babu wanda ya sani, Toh