Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   30 / 38

87K to 90K   out of 111.1K words

yarda umma ta faWa haka taga meenal kwance tana bacci tasa riga iya guiwa kan ta ba dan kwali duk gashin kanta ya baje ya rufe mata fusa.



Ma'eeshat bata tashi meenal ba ajiye jakarta tai sannan ta cire mayafin ta, ta fuce daga bedroom Win meenal. daga haka ta wuce kicin ta fara taya umma girki, ma'eeshat tayi farin ciki sosai ganin umma tana dafa dambun shinkafa, saboda ma'eeshat tana bala'in son dumbu a rayuwarta.



cikin farin ciki ma'eeshat tace "lah! umma kice yau favorite Wina kike girkawa". itama umma murmurshi tai tare da cewa  eh wallahi kinga kamar nasan yau zaki zo, kinga na dafa a sa'a ai" "eh wlh umma gaskiya naji daWi sosai dama na jima banci ba", "aikuwa yau za kici ya ishe ki kuwa". to haka umma da ma'eeshat suna girki suna hira abun su. umma tana gayawa ma'eeshat irin halin damuwa da meenal take ciki.



ma'eeshat kuwa cewa umma tai, ya kamata meenal ta koma school in suna tafiya school tare, tunda meenal tana son makaranta maybe zata dawo normal in tasa karatu a gaba zata manta da komai, saboda meenal ma'abociyar son karatu ce sosai.



Umma ba tayi wani dogwan nazari ba ta amince saboda ita har ga allah ta gaji da ganin yarinyarta meenal cikin wannan halin, saboda duk wani rarrashin duniya da ban baki tayiwa meenal, duk da kuwa meenal Win tana nunawa umma ba komai, komai ya wuce amma, umma ta fahimci meenal tana cikin damuwa, kuma in ta tambayeta sai tace ba komai.



Bayan umma da ma'eeshat sun gama yin dambun shinkafa, umma cewa tai "yauwa aishatu tunda ya sauka sai ki zuba kici yarda kike so". murmurshi jin daWi ma'eeshat tai kafin tace "a a umma ki bari sai meenal ta tashi sai mu ci tare da ita, saboda in muna ci tare da ita sai dumbun ya fiyemin daWi".



"Tom shikenan, bari naje na arasa wanke-wanke can". da sauri ma'eeshat ta ruo hannu umma tare da cewa "haba umma ki bari ni zanyi kafin meenal Win ta tashi" "aa ki barshi aishatu kinga rigar jikin ki me dogon hannu ce nasan halinki sai kin Sata jikin ki da ruwan wanke-wanke". dariya ma'eeshat tai tare da cewa tom bari naje na canza wata mara dogon hannun, dan allah umma ki bari nayi Ina so".



Daga haka ma'eeshat bata bari taji amsa umma ba ta wuce bedroom Win meenal domin canzo wata rigar. ma'eeshat tana son tayi wanke-wanke saboda a gidan su bata saba yin wanke-wanke ba ar aiki ce take yi, kafin ma ta tashi daga bacci, in kuma an tara na rana tana can sabgar gabanta ko school bare ma tayi".



in wataran ar aikin su bata jin daWi kuma akace sa'a ma'eeshat tana gida in mami tacewa ma'eeshat tai wanke-wanke har daWi take ji. bayan ma'eeshat ta buWe wabar kayan meenal ta bacci, daga sama taga wata riga iya guiwa mai siririn hannu. irin ta jikin meenal Win ce sak, kalace kawai ta babbanta, zaro rigar ma'eeshat tai da sauri sannan ta rufe kwabar a hankali saboda bata so arar ta tashi meenal daga bacci.



Daga haka ma'eeshat ta cire kayan jikinta tasa rigar, ko tsayawa kwashe kayan nata ba tai ba in da ta cire haka ta mai da, ta fuce, saboda taje tai wanke-wanke. ma'eeshat tana isa wajan kwaninka ta tsuguna ta fara haWa kunfa, saboda umma ta tarar mata ruwan wanke-wanke ma a fomfo ba Sata lokaci ma'eeshat ta fara wanke-wanke.



Duk da kwanikan basu da wani yawan arziki sai da ma'eeshat ta Wauki muntuna da yawa tana wanke-wanke kafin ta gama, sannan ta koma kicin taje ta kife su. bayan ta futo ta Wauki tsintsiya ta fara sharce wajan wanke-wanke. "manya gari saukar yaushe". muryar meenal ma'eeshat taji tana mata magana ta bata.



Da sauri ma'eeshat ta juyo tare da cewa  har kin tashi kenan ai ni na daWe da zuwa kiji in gaya miki".ma'eeshat ta arasa magana tana sakin murmurshi kamar yarda meenal Win take saki. "Amma shine baki tashe ni ba" meenal ta faWa tana bin ma'eeshat da ido. girgiza kai ma'eeshat tai tare da cewa "aa meye na tashin ki kina bacci, yanzu ba gashi kin tashi ba".



Takalmi meenal ta saka tare da cewa "amma da kin tashe ni bari nayi alwala, saboda yanzu za kiji an fara kiran sallah la'sar". daga haka ma'eeshat da meenal suka Waura alwala bayan sun koma suka shige bedroom Win meenal. "ma'eeshat nasha gaya miki in kika cire kaya ki dena ajiye su asa ba kyau". meenal ta arasa maganar tana duusawa asa tana Wauke rigar ma'eeshat Win".



Bayan meenal ta Wauke durowa ta buWe ta Webo musu hijaban sallah. meenal tana juyowa cikin mamaki tace "haba ma'eeshat wannan kalar kallon da kike min, nasan akwai zance mene?". "warai kuwa meenal akwai, kinga yarda kika waWa ido yayi zuru-zuru me yake damunki? ma'eeshat ta arasa maganar tana yiwa meenal kallon tuhuma".



Ajiyar zuciya meenal ta sauke tare da cewa "ma'eeshat kenan ke har sai na gaya miki damuwata ai kin san damuwata uku ce mutuwar baba, waleed, da kuma engagement Win da aki min na dole wanda ban so ba" ma'eeshat tana oarin magana suka ji an tayar da sallah, dan haka ba wanda ya sake cewa komai a cikin su, meenal ta shinfiWa musu dadduma suka fara gabatar da sallah.



Bayan sun idar sun kammala addu'o'i da lazimi, miewa ma'eeshat tai. kallon ta meenal tai tare da cewa "ina zuwa kuma?". "abinci zan zuba mana yau umma ta dafa mana favorite Wina tun dazun yawuna yake tsinkewa ina so naci amma nace sai kin tashi daga bacci zan ci to yanzu gaskiya na gaji da hauri". ma'eeshat ta arasa maganar tana fucewa daga Wakin.



Meenal murmurshi tai ba tare da tace komai ba sannan ta janyo wayarta ta fara dannawa. Ba a Wauki muntuna masu yawa ba ma'eeshat ta dawo bedroom Win hannu rie da madedecin ture wanda ta cika shi da dambu dam har wani tsiri yake. bayan ta ajiye ta sake fita ta Wauko tasar soyayye mai tare da robar yaji.



Bayan nan bata zauna ba sai da taje ta Wauko musu leman kwali da ruwan jarka tare da 2 cups. ajiye wayar meenal tai a gefe tare da sake faWaWa fuskarta da murmurshi tana cewa "hmmm rabin rai sannun ki da aiki, yanzu wannan duk uban abinci zamu iya cinyewa kuwa?". murmurshi ma'eeshat tai tare da sauke ajiyar zuciya tana gyara zama, sannan ta Wago ta zubawa meenla kallon kan ki ake ji.



sorry kwana biyu kun jini shiru-shiru ko, wlh na tafi hutun da ba shiri ne but yanzu in sha allah na dawo...



Aringa yimin reaction kuma ga link kuyi following Win channel Wina, dan samu posting da zarar na Wora.



Game bukatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga



link din channel yayi fallowing.

https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d





_page 40



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Daga haka ma'eeshat ta Wauki spoon ta fara cin dumbun ta, tana kai lomar farko baki, taji daWi har kwanyar kanta, ai ma'eeshat bata san sanda ta ajiye spoon Win, ba ta cigaba da ci da hannu, saboda gani take sai tafi gamsuwa. meenal murmurshi ta saki tare da Waukar spoon Win ta fara ci a nitse.



Ma'eeshat sai da taji cikinta ya fara Wauka sannan tace "meenal ki dena sa damuwa a ranki karki Waurawa kan ki ciwan zuciya fa". ajiye spoon Win hannnu ta meenal tai cikin damuwa tace "ma'eeshat na gaji da rayuwar nan gwara ciwan zuciya ya kamani zuciyar tawa ta buga kowa ya huta".



"A uzubillah meenal kin san me kike faWa kuwa". ma'eeshat ta faWi haka cikin tashin hankali tana tsare meenal da ido. "hmmm ma'eeshat ba zaki gane ba wallahi duniyar nan ta ishe ni, na rasa mahaifina kuma anaso a rabani da wanda nake so, sannan za a auramin wanda ban san shi ba ban taSa ganin sa ba".



"A'a meenal ki dena faWin hakan wallahi muna son ki bamu gaji dake ba, in sha allah mutuwa ba yanzu ba, ki dena damuwa ki barwa allah komai zai share miki hawaye nima ina nan ina tayaki da addu'a, komai zai dedeta. kuma Bama ke Waya ba nima ina so nasan wanda zaki aura amma doctor ko da wasa bai taSa yimin maganar ba, kuma gashi doctor baya son mutum ya ringa shiga abinda bai shafe shi ba, shi yasa nake shakkar tambayar sa, baya gayamin komai da ya shafi gidan su. Bani ba de yana yimin zance anwarsa yesmeen dan naga yana aunarta".



"ma'eeshat ni ba wai sanin wanda ake so a aura min bane damuwata ko labarin sa, damuwata fa akan bashi yace yana so na ba kuma bai taSa ganina na ba" meenal ta arasa maganar tana zubar da zafafan hawaye". dan allah meenal ki dena kukan nan kamar yarda na gaya miki addu'a itace mafita kawai, maza ki share hawayan ki dan Allah".



kamar yarda ma'eeshat ta roi meenal haka meenal ta fara share hawayan ta. "dan allah meenal ki dena yawan kuka, watarana sai labari, kin san de babban tashin hankali na bai wuce ace na ganki kina kuka ba ko?". murya na rawa meenal tace "hakane ma'eeshat kiyi hakuri na dena".



"Yauwa rabin rai na kin san menene kuwa?" ma'eeshat ta tambayi meenal tana binta da ido. "a'a ma'eeshat sai kin faWa". "shawarar da zan baki shine kizo mu koma school tunda an gama yi mana registration tare, abba ne yace wai a bari mutuwar baba ta sake ki, kuma yanzu kinga in kin koma school zaki cigaba da karatu, in busy karatu yayi miki yawa komai mantawa zaki yi da shi dan allah kizo mu ringa tafiya tare".



"Hakane ma'eeshat nima ina son zuwa school Win nan amma umma ce naga kamar bata so". "in de umma ce matsalar, tom albishir ki" kallon ma'eeshat meenal tai cikin mamaki tace "goro" "yanzu umma ta amince, mu ringa zuwa makaranta". "what! are you shower?" meenal ta faWi hakan fuska Wauke da mamaki da kuma Soyayyan farin ciki.



"eh mana da gaske umma ta amince, yau munyi maganar da ita bayan nazo". cikin farin ciki meenal tace "alhamdulillah ma'eeshat nayi farin ciki sosai wallahi, nasan yanzu de damuwata zata ragu". "sosai ma meenal zakiji daWin school Win sosai, ko mutane kike gani suna zurga-zurga ai zakiji daWi".



"Tom yanzu yaushe zan fara zuwa?". meenal ta tambayi ma'eeshat tana kallon ta. "Monday zaki fara zuwa in sha allah". ma'eeshat ta faWi hakan ciki farin ciki, dan ma'eeshat tafi meenal jin daWin komawar meenal makaranta, gaba Waya bata jin daWin school Win.



Haka meenal da ma'eeshat suka cigaba da cin abinci suna hirar su gwanin sha'awa. itama meenal yau taji daWin zuwan ma'eeshat Win, dan raban da meenal ta saki jiki taci abinci sosai kuma tai hira kamar haka, harta manta. ma'eeshat ta sa meenal cikinfarin ciki sosai, sunci abinci sosai sun oshi kuma sun sha hira harda dariya.



Ma'eeshat ba ita ta fara oarin tafiya gida ba sai da tayi sallah isha'i, ji take kamar karta tafi gida ta wana a gidan su meenal, amma bata sanar da mami zata kwana ba. ko da ma'eeshat zata tafi har waje meenal ta raka ta. ma'eeshat tace zata bigo mata waya ta sanar da ita yarda su kai da abba wajan komawarta school.



Bayan ma'eeshat ta shiga mota driver yaja, meenal komawa tai cikin gida. gaba Waya meenal ji tai tana cikin farin ciki yau, a cikin bain cikinta kaso 100% 60 ya ragu. itama umma ta lura da hakan sabida sai da suka zauna suka sha hira abun su, wanda suka jima basuyi hakan ba.



Sai wajan goma dare meenal tai sallama da umma, bayan sunyi sallama bedroom Winta ta wuce, ta shiga toilet tai wanka sannan tasa kayan baccin ta. tana gama shirin bacci kamar wanda waleed yake jira ya kirawo ta. meenal cikin farin ciki ta shige blanket Win ta mai kauri sannan ta saita muryarta asa-asa yarda ba mai jin abinda take cewa, saboda umma.



Daga haka meenal da waleed suka hau shan hirar su ta soyayya. shima kan sa yau waleed ya gane meenal tana cikin farin ciki, ko da ya tambayeta meenal bata Soye masa ba ta gaya masa school zata koma. shima waleed yayi farin ciki har zuciyarsa, sabida yasan ko ba komai wataran zai iya ziyarta in taje school su haWu.



Har yau waleed bai san anyiwa meenal engagement ba, ko da wasa. ko wajan su mami da abba ma bai ji zance ba bare ma'eeshat kuma. Mami da abba sun yanke shawarar, kar waleed yasan zancan, nan kusa sabida zai iya shiga wani hali, dan sun lura ba aramin so yakewa meenal Win ba.



Ma'eeshat



Bayan ma'eeshat ta koma gida, direct wajan abba ta nufa dan taga alamun yana gida. knocking ma'eeshat take baki ofa, ma'eeshat da taji shiru hakan ya tabbatar mata yana can ciki bedroom Win, dan haka tura kai tai tunda tasan mami bata ciki ta barota a asa, dan da abba yana tare da mami in taji shiru sai dai ta juya, kamar yarda aka basu tarbiyya.



bayan ma'eeshat ta shiga fallon sai da tai sake knocking bedroom Win abba haWi da sallama kafin abba ya bata umarnin shigowa. zaune ta samu abba kan bed ya baje takaddu idon sa Wauke da glass Win arin gani. kusa da shi ma'eeshat ta zauna tare da cewa "abba na sannu da aiki".



"yauwa ma'eeshatu na sannun ki, dana dawo na tambaye ki aka cemin kin tafi gidan su meenal" "eh dady ina can too days ban ganta bane shi yasa naje yau, tunda ita har yanzu naga bata fara fita ba, tun rasuwa baba" "Allah sarki baban amina, allah ya jiansa ya jaddada rahma gare shi" "ameen abba".



"To ya kika baro su ita da umman ta fatan komai lafiya koh" "ah abba duk suna lafiya". "masha allah ya makaranta fatan de kina karatu dayawa koh". murmurshi ma'eeshat tai kafin tace "alhamdulillah abbana ina karatu da yawa sosai da sosai".



"Masha allah haka ake so allah ya temaka a cigaba da mai da hankali sosai" ameen in sha allah". daga haka ma'eeshat ta gyara zama tare da cewa  abba dama akan maganar zuwa makarantar meenal ne, gaskiya ya kamata yanzu ta fara zuwa, saboda karatu yana wuce ta".



jinjina kai abba yayi kafin yace "hakane ma'eeshat amma ya kamata ace anyi ko 3 moths ne kafin ta fara zuwa, baban ta ne ya rasu fa". "Abba zuwa makarantar meenal ne zai sa ta dawo normal gaba Waya yanzu ta canza tana cikin damuwa, meenal tana son karatu, tana komawa school hankalin zai koma kan karatu damuwar da take shiga zata ragu".



"Hmmm gaskiya ne ai sai a hankula zata watstsake dama mutuwa haka take da cin rai bare ma, mutuwar iyaye, to yanzu ita meenal Win tana son ta fara zuwa yanzu, zata amince kuwa" abba ya tambaya yana kallon ma'eeshat. "eh mana yanzu ma da izinin ta nazo na gaya maka, har umman duk sun amince".



"masha allah haka ake so allah ya bada ilimi mai amfani, ranar monday sai ta fara zuwa in sha allah". cikin jin daWi ma'eeshat tace "tom shikenan abba Allah ya kai mu" "ameen aishatu allah yayi miki albarka" "Ameen abbana wallahi ina son ka sosai" ma'eeshat ta faWi hakan tana rungume abban ta gefe.  i love you too my special daughter .



Daga haka ma'eeshat ta tashi tare da cewa "okay abba good night bye". bayan ma'eeshat da abba sunyi sallama ma'eeshat fucewa tai ta kama hanyar bedroom Win ta zuciya cike da farin ciki. tana komawa ta Wauki wayarta ta buWe WhatsApp domin duba saon doctor.



kamar yarda ma'eeshat tai tunani doctor ya turo mata message. bayan ta bashi amsa reply yayi mata da cewa "okay sannun ki da dawowa in kin huta zamuyi waya nima yau da wuri na dawo gida na gaji". "Wani murmurshi ma'eeshat tai naji daWi tare da masa reply da cewa "a'a ba abinda nake na gama komai kwanciya zanyi yanzu, kawai ka bugo musha soyayya mu".



Ma'eeshat tana turawa doctor reply ya saki murmurshi sannan ya danno mata kira ta WhatsApp call. sai da ma'eeshat ta kashe globe Win bedroom Win ta canza zuwa green, sannan ta Wauki wayar tana Wauka, ta wanta tare da shigawa ciki blanket Winta da yake yau ana Wan sanyi sosai a garin tun bayan sallah isha'i.



daga haka de ma'eeshat da doctor suka faWa kogin zumar masoya. soyayya suke mai tsafta ba ruwan su da faWar abinda bai dace ba, ko ma'eeshat ta faWi wani abun wanda bai kamata ba a matsayin ta na yarinya sai doctor ya Wan gwaSeta cikin kulawa da soyayya ya hane ta.



Doctor yasan kan sa yana kare mutuncin sa sosai, koda suna waya feeling Win shi ya tashi yayi masa arfi sallama yake mata ya katse wayar sabida baya so, in ya fita hayyacin sa a samu matsala.



Momy and daddy



angaran momy da dady, babu wanda suka sanar gaba Waya gidan akan engagement Win da akayiwa muhseen da meenal. su kaWai suka san abun so, ko doctor basu gayawa ba, haka momy da dady suke ta fama Soye abun kamar wani sirri. Kamar yarda doctor be sani ba shima kan sa muhseen Win bai san an masa Engagement Win ba.



Momy da dady sun bawa kan su arfin guiwa akan komai zai tafi normal, in lokaci yayi kowa ya sani, amma ba yanzu ba, saboda basa so wani ya kawo musu cikas akan abinda soke so suyi. sabida suna ganin ko ba komai sun ceci rayuwar meenal daga auran waleed, dan su momy kallan mutumin banza sukewa waleed.



Ga shi momy tana son meenal har cikin ranta, shi yasa take so nan da 'yan few months, a Waurawa muhseen da meenal aure, saboda meenal ta dawo wajan ta da zama. dan momy da daddy suna kan bakan su na, ko anyi aure ba za'a bawa muhseen meenal ba, sai ya sake hankali ita kuma meenal tayi karatu ko de bata gama ba ya kasan lce karatun ta yayi zurfi........



Kar ku manta ku ringa yimin reaction kuma ayi following channel Wina saboda a can zan cigaba da posting yanzu.



mu haWe a next page

30 / 38