kuma haihuwa. Wallahi Jamil hankalina a tashe yake, ji nake kamar shima Amir zai mutu yanzu." Kuka ya kuma suɓuce mata tana saman kirjinsa yana bubbuga bayanta.
"Kidena damuwa, waye kike tunanin zai yi miki gori dan baki da yara? Ba dai nine mijin naki ba?" Ta ɗaga masa kai alamar 'eh' Yace.
"Toh ni bazan taɓa yi miki gorin ƴaƴa ba tunda nasan nine bana son su da yawa. Ba kuma zan iya rabuwa dake ba sai dai mutuwa. Ki dena kuka."
Da waɗannan kalaman Jamil ya samu Salima tayi shiru, sai fa zuciyar ta taƙi nutsuwa akan wannan lamarin, ta kasa yadda Amir zai rayu tare dasu kamar yadda take mafarki. Sun jima a ɗaki kafin ya fito yaje ƙofar gida inda yan uwa maza ke zaune. Sai da aka yi bakwai sannan yace zai koma Kano saboda akwai wani aiki da zai ƙarasa. Yayi sallama da kowa ya dawo kano bayan yaje ya biya kuɗin baƙaƙen akuyoyin da bokansa yace za'a yi amfani dasu. Abinda kawai ya rage masa shine sahun ƙasar da Iman ta taka, wanda ya rasa yadda zai yi ya samu.
_______
Da sallama ya shiga cikin falon, bai shiga ba ya tsaya daga bakin kofa yana jiran ayi masa iso. Mamah ce ta fito daga kitchen tana amsa sallama da ake yi. Tana ganin Jamil mamaki ya kamata, alamar haka da ya gani ne yasa shi yin murmushi tare da gaishe da ita. Daurewa tayi tace dashi.
"Shigo ka zauna mana Jamil sai kace wani baƙo." Ya ƙarasa ya zauna akan kujera yana sake gaida ita cike da alkunya.
"Baka tafi Zamfarar ba kenan?" Mamah ta tambaya tana kallonsa.
"Tun a ranar na koma Mamah, yau na dawo kawu na ne dake nan kano jiya aka kiramu aka shaida mana cewa Allah ya yi masa rasuwa, shine muka zo nace bari na ƙaraso mu gaisa naji ya jikin Iman kuwa." Murmushi tayi tare da cewa.
"Da sauki za'a ce, sai dai tun bata iya takawa da batajima bata magana. Amman yanzu alhamdulillahi bakin ya dawo tana kuma ji sai dai ba tafiya har yanzu."
"Subahanallahi! Wannan wane irin abu ne yake damunta? Amman Mamah baku tunanin ko dama can tana da aljanu?" Ya tambaya cike da nuna damuwa akan lamarin.
"Toh waya sani Jamil? Mudai tunda muke da ita bata taɓa yin iskokai ba, idan ma tana dasu toh basu taɓa tashi ba sai randa aka daura mata aure da Areef."
Jin kalmar daura aure da Areef yasa Jamil rintsa ido yana cizon leɓensa na sama. Da kyar ya iya daurewa ya dago cikin raunana fuska shi a dole ga wanda lamarin ya taɓawa zuciya, yace cikin damuwa.
"Kuma Mamah kunje asibiti?" Mamah taja numfashi ta sauke.
"Ai lamarin sam bana asibiti bane Jamil, mundai kaita wajan wani malami ya bamu taimako shinema har aka samu baki da kunnen suka buɗe. Kafar ce dai itama kuma wani lokacin Iman ɗin takan ce taji kamar zata iya, amman idan tazo gwadawa sai ta kasa."
Tunda ta ambaci malami Jamil ya shiga gyaɗa kai yana taune leɓe. Su Hanan suka shigo, gaishe dashi suka yi basu tsaya ba suka shiga cikin ɗaki. Tararwa suka yi Iman ta faɗo daga kan gadon tana jan ciki zata fito waje. Cikin daga murya Ikram ta kirawo Mamah sai gata da gudu.
"Ina zaki kuma Iman?" Ta dago tana kallon Mamah still bakin yaki buɗewa bare tai magana. Ganin tana ɗaga kai yasa Mamah saurin ɗagota tana cewa.
"Bakin ne kuma ya rufe?" Iman ta ɗaga kai.
"Subahanallahi yanzu fa na barki a ɗaki muna hira Iman." Ɗaga kai ta shiga yi kafin hawaye su biyo baya.
Kan gado ta maida ita ta dakko rubutun da ake bata tasa mata a baki amman taki sha.
"Sha mana Iman, rubutu ne fa." Still ta kawar da kai tana gumtse baki.
"Bari muyi sallama da Jamil." Mamah ta faɗa tare da tashi ta fito falon. Yana zaune a inda ta barshi.
"Yanzu zaka koma ne Jamil?" Yaji tambayar tamkar saukar ruwan sama. Cikin dakiya da jarunta ya daure yace.
"A'a zamu ɗan kwana biyu Mamah."
"Ayya a wace unguwa aka yi rasuwar, saboda idan mun samu dama mu bullo muyiwa ƴan uwan naka gaisuwa. Gashi ɗakin abokin naka an fara kwalema za'a rushe a gyara."
'Wannan yana nufin ba gidan zai zauna ba kenan? Kuma wace unguwa zai ce musu bayan karya yake yi ba mutuwar aka yi ba. Ya kakalo murmushi yana gyara zaman hularsa yace.
"Kai Mamah an hutar daku, waye zai janyo muku tafiya mai nisa gaki da marar lafiya. Doguwa local gwammant ai ba nan bace." Cikin fitowa da idanu Mamah dafe da haɓa tace.
"Tun daga can kazo nan?" Babu kunya bare tsoran Allah yace.
"Wallahi kuwa Mamah. Toh dan kawai Sa'id (Haneef) baya nan sai kawai naki zuwa duba halin da kuke ciki? Ahhh no..no..no indai muna cikin kano zamu zo duba lafiyarku."
Cike da jin daɗi Mamah ta shiga yi masa godiya yana cewa ta dena su kawai albarka suke nema. Ya tashi tare da zura hannu cikin aljihu ya zaro kuɗi dubu ɗari a kyauran su a ajiye akan kujera yana cewa.
"Gashi Mamah ba yawa."
"A'a Jamil karmuyi haka dakai dauki kuɗinka, ni wallahi zuwan da kai ya isa." Sai ya kuma zura hannu cikin daya aljihun ya zaro dubu gomar da ta rage ya ajiye yana cewa.
"Toh Mamah kaɗan suka yi kenan, gashi toh a gaida Abba idan ya dawo." Ya sake direwa ya bar gidan cikin sauri.
Gaba ɗaya sai ya bar Mamah cikin mamaki, taya za'a ce da saka hannun Jamil cikin wannan lamarin na Iman? Gaskiya ba daidai bane kawai hasashen Areef ne daman kuma shi baya kaunar yaga wani yazo gidan da sunan zama koda na kwana guda ne. Tayi bismillah tare da daukar kuɗin ta koma cikin ɗakin. Iman nata kuka kamar wacce ake duka, su Ikram sai bata hakuri suke yi, babu wanda ya gane cewa gurin Jamil take son zuwa.
"Tasha rubutun kuwa?"
"A'a turewa ma tayi ya zube." Cewar Hanan.
Ƙarasawa Mamah tayi gurinta tana yi mata addu'a tana shafa bayanta har tayi bacci a haka, kwantar da ita tayi tasa mata filo. Hanan ta tambaya.
"Mamah wannan kuɗin fa daga ina?"
"Jamil ne wallahi."
"Kai duka ya baki Mamah.?!" Ikram ta tambaya tana jujjuya kuɗin.
"Eh wallahi. Allah dai ya saka da alheri yana da kirki tun daga doguwa yazo ya gaishe mu ya kuma duba jikin Iman."
"Allah sarki, gashi Iman tana son shi. Dama ace kawai Yaya Areef ya rabu da ita ta aure shi tunda shi take so." Ikram ta faɗa Mamah ta zabga mata harara tare da cewa.
"Kudai wallahi wawaye ne, waye zai auri Iman yaki yi mata gori bayan komu kanmu bamu san suwaye ahalinta ba? Kuma itace take son shi ba wai shi Jamil ɗin bane ya faɗa kunga kuwa akwai matsala idan har aka yi auran. Areef kuwa koya wulakantata ba zamu bari ya saketa ko yaci zarafinta ba."
Basu sake cewa komai ba sai aiki da suka ci gaba da yi.
__________________
Jamil kuwa yana fitowa daga gidan ya ciro waya yana kiran bokansa bata shiga, a kalla ya kira yafi sau ashirin ana cewa not rechargeable, sauran kaɗan ya yi cilli da wayar wani mai mashin yai masa horn ganin ya tsaya a hanya. Matsawa yayi can gefe yana sake ci gaba da kira ko Allah zai sa ta shiga. Duk ya kasa nutsuwa saboda ya kasa samun shi, so yake ya sanar dashi halin da ake ciki ko akwai wata hanyar da zai samu ƙasar. Hotel ya kuma zuwa ya kama, gumin da yake ta yi ne yasa shi yin wanka yana fitowa ya tsakuri abincin da aka kawo masa.
Sai kusan gab da magariba sannan ya samu wayar ta shiga. Tas ya sanar da shi abinda Mamah ta gaya mishi na halin da Iman take ciki, ya kare da cewa.
"Ina son a warware na riƙe kafar nan da bakin da kunne, idan na samu ta fito na samu ƙasar sai mu nemo wata hanyar wacce zata ZO GARENI ba tare da anyi mugun tunani akai na ba."
"Toh shikenan za'a warware, amman sai kaci soyayyan mushen ɓera saboda gashinta da ka haɗiya."
"Ɓera kuma?" Ya tambaya cike da ƙyanƙyame.
"Kwarai kuwa, domin dashine akai aikin."
"Shikenan zan san yadda za'a yi." Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.
"Idan ka gama komai muna jiranka."
"Zanyi a gobe idan Allah ya kaimu."
Suka ajiye wayar yasa kaya ya fita. Wata makarantar almajirai yaje ya samu wasu su biyu yace yana son matattun ɓeraye, su nemo mishi gobe zai dawo ya karɓa. Ya basu ɗari biyar yace idan sun samo gobe zai kara musu wasu kuɗin. Suka dinga murna saboda kawai zasu samo ɓera shine aka basu ɗari biyar, gashi idan sun kawo ance za'a kara musu, kuma bawai ɓeraye da yawa ba a'a guda ɗaya rak. Jamil ya koma hotel kiran Salima yayi suka jima suna hira kafin ya ajiye ya shiga tunanin yadda zasu yi sabuwar rayuwa da amarya Iman......
(Hello Jamil fan's 👋Wani abun sai mugu)
*More garaɓasar TOP 10 akan kuɗi Naira 500 kacal, kiyi register da TAKUN HASKE domin samun garaɓasar ƙayatattun littattafai har guda 7, tare da wasu manyan shirye-shirye har guda uku. ƴar uwa daga jin wannan takun ba irin waccan tafiyar bane, a top 10 class ne kaɗai zaki nishaɗantu, ki ilmantu. Maza garzaya ki saka kuɗin ki a inda ya dace domin koyo da sanin abubuwan da suka dace..... Kar ku manta da kuɗinki ƙalilan zaki kwashi kasiran. 500 kacal......Don't miss this opportunity*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya ta wannan number👇🏼👇🏼*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
*HAJJA CE 👈*
3/2/22, 19:49 - Buhainat: *ZO...GA...N...*✍️
*Wattpad:- Hajjac*
*Top 10 Takun haske batch A*
*HAJJA CE 👈*
*23*
A daran ranar Abba na dawowa daga asibiti cike da murna da farin ciki, sai da yaci abinci ya koshi saboda tunda abubuwan nan suka fara faruwa baya iya cin abinci mai nauyi sai yau. Mamah ta fito daga ɗaki ta baro su Ikram a wajan Iman, kusa da Abba ta zauna itama tana ɗan murmushi tace dashi.
"Naga sai fara'a kake yi kamar wanda aka yiwa albishir da gidan aljanna, meye labarin?" Abba ya sake faɗaɗa murmushinsa tare da cewa.
"Wani farin ciki ne ya riskeni ɗazu a asibiti. Ina Alhaji Sammani mai shanu? Kin ganeshi?"
"Kwarai kuwa na sanshi, ba wanda yace ka shiga harkar siyasa ba lokacin da mukaje biki gidan Shazali minister?"
"Kwarai kuwa shi, kira na yayi ɗazu yana ƙorafin wai na aurar da yara amman ban sanar dasu ba. Shine nake sanar dashi ai auran ne aka yi cikin gaggawa yaron ma ko karatu baici gaba dayi ba, nake sanar dashi aiki nake son samar masa ta yadda zai riƙe kanshi da matarsa. Wallahi Hajiya ina gaya miki sai yace min Toh na tura yaron can Abuja za'a yi masa interview, kuma idan an dace ya haye zai samar masa gidan da zai zauna a can."
Dai-dai lokacin Areef ya shigo falon yana sallama. Mamah kuwa sai murna rake tana guɗa dan ba ƙaramin farin ciki suka yi ba. Abba ya kira Areef ganin zai shige ɗaki, ya juyo kansa a ƙasa ya tsugunna yana sosa keya.
"Ka shirya komai yau, gobe idan Allah ya kaimu zamuje Abuja." Mamaki ya kama Areef.
"Aiki za'a samar maka kayi addu'a Allah yasa alkairi ne."
Jin ance aiki za'a samo mishi yasa shi yin murmushi, murmushin da idan yayi yake kuma ƙara masa kyau da kwarjini sai dai be fiye yi ba idan har ba abinda yake so ya samu ba.
"Abba a ina?" Ya tambaya cike da zumuɗi.
"Sai munje can tukunna zamuji. Alhaji Sammani abokina ne tun a firaimari, yayi kuɗi amman har yanzu bai manta damu tsofaffin abokai ba."
Farin ciki ya cika zuciyar Areef, wai shine zai fara samun aiki tun bai yi karatu mai zurfi ba. Koda dai kasuwanci ne ya kuma ji daɗi ko babu komai zai dinga samun kuɗin kashewa ba sai ya yi ƴar murya gurin Mamah ba. Tashi yayi ya nufi ɗakinshi, kan gado ya faɗa ya shiga mirgina-mirgina kamar yaro ƙarami. Ya fara hango kanshi a matsayin babba, sai kirewa su Aslam a komai.
Can kuma Mamah ce ta nunawa Abba kuɗin da Jamil ya bayar, shi kansa ya sake yabawa da mutunci irin na Jamil musamman da yaji cewar zuwa yai ya duba lafiyar ƴarsu. Sai yaji baya wani zarginsa akan matsalar Iman da take cewa shi zata aura, ya kuma tabbatar da cewa aljannu ne suke sata faɗar hakan. Suka taɓa hira sannan ya koma ɗaki itama Mamah ɗaki ta wuce saboda tun faruwar al'amarin bata kwana ɗakin Abba.
*WASHE GARI....*
Da wuri Abba da Areef suka shirya su Mamah suna ta yi musu fatan alkairi, har wajan mota suka raka su, sai da sukaga tafiyarsu sannan suka koma ciki. Suna zaune Hajiya ta shigo, su Ikram suna ta zolayarta irin wasa da jikar nan. Can ta nutsu ta kalli Mamah cikin serious ɗinta tace.
"Ku fito Muje can ƙauye, yanzu nasa aka kira min mai gidan naki na sanar dashi zuwan mu ƙauye yau, kwana biyu zamuyi sai mu dawo."
Mamah dai bata so zuwa ba amma babu yadda zata yi dole ta amsa da toh. Suka tashi suka shirya Uncle Imran yazo ya ɗauke su suka tafi.
___________
Wahalallan baccin da Jamil yayi shi ya hanashi fita da wuri. Alwala ya yi yaje yayi sallah a lokacin ƙarfe tara da kwata, wannan makarar ba wani abu bane a gurin Jamil domin a yadda malamansa suke cewa ƙin yin sallah gaba ɗaya shine babban laifi a gurin Allah, amman zaka iya yi a duk lokacin da ka tashi. Tsab ya shirya cikin shadda brown ya ɗora hula, idan ka kallesa ba zaka taɓa cewa zai iya kashe kiyashi ba saboda tsabar kamalar da ta baibayeshi.
Kai tsaye inda yace da almajiran su tsaya ya nufa, cikin sa'a ya tarar dasu sai leƙe-leƙe suke alamar suna nemanshi. Yayi mamaki da suka gane shi, saboda jiya da daddare suka hadu. Da gudu suka nufeshi hannunsu rike da leda wacce yana ganinta yaji tashin zuciya. Kamar yadda yace musu haka suka yi wato su yanko shi. Karɓa ya yi tare da basu dubu biyu suka dinga zabga godiya kamar zasu yi masa sujada. Tafiya ya yi mai ɗan nisa inda ba za'a ganshi ba, ya buɗe ledar ya leƙa yana toshe hanci da ido. Wallahi banda ya kwallafawa Iman rai da ba zai yi wannan abin ba. Ya ɗakko ɗaya yasa a baki yanaci yana kakarin amai ga hawaye da zuke zubowa daga cikin idanunsa, yana hadiyewa yasha ruwa, sai amai tamkar mai laulayin ciki.
Sai da ya amayar da komai sannan ya tashi da kyar ya tsinko ganyen darbejiya guda biyu yasa a baki ko zaiji relief. Wayar malamin ya kira bugu ɗaya ya ɗauka, tun kafin yayi magana yaji malamin yace.
"Wannan ya wargatse sai wanda za'a yi nan gaba. Ka ɗakko baƙaƙen akuyoyin da mukace, sannan ka taho da ƙasar wace itace abin buƙata a aikin da za'a yi."
"Amman kuma malam ai ban iya cin ɓeran nan, gaba ɗaya wanda naci ma na amayo shi t...."
"Ya isa Jamilu, daman abinda muke bukata shine ya shiga bakinka da cikinka, ya yi kuma har aikin ya warware, da anyi wannan aikin Iman ta zama mallakinka."
Jamil ya saki murmushi tare da ɗaukar ragowar ɓeran ya cilla shi. Mota ya koma yaja da nufin zuwa gidan su Iman bayan ya gama tsara abinda zai faɗa musu a zuciyar shi. Sai dai yana zuwa ya tarar da gate ɗin a kulle harda kwaɗo, alamar basa ciki. Hankalinsa yai mugun tashi da sauri yaje gurin wasu dake zaune a wajan bishiya ya tambaye su, suma suka tabbatar masa da basu san inda suka tafi ba, amman tabbas sunga fitarsu a mota.
Jamil ya shiga cikin tashin hankali da damuwa, kaɗan ya rage ya saki ihu. Mota ya koma ya kira malam ya sanar dashi.
"Karka damu ka bari ko nan da kwana nawa ne idan sun dawo sai ka samo mana ƙasar."
"Amman kuma malam duk harkokina sun tsaya cak saboda wannan lamarin, ina son na koma aiki na."
"Yanzu aikin naka kafiso ko yarinyar kake son mallaka?" Malam ya tambayeshi cikin kakkausar murya.
"Ina son yarinyar."
"Toh sai ka ƙarasa aikinka."
"Zan kawo maka a ranar da suka dawo zanyi duk yadda zanyi ta fito."
Katsewa suka yi daga nan kowa yaci gaba da abinda yake gabansa.
*ƘAUYE....*
Suna dira kauyen abinda ya basu mamaki bai wuce ganin Iman ta taka da ƙafarta ba. Sosai suka yi matuƙar mamaki da wannan al'amarin kafin murna da farin ciki ya mamaye zuƙatan su. Awannan lokacin ne Iman ta dinga jinta fresh kamar yau aka haifota. Tun a hanya Ikram take labarta mata irin abubuwan da ta dinga yi har yadda ta shaƙe Areef tace sai ta kashe shi.
Suna zaune a ɗakin Gwaggo Safiyya Iman na ta kallon Mamah tamkar a yanzu ta fara ganinta. Mamaki ne yake damunta na cewar wai ba ita ta haifeta ba, tsintarta aka yi cikin tsumman Zani. Toh wai shin ita ɗin wacece? A ina take? Suwaye ahalinta? Menene dalilin da yasa aka jefar da ita?
Tasa bayan hannunta tare da share hawayen da suka zubo. Ɗan guntun murmushi tayi lokacin da taji Mamah ta nayi mata magana.
"Auta mai kike son ci?"
Wannan kalmar ta 'Auta' da Mamah ke kiranta dashi, yau sai taji sam basu dace da ita ba, ta juya ta kalli Ikram a ranta tace. 'waccen itace autarki Mamah' ni waye yasan ko ta nawace a gurin iyaye na? Waya sani ma ko babu aure aka haifeta tunda yarda ita aka yi babu ko ɗan Pant.
"Iman tunanin me kike yi?" Tai saurin sunkuyar da kai.
"Mamah ba komai."
"Inata tambayar me zakici kinyi shiru."
"Na koshi Mamah."
"A'a ban yadda ba, mekika ci da zakice kin koshi? Ko wani abin ke damunki yanzu?" Tace.
"Kaina ke ciwo Mamah."
"Subahanallahi bari na samo miki magani." Gwaggo Safiyya tace.
"Muna da magani na gargajiya, kuma naga alamar shawara tana damun yarinyar ji yadda take wani yalayalo korekore. Haka zaku kaita gidan mijin babu wani gyara?"
"Yo Gwaggo wane gyara za'a yi mata? Kina ganinta fes." Cewar Ikram.
"Toh karku yi shi Mustaphan (Areef) ce muku akai baya son gayu? Kodan kun ganshi