Kai ta sake gyaɗawa tana son kwace hannunta daga riƙon da yayi mata.
Haushi yasa shi sanya ɗayan hannun ya matse mata leɓanta na sama dana ƙasa, ya kuma kai fuskarsa kusa da tata kamar zai sumbata tai saurin kawar da fuska yayi murmushi.
"Karki damu ni ba kissing ɗinki zanyi ba lil sis, zan kula dake kamar yadda na saba, abinda zai canza kawai shine ki dena yi min rashin kunya da sa ido kinji ko?"
Wannan yanayin bai taɓa haɗa su ba tun tasowarta saboda Mamah bata bari dan kuna gida ɗaya jini ɗaya ku dinga kusantar juna. Iman tace.
"Naji."
"Good girl. Yanzu ki jera bedside drower dana madubi ni kuma sai naji da sauran." Ta kuma cewa.
"Toh."
Sakar mata hannun yayi ta nufi inda ya sata, shi kuma yaci gaba da nasa. Ta riga shi gamawa tazo zata tafi yace ta tsaya su ƙarasa. Babu yadda ta iya dole hakan ta tsaya suka yi komai tare duk da cewa babu mai yiwa ɗan uwansa managa. Kafin kace mene gida yayi tsab ya yi kyau sosai su Abba sunyi kokari matuka.
Cikin sati ɗaya an gama shirya musu komai ranar da ta kasance su Ikram zasu baro Abuja Abba da Aslam ne sukaje ɗakko su. Tunda aka ce gobe zasu tafi Iman ke kuka suna bata hakuri. Areef da yayi shiru shima ganin kukan nata yayi yawa yasa shi sa baki yana bata hakuri Amman kamar kara mata ake yi. Yaja karamin tsaki tare da cewa.
"Idan sun tafi cewa aka yi miki yankaki zan dinga yi ina ci? Toh kisa ranki a inuwa ni ba gutsirarki zanyi ba."
"Kai Yaya Areef Itafa batace zaka yankata ba." Ikram ta faɗa tana rungume da Iman.
"Toh uwar iyayi kareta."
"Missing ɗin mu zata yi ne shi yasa take kuka." Cewar Hanan.
"Sai kuma ku zauna ai waye zai hanaku?" Ya faɗa yana sake duba agogo. Haka suka zauna suna ta musu da gardama shida Ikram daman Hanan ba surutu gareta ba Ikram ta fita magana.
Koda su Abba suka ƙaraso sun sha murna inda Aslam da Areef suka koma gefe Aslam na ta yiwa Areef tsiya.
"Shegen ƙauye kaga Feenah taja maka mallakar mata da gida ga kuma aikin yi ka samu. Gaskiya abokina kayi zarra a cikin mu, sai kayi ƙoƙari nan da 9 month's muzo suna."
"Kai dalla can banza kawai waye yace maka zanyi?"
"Ahhh! Kai! Lallai ma, toh an gaya maka gunki aka ajiye maka a gidan? Dan bakwa son juna sai aka ce muku karku raya sunnar ma'aiki? Dalla ware alhaji ka kwashi rumo wallahi."
"Ina zaka nemo min Feenah dan Allah?" Areef ya bagarar da waccen maganar. Mamaki ya kama Aslam yace.
"Wai kana nufin har yanzu baka goge yarinyar nan a ranka ba?"
"How? Kasan kuwa yadda muka ƙulla alƙawarin kasancewa tare da juna?" A hasale Aslam yace.
"Toh alƙawarin ku na Allah ne da zaku ce dole sai ya cika? Nifa bari na gaya maka tun lokacin da aka kamaka da yarinyar nan naji bana son ka aure ta. Allah ya rufa maka asiri ka samu nagartacciya wacce kuka samu tarbiya a guri guda me zakai da waccen barbaɗaɗɗiyar matar? Bazawarace ma fa, gashi bata jin maganar iyayenta."
"Ya isheka Aslam, zuwa kayi dama kaci min fuska ko me kake nufi? Duk wannan abubuwan daka lissafo Feenah ta aikata su ne saboda soyayyar da take min. Shikenan sai nima na juya mata baya? Kowa ya tsaneta saboda ta nunawa duniya cewa ni take so? Karfa ka manta Iman ɗinma da aka bani har zuwa wannan lokacin babu wanda yasan asalinta, ta iya yiwuwa ma a irin soyayyar da muke da Feenah itama iyayenta suka haifeta."
Taratsatsatsa...suka jiyo karar fashewar tangaraye a bakin ƙofar. Da sauri duk suka waigo dan ganin wacece suka ga Iman jikinta yana kyarma kamar wacce aka jonawa shock.........
(Oh my God Areef! Areef!! Areef why na) 😒
*ZO GARENI yana cikin tawagar Top 10 ki biya kafin ki karanta daga page 11. Zaki iya tuntuɓar wadannan. +447894142004 ko kuma 0706 528 3730*
*HAJJA CE 👈*
3/6/22, 07:13 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*
*25*
Turus suka yi ganin Iman tsaye gabanta kayan abincin da tazo kawo musu duk ya tarwatse, idanunta akan Areef tana yi masa wani irin matsiyacin kallo mai cike da abubuwa da yawa. Abba dasu Ikram suma suka zo suna tambayar lafiya? Ta daure dakyar tana jin wani mugun kuka nason kwace mata tace.
"Ba komai Abba zamewa na kusa yi shine kayan suka zube."
"Subahanallahi Allah yasa bakiji ciwo bako?"
"Banji ba Abba sai dai kayan kaga duk sun fashe daga kawowa."
"Wannan ba damuwa bane lafiyarki itace abar bukatar mu, tunda kuma babu rauni alhamdulillahi." Yayi murmushi suka juya suka koma inda aka ajiyewa Abba abinci.
"Kuma Yaya Areef ku fito nan kuci mana, bari a zubo muku ragowar."
Gaba ɗaya Areef da Aslam basu da kuzari musamman ma Areef da yayi furucin. Koda Ikram ta kawo musu abincin kasa ci suka yi sai tsakura suke kamar masu cin maɗaci. Da sauri Areef ya fita zuwa wajan motar Abba ya dafe kai saboda shi kansa beso Iman taji maganganunsu ba yasan tabbas zataji babu daɗi duk da cewar ba karya ya yi ba. Ji yayi an dafa kafadarsa yayi saurin ɗagowa, yayi zaton itace ta biyo shi zata kashe shi.
'Anya zai kwana a gidan nan kuwa? Daga shifa sai ita za'a bari, gashi ya yi maganar da ta sosa zuciyarta.'
"Kayi abin yazo ya shamaka kai, sai ka bari idan mun tafi kaje ka bata hakuri dan ni na bata ta kuma ce ta hakura. Idan kuma ka zauna girman kai ya hanaka toh tabbas alhakinta ba zai barka ba." Sauke numfashi yayi tare dace.
"Banji daɗi ba Aslam, sai dai nayi furucin ya kuma fito anji, bansan yadda zan goge shi a ranta ba."
"Kaiko kake da hanyar lallashi yaro, ba yau zamu tafi da su Ikram ba?" Areef yace.
"Yau ne." Dariya Aslam ya shigayi yana cewa.
"Toh Sai kawai ka lallasheta yadda kake lallashin Feenah idan tayi fushi da kai.."
"Amman dai baka da lafiya ko Aslam?" Areef ya tambaya.
"Ras nake wallahi karka raina min wayo mana."
"Toh Amman taya zan doshi Iman da wannan abin? Kai karfa ka ɗauka cewar ni ɗan iska ne wallahi a'a karka soma wannan tunanin dan ban taɓa ba."
"Anji to Amman ka rantse baka taɓa rungume ta ba."
"Sannu uba na." Cewar Areef yana jan tsaki.
"Toh kuwa zaka iya yiwa Iman fiye da abinda kake yiwa Feenah, kaga ita matarka ce yanzu komai kukai lada ne, ita kuma Feenah zunubi kuke ɗauka amman nasan kafi son Feenah saboda shaiɗan yana tsakaninku." Rai a bace Areef yace.
"Dan Allah ku gaida gida, ka gaida Irfan da Sudais basai sun zo ba zamu dinga waya."
"Iyeee saboda kayi gida da mata ko?"
"Ba haka bane, naga kaima zuwan naka ɓata min komai yayi, suma kuma nasan idan sunzo isata zasu yi."
"Zakaga rashin mutunci, idan ka sake ganina a gidan ka ɗan wulakanci kawai."
"Naji ɗin kasha zamanka."
A can gidan kuwa Iman na ganin sun tashi zasu tafi tasa kuka tana riƙe su Hanan.
"Abba dan Allah karsu tafi su barni." Abba ya yi murmushin karfin hali tare da cewa.
"Zasu dawo Insha Allahu, kiyi hakuri kinga yanzu jamb zasu yi suna gamawa zasu zo miki su daɗe." Ta sunkuyar da kai hawaye na sharara tace.
"Toh Abba nima ina son karatun." Su Areef da ke shigowa sukaji Abba yace.
"Yauwa Areef ka ɗaukar min alƙawari cewa idan komai ya warware zaka bar Iman taci gaba da karatu." Areef yaki bari su haɗa ido, kansa a gefe yace.
"Insha Allahu Abba." Abba ya riƙe hannunta cikin lallashi yace.
"Kiyi hakuri yace zaki yi, nasan kuma zai cika alkawarin kamar yadda yace Insha Allahu." A raunane tace.
"Abba nagode Allah ya saka muku da alkairi ya..." Kuka yaci ƙarfinta ta kasa ƙarasawa.
Nuni Abba ya yiwa su Ikram cewa su fita sannan ya ja hannunta suka isa gurin da Areef yake. Kamo hannunsa yayi ya haɗa cikin nata yace.
"Ka kula da ita." Tana cewa haka yabar gurin yana jin wani irin tausayin su.
"Allah ya bada zaman lafiya abokina, next year mu zo suna."
Wata uwar harara ya jefawa Aslam wanda tuni shima yabar gurin yana dariya. Yana fita daman shi suke jira Abba ya tada motar suka bar unguwar.
Iman kuwa Aslam na fita tayi saurin fizge hannunta daga haɗewar da Abba yayi musu, kallon juna suka tsaya yi wanda kallon da Iman ke yiwa Areef kallone irin na tsana da rashin ganin girmansa, tunda taji kalamansa taji bata yi masa kallon mutunci. Shima kallon sama da ƙasa ya shiga yi mata, sam yaji ba zai iya bata hakuri ba, izzarshi ta motsa ya juya zai bar gurin yaji tana magana.
"Kota wane irin hali iyayena suka yi sanadin zuwana duniya, karka manta su ba tsaran wasanka bane. Raini da wulakanci sunfi karfin kayi musu ina gurin. Duk da cewa ban san su ba hakan baya nuna cewa zan bari aci musu tunci, bazan hanaka zuwa wajan tambaɗaɗiyar karuwarkaba, kaje kuyi duk abinda ranku yake so. Amman ka sani, koda ta hanyar assha aka haifeni, ni bazan so ace na kuma haɗa iri da mai yi ba. Sudai sun haife ni gashi har nazo duniya, ni kuma zan zame musu farin ciki ta hanyar zama nagartacciya a idanunsu."
Tana kaiwa nan tabar gurin, da gudu ta ƙarasa ɗaki tana toshe bakinta da kuka ke son bayyana. Areef yayi shiru yana kallon hanyar da tabi jikinsa yayi sanyi da jin kalamansa. Yaga alamar ba zasu gane cewa basu taɓa kusanta shida Feenah ba, be kuma san abinda zai gaya musu ba. Ya shafa gashin da ya kewaye bakinsa wanda yake ƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini. Kasa shiga ɗakinsa ya yi ya fita daga gidan.
Iman kuwa kuka kawai take yi gaba ɗaya duniya tayi mata baki. Me yasa aka haifeta ta wannan hanyar? Fyaɗe aka yiwa mahaifiyarta ko kuwa dama can bata da kamun kai? Sun san ba zasu iya kula da abinda suka samu ba me yasa tun tana ciki basu zubar ba, gashi sun yi sanadin zuwanta duniya ta rayuwa cikin farin ciki dajin daɗi gashi yanzu tana fuskantar wulakanci? 'Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun' shine abinda yake maimaituwa a ranta.
Shi kuma Areef soyayi kawai ya koma gurin aikinsa, tafiya kawai yake yi zuciyarshi tana tuna masa cewa amana aka baka Iman, kai kaja mata yin kuka a wannan lokacin domin kaci zarafinta. Sai kawai ya juya ya koma gidan, kai katsaye ɗakinta ya nufa ya tarar da ita tana ta kuka. Yadda yaga tana girgiza kai Shine ya tabbatar masa da cewa damuwa tayi mata yawa.
Ita kuwa taji shigowarsa amman da yake tana jin haushinsa ko kallo be isheta ba. Abinda duk ya basu mamaki shine Areef da ya kwanta a saman bayanta kasancewar ruf da ciki tayi, ya kuma saka hannu tare da zura hannu ya rungumeta a jikinsa. Cikin sauri Iman ta waigo tana zaro ido shi kuma ya lumshe nashi yana sake kwantar da kansa a nata, murya ƙasa-ƙasa yace.
"Sorry lil sis, ki yafe min."
'Meye hakan ya yi mata? Me hakan yake nufi? Gabaki ɗaya a jikinta yake yana kuma matseta, anya yasan cewar itace? Ta fara ƙoƙarin kwace jikinta amman ya hana hakan faruwa duk kuwa da cewa ba wani kato bane ɗan daidai ne iya shekarunsa.
"Ni ka ɗaga ni." Ta faɗa a kufule. Ya rike kanta tare da sanya bakinsa cikin kunnanta, iskar dake fitar da wani huci mai dumi Shine ya kasa sanya Iman cikin yanayin da bata taɓa samun kanta ciki ba.
"Kin hakura?" Ya faɗa yana leƙa fuskarta.
"Ka dagani please bana son wannan abun Areef." Yasa hunnu ya sake juyo da fuskarta, cike da mamaki yace.
"Areef kai tsaye?" Ta shiga ture shi tare da cewa.
"Kaji haushi?" Bai bata amsa ba sai da ya jirkitota, shi ya koma ƙasa ita kuma ya zamana ta dawo saman kirjinsa.
Kawar da kai tayi tana huci sai kace wacce tasha dambe, gashin kanta daya bayyana sakamakon ɗankwalinta da ya zame, Areef ya shiga gyarawa yana maida mata baya saboda suna taɓa mishi fuska. Idanunsa ya kafa a guri guda ba tare da yace komai ba, ita kuma Iman a jikinta taji cewar akwai inda yake kallo, ta juyo a fusace idanunsa kyar akan kirjinta da alama ƴan fitulun biyu yake kallo, haushi da takaici yasa ta ture shi tana cewa.
"Dalla malam menene haka?"
Yadda yaga ta tunkuɗeshi ne ya bashi tsoro, yai saurin sakinta gaba ɗaya yana miƙewa tsaye dan karta samu damarsa.
"Allah baki hakuri." Ya faɗa tare da haɗiyar yawu sakamakon maƙogwaronsa dayaji ya bushe.
"Ka fita." Yaji ta faɗa idanunta a rufe.
Sim-sim-sim Areef ya fice badan komai ba sai gudun kar abin yazo da matsala. Iman ta bishi da kallo tare da kawar dakai. Yama raina mata hankali, idan hakuri zai bata sai ya wani taɓa ta? Haushinsa takeji matuƙa ko jiki bata son su haɗa tunda tasan ya taɓa Feenah, ita kuma ta tsaneta.
Basu sake haɗuwa ba har dare. Koda ya dawo ɗakinshi ya wuce ya gama shiryawa yai kwanciyarsa. Itama Iman ɗin bata kuma bi ta kanshi ba, tana nata ɗakin tayi sallah tabi lafiyar gado tsakanin kwanta. Can cikin bacci taji ana tashinta a hankali, tasan Areef ne sai tai masa shiru bata motsa ba. Can taji ana shafa mata jiki, wato shi ya manta da kalamansa gareta ɗazu shine saboda rashin kunya yake mata wannan abun.
Tasa ƙafa tare da ture hannun, ta kuma ji an shafo mazaunanta tayi saurin shi zaune tana ƙoƙarin zaro wayarta ta kunna. Flashlight ta kunna tana haska gadon, abin mamaki babu kowa sai ita kadai akai. Ta sakko da sauri ta shiga dube-dube bata ga kowa, sai tayi tunanin ko mafarki tayi. Ɗan ƙaramin tsaki taja tare da komawa ta kwanta, wayar ta shiga dubawa sakamakon tunda Hanan ta bata lokacin da zasu tafi bata kunna ba sai yanzu.
Misscall ta gani rututu da kuma sakon sms sai dai wasu bata san numbern ba kuma duk sakon tayin soyayya ne, sai su Islam amarya da sauran ƙawaye. Kanta da taji yana sarawa yasa ta kuma lumshe idanuwa, tana rufewa taji an kuma sanyo mata hannu. Ta shiga kurma ihu tana buge-buge da make-make tana cewa.
"Wayyo Allah na nashiga uku. Yaya... Yaya Areef."
Yana can ya baje kan gado yana sharar, sama-sama ya dinga jiyo ihu kafin ya jiyo kiran sunansa da ake yi. Kafin ya tashi yaji ana ta buge-buge a falo. Tasowa ya yi da sauri, a hankali ya buɗe ƙofar yana leƙowa da fuskarsa. Duhu falon sai inda yake hango haske inda yake jiyo kukan Iman. 'Me take yi haka? Wannan wane irin ihu ne?' zuciyarshi take ta tambayoyin amman tsoro ya hanashi fitowa gaba ɗaya. 'Kar ta kashe shifa' ya sake rayowa zuciyarshi.
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun dan Allah dan Annabi kowaye ya dena min haka, me nayi muku? Dan Allah ku rabu dani dan Allah.. Dan Allah... Ba danni ba.." Ta ƙarasa cikin fashewa da wani irin kuka.
Areef dake bakin ƙofa ya fara zare ido yana kuma buɗe kunnuwa. 'ita kuma kaddararta ta aljannu ce, idan ba aljanu ba da wa take magana yanzu?' Ya sake leƙawa, jin yadda take kuka ne yasa shi yin kalmar shahada ya fito tare da saddaƙar da rayuwarsa, yasan kila yau kwanansa ne ya ƙare. Nesa da ita ya tsaya yana mata magana.
"Iman." Ta ɗago cikin hawaye tana kallonsa.
"Menene ya saki kuka cikin daren nan?" Ɗakinta ta kalla cikin kuka tace.
"Wallahi Yaya Areef aljanune a gidan nan." Da mamaki yace.
"Aljanu kuma?" Tana goge hawaye tace.
"Eh wallahi ina bacci naji ana shafani, na ɗauka kaine ina dubawa naga babu kowa. Dana sake kwanciya sai naji an kuma shafamin....." Tayi shiru ta kasa faɗa saboda girman furucin.
Nan da nan Areef ya shiga raba idanuwa yana mamakin jin furucin ta. Aljanu ana zaune lafiya? Kodai iskokanta ne suke yi mata hakan? Ya daura yace da ita.
"Babu wasu Aljanu a gidan nan, kiyi addu'a kawai kije ki kwanta." Iman ta sake fashewa da kuka jin abinda ta faɗa tace.
"Wallahi bazan shiga dakin can ba saboda ni naji a jikina ana taɓani." Rintsa ido yai ya buɗe tare da cewa.
"Shikenan ki kwana a falon kaw...." Kafin ya rufe baki Iman ta ruga da gudu ta rungume shi sakamakon inuwar mutum da tagani ya wuce yana kallonta.
"Ke wai menene haka Iman? Ko sokike ki haukatani ne?" Ta sake kankame shi tana girgiza kai a kan bayanshi.
"Wallahi naga ya wuce, can yabi yaya Areef na ganshi da ido na wallahi."
"Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, shikenan naji muje ɗakina, amman wallahi ni dai na shiga uku. Kuma koma menene zanyi maganinsa."
Ai yana rufe baki yaji kamar ana dariya a bayansa, ya zabura shima duk suka kankame juna a tare kaɗan ya ragewa Areef yin fitsari saboda tsoro..........
(Mazaje😂 Iman kina ruwa domin shima zabone ba zaki ba)
*ZO GARENI yana cikin tawagar Top 10, ki biya kafin ki karanta daga page 11. Zaki iya tuntuɓar wadannan idan kina bukata. +447894142004 ko kuma 0706 528 3730*
*HAJJA CE 👈*
3/6/22, 07:13 - Buhainat: *ZO...GA....N....*✍️
*Top 10 Takun haske batch A...*
*Wattpad:- Hajjac*
*HAJJA CE 👈*
*(https://www.youtube.com/channel/UCeGSNgC7XO2yjL5Au6LYp2g Please subscribe my YouTube channel please 🤲 please Good people, thank you Allah ya yi muku kuma)*
*26*
Suna kankame da junansu yajata suka ƙarasa ɗakinsa, still basu saki juna ba har yaje gurin ƙofa ya kulle ɗakin da sauri yana murza mukulli. Ta kallesa da sauri tana zazzaro ido cikin faduwar gaba tare da cewa.
"Ya Zaka kulle mu, yanzu idan aka biyo mu ya zamu yi? Ta ina zamu fita Yaya?"
"Oh...! ke fatan a biyoma kike yi ko?." Iman kamar zatai kika tace.
"Amman dai Yaya akwai risk hakan, dan Allah kabuɗe mu." Tana rufe baki sukaji ana zuge glass ɗin window, gabaki ɗaya suka sake sakin ihu tare da makure junansu a jikin ƙofar.
Kukan mage ne ya sake gigita su, Iman na kuka tana cewa sai da tace karya rufe yaki gashi nan yanzu za'a kashe su. Hannu na rawa Areef ya shiga neman mukulli daya faɗi ƙasa, suka sake jin kukan magen nan wannan karon tsige Iman ya shigayi ganin yadda ta cakumeshi jikinta nata kyarma.
"Wai bazaki sakeni bane?" Cikin ruɗani tace,
"Ina zakaje?" Yaja tsaki,
"Malama ki sakeni mana haba." Yana ta faman kwakule mata hannu daga rikon