Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   9 / 38

24K to 27K   out of 111.1K words

zan mutu sabida tsabar damuwa . Murmushi meenal tai tare da cewa  bama zaka mutu ba dama ina so muyi magana ka bugo akan gaSa .



Da sauri waleed yace  tom ina jinki meenal maza-zama mai kike so nayi miki? .



 Dama ina so na gaya maka, kaga de bani nake da kai na ba kuma umma ta fara lura da yawan wayar da muke, dan haka ya kamata in ka dawo kazo ka samu baba, ka gaya mai abinda yake tafe da kai, kaga in ya baka izini sai munfi Jin daWin fahimtar juna Koh? .



 Inalillahi meenal Wina, dama har na kai wanan matsayin a wajan, da bakin ki, kike cewa nazo neman izini wajan baba, wayyo Allah daWi kar ka kashe ni Allah na gode ma wallahi meenal kin gama yimin komai .



Murmushi meenal tai tare da cewa  kai ba fa cewa nai, kazo ka nemi aure na ba da kake wanan abun . Dariyar jin daWi waleed yayi tare da cewa  hmmm ba zaki gane ba wallahi, in de na samu baba ai mafarin auran kenan . Meenal kuwa  hmmmm kawai tace,.



 Kai meenal Wina nagode sosai da sosai Allah ya bar auna, yaushe kike so na dawo? .

 A'a ni ba ruwa na duk sanda kake so ka dawo zaka iya .  Tom shikenan jibi zan dawo in sha Allah .



Cikin mamaki meenal tace "da wuri haka kuma?".

 Tabb to da a makare kike so nazo ai da zafi-zafi akan bigi arfe, wallahi bazan tsaya wasa ba ai banga sauran zama ba, daga yau ma bazan sake daWewa a nan ba, tunda na samu kin amshi soyayah to dole na ringa dawowa ina ganin ki naji daWi a zuciya ta .



 Hmmm naji yanzu de ka rabu dani haka, zanje na cigaba da taya umma aiki anjima in na gama aikin sai muyi wayar .  Ah maza-maza kije kar kibar umma da aiki, amma in kin gama ki kirawo ni pls .  Tom shikenan zan kira .  Hmmm meenal Wina nasan halinki ba zaki kira ba kullum haka muke dake amma zan kintati lokaci in kin gama na kiraki da kai na, dan Allah ki gai da min da umma da kyau .  Tom shikenan yaya waleed zata ji sai anjima .



Daga haka meenal da waleed su kai sallama zuciyoyin su cike da aunar da kewar junan su.......



DOCTOR ASHMAL



Wunin yau gaba Waya jikin sa a sanyaye yake, yana duba mutane ne kawai amma shi kan sa yasan baya jin daWin zuciyar sa yarda kasan anyi mai mutuwa haka yake ji.



Sai da yayi sallah magriba ya samu ya futo daga hospital, direct ya shige motarsa sai gida.



Yana isa gida ya shiga toilet yayi wanka, sanan ya Waura alwala yasa jallabiya ya nufi masallaci, bayan yayi sallar isha'i gida ya dawo, ya zauna akan daining su kayi dinner shi da mutan gidan harma dady.



Suna yi suna tsokanan junan su suna wasa da rahama, amma doctor ashmal sam ya kasa, sa baki a hirar tasu, sabida shi tunanin sa da hankalin sa duk sun karkata wajan ma'eeshat.



Suma su momy sun lura doctor ashmal ya canza baya mood mai daWi, dan haka rabuwa su kai da shi kar su takura mai, duk da basu wani saba ganin sa a cikin wanan halin ba, amma sai su kai tunanin ko a hospital ne yaga abinda yasa jikin sa yayi sanyi ko wani abu makamancin haka de.



Bayan doctor ashmal ya gama cin abinci miewa yayi yabar wajan, gaba Waya ya manta da mutane a wajan bare yayi musu sallama kamar yarda ya saba yi musu kullum, cikin farin ciki suke rabuwa.



Yesmeen kamar za tai kuka tace  momy wai yau mai yake damun yah ashmal ne? .



Girgiza kai momy tai tare da cewa "a'a yesmeen ban sani ba may be de abunuwa ne, su kai mai yawa ki barshi ya huta zuwa gobe za kiga ya dawo dai-dai .  Dady to kai kasan meke damun shi? yesmeen ta faWa tana kallon dady. fadeel da muhseen dariya suka kwashe harma da momy, shima kan sa dady sai daya dara.



 Dady nayi tambaya kuma kuna yimin dariya sabida kunga yah ashmal baya nan ko? .



 hmmm auta kenan ai dole ai miki dariya, momy ma da take gida tace miki bata sani ba, bare ni da ba a gida na wuni ba, kuma kamar yarda momyn ki ta gaya miki may be busy ne yayi masa yawa, zuwa gobe zai dawo dede ki kwantar da hankali ki ....



Doctor ashmal yana komawa bedroom ya ure a.c sannan ya Wauko wayarsa, ya lalubo number ma'eeshat ya fara kira. har sai da ta kusan tsinkewa ma'eeshat ta Waga ba tare da tace komai ba. shima kuwa doctor ashmal Win bai ce komai ba yayi shiru yana sauraran ta.



Ma'eeshat da taji shirun yayi yawa wani dogwan tsaki taja tare da katse kiran. doctor ashmal kuwa kira ya sake yi, amma har ta katse no answer, dama yasan zaiyi wuya ma'eeshat ta sake Waga number.



Gajeran message ya tura mata kamar haka" Please ki Waga mana ina so muyi magana ne .



angaran ma'eeshat kuwa, gani tai an turo mata message, amma tun daga saman wayarta karanta shi ba tare da ta shiga ba, shi yasa har lokacin bata gane doctor ashmal Win bane bare ma taga tsowan message Win daya taSa shiga tsakanin su.



Tana gama karanta message Win, wani kira ya shiga, Wauka tai kamar yarda ya buata cikin faWa-faWa tace "wai wane wallahi in ba'ayi magana ba bazan sake Wagawa ba .



Cikin siririyar murya ma'eeshat taji ance  nine .



Ma'eeshat har tsakiyar kan ta taji maganar tasa, tana son tuna inda tasan muryar ta kasa, amma dan haka arawa tai da cewa "kai wa kuma?". ba tare da Sata lokaci ba, ya sake bata amsa da "ni doctor ashmal............



wanan page Win friday ne, amma bana posting ranar weekend.



Kar ku manta da yimin like (rejected)



Ayi share and follow my channel.



mu haWe a next page.







_page 11





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Gaban ma'eeshat faWuwa yayi rass rass rass har sau uku. Sabida tsabar mamaki ko wawaran motsi ta kasa bare tai magana. Doctor ashmal kuwa cewa yayi "kina jin na?".



Aro jarumta ma'eeshat tai tare da cewa  eh ina jin ka ina wuni? . Murmushi doctor ashmal yayi tare da cewa "ina wuni .



Yamutsa fuska ma'eeshat tai tare da cewa  ina wuni kuma, ni kake gai dawa sai kace wata tsohuwa? . Cikin mamaki doctor ashmal yace  oh sai tsofaffi ake gaidawa kenan? .  Eh gaskiya de ni bana son a gaishe ni sai naji kamar an mai dani tsohuwa .



 Hmmm tom shikenan tunda bakya so na karSi abata, yakike? .murmusawa ma'eeshat tai tare da cewa  lafiya alau ashe kai ne kake ta kira sai kayi shiru, kayi hauri kaga nayi tunanin wani ne har faWa nai ban sani ba .



 No ba komai, Ya jikin naki kuwa fatan kin samu lafiya? .  Ah jiki da saui ma, dama rashin bacci da wuri ne, da banayi sabida exams, kuma yanzu nasha magani na warke sosai .  Tom masha allah ya makaranta fatan de ba'a yi miki demotion Win da kike tsoro Ba Koh? .



Dariya ce ta wacewa ma'eeshat tare da cewa  kai! kai! kai!, dama kana magana kenan .  A'a ba sosai ba kawai arfin hali nai sabida kar a kashe min wayar ai Wauka .



 A'a taya za a kashewa manya irin ku waya, ai mu bamu kai ba, jarabawa ta alhamdulillahi tayi kyau sosai, ba za ai min demotion ba na cinye .

 Ah masha allah haka ake so to Allah ya bada sa'a .  Ameen doctor nagode sosai ma'eeshat ta arasa maganar tana sakin siririn murmushi.



 Ok ba komai bari na barki haka kar na takura miki ki gai damin da afnan . ma'eeshat har zata ce a'a bai ishe ta ba kar ya kashe amma sai taga kamar yarfi ne, dan haka murmushi ta sake yi tare da cewa  tom in sha allah zan gaya mata kuwa .



 Yauwa fatan next time in na sake kira za'a daga min waya? .  sosai ma in sha allah duk sanda ka kirawo zan Wauka .  Yauwa nagode sai anjima daga haka doctor ashmal bai sake cewa komai ba ya katse wayar.



Ma'eeshat kuwa yana katse wayar ta fara birgima akan bed cikin farin ciki tace "wayyo daWi zai kashe ni, wayyo Allah nah alhamdulillahi wai ni wanan kyakyawan mai aji ya kirawo oh Allah ya dubi zuciyarta Allah nagode ma wallahi yeeeeee .



Haka ma'eeshat ta kwanta tana ta burgima da murna tana sake godewa Allah bisa ni'imar da yayi mata. Jim ma'eeshat tai a fili tace  tom Allah de yasa so na yake yi, allah ka dubi zuciyata, Allah dan darajar annabi Muhammad s a w kasa yace yana so nah, Allah kana gani nima ina son shi tun sanda na fara ganin sa .



Haka de ma'eeshat tai ta sambatu tana addu'o'i a kan doctor ashmal ya furta mata kalmar so. ma'eeshat har Allah-allah take gobe tayi ta haWu da aminiyar ta meenal ta bata labarin yarda doctor ashmal ya kirawo ta da kan sa. cikin wanan tunanin bacci yayi awan gaba da ma'eeshat Win....



Bangaran doctor ashmal kuwa yana ajiye wayar ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya tare da cewa  alhamdulilahi, Allah nagode ma, wai dama ashe haka soyyayyah take. iri-iri na kasa sukuni sabida soyayyah ya ilahi, Allah de kasa ta amince dani .



Doctor ashmal ji yayi zuciyar sa tai masa wani sanyi sosai da sosai, gaba Waya farin ciki ya rufe shi ta ko ina, jikin sa har wani wari ya sake yi lokaci guda yaji babu damuwar a zuciya sa.

Daran yau de cikin farin ciki doctor ashmal ya kwanta bacci, haka yayi ta tunanin ma'eeshat har bacci yayi awan gaba da shi, shima.



MEENAL



Meenal tana shigowa motar ma'eeshat ta sakar mata murmushi tare da cewa  ke yau fa da labari . itama meenal murmushi ta saki ta rufe murfin mota sanan tace "kai ma'eeshat ai kya bari mu gaisa daga shigowa sai labari kuma .



Dariya ma'eeshat tai sanan tace  hmmmmmm rabu da gaisuwar nan ke de kin san jiya da daddare mai ya faru kuwa? . Girgiza kai meenal tai tare da cewa  a'a sai kin faWa ina jin ki .



 Daran jiya ma'eeshat ta faWa tana dafe irji tare da sakin wani kyakyawan murmushi.  kai ma'eeshat kin fiya jan aji mai akai a daran jiyan kuma? . Gyara zama ma'eeshat tai tare da cewa  ina wanan doctor Win da wanaki afnan ta Wauko mai waya har yazo ya karSa .



 Eh na tuna shi, wanan de Wan kyakyawan Koh?  Shifa meenal, kin san jiya kirana yayi da daddare wai mu gaisa har da yimin ya jiki fatan naci exams .  Ah masha allah garin yaya ya samu number ki? .



 Hmmm kin manta da wayar ta kusan Waukewa bake kika ce na Wauko number sa ba har na kirawo shi bai Waga ba, daga arshe kuma na tura mai message yayi min reply .  eh na tuna tanan ya samu number ki ashe to alhamdulillahi allah ya temake ki dama kuwa kin yasa sosai .



 Hmm wallahi kuwa meenal amma matsalar bai cemin yana so na ba fa wallahi . Dariya meenal tai tare da cewa  kai ma'eeshat harda sauri haka komai a hankali akeyi, in sha allah zai ce yana son ki kar ki damu .



 Ameen meenal tawa nagode sosai nifa wallahi in yace yana sona har azumi zanyi sabida farin ciki in gaya miki .  kai! kai! kai! gaskiya ma'eeshat kin kamu da yawa har azumi nawa zaki yi to? meenal ta arasa maganar tana tsare ma'eeshat da Ido.



 Azumi 1 zanyi ba yawa  oh to da saui lallai ma'eeshat kin iya faWawa soyayya wallahi .  hmmm meenal kenan wallahi guy Win ne ya haWu ba lefi duk abinda nake so a Wa namiji yana da shi har ya wuce yarda nake tunani ma .



 To allah ya baki shi, wai kin san waleed gobe zai dawo kuwa? . Wan zaro ido ma'eeshat tai tare da cewa  haba de, masha allah wato kun kusan ku haWu kenan .



murmushi meenal tai tare da cewa  eh zamu haWu mana tunda sabida ni zai dawo ma .  ah ai meenal ko baki faWa ba nasan sabida ke zai dawo, in kika ce dawowar kan sa ne ai aryata ki zanyi ma, to tunda ni kai na ban san zance ba, kuma kwanaki ya gayamin in de baki amince da soyayya sa ba baze dawo nan kusa ba .



 Kuma kin san, yace har baba zai zo ya gaisar in ya dawo? .  Ah masha allah wallahi meenal lamarin nan yana tafiya yarda ya kamata, yanzu yana dawowa kawai ai sai asa muku ranar aure .



 Kai ma'eeshat ke baki da magana sai ta aure, ina de so baba yasan da zuwan sa, sabida kar muyi ta abu ba izini amma maganar aure ni de ba yanzu ba sai na gama karatu na .



 Wai sai ki ta cewa karatu karatu, wallahi yarda waleed yake son ki zai barki kiyi karatu ko kunyi aure kin san yana da sauin kai sosai ba ruwan sa .  eh gaskiya in de ta wanan Sangaran ne nasan bani da matsala da waleed yace min ma, ko da munyi aure zai barni na cigaba da karatu na .



 Yauwa ko ke fa, wallahi meenal gwara muyi auran nan yanzu de kin san duniya tazo arshe .  hmm ma'eeshat kenan tom shikenan Allah uban giji ya tabbatar mana da alkhairi .  Ameen ya rabbi meenal .



To fah, yau ma'eeshat ta kasa tsaye ta kasa zaune tun arfe bakwaii na dare har zuwa 11 na dare take jiran doctor ashmal ya kirawo ta amma shiru kake ji, gaba Waya jikin ma'eeshat yayi sanyi dole haka ta haura ta kwanta bacci abun ta.



MEENAL



To yau tunda meenal ta tashi cikin farin ciki take over, sabida yau masoyinta zai dawo waleed. Ji take kamar kar taje school saboda zumuWi. gashi waleed yace mata a yau Win zai zo yana dawowa, tunda a jirgi zai dawo.



Lokacin da aka taso daga school, meenal tacewa ma'eeshat tazo suje gidan su, sabida ko da waleed yazo ba zata iya sakin jiki sosai ba. ma'eeshat ta amince da hakan dan haka direct suka wuce gidan su meenal.



Bayan sun isa sunyi wanka sunci abinci, ma'eeshat taya meenal shirye-shiryen tarbar waleed tai. ma'eeshat tana ta tsokanar meenal akan bakin ta yai rufuwa saboda sahibin ta waleed zai dawo, suga juna. To misalin arfe biyar meenal ta gama shiryawa taff tayi jigum tana jiran zuwan waleed da yake yace mata gashi nan zuwa, yana kan hanya.



ma'eeshat Wagowa tai ta kalli meenal tare da cewa "kai meenal gaba Waya kin kasa samun nutsuwa tun dazu sai duba waya kike yi, mai kike dubawa ne wai? .  hmmm wallahi ma'eeshat ba zaki gane ba, wai kar naje ya kira ban ji ba . Wata dariya ma'eeshat tai tare da cewa  baki saba bane wallahi shi yasa, gashi dama ba wata magana kuka saba yi ba mai tsayi ido da ido ba, sai de gaisawa Koh? .  Eh gaskiya kam bamu wani taSa magana mai tsayi ido da ido ba .



 Hmmm gashi kuma yau takanas zai zo wajan ki Koh, hmm inye lallai za'a sha soyayya hajiya meenal . girgiza kai meenal tai tare da cewa  kai ma'eeshat ni bana son irin haka ai sai ki ta sawa ina jin kunyar wallahi .



Ma'eeshat tana oarin magana ringing Win wayar meenal ya katse ta, kallon meenal tai wanda gaban ta ya faWi rasss, sanan tace  shine yake kiran naki? . Jiki na rawa meenal tace  shi ne wallahi .



Murmushin ma'eeshat tai tare da cewa "to meye haka maza ji Waga mana" jiki na rawa meenal ta Wauka tare da karawa a kunne tana cewa  hello salama'alaikum . Bayan meenal tai Jim, cewa tai  tom shikenan gani nan zuwa daga haka ta katse wayar.



 Ma'eeshat kinji wai har ya araso, masha allah gaskiya yaya waleed bade wawalwa ba har ya gane watance da nai masa? . Murmushin ma'eeshat tai tare da cewa  eh yana da ganewa zaki ce, wanakin baya fa sai da ya tuso eyata yace sai na rako shi gidan ku, lokacin kin tsane shi, Ni kuma na rako shi, amma ban gaya miki ba .



 Kai Allah sarki kice ya daWe da zuwa gidan, amma ya kama mutuncin sa da baya zuwa sai da muka dedeta .  wallahi kuwa meenal da wani mayan ne ai da tuni ya ishe ki da zuwa, ki tashi ki je ku gaisa sai ki shigo da shi Koh? .



Girgiza kai meenal tai tare da cewa "kai haba ma'eeshat kin san de bazan iya zuwa ba dan Allah ki raka ni mana .  To tashi muje, bari na Wauko mana mayafai naki :



 A'a ni de gaskiya hijab zan sa jibi fa haka zai ganni, gani masha allah, komai sai ya futo fa in nasa hijab . hararar meenal, ma'eeshat tai tare da cewa "ke dallah ki Wauke mayafin kisa, shi hijab Win da kike cewa kika sa shi ai sai anfi ganin jikin naki, saboda kwanciya zai yi a jikin ki, wallahi kisa mayafin ki sai kin fi kyau ma .



 Tom bari na Wauko mayafin amma de ni wallahi mayafin ne in nasa sai naji kamar ana ganin jiki na . daga haka meenal ta Wauko musu mayafai ita da ma'eeshat Win. meenal rufe jikin ta tai sosai kamar wata matar aure. Itama kuwa ma'eesha yafa nata tai yafan 'yan mata sanan suka jera suka fuce abun su, zuciyar meenal sai bugawa take bum!

9 / 38