Zo Gare Ni Inda Zuciya Ta Sami Mafaka By HAJJA CE

Author :  HAJJA CE Category :  Romance

Chapter   4 / 38

9K to 12K   out of 113.7K words

yasa yanzu ta fara sakkowa harda gudun mawar murmushi.

Ya karaso kusa da ita tare da mika mata kayan ya kai mata sumba a gefen kumatunta na hagu tare da furta.

“Ina son ki Feenah.?

Muryar Sultan ta katse mata tunanin da ta fad'a ciki, nan da nan ta ɗago tare da kallansa, ganin yana mata kallon kurrulla yasa ta juya masa baya tana jan d'an karamin tsaki. Ganin zata dawo normal yasa shi barin ɗakin shima yaje ya yi wankan ya shirya cikin kananun kaya jeans da riga armless sai zuba k'amshi yake yi. A kwance ya sameta kan gado tana faman danna iPad d'in ta, duk da taji shigowarsa hakan be sa ta kallesa ba bare taga a yanayin da yake ba.

“Zanje na dawo, idan kina son wani abun ki min text message.?

Feenah tayi masa banza kamar ba da ita yake ba, a ransa yace 'ta dawo hayyacinta gashi nan ta dora ma a inda ta tsaya' ya juya tare da ficewa ya barta. Ita kuma ta juyo tana bin kofar da harara cike da jin wata zazzafar tsanar shi a zuciyarta.

Tun daga wannan lokacin Sultan yake amfani da kwayar sanya bacci yana tarayya da matarsa Feenah, duba da yadda bata amince masa yasa shi zabar wannan hanyar wajan ganin ya biya buk'atarsa akan ta.

Ga wata kulawa ta musamman da Sultan d'in yake nuna mata, duk iya rashin mutuncin da zata yi masa baya daga kai ya kalla bare har ya dame shi. Ana cikin haka ne ta fara laulayi wanda ta rasa ko na menene, ga kasala da yawan kwad'ayi musamman na manja da yajin tafarnuwa.

Duk lokacin da tace masa ya kaita asibiti sai yace mata to amman ba zai kai ta ba, ya zamana ko school ba ta iya zuwa saboda yawan bacci da amai. Ranar wata Monday ne ta takura masa akan ita sai taje makaranta saboda ana ta yin abubuwa bata nan, daman ya santa da kafiya sai ya ɗauke ta suka tafi, ta shiga ajin su ƙawayenta suna ta tsokanar ta akan cewa tayi kiba tayi kyau na musamman. Ita dai kawai tana jin su bata ce komai ba har aka tashi. Cikin sauri ta nufi motar su kawarta Amal tace dan Allah tana son su ajiye ta a asibiti.

Suka ɗauke ta kuwa suna tafiya sai ga sultan yazo daukarta. Ya sha zama da dube-dube amman babu ko mai kama da ita. Feenah kuwa tana can tana ƙoƙarin ganin likita, da yake tana da experience a ilmance ta dinga yin komai har ta samu ta shiga office d'in Dr Sharif, wanda shima ɗan asalin Nigeria ne karatu yazo ya kammala har ya samu aiki a can ya yi aure harda yarsa guda daya. Sai da ya gama rubuce-rubucensa kafin ya dago ya kalleta.

“Yan mata lafiya dai ko??

Feenah taja numfashi mai tsayi kafin ta fashe da kuka, Dr Sharif ya tsaya yana binta da kallon mamaki. 'Ya daga tambaya sai kuka kamar dai dama jira take yi ya tanka mata? Sai dai ganin ta da kuma auna shekarunta da ya yi ne ya sa mamakin nashi sauyawa, zata Iya yin fiye da haka ma kasan cewar har yanzu bata wuce tana gaban iyayenta ana kulawa da ita ba.

“Kiyi hakuri ki sanar dani abinda yake damunki kinji little girl.?

Bayan hannunta tasa ta shiga share hawayen tare da sanar dashi duk abinda yake faruwa da ita, hatta yanayin bacci da farkawa taji kasanta na zafi duk ta sanar dashi, inda ya tambaye ta cewa.

“Aure aka yi miki ne?? Ta gyada kai alamar eh.

“Toh yanzu Ina mijin naki?? Ragowar hawayen suka ƙarasa zirarowa ta ce.

“Baya nan.?

Rubuce-rubuce Dr Sharif ya yi sannan ya kuma ɗagowa ya kalli Feenah cike da kulawa yace.

“Amman ai kinsan cewa idan akai aure namiji ya kusance ka dole zaka Iya samun ciki ko.?

Gyada kai tayi a iya fahimtar da ta yiwa maganar Dr. Yaci gaba da cewa.

“Toh ke tunda ya aure ki kun daɗe be kusance ki ba?? Tace.

“Ai bana kulashi, Iya Kaci ya kai ni makaranta ya dawo dani ko magana bana son ya yi masa saboda ni bashi nake so ba aka aura min.?

Cike da ɗinbin mamaki Dr Sharif ya kuma kallonta har yana zare glass d'in dake manne a idanunsa.

“Kina nufin baki taɓa bashi kanki ba?? Ta zaro ido.

“In bashi kai na Dr? Toh ni kuma fa, sai in kashe kai na saboda shi?? Ganin ba ta gane maganar tashi ba yasa shi cewa.

“No Nafisa ba haka nake nufi ba, Ina nufin be taɓa mu'amula dake ba? Baku taba kwanciya guri ɗaya ba ya yi miki wani abun.??

Ta sake gyada masa kai alamun eh basu taba kwanciya tare ba duk da cewa bata gane ba sosai. Da kanshi cikin tambayoyin da yake yi mata yasa tayo fitsari ya gwada sannan ya gano cewa mijin na ta sai ya gusar mata da hankali sannan yake mu'amula da ita. Bayani ya yi mata sosai yadda zata fahimci abinda yake nufi. Daga karshe ya kare da cewa.

“Yanzu ciki gareki na wata ɗaya da sati ɗaya, shi yasa kike jin wannan kwad'ayin da kuma kasala. Kiyi hakuri da kaddarar da Allah ya ɗora miki na auran sa tunda gashi nan harda rabo a tsakani, ba kisan abinda Allah yake nufi ba da hakan.?

Feenah tun bayanin da ya yi mata dalla-dallah na cewa Sultan yana sa mata kwaya a lemo dan ya dinga samunta, ya yi mata bayani game da yadda abin yake, shikenan tunanin Feenah ya tsaya daga duk wani bayani da Dr Sharif yake yi. Wata mummunar tsanar Sultan ta sake tsaya mata a wuya fiye da yadda take jin sa a farko.

Nan dai ta samu Dr ya rubuta magani yace ta dinga amfani dashi saboda lafiyarta da ta abin da ke cikin nata. Da kyar Feenah ta iya baro asibitin ta fito bakin titi tare da samun taxi ta shiga, da kyar ta Iya samun dama ta gaya masa inda zai kai ta daga nan ba ta kuma cewa komai ba har suka je. Kudin sa ta mika masa ta shiga gidan, tana murd'a kofar Sultan shima yana dawowa cike da tashin hankali.

Kitchen ta wuce ta dauki sabuwar wuka tana shafawa zuciyarta na yi mata hud'ubobi daban-daban akan irin matakin da zata dauka na fansar rainin hankalin da ya yi mata ba tare da saninta ba. Sink ta nufa tare da tara cup ta dibu ruwa tasha dan tayi alkawarin ba zata kuma ci ko shan wani abu da zai ajiye a gidan ba. Shi kuma yana can ɗakuna yana ta nemanta bata nan, sai ya taho kitchen d'in suka yi kicibus da juna.

Cikin sauri ta ɗago wukar tare da saita shi tana zubar da hawaye idanunta a waje jikinta na kyarma take son aiwatar da kuduri umarnin da zuciyarta ke yi mata.

“Feenah menene haka baki da hankali ne??

Kamar wata zararriya haka take yin kansa yana kufcewa tace.

“Wallahi idan baka rabu dani ba sai na kashe ka Sultan, na tsaneka tun ba yau ba, gashi na kuma tsanarka bana son ganinka cikin rayuwa ta.?

“Naji Feenah amman ki ajiye wukar sai muyi magana please.? Cike da masifa tace.

“Bazan ajiye ba, naki na ajiye ɗin azalumi macuci kawai. Kuma wallahi sai ka sake ni sakin da babu dawowa gareka.?

Ganin abin nata ba barazana bane da gaske idan ya bari zata iya illata shi, yasa Sultan janyo jarumtarsa da karfinsa. Sai dai kafin ya kai ga aiwatar da abin da ya yi niyar yi Feenah ta yo wata irin sufa kansa ta d'aga wukar tare da zura ta a............


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A*💪

*ALBISHIRIN KU MUTANEN KIRKI? KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION*

*TAZO MUKU DA SABON TAKU, SABUWAR FITA, SABON KARUWA, SABON ILIMI, SABON NISHAƊI SABON KARATU SABON AJI.*

*INDA SUKA ZO MUKU DA K'YAYATATUN LITTATTAFAI GUDA 7, WANDA ZASU NISHADANTAR DAKU SU FADAKAR DAKU. WANDA GWARAZAN MARABUTAN KU ZASU GABATAR*

*IBTISAM:- NA AYUSHER MUH'D*

*WATA SOYAYYA:- NA OUM HANAN*

*WASU MAZAN:- NA BILLY S FARI💎*

*NIDA RAHEEMA:- NA ASMY B ALIYU👄*

*ZO GARE NI:- NA HAJJA CE👈*

*KUKAN ZUCI:- NA SLIMZY*

*AZAAD JUNAID (the young billionaire):-NA JEEDDAH ALIYU*

*TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A BASU TSAYA NAN BA, ZASU GABATAR MUKU DA WASU SHIRYE SHIRYENSU*

KALOLIN GIRKI TARE DA:- *DEEJARH BERVER*

SHIRIN
YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN KARIN NI'IMA DA INFECTION (NI'IMARKI A TAFIN HANNUNKI) TARE DA *MAMAN KHADIJA*

SHIRIN TSAFTA YADDA ZAKI GYARA JIKINKI DA MATSALOLIN JINI TARE DA:- *UMMI AISHA*

*ZASU KARA MUKU HASKE AKAN ABUBUWA DA SUKA SHA KANKU, MATSALAR AURATAYYA MATSALAR INFECTION, MATSALAR NI'IMA, MATSALAR FUTAR ISKAR GABA, MATSALOLI DA DAMA.*

*DUK ZAMU GABATAR DA WANNAN KARATU NE TA HANYAR WAYOYIN SADARWA, WATO WHATSAPP GROUP'S*

GARABASA MAI CIKE DA ALBARKA DA KUMA KARUWA. GABA D'AYA WANNAN AJI ZAIZO MUKU NE AKAN 500 naira only...Nair ɗari biyal kacal.

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number👇🏼👇🏼*

07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER🇳🇪, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.







*HAJJA CE 👈*
2/4/22, 11:17 - Buhainat: *ZO GARE NI....*
Free page 5

Na
*HAJJA CE 👈*

Wattpad:- Hajjac

*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH A 2022*




A tsakani hammatarsa, Allah ya tsare bata soka mishi a gefen kirji ba. Ya fuzge wukar tare da wurgata gefe yayin da ita kuma Feenah ta shiga dukansa ido rufe kamar wata marar hankali. Shi kuma sai rike ta yake yi yana so ta dawo cikin hayyacinta amman abu ya gagara, ya dinga tura ta har sai da ya kaita cikin bedroom d'in ta ya rufe ya jingina bayansa jikin kofa yana sauke numfashi.

“Wallahi ba zan zauna da kai ba duk abinda zaka yi sai dai kayi macuci azzalumi wanda yake son kanshi. Ana so dole ne? Nace bana sonka bana yin aure dole sai dani zaka zauna? Na rantse da Allah sai ka rabu dani bazan taɓa rayuwa da kai ba.?

Duk yana jiyo ta idanunsa a rufe yana son gano asalin abinda ya faru yau ta birkice masa haka, saboda duk wannan haukan da take yi bata sanar dashi dalili ba. Yaja kafarsa da kyar ya koma parlor ya zauna tare da dafe kansa yana tunanin mafita tunda gashi har ta fara neman salwantar masa da rayuwa gaba daya.

Daya rasa mafita sai ya tashi ya shiga ɗakinsa ya kulle yana faman cizon yatsa.

____Feenah kuwa a haukace ta faɗa kan gado tana kurma uban ihu, ji take tamkar ta kashe kanta saboda bakin cikin da ta ke ciki. Sultan ya raina mata hankali iya raini, ya kuma gama da ita dan ba zata taɓa yafe masa ba koda kuwa yafiyar ce zata kai ta ga shiga aljanna. Haka ta dinga yakushin cikin ta tana kuma yakusowa gani take kamar cikin zai Iya buɗewa ta ciro abinda yake ciki dan bata shirya haihuwa yanzu ba.

Wayarta ta dakko ta nemo lambar Areef amman a kashe, daman tunda ta baro Nigeria bata kuma samun wayarsa ba kullum sai dai a ce mata a kashe take. Kuka ya sake kwace mata lokacin da ta tuna Areef masoyinta, wanda take yiwa so irin na mutuwa, so ne take yi masa da ta rasa daga inda yake dan tsabar tasirin da ya yi a rayuwarta.

Karshe ta kira Mommyn ta, bugu biyu ta ɗaga cike da fara'a walwala da farin ciki. Sai dai kuma lokaci ɗaya suka gushe sakamakon kukan da taji ta na yi.

“Nafisa lafiyar ki kuwa??

“Mommy ya kashe ni, wallahi ya cuce ni Mommy na shiga uku.?

“Qalu innallilahi wa'inna'ilaihir raji'un. Nafisa me ya faru? Ina Sultan d'in yake?? Hajiya Saratu ta tambaya cikin dimuwa.

“Mommy bana son wannan mutumin, wallahi bana son shi kullum tsanar sa kuma shiga zuciya ta take yi. Idan baku dawo dani gurin ku ba Mommy zan iya rasa rayuwa ta, dan Allah kuce ya rabu dani dan Allah Mommy na.?

“Shikenan Nafisa tunda auran kike son b'allowa, Allah ya rufa miki bargon asiri amman zaki tunawa kanki. Ga 'yan uwanki nan zaune a gida suna jiran mazajen aure, ke Allah ya daukakaki ya baki nagartaccen miji, meye aibun Sultan dan Allah Nafisa?? Hajiya Saratu ta yi maganar cikin salon tambaya.

“Mommy bana son shi wallahi, ji nake kamar zan mutu idan na kalleshi.? Rai a b'ace Hajiya Saratu tace.

“Shikenan ki bari zan kiraki.? Bata jira jin me Feenah zata kuma cewa ba kawai ta yanke kiran.

Wasu hawaye ne suka shiga zubowa daga cikin kwayar idanun Hajiya Saratu, babu abinda take jin takaci irin yadda ƴarta zata kaso auranta. Shi kenan kuma ta dawo ta zauna daman ga 'yan uwanta nan su hud'u auren ya gagara, anata murna tayi gashi zata b'allo shi ta dawo a ci gaba da sanya musu ido kamar kullum.

Shi yasa tun farko da taga Feenar bata son auran tace toh a barshi kawai tunda ita zata zauna dashi, ganin daddyn su ya matsa kuma shima Sultan d'in ya dage yasa kawai ta barwa Allah lamarin, gashi yanzu za'a mayar mata da ƴar kankanuwar yarinya bazawara.

Tana zaune sai sak'awa da kwancewa take yi akan yadda zata b'allowa al'amarin, ganin ta rasa mafita yasa ta mikewa taci gaba da aikin ta duk da cewa ranta babu dad'i.

Alhaji Nura yana dawowa da daddare bayan ya gama cin abinci yana kishingid'e yana sauraron news Hajiya Saratu ta shigo da maganar Nafisa cikin sanyin murya.

“Alhaji magana nake son muyi da kai.?

“Toh Hajiya ina sauraronki lafiya dai ko.?

Hajiya Saratu ta ja numfashi tare da d'auke kai daga kallon mijin na ta dan bata son ta kasa gaya masa abinda yake cikin zuciyar ta.

“Waya muka yi da Nafisa d'azu.?

“Toh mutanan turai kenan, ince lafiya dai ko??

“Ba zan iya cewa kalau ba alhaji, tunda ta kira ni ne tana kuka tana cewa ita dole sai Sultan ya rabu da ita.? Hajiya Saratu ta yi shiru yayin da Alhaji Nuran ya d'ora da cewa.

“Toh me kuma yake faruwa haka? Wannan yarinyar dai fitinanniya ce wallahi tallahi. Dan k'aniyarta auran take son a raba ko kuma uban me take son ayi mata??

Yayi maganar cikin fad'a da b'acin rai, da alama shima abin ya bashi haushi duba da yadda yake hucin da zai tabbatar maka da cewa da Feenah na kusa dashi babu abinda zai hanashi lallasa mata duka a jikinta.

Ya shiga fad'a babu kakkautawa har sai da sauran mutanan gidan suka jiyo shi, suna ta mamakin yau me yasa daddy wannan kwarmaton. Yaci gaba da magana cikin masifa da b'acin rai.

“Kirawo min ita wallahi naci uban ta, sakaryar yarinya marar hankali kawai.?

Hajiya Saratu ta janyo wayar ta tare da kiran Feenah wacce ke zaune tana kallon cikinta mamaki na d'ibarta ace wai d'a ko 'ya ne a cikinsa. Ganin kiran Mommyn su yasa jiki na rawa ta dauka, sai dai maimakon taji muryar Mommy kamar yadda taga sunan a jikin alon wayar sai taji daddyn ta cikin fad'a yana cewa.

“Nasan kina jina marar mutunci, kina nufin ni zaki tonawa asiri dan baki da hankali? Toh kice ya sake ki d'in tunda ke baki san mutunci ba.?

Yana direwa kuwa Feenah ta dauka cikin tashin hankali tana kuka wiwi kamar wace ake zarewa rai cikin karfi, cewa take yi.

“Daddy idan kuka barni dashi zan mutu wallahi.?

“Da yafi miki kuwa Nafisa, domin kin mutu ne a gidan mijin ki. Allah ya yi miki rahama tun yanzu ma ni na fara miki fatan samun dacewa.? Cewar Alhaji Nura yana huci shima.

“Na shiga uku daddy wallahi ba zan zauna dashi ba, na hakura gwara na tafi wani gurin da naci gaba da zama da Sultan.?

Tana gama fad'in haka ta katse tare da yin wurgi da wayar tana kuka. Duk abinda take Sultan yana jiyo ta, jin shiru yasa shi jan dogayen kafafuwansa ya bar gurin.

Lallai ya tabbatar Feenah ba karamar tsana tayi masa ba, tunda gashi alama sun nuna masa cewa sa'in sa suka yi da mahaifinta.

Shin me ya yiwa yarinyar nan da har ta tsane shi kamar haka? Gashi shi kuma kullum sake ninka masa wutar sonta ake yi a cikin rayuwarsa. Anya ba zai cuci kansa ba idan ya ce dole sai ya zauna da ita? Gwara ya hakura ya sallama mata tunda dai har ta nuna rashin amincewarta da shi...

Can gidan su kuma daddy ne ya sauke wayar daga kunnensa yana bin ta da kallo, ya kalli Mommy da ta yi zugum bakin ciki ya gama yi mata yawa har tama kasa cewa komai bare ta yi masa magana, sai shine yace.

“Wannan yarinyar ta zama kangararriya wallahi, ni zata kashewa waya saboda ta rik'a wuyanta ya yi kauri? Lallai zan yi maganinta kuwa tunda ta nuna min ita din mai taurin kai ce.?

Daga haka ya tashi ya dauki hularsa ya bar gidan duk da ba al'adarsa bace idan ya dawo ya kuma fita a wannan lokacin. Gidan wani babban malamin addini yaje, bayan anyi masa iso ya shiga suka gaisa da malam Ahmadu tare da tab'a ƴar hira, daga bisani Alhaji Nura ya bijiro masa da zancen da ya kawo shi cewa.

“Wallahi malam ƴar waje na ce tayi aure, kuma yanzu tasa fitina cewa dole ya ta kaso auran shine nace ko akwai wani taimako da za'a iya yi min, dan Allah malam a kafe ta a gidan mijin ta dena marmarin kashe wannan auren. Wallahi duk ƴan uwanta suna nan zaune a gida, ita kadaice Allah ya yi mata arzikin yin auran kuma gashi tana son b'allo shi.?

Murmushi malam Ahmadu ya yi yana gyara rikon carbin dake hannunsa. Alhaji Nura ya kwantar da hankalinsa ganin malam yana Murmushi sai yaji duk rabin damuwarsa ta kau duk da cewa bai yi masa wani Karin bayani ba a lokacin. Numfasawa malam ya sake yi tare da cewa.

“Alhaji Nura kasan yaran da, dana yanzu ba d'aya bane ba. A da matar da aka aura maka ma baka santa ba sai ka shiga dakin ka sannan kuke sanin juna. Yanzu kuma yaran zamani an ɓata su da cewa suje su zab'o duk kalar mijin da ya yi musu za'a daura musu shi. Wannan

4 / 38