ya damu da yarinyar ba sai yanzu da yaga kiri-kiri yana neman ya rasata gaba ɗaya. Cikin ɗaki Ikram ta wuce Hanan kuma ta nufi inda yake tsaye, jikinta a matuƙar sanyaye ta kalleshi cikin sanyin muryarta tace dashi.
"Kana san Iman yanzu Yaya?"
Ya kasa cewa komai idan yace baya santa har yanzu bafa za'a bashi ita ba, zasu dage wajan ganin sun hanashi musamman ma Mamah da yaga ta dauki lamarin da matuƙar girma. Shi kuma yana so yai musu biyayya kamar yadda tun farko da suka bashi ita beyi musu dasu ba. Shi ba wani ji yayi yana santa ba, kawai dai yana so ne susan cewa har yanzu Iman tana matsayin matarsa.
"Shiru aka ce amsa ce ta 'eh' amman kuma kai na kasa yadda da cewar 'eh' ɗin kake nufi. Da gaske lokacin da ka yi saki kace ka maida auranku?"
"Hanan wacce irin gudunmawa zaki bani akan wannan matsalar? Kina ganifa Mamah yadda take dagewa akan cewa lallai na saki Iman babu wata maganar kome da nayi. Shin addini ya haramta mana yin hakan ne duk da cewa bamu taɓa ku....." Da sauri ya rufe bakinsa tunawa da yayi Hanan ce a gabansa ba wai aboki ba.
"Na gane abinda kake nufi fa, kawai ina so nasan da gaske kana san Iman? Idan ka gaya min zan baka gudummawa fiye da tunaninka."
Areef ya kawar da kai gefe, taya da auransa akan yarinya amman a dage sai yace yana santa? Da tambayarsa akai ne ko bashi kawai aka yi? Toh bazai faɗa ba sai dai suje su cinyeta, shi da yake da ƴan mata kamar a juji, banda ma an nesanta shi da Feenah shi ai yasan da yanzu ba wannan maganar ake yi ba. Hanan taja numfashi ta sauke a hankali, murya a sarke tace.
"Yaya Itafa soyayya sunanta kenan bata canzawa, idan har kana san Iman tabbas kana santa. Amman mai yasa ka nuna ra'ayinka akan wannan Feenahr ka kasa bayyanawa Iman? Iman fa matarka ce har yanzu a yadda kace, me yasa ba zaka faɗi abinda kakeji game da ita ba?."
"Kinga Hanan babu maganar wani ina santa ko bana santa, idan za'a maida ita shi kenan, idan kuma rike ta zasu yi fine."
"Yaya kaga samarin Iman kuwa? Wallahi masu aji ne, dan ma dai an samu ƴar matsala akan wani wanda ya kawo mata kuɗi..." Cikin fushi ya kalleta.
"Wai wane irin kuɗi aka kawo mata? Daman ana yin aure akan wani auran ne? Kuma da zaki ce samarin so fine ni zaki gayawa fine? Gaya min da abinda zasu fini Hanan, oya tell me please Hanan..." Yayi maganar yana kamo kafadunta da karfi. Kai ta girgiza ganin ya kasa fahimtar abinda take nufi, sai kawai ta zame hannunsa ta kalleshi tace.
"Kayi hakuri Yaya." Tana faɗa ta wuce ɗaki tabar shi a tsaye. Yatsa ya jiza ya sake bin ɗakin Mamah da kallo.
_________
Dogon numfashi Mamah ta sauke tare da jan ɗan ƙaramin tsaki, gabaki daya Areef ya hargitsa mata duk wani lissafi nata. Ya za'a yi ace ya maida auren amman besanar da su ba? Yanzu da ta auri wani meye matsayin auran da aka yi? Ta yadda cewar wani ya gani a ɗakin Iman tunda tasan an sako yarinyar a gaba, babban misalima gashi akan Jabir sun gani.
"Iman kinji abinda yace, meye ra'ayinki?" Iman ta shiga raba idanuwa, me zatace ita kuwa? Farin ciki zatai ko me tunda be saketa ba? Shiru ta kasa cewa Mamah komai har sai da tace.
"Shikenan bari Abban ku ya shigo sai muji abinda zai ce. Tashi kije karki sake kulashi."
Miƙewa tayi da sauri tabar ɗakin. Yana zaune shi kadai a falo jin motsi yasa shi ɗaga kai, ganin Iman yasa shi maida kansa ƙasa. Har zata wuce sai kuma ta saci kallon ɗakin Mamah, ganin babu alamar fitowa yasa ta saurin ƙarasawa gurin Areef ta tsaya daga nesa dashi murya kasa kasa tace.
"Zakaci abincin?" Banza da ita ya yi ta sake matsawa tana ɗan rankwafawa.
"Yaya naje na zubo maka?"
Ya miƙe tsaye tamkar zai bar gurin sai kawai taji ya ɗanki hannunta yaja ta zuwa waje, can wajan ɗakin Yaya Haneef ya tsaya tare da kallonta jikinsa har rawa yake yi yace da ita.
"Me zanyi ya tabbar muku da cewar har yanzu akwai aure na akan ki?"
"Sakar ni sai muyi maganar." Ta faɗa cikin basarwa.
"Ki gaya min tukunna." Ya kura mata yana jiran amsa.
"Nifa gaskiya ban gane nufinka ba, taya za'ai ka wani ce muna da aure? Ni karka wani canza min lissafi. Ina son Na auri babba wanda zai iya jure duk wani abu da zan yi mishi cikin sani ko akasin shi. Kuma ni gaskiya ina da tsarin auran cikakken namiji Yaya kayi hakuri kawai." Bakinsa buɗe tsabar mamaki yace.
"Ni rabin mutum ne?" Ta yatsina fuska.
"Gaskiya wanda ya fika shekaru nake son aura, kuma w....." Ai bata ƙarasa ba taji bakinsa cikin nata bayan ya manna bayanta a jikin bango.
Gabaki ɗaya guiwoyin Iman suka yi wani irin sanyi, yadda yake sarrafa harshensa cikin bakinta shine ya haddasa mata wata irin kasala mai matuƙar sanyaya gaɓan jiki, ta kasa komai sai wani irin numfashi da take saukewa. Shi kansa Areef kasa controlling ɗin kanshi yayi, duk wani noti dake jikinsa sai da ya kwance, ya riga ya shagala burinsa kawai ya isar da saƙon zuciyarshi. Basu san lokacin da suka zube a kasan gurin ba, romancing ɗinta kawai yake yi, barar da almajiri ya shigo parking lot yana yi shiya dawo da Areef cikin hayyacinsa.
Iman kuwa motsin kirki bata iya yi, gabaki ɗaya ya canza mata network ɗin kanta wanda yasa har lokacin da ya zare bakinsa daga nata ta kasa motsawa. Ya riko ta sosai zuwa jikinsa yana magana cikin mutuwar jiki yace da ita.
"Kina min kallon yaro ne? Kina min kallon bansan meye aure ba? Zan iya duk abinda kika san cikakken namiji zai yi. Kinga yanzu duk kin tayar min da hankali am in need some help, please Iman ina cikin buƙata please help me."
Ta kasa koda kwakkwaran motsi saboda jikinta a matuƙar mace yake, gashi ta kasa gane manufarsa gareta bare ta bashi amsa. Gani kawai tayi ya kwanta a kasan gurin babu ruwanshi da ƙasa ya janyota jikinsa tare da......💪
___________
Cikin gidan kuwa bayan Iman ta fito Mamah bandaki ta shiga tayo alwala, kayan bacci tasa doguwar riga mai laushi ta ɗebo takartunta da medical glasses ɗinta ta dawo falo ta zauna. Aiki Ta fara yi kafin ta kwalawa Ikram kira, ta fito hannunta rike da arba'una hadith ta zauna kusa da ita tana cewa.
"Mamah gani."
"Ruwa zaki kawo min, Iman taci gaba da karatun?" Ikram da mamaki tace.
"Ba kuna tare a ɗakin ki ba?" Bata dago ba tace.
"A'a ai ta fito tun ɗazu, bata ɗaki kenan?"
"Gaskiya bata shigo ba."
"Ina Areef?" Mamah ta tambaya cikin wani tunani.
"Uhmmm! Da kam yana nan a falo, da kika fito baki ganshi ba?"
Mamah tayi shiru mamaki na shirin kasheta. Kardai suna tare yaran nan? Lallai kam sun raina mata hankali, ina suka tafi ba tare da sun gaya mata ba? Kafin ta samu amsa suka ji motsi daga bakin kofa. Areef ne ɗauke da Iman a hannu ya yo mata ɗaukar jarirai, ita kam ko motsi bata yi. Cikin tsantsar matuƙar mamaki Mamah ta saki baki galala tana kallon shi har yaje ya kwantar da ita saman kujera, ƙala bece ba ya bar falon da sauri.........
(😂 Areefullah gayen nan ko? 🤣 hmmmm bari nai shiru kar su o'o su....)
https://youtu.be/qR81anYaPdQ SUBSCRIBE please
*Top 10 Takun haske batch A, in kina son karantawa ki tuntubi wannan numbers ɗin. 0706 528 3730 or +447894142004 for more information.*
*HAJJA CE 👈*
3/14/22, 19:45 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*
*31*
Ikram ce ta isa gurin da ya kwantar da Iman, ta kalleta sosai idanunta a lumshe, kallon Mamah tayi wacce ke zaune ta kasa koda kwakwaran motsi bare tasan abinyi. Jin muryar Ikram tana cewa.
"Mamah kizo ki ganta." Cike da takaici tace.
"Inga me? Babu abinda zanzo in gani tunda ta kai masa kanta. Banda ma dai sakarci da karancin tunani irin na Iman taya zaki aikata wannan dayan aikin? Toh kuwa kin siwowa kanki raini da wulakanci a gurin shi. An gaya miki ana yiwa namiji irin wannan abun? Mtwww wallahi da ina da hali sai na miki shegen duka Iman."
Iman najin faɗan da Mamah keyi amman taki motsi bare ta buɗe ido, yi tayi tamkar tana bacci. Ikram tai ta mata magana amman shiru bata amsa ba.
"Mamah bacci takeyi fa." Cewar Ikram tana wucewa dan dakkowa Mamah ruwa.
"Karya ne ba wani baccin da takeyi, kinibibi ne kawai da borin kunya." Mamah ta faɗa tana kuma sakin wani tsakin, duk ranta ya ɓaci saboda zargin abinda sukaje suka aikata.
"Mamah ga ruwan." Cewar Ikram tana miƙa mata.
"Maida shi Ikram wallahi naji sam banajin ƙishin, yaran nan duk sun ɓata min rai. Ke Iman tashi ki koma ɗaki kafin nazo nai miki tsinannan duka a gurin nan."
Ai kuwa taki koda motsi bil hakki ta nuna Itafa bacci takeyi, cikin fushi Mamah ta miƙe ta isa gurin tana kallonta. Ganin bakinta ɗan buɗe alamar da gaske baccin take yi yasa ta bubuga ta tana cewa.
"Tashi."
Iman ta daddage ta janyo juriya da karfi ta farka a zabure tare da riƙo Mamah tana furta.
"Subahanallahi Yaya please bana so....!"
"Ke bashi bane ki dawo cikin hankalinki." Iman ta ɗan kyalle ido ɗaya tana kallan Mamah, da sauri ta rungumeta tana cewa.
"Mamah na..."
"Na'am ya akai? Me Areef ɗin yai miki?"
"Ba komai Mamah wai shi a dole sai na yadda cewar matarsa ce." Cikin takaici Mamah tace.
"Keni duk ba wannan ba, sai kinje ya kunsa miki ciki bayan ba'a gama tabbatar da gaskiyarsa ba, yanzu da ya ɗakko ki shame-shame meya faru?" Iman ta shiga muzurai tana faman turo baki, batasan me zata cewa Mamah ba gaskiya, saboda lamarin akwai kunya.
"Bazaki gaya min ba sai na mareki?" Cikin kwantar da kai a jikin Mamah dake tsaye a gaban ta, Iman ta rintsa ido tare da cewa.
"Ki.. Ki.. Kis...." Ta kasa ƙarasawa cike da jin kunya kawai ta koma kan kujerar da sauri ta kwanta sai faman bubbuga ƙafafuwa take.
____________
Shi kuwa Areef ficewa yai daga gidan zuciyar shi na tafasa, mota ya shiga yajata, bai tsaya ko ina ba sai ƙofar gidan su Aslam. Yayi parking a hankali ya fito ya shiga gidan kai tsaye. A kitchen yaga Umma suka gaisa cike da mutuntaka sannan yace.
"Umma Aslam fa yana ina?" Sai da ta ajiye plate ɗin hannunta kafin tace.
"Aslam kuwa tun ɗazu ya fita bai dawo ba, ka kirashi a waya?"
"A'a daman cewa nayi bari nazo kila yana nan, amman bari naje majalisa kila yana can."
"Toh shikenan Areef a gaida mutanan gidan." Ya amsa tare da ficewa daga gidan.
Wajan motarsa ya tsaya tare da kifa kai, duk ya rasa madogara, gashi ko lambar Aslam ɗin bashi da ita sakamakon layi daya canza. Gashi yanzu yazo bashi da wata manufa. Kasancewar ya kifa kai jikin motar yasa bema san da tsayuwar mutum ba, ji yayi an masa sallama ya dago a hankali. Aslam na ganin Areef yaja tsaki zai shige gida saboda gabaki ɗaya Areef ya canza musu baya nemansu tun da ya tafi Abuja. Da sauri Areef ya rikoshi tamkar zai fashe da kuka yace.
"Am so sorry abokina, please forgive and forget dan Allah dan Annabi." Yana magana yana rungume shi cikin bada hakuri.
"Kai wallahi ka bani mamaki, daman har akwai abinda zaka samu a duniyar nan ka juya mana baya Al-Mustapha? Look ni duk ba wannan bama ashe sai da kayi yadda zakai ka saki Iman ko? Mtww ja gefe malam ka bani hanya na wuce."
Yasan dole suji haushinsa akan sharesu da yayi, amman yanzu ai ya dawo, jiki babu kwari ya riko hannun Aslam yana ta magiya kafin yace yazo su shiga daga cikin ɗakinsa. Daman abinda Areef yake so kenan, suna shiga ya samu guri ya zauna tare da kwantar da kai gefen wata loker sai faman cizon yatsa yake yi.
"Bari na samo mana abinci a cikin gidan." Areef yaja numfashi yace.
"Okay thanks." Daga haka ya fice daga ɗakin shi kuma yaci gaba da jiransa. Dawowa yai dauke da alkubus da miya ya ajiye a gaban Areef yana cewa.
"Bari na samo mana Lemo da ruwa a can shagon." Areef ya sake cewa.
"Okay ba damuwa."
Ba daɗewa sai ga Aslam ɗauke da leda ya siyo musu ya ajiye kusa da abincin. Sai da ya rage kayan jikinsa kafin yazo ya zauna yana cewa.
"Sakko muci."
Areef ya sakko duk da cewar yama denajin yunwar, amman dan kar Areef yaji babu daɗi yasa shi sakkowa suka faraci.
"Wai bakada lafiya ne?"
"Kusan haka wallahi."
"Oh ba tabbas kenan?''
"Aslam wallahi har yanzu da auran Iman a kaina, nayiwa Mamah bayani taki amincewa nema take tace yanzu Iman tafi karfi na wallahi." Aslam ya kallesa cike da mamaki tare da cewa.
"Aure? Kaida Iman ɗin ne kuke da aure? Kai dalla tafi can, ko ka fara shaye-shaye ne.?" Ya faɗa yana maida hannu ya dauki ruwa.
"Hmmmm wallahi shi yasa yanzu naso na karɓi hakkina, kawai akai rashin sa'a yarinyar nan tana under menstruation." Aslam ya gwalalo ido jin abinda abokin nasa yake faɗa.
"Kai! A gidan naku zaka hike mata?"
"Toh sunki yadda cewa matata ce, itace kawai hanyar da zanbi dan na tabbatar musu da cewa matatace."
"Amman wallahi baka da sense, kai! Tab da kayi kuskure wallahi dan da kyar idan iyayenta zasu kyaleka. Kuma ka manta dalilin da yasa akai maka aure? Ganinka da Feenah ne, yanzu idan ka yiwa Iman duka zakaci saboda zasu yi tunani iskancin naka ne ya motsa." Jan munfashi Areef yayi tare da ɗaukar cokali ya faracin abincin.
"Feenah fa tayi aure." Abinda yaji Aslam ya faɗa kenan, furucin nasa kuma sai yaji sam be dameshi ba. Sai cewa ma yayi.
"Masha Allah ina mata murna, a ina tayi auran?" Tsabar mamaki yasa Aslam tuntsurewa da dariya yace.
"Wai dan Allah bakaji komai ba da na gaya maka?" Areef ya yatsina fuska.
"Wani abun zanji? Kace tayi aure nima ai nayi ko?"
"A'a aka yi maka dai ɗan rainin wayo, kuma ai yanzu dani da kai duk ɗaya muke, baka da mata bani da ita."
"Wallahi karya kake ba ɗaya muke dakai ba, ni ko yanzu naga damar kwana da matata toh tare zamu kwanta, kai kuwa daga kai sai katon filo, gashi nan ma sabo ne kaje ka siyo." Aslam yace.
"Naji, amman ai ko kun kwana babu abinda zaka iya tsinanawa tunda period take. Feenah kuma tana gidan wani."
"Dan Allah ka dena yi min maganarta, yanzu fa ni ba yaro bane ina da iyali. Nida Feenah soyayyar yarinta mukai, har muke jin idan bamu auri juna ba akwai matsala, ni kam yanzu ne nake jin muhimmancin iyalina wallahi." Yayi maganar iya gaskiyarsa. Yaji ya tabbatarwa da zuriyarshi cewar auransu da Iman yana nan daran-dam, dan gani yake yanzu da ya ganta shine take a matsayin matarsa ba da ba da yake yi mata kallon ƙanwarsa da suke same Ma same Pa.
"Woww abokina, gaskiya ka burgeni wallahi, amman dan Allah yaushe kayi hankalin nan duk bamu sani ba? Azato na idan kaji labarin auran Feenah zaka damu sosai sai kuma naga saɓanin haka."
"Da kana min kallon mahaukaci ko?" Areef ya tambayesa cikin bacin rai.
"A'a ni bakaji haka daga gareni ba, oya muci abinci yau ka wanke duk wani laifinka a zuciyata."
"Yauwa toh tunda na wanku dan Allah dan Annabi ka tayani nunawa su Mamah cewa auran nan yana nan dan Allah kayi min wannan alfarmar Aslam." Sai da Aslam ya yi murmushi kafin ya kallesa yace.
"Sha kuruminka ka kyale su Mamah, mu muje mu kama kafa da asalin iyayen Iman ɗin." Cikin rashin fahimta Areef yace.
"Ban gane ba, su waye asalin iyayen nata?" Aslam ya gyara zama tare da cewa.
"Iman da kake yi mata wani irin kallo, kake tunanin ba ta hanyar aure aka haifeta ba, kwanaki iyayenta suka zo suka gabatar da kansu." Duk yadda Iman ta bashi labari haka ya kwashe ya sanar da Areef, ya kara da cewa.
"Nasan kauyan idan ka shirya lokaci sai muje na rakaka mu nemo gidan." Cikin tsananin farin ciki Areef ya saki wani kayataccen murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillahi, gaskiya naji daɗin wannan labarin, idan baka komai gobe muje dan Allah saboda ran Alhamis zan koma gurin aiki."
"Babu damuwa Allah ya kai mu goben." Ya amsa da.
"Amin." Daga nan suka ƙarasa cin abincin sukaci gaba da hirar duniya.
____________
"Tunda ba zaki faɗa ba shikenan, amman bari na gaya miki, wallahi idan har kika biyewa Areef a haka baki tsaya an ƙwato miki hakkinki ba zaki sha mamakin ɗa namiji."
"Assalamu alaikum." Abba yayi sallama suka amsa, ganin su tsaye yasa shi ƙarasawa wajan yana tambayar abinda yake faruwa. Wata irin azababbiyar kunya ta luluɓe Iman wacce dama can a kwance take sai ta sake curewa guri ɗaya.
"Ita da Areef ne." Cewar Mamah cikin takaici.
"Areef kuma? A ina suka hadu? Kuma me yayi mata." Abba ya faɗa cike da son jin abinda yake faruwa.
"Zuwa yayi yana ta kumfar baki wai shi be saketa ba, wai a ranar da ya yi a bara ya maida auran kaji fa?" Wani kayataccen murmushi Abba ya saki, kai daka gani kasan yaji daɗi sosai.
"Ashe dai yana da sauran hankali? Masha Allah gaskiya naji daɗi da har yanzu akwai auran nan tare dasu. Ina yake Areef ɗin?"
"Alhaji kana nufin kace ka yarda dashi?" Mamah ta tambaya cikin mamaki.
"Ahhh toh Hajiya mu muye namu a ciki? Idan ma karya yake yi wannan tsakaninsa ne da ubangijinsa babu ruwan mu a ciki."
"Amman gaskiya Alhaji b..." Yayi saurin dakatar da ita,
"Kinga Hajiya wai meye naki a ciki ne? Bana san yawan maimaita ba, suje su sasanta kansu kawai."
"Yo wane sasance bayan ya gama abinda yaga dama, zuwa yayi yajata, ina yakaita oho taki faɗa haka ya shigo da ita raɓaɓe-raɓaɓe a hannu ya dire ta anan ya fice, waya sani ma ko ya koma Abujan tunda ya samu abinda yake so." Tsab Abba ya gane inda maganar Mamah ta nufa dan haka ya kuma yin murmushi yace.
"Shi yasa nake so ki cire hannunki akan lamarin mata da miji, idan ba haka ba su sa kiji kunya