Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   27 / 38

78K to 81K   out of 111.1K words

yasa meenal lumshe ido sannan ta mai da kallon ta kan sa.



Shima waleed a dede lokacin ya Wago ido yana amsa sallamar su meenal Win. karaf su kai 4 eyes shi da meenal a tare gaban meenal da waleed ya faWi rass, rass,rass, har sau uku cikin ananin lokaci meenal taji shauin waleed ya kamata sosai, duk da kuwa bata da ishashiyar lafiyar da zataji shauin namiji a halin yanzu.



Lumshe ido meenal tai sannan ta zauna asa ba tare da tace komai ba,. ma'eeshat kuwa bama ta kai da zama ba, ko me ta tuna oho ta fuce daga fallon da sauri tana cewa "meenal ina zuwa".



Meenal tana Wagowa suka sake haWa ido da waleed Win, amma wanana karan meenal ji tai ta kasa janye idanunta. haka suka cigaba da kallon-kallon juna, meenal tana so ta janye idon ta amma ta kasa wani irin shaui da nutsuwa take samu a tattare da waleed da suka haWa idonun su.



Shima Sangaran waleed Win wata nutsuwa yake samu harda ajiyar zuciya yake saukewa. can de meenal tai arfin halin janye idanuwan ta tare da cewa "ina wuni"?. murmushi waleed yayi sannan shima yace "ina wuni meenal Wita".



"lafiya alhamdulilahi yakake ya hanya fatan ka sauka lafiya". "lafiya alhamdulilahi ya arin haurin mu kuma allah ya jian baba da rahma". gyara zama meenal tai tare da cewa "hauri da godiya ameen ameen nagode".



"Ba godiya tsakanin mu meenal nima ai babana ne Allah yasa can tafi masa nan Win" meenal sake amsawa tai da"Ameen ya rabbi". daga haka meenal miewa tai tare da cewa  bari na kira maka umma kai mata gaisuwa ko?". jinjina kai waleed yayi tare da cewa  tom shikenan babu damuwa . waleed yana rufe baki sai ga ma'eeshat ta dawo, cikin mamaki ma'eeshat tace "ah har kun gama gaisawar ne?" "eh umma zanje na kirawo yayi mata gaisuwa".



"To ki zaman ki ni bari naje na kirawo ta daga haka ma'eeshat ta juya ta sake futa. meenal zama tai ba tare da ta sake cewa komai ba, shi kuwa waleed ya zuba mata ido kamar wani tsowan maye.



Ba'a wani jima ba sai ga ma'eeshat da umma sun shigo, waleed har asa ya tsuguna ya gai da umma tare da yi mata gaisuwar baba, cikin sakin fuska umma ta amsa tare da yiwa waleed godiya, daga haka ba jimawa umma ta tashi ta koma ciki.



Shima waleed Win miewa yayi duk da kuwa be so tafiya ba, amma yaga meenal bata wani bashi fuska ba kuma, yaga har time Win mutuwar bata sake ta ba, ba zasu samu damar ganawa sosai ba. haka waleed yayiwa meenal sallama, jiki a sanyaya ya fuce abin sa.



DADY



Zuciya cike da damuwa dady ya nufi bedroom Win mommy, yana zuwa ya murWa handel Win ofar ya shige baki Wauke da sallama. momy kuwa bama ta san dady ya shigo ba dan tana zaune ta rafka ukan tagumi, ta tafi duniyar tunani.



Dady arasawa gefan momy yayi ya zauna tare da Wan dafata, firgigit momy ta dawo cikin hayyacin ta. aalo murmushin dole tai tare da cewa "ah yaushe ka shigo, ka bani tsoro haka ake shigowa ba sallama".



Hmmm in banda abinka momyn dtoctor ina zakiji sallama ta kin tafi dogwan nazarin nan?". "hmmm wallahi dady ina cikin damuwa" momy ta arasa maganar tana sauke ajiyar zuciya. Cikin mamaki dady yace "subhanallahi mai yake damun ki?" cikin damuwa momy tace "kai ma Dady kasan ai baze wuce magana akan iftila'in daya faWa mana ba fadeel ya bige bawan allah nan har ya rasu".



"Allah sarki nima abinda yake damuna kenan, shi yasama na taso afa da afa muyi magana". gyara zama momy tai tare da mai da hankali ta kan dady tana cewa "tom shikenan dady ina ji".



Tunda fadeel ya aikata wannan abun gaba Waya bamu da wanciyar hankali, musamman ma fadeel da muhseen ko ishashan abinci basa ci, bakiga fadeel ba ya zama abun tausayi ba?". gyaWa kai momy tai tare da cewa  eh wallahi dady na gani".



"Kuma ni babban abinda yake Wagamin hankali yarda ahalin bawan allah nan suka zama marayu musamman ma Wiyarsa aminatu, kin san daran da zai rasu mun dade muna magana ashe wasiya yake barmin ataaice ni ban gane ba".



Cikin mamaki momy tace  haba mai yace maka haka? "hmmm munyi magana da shi da dama sosai da sosai, amma ni gaskiya yanzu na yanke shawarar zamu haWa meenal aure da fadeel, saboda gujewa hatsarin wani saurayin da yake bibiyar ta, daran da zai rasu naji mahaifin ta yana ce mata ta rabu da saurayin nan nata, ko bayan ransa bai yarda ta aure shi ba saboda bashi da kyan hali, kuma bayan haka da bakin sa yace min ya bani amanar Wiyar sa ko bayan ransa dan Allah kar na bari ta auri yaron, a zaSa mata miji na gari".



Momy wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "kai gaskiya de bai cancanta a aurawa Amina fadeel ba saboda fadeel yana da rawar kai kuma ko ta aure shi zata cigaba da ganin taban sa a matsayin shi ya kashe mata mahaifi".



Jinjina kai dady yayi kafin yace "tabbas haka ne, amam kin san in bamu Wauki matakin nan ba, wancan saurayin da yake bibiyar yarinyar zai zo ya aure ta". "tom mai zai hana a bata muhseen kawai madadin fadeel tunda shi yafi fadeel nutsuwa" momy ta faWa tana tsare dady da ido.



Dady yayi farin ciki da shawarar momy kuma ya karSeta hannu biyu-biyu. amma sun yanke shawarar zasu aurawa meenal fadeel in mahaifiyarta ta amince, daga nan meenal tai ta dawo gidan, ta zauna wajan momy ta cigaba da karatu na tsawan 3 years kafin nan muhseen ya sake wayo ya kammala nasa karatun.



Amma momy ta shawarci dady da, a bari sai bayan sadakar 7 in sun samu dangana sai ajewa mahaifiyar meenal da zance. Haka de momy da dady su kai ta tattauna yarda lamarin zai kasance.......



mu haWe a next page







_page 36





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Barkan mu da dawowa rubutun littafin DOCTOR ASHMAL, wanda muka tafi hutun azumi, muna fatan Allah uban giji ya karSi ibadun mu.

Ameen..........





Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa Waya daga cikin members Win gidan nan rasuwa, tana bibiyar litattafan mu kuma Waya daga cikin admin din group Win mu na doctor ashmal, dan Allah dan annabi muna barar addu'a a gare ku Allah ya jian Hafsah (oum farhan) da rahma, ya kyautata mawanci yasa ta huta, wallahi munyi babban rashi.=-=-=-=-=-=-



Yanzu zamu cigaba.



To kwance tashi ba wuya a wajan allah yau har anyi sadakar bakwan baba. dare tanayi kowa ya riga ya watse gida ya rage daga umma sai meenal da kuma ma'eeshat.



Washe gari da safe ma bayan sun karya ma'eeshat taiwa meenal sallama driver yazo ya Wauke ta domin komawa gida. Gida ya rage daga umma sai meenal ya Allah.



Lokacin guda mutuwar baba ta dawowa meenal da umma sabuwa a rai, gaba Waya sun kasa sukuni. ko abinci rana basu iya ci ba suna cikin jimami,. umma da meenal basu arasa shiga cikin jimami da tashin hankali ba sai da dare yayi.



Lokacin ne mutuwar ta dawo musu sabuwa kamar yau akayi ta. haka suka sha kukan su suka gode Allah sai umma ce tai arfin halin danne kukan ta, sannan ta rarrashin meenal, suka kwanta bacci a bedroom Win meenal.



duk da wayar meenal a silent take tana gani waleed yana ta faman kiranta, taso Wauka amma umma tana kusa da ita dan haka kifa wayar tai ta share shi sannan ta rufe ido kamar mai bacci. to umma da meenal sam sun kasa bacci idon su ya soye bacci ya aurace musu.



2:00 am ( na dare) umma tacewa meenal gwara su tashi suyi sallah dare, tunda sun kasa bacci suyiwa baba addu'a. haka meenal ta mie suka Wauro alwala ita da umma sannan suka fara gabatar da sallah su.



Baba yasha addu'a wajan umma da meenal, umma da meenal basu suka kwanta ba sai bayan da su kayi sallah asuba, bayan sun idar sun kammala azkhar, komawa su kai suka kwanta ba jimawa bacci ya kwashe su.



Umma da meenal basu suka tashi daga bacci ba sai 1:00pm na (rana) lokacin har an fara kiraye-kirayan sallah azahar. Miewa su kai domin sallah, ita de meenal sai da ta fara watsa ruwan a jikin ta da yake ita mai jin zafi ce sannan ta ta Waura alwala ta fara gabatar da sallah.



Basu daWe da idar da sallah ba suna oarin Wora abinci suka ji an fara wanwasa ofar gida, kallon umma meenal tai sannan ta mike tana cewa "umma bari naje na buWe koh?". "Tom jeki ki duba" daga haka meenal bata sake cewa komai ba ta fuce abinda.



Meenal tana buWe kofa ladidi me aikin momy ta gani tsaye fuska a sake. itama meenal aalo murmushi dole tai sannan ta matsa mata cikin farin cikin ganin ta tace "aunty ladidi sannu da zuwa shigo mana".



Shigowa ladidi tai sannan tace "yauwa hajiya meenal sannun ki de ya kuke fatan na same ku lafiya?" "alhamdulilahi aunty ladidi ina wuni" "lafiya alau alhamdulilahi kin ganni da tsakar rana ko wallahi momy da dady ne suka aiko mu ni da driver amma bari nai masa magana ya shigo da saon, sai in shiga ciki mu gaisa d umma".



Ladidi bata jira meenal ta bata amsa ba ta wuce waje, bata wani jima ba ta dawo, suka shige ciki ita da meenal Win. kamar yarda meenal ta bar ummanta haka ta dawo ta same ta a zauna kan dadduma tana jan carbi.



Amma sallamar ladidi umma tai, nan da nan umma ta faWaWa fuskarta da murmushi sannan tace "ah ladidi sannu da zuwa ga waje zo ki zauna ya hanya?" zama ladidi tai kafin ta fara cewa  hanya alhamdulilahi umma ya kuke fatan na same ku lafiya ya arin haurin baba kuma?" gyara zama umma tai cikin dauriya tace "alhamdulilah ladidi hauri sai ma'aiki" "tom umma Allah ya sake jaddada rahma gare shi".



"Amen ya rabbi, meenal kije ki kawo mata ruwa mana ba kiga yarda ake rana ba" da sauri meenal ta mie ta fuce ita kuma ladidi cewa tai "nagode sosai umma".



Ba jimawa meenal ta kawowa ladidi ruwan pure water guda biyu a plate, sannan ta ajiye a gaban ladidi. "ya wajan su momy fatan kowa lafiya" umma ta tambaya tana gyara zama.



"Ah lafiya alau alhamdulilahi, yanzu dady da momy ne suka aiko mu ni da driver mu kawo muku sao" ladidi tana kai nan da zan can su umma suka ji sallamar driver, daga nan kuma su kaji alamar sauke abu.



Haka su kai tajin shigowar drive da futa da alamun sauke kaya amma ba zasu sheda menene ba. Ladidi bayan ta kammala shan ruwan meenal ta kalla tare da cewa "momy tace tana gai dake da kyau yaushe zaki zo wajan ta ki wana yesmeen ma kullum zan can ki take".



Murmushi meenal tai ta sunkuyar da kai asa ba tare da tace komai ba. to driver ya Wauki kimanin 20 minutes kafin ya gama shigo da kayan nan, sannan yayiwa ladidi waya yana cewa "ta futo su tafi ya kammala".



Miewa ladidi tai hannu rie da wayarta tace to umma zamu tafi ya kammala. miewa umma tai tare da cewa "tom bari mu taka miki" daga haka itama meenal miewa tai domin rakiya.



Suna fita umma da meenal suka daskare da mamaki saka mawan ganin uban himulin kayan arzikin da aka shigo musu da shi. kayan abinci ne kala-kala, manyan buhun shinkafa yar gomnati uku, sannan ga buhun shinkafar tuwo shima uku, ga na basmati shima uku.



Ga taliya katan biyar macaroni katan biyar kuskus ma haka, gefe guda buhun flower biyu da buhun suga Waya, ga kuma doya baje wajan ashirin da dankalin turawa kwando-kwando har kwando shida. sannan ga kwalin magi kala-kala, da jarkokin mai, jad da fari manya Sanya, ga ruwan jarka da lemukan roba katan-katan egg kirat 10 ga kuma kayan miya shima wando Waya, da sauran nau'in kayan abinci.



da sauri ladidi ta buWe jakarta tare da zaro rafa ta sababbin an dubu-dubu, miawa umma tai tare da cewa "kuma ga wannan sun ce a ringa cefane, in kuna da wata matsalar ta kuWi ko wani abun dan Allah ku tuntuSe ta.



Jiki a sanyaye umma ta girgiza kai tare da cewa "a'a ladidi wannan kayan abincin ma da suka kawo da yawa ai zamu shekara muna amfani da shi wallahi ko iya shi ya isa ba sai an aro wani abun ba dan Allah a barshi haka nan .



Girgiza kai ladidi tai tare da arasowa wajan umma tana cewa "a'a umma kinga nima ar aike ce, in baki karSa ba laifi na momy za ta gani dan Allah ki karSa tunda aiko ni akai wallahi ba komai, dan in baki karSa ba ma momy da dady ba zasu ji daWi ba".



ladidi ta arasa maganar tana sawa umma kuWin a hannuwan ta bibiyu. hannu na ruwa umma ta karSa baki na rawa tace  mungode sosai ladidi dan Allah ki sanar da mutanan arzikin nan mun gode sosai duniya da lahira Allah ya saka da alkhairi, meenal maza ki Wauko wayarki ta baki number hajiya mu biga muyi mata godiya".



Da sauri itama meenal jiki na rawa ta nufi Waki domin Wauko wayarta ba jimawa ta futo hannu rie da waya. nan da nan saratu ta hau karantowa meenal number momy, meenal tana sawa. Bayan ta kammala sawa har bakin ofa meenal da umma suka raka saratu umma tana faman sake bawa saratu saon godiya.



Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa Waya daga cikin members Win gidan nan rasuwa, tana bibiyar litattafan mu kuma Waya daga cikin admin din group Win mu na doctor ashmal, dan Allah dan annabi muna barar addu'a a gare ku Allah ya jian Hafsah (oum farhan) da rahma, ya kyautata mawanci yasa ta kin huta, wallahi munyi babban rashi.=-=-=-=-=-=-



Pls duk sanda kuka karanta book Win nan kuyi mata addu a.



Bayan ladidi ta futa rufo gidan meenal tai sannan ta juyo ta kalli umma wanda gaba Waya mamaki ya gama malale fusakr ta. Baki na rawa umma tace "meenal kinga abun arziki koh?" itama meenal cikin mamaki ta bawa umma amsa da  eh umma na gani gaskiya mutanan nan suna da kirki sosai Allah ya saka musu da alkhairi".



"Ameen ya rabbi meenal, yanzu de bari mu washe kayan mu kai su ciki saboda rana daga nan sai ki bugawa hajiyar in mata godiya". to meenal tace daga haka umma da meenal suka arasa ciki bayan sun ajiye kuWin suka hau washe kayan.



FADEEl.



Har lokacin hankali fadeel bai wanta ba duk ya rame ya zama abun tausayi. momy da dady harma da sauran mutan gidan duk sun tausaya masa, ganin lokaci guda yarda ya zama abun tausayi. Haka momy da dady suka dawo rarrashin fadeel suna nuna masa kaddara ce tunda bada sani yayi ba amma, ya ringa istigfari.



sannan daday ya shawarci momy akan ya kamata fadeel ya fara azumin kaffara na alhakin kisan kai da yayi bisa rashin sani. momy ta goyi bayan dady, sannan kuma ta bashi shawara akan ya tura shi saudiya, sai yayi azimin acan sai yafi masa saui kuma yafi samun nutsuwa yana yi yana ibada acan.



Dady yayi na'am da zancan momy sannan kuma yace sabida fadeel yaji daWin hankali sa ya dawo cikin jikin sa, ya kamata a tura shi, shida Wan uwan sa muhseen saboda Webe kewa. Ai kuwa haka akai cikin one week dady ya kammala komai visa su ta futo shi da muhseen, dama already sun gama shirya tafiyar dan haka tashi su kai zuwa saudiya& & ..



an garan Doctor da ma'eeshat kuwa soyayya su sai ara zafi take suna sake son junan su, kullum sake shauwa suke sun zama an soyayya sosai, musamman ma doctor kamar ya cinye ma'eeshat baya bari yaga tana cikin Sacin rai itama ma'eeshat Win tana kiyaye nata.



Ma'eeshat har ta fara shirya-shiryan komawa school da yake takaddun ci gaba da karatun su ita da meenal ya futo amma sai abba yace ita ma'eeshat ta fara zuwa, ita kuma meenal sai mutuwa ta sake ta in anyi arba'in haka sai ta fara zuwa itama.



MEENAL



Yau kimanin too weeks da mutuwar baba. meenal tana kwance a Waki bayan sallah la'asar tana ta tunani iri-iri na rayuwa, taji wayarta da take gefe ta fara ringing. meenal ajiyar zuciya ta sauke sannan ta Wauki wayarta ta.



Wanda meenal tai tunani shi Win de yake kira wato waleed, tunda baba ya rasu basu wani samu damar yin magana sosai ba gaisuwa ce kawai take haWa su. gyara kwanciya meenal tai, kafin ta Wauki wayar a nitse sabida har ga Allah taji daWin kiranta da yayi dan tana cikin tsananin kewar sa.



Bayan meenal ta amsa sallamar da waleed yayi mata cikin mutunta juna suka fara jin lafiyar junan su. Waleed sai oarin jan meenal yake da hira meenal tana kaucewa sai de ta bi shi da eh da to. Tun meenal tana iya dannewa har ta fara biyewa waleed suna hirar soyayya dan gaba Waya in taga waleed ya bugo mata mantawa take an yi mata wani tsakani da shi ma.



Meenal sun Wauki 30 minutes suna waya ita da waleed yana mugun sata a nishaWi da farin ciki, dan raban da ta shiga irin farin cikin da yake sata yanzu tun kafin baba ya rasu soyayya suke sha haian abun su, waleed shima daWi yake ji sosai yarda yaji meenal ta bashi fuska, farin ciki yake kamar an masa bushara da gidan aljannah.



Meenal da waleed suna cikin wannan yanayin na mosaya umma ta shigo Wakin meenal baki Wauke da sallama. tsayawa cak umma tai tana kollon meenal, raban da taga Wiyarta cikin farin ciki kamar haka har ta mance.



Ko ba'a gayawa umma ba, umma tasan meenal da waleed take waya. umma gyaran murya tai tare da sake sallama, a taaice de sai da umma tai sallama sau uku amma ina meenal bata sani ba ta tafi duniyar masoya.



arasawa umma tai kusa da meenal sannan ta fara taSata, firgigit meenal ta Wago, tana ganin umma a tsaye tai saurin katse wayar

27 / 38