Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   35 / 38

102K to 105K   out of 111.1K words

momy ta fara cin dambu mi™ewa tai tare da cewa momy bari taje ta dawo, duk sabida umma ta bawa momy waje ta iya cin abinci.



Momy kuwa a hankula ta fara cin dambu zuciyarta cike da farin cikin lamarin auran muhseen da amina, sai kace shine yaronta na fari ko iri. wanda ya daWe bai yi aure ba, kamar de doctor, dan yanda momy take farin cikin auran nan ko auran doctor batai farin cikin kamar haka ba.



Duk sabida tausayin maraicin da momy takewa meenal, shi yasa take son haWin. Momy ta Wauki alwashin sai tasa meenal farin cikin sosai a rayuwarta, sai ta manta tayi rashin mahaifi. To haka momy tai tacin abinci tana tunani kala-kala.



Harga allah momy taji daWin dambun nan sosai nesa ba kusa ba, raban da taci dambu me daWin irin na umma harta manta ma ita. Momy sai da ta cinye wanda ta zuba dukansa, dan badaban cikin momy ya cika ba sai ta ™ara cin dambun shinkafar. Bayan momy ta kammalaci ruwa ta tsiyaya a cup ta farasha.



Momy tana cikin shan ruwan dady ya bugo mata waya. Sai da momy ta kammala shan ruwan sannan ta Wauki wayar baki Wauke da sallama. Daga can bangaran dady amsa sallamar yayi, bayan ya amsa sallamar momy cewa tai  dady ya aiki .



Hankali kwance dady yace  aiki alhamdulillahi, dama kinga bugo miki nai, naji ya ku kai da maman amina, ta amince ko yaya, gaba Waya hankalina yana kan maganar . Murmushi jin daWi momy tai tare da cewa  alhamdulillahi maman amina ta amince amma kuma tace



In ka samu time sai ka haWu da abban aisha, ku ™arasa maganar sabida shine wakili kuma uban wajan amina, in shima ya amince shikenan ba damuwa . Cikin jin daWi dady yace  masha Allah ba damuwa in sha allah kamar yarda ta bu™ata zamu sanar da abban aisha, yau ma zanje mu haWu, in na tashi daga office .



To daga haka momy da dady suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali har sai da momy taga umna ta dawo sannan su kai sallama da dady. Bayan momy ta katse wayar kallan umma tai tare da cewa  ina ta jiranki shiru, nace wata™ila kin faWa wani aikin .



 Eh har kin kammala kenan, wallahi kam kin san aikin gidan ne baya ™arewa .  Wallahi kam baya ™arewa, tun dazuma na kammala, yanzu nake ™o™arin tashi na tafi ma momy ta ™arasa maganar tana zura wayarta a jaka.



 Ah yanzu zaki tafi ai da kin bari sai anjima kun sake gaisawa da yayan naki .  Wallahi kam dan ina son nayi hira da surukan nawa, amma kin san lokutan yanzu gudu suke yi, yanzu za kiga an fara kiran salla magriba ga driver na jirana a waje, amma a sake kiramin ¼yayan nawa muyi sallama da su .



Mikewa umma tayi tare da cewa  hakane lokutan gudu sukeyi wlh, amma bari na kira miki su kuyi sallama daga haka umma ta fuce daga palour. Amma bata jima da futa ba sai ga su meenal da ma eeshat sun dawo wajan momy.



Mikewa momy tai cikin sakin fuska tace  Yauwa ´ayana yan albarka zan tafi kuzo ku raka ni hanya . Murmushi ma eeshat tai tare da cewa  to momy har zaki tafi da wuri haka dama kin bari sai bayan magriba ai . Dariya momy tai tare da cewa  aa bayan magriba kuma aishatu, ai yesmeen kuka za tai tayi, in ta dawo bata ganni ba .



Dariya ma eeshat tai tare da cewa  haba momy kuka kuma, sai kace yarinya ko yar baby .  Ah ai yesmeen tafi ´ar baby rigima aishatu, ko da yake yarinyarce itama 13 to 14 take fa, girman jiki ne kawai .  Ah momy 13 to 14 fa, da ni nayi tunani in bata girme ni ba za muyi sa anni .



 Ah ina aishatu ai kin girmeta nesa ba kusa ba, girman jiki ne kawai duk da bansan age Win ki ba, ke da amina waye babba ne? . Momy ta tambaya tana kallon amina wanda take faman sunkuyar da kai, kamar sabuwar amarya .



Cikin jin daWi ma eeshat tace  momy ai duk sa anni ne nida ma eeshat 17 muke, tazarar mu 2 weeks ne fa .  Ah masha allah, Kice duk age Winku Waya to allah yayi muku albarka yarin kirki . Sai a lokacin meenal ta buWe baki tace ameen a hankula, har suna haWa baki ita da ma eeshat wajan cewa  ameen .



Daga haka momy cewa tai  aishatu Wauko ruwa ko lemon mu tafarwa da driver nasan yana can yana jira, maybe yana jin ™ishirwa . Ba musu ma eeshat ta dur™usa ta Wauki lemo da ruwa masu sanyi daga haka ta mi™awa meenal lemon ™wali ita kuma ta ri™e bottle Win ruwan.



Daga haka momy da umma su kayi sallama, ita kuma ma eeshat da meenal suka bi bayan momy domin rakata bakin mota kamar yarda momy ta bu™ata. Umma har bakin ™ofa ta raka momy sannan ta juya ta koma gida.



Meenal da ma eeshat haka suke tafiya biye da momy har suka ™arasa bakin motar. Koda suka karasa, ma eeshat ce ta karSi lemon hannun meenal sanan ta mi™awa driver momy. Driver kuwa ba musu ya karSa hadi da cewa  Yauwa nagode .



Bayan haka momy ta shiga bayan mota bayan ta, shi ta sake yiwa su meenal addu o i, tare dayi musu sallama, suka wuce gidan, ita kuma driver yaja motar su kabar wajan. Suna cikin tafiya ma eeshat ta kalli meenal tare da cewa  meenal ya kikaga momy doctor tana da kirki koh? .



GyaWa kai meenal tai tare da cewa, sosai ma, mutunci ba kaWan ba ai mutuniyar arzikice sosai .  Wallahi kam ke de bari shima haka doctor yake, yana da kirki sosai ya kwaso halin momy, kuma ina da taabbaci in sha allah haka ™anin Doctor yake da kirki mijin da zaki aura .



Meenal haWe rai tai tare da taSe fuska tana cewa  kai ma eeshat nifa bana son wannan auran fa, kima dena haWani da auran wannan, in sha allah waleed zan aura in kuma bashi ba na auri khaleefa . Jim ma eeshat tai kafin tace  tom shikenan meenal allah ya zaSa miki abinda yafi alkhairi a takaice meenal tace  ameen .



Bayan sun koma ciki direct falo suka nufa suka zauna. Itama umma tana zaune tayi jigum. meenal tana gani fuskar umma, tasan da akwai abinda yake damun umma amma sai tayi shiru, ba tare data tambayeta ba. Meenal zuciya cike da tunani ta cire hijab Win jikinta.



Umma kuwa gyara zama tai tare da cewa  meenal kin san me yake faruwa? Gaban meenal ne ya dan faWi rasss, duk da bata san mai umma zata ce ba. dakewar meenal sannan ta kalli ma eeshat wanda ta zubawa umma ido kamar sunanta umma ta kira. Meenal daurwa tai tare da cewa  aa umma sai kin fada .



Ajiyar zuciya umma ta sauke tare da cewa  akan maganar auran ki da yaron momy muhseen ne . Meenal a fili tace  Innalillahi maganar aurena kuma me tace umma? . Cikin danne damuwa umma tace  mene kuma na Innalillahi meenal? .



Shiru meenal tai ba tare da tace komai ba. Ma eeshat kuma tsomo baki tai da cewa  umma ki mana bayani me yake faruwa? . Umma kallon meenal ta sakeyi tare da cewa  momy tace nan da sati biyu za a kawo lefan auran meenal, kuma bayan an kawo wata Waya za a saka lokacin Waura aure& & & ..



Mu hade a next page dan jin yarda zata kaya.



Game bu™atar littafin doctor ashmal daga farko har inda aka tsaya, yayimin magana ta private 09162226240 in sha Allah zan tura masa, in yayi following Win channel bai samu ba bye&



Game bu™atar littafin doctor ashmal tun daga farko har zuwa inda aka tsaya ga link Win channel yayi fallowing.

=ØGÜ=ØGÜ=ØGÜ=ØGÜ=ØGÜ

https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d



Game Su™atar cigaba da karanta littafin doctor ashmal da comment, akan littafin bayan ya karanta, dama wasu sauran sababbin littattafan novel ga link din WhatsApp group yayi joining

=ØGÜ=ØGÜ=ØGÜ=ØGÜ=ØGÜ

https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc



_page 48



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=ØòÜ



Wani yawun tashin hankali me zafi da Waci meenal ta haWiye, baki na rawa tace  umma me kikace kin amince kuma? .  Hmmm meenal bani da abin cewa, amma in baki manta ba haka aka sa lokacin auranki lokacin da akai engagement a hakan ma an ™ara wata Waya ai .



Cikin rashin annurin fuska meenal ta sake cewa  aa umma ni so nake naji kin amince ko aa . Jim umma tai na wasu daki™u kafin tace  eh meenal na amince amma nace su samu abban ma eeshat su ™arasa zancan .



 Innalillahi wainna ilhai hirraji un umma kin amince fa kikace meenal ta ™arasa maganar tana fashewa da wani gigitaccan kuka mai ban tausayi. Cikin dauriya umma tace  meenal ya kike so nayi ne, tun farko fa kin san da zancan nan har kin amince .



Cikin kuka meenal tace  amma wallahi umma ba a san raina na amince ba .  Meenal nima ban san yarda zanyi ba gaskiya, bazan iya cewa hajiya aa ba mutanan arziki ne sosai, kuma hasalima ba Wan mafiya za a aura miki ba ko Wan iska kode wani mara kyan hali da zaki Waga hankalin ki ba!



Ko kuma kina da wanda kike so ne bayan waleed, kuma sani kan kine, baban ki kafin ya rasu ya bani wasiya ya baki kuma ya bawa alhaji, akan kar a sake a aura miki waleed, hakan ne ma yasa alhaji da hajiya suka mi™e tsaye wajan ganin sun aura miki Wan su .



Meenal kuwa sake fashewa tai fa kuka sosai, wanda kowa yana iya jin sautin kukan nata. Ma eeshat kuwa rafka tagumi tai zuciya cike da tausayawa ™awarta ma eeshat dan harga allah bata so taga ma eeshat cikin damuwa.



Umma kuwa cigaba da magana tayi da cewa  meenal ina da ya™ini akan, ba zaki taSa ladama ba, in de kika bi zaSin iyayanki. Meenal kullum bana bacci tun kafin ki kai haka nake roko allah ya haWaki da miji na gari, tabbas na sheda kuma ina kyautata zaton allah baze, taSa zaSa miki wanda bai dace ba.



Kuma har yanzu akwai lokaci, tunda ba a daura miki auran ba, koda yaushe ™addara zata iya canzawa, ki cigaba da addu a kawai allah ya futo miki da mafita, ta alkhairi, meenal karki Worawa kan ki ciwan zuciya ki mi™awa allah lamarinki kamar yarda nai .



Umma ta ™arasa maganar kamar za tai kuka. Daga haka umma mi™ewa tai ta fuce tabar Wakin, zuciya cike da tausayawa meenal. Sai da meenal tayi kukan ba™in ciki mai isarta sosai sannan ma eeshat ta fara rarrashinta.



Daga haka zazzaSi mai zafi gaske da ciwan kai suka luluSe meenal. Hankalin ma eeshat ya sake tashi ainun ganin yarda lokaci guda meenal ta zube ta kwanta, duk da kuwa ba yau ma eeshat ta saba ganin haka a tattare da meenal ba.



Dama haka meenal take, in de ta shiga cikin tashin hankali, lokaci guda cuta take rufe ta, saboda meenal bata iya ri™e damuwa a ranta ba. Ma eeshat ta fara tunanin kota sanar da doctor halin da ake cike ne akan meenal bata san auran da za ai mata da kanin sa muhseen, ko zai iya sanarda su momy.



Haka ma eeshat ta fara tunanin nan, duk da tana tsoron tunkarar doctor da irin maganar nan amma, ta yanke shawarar sai ta sanar da shi ko allah zai sa, a samu mafita, dan ma eeshat ba zata iya jure ganin yar uwarta meenal cikin tashin hankali ba& & ..



Dady



Kamar yarda dady ya sanar da momy haka kuwa akai bayan ya taso daga office direct gidan su ma eeshat ya nufa domin haWuwa da abban ma eeshat. Da yake ya buga masa yace in yana gida zai zo suyi mahimmiyar magana, in ya futo daga office.



Dady yaga tarbar alfarma sosai wajan abba yarda kasan ya goya shi abayansa, ga girke-girke kala-kala yasa ai masa. Dady kuwa yaji daWin ganin yarda abba yake karrama shi kuma yake bashi respect a matsayinsa na gaba da shi.



To bayan abba da dadyn sun gaisa sun Wanyi hirar su ta rayuwa kafin dady ya fara magana kamar haka.  To ka ganni bakatatan ko, zuwa basa rana, wallahi abun ne yana da mahimmanci, shine nake so mu haWu muntattauna .



Murmushi abba yayi cikin girmamawa yace  ah haba ba komai alhaji, ai duk lokacin da kake son mu haWu zamu iya haduwa, in ta kama, ma ni zanzo har gida na same ka, ba sai kasha wahalaba .



Jinjina kai dady yayi tare da cewa  aa mene abun wahala dan nazo, daga office ma na tawo nan badaga gida ba wlh, dama magana ce akan auran yaron wajena muhseen da kuma yarka amina jinjina kai abba yayi tare da cewa  okay masha allah na am .



Dady cigaba da magana yayi da cewa  kasan Lokacin da aka kawo kuWin sarana ansa wata uku jinina kai abba yayi tare da cewa  hakane ranka yadade dady kuwa cigaba da magana yayi da cewa  to yanzu lokaci ya matso ya zamana a kwanakin da mukasa bai fi 2 week ba.



Hakan ne yasa nida mai Wakina muka yanke shawarar Waura auran kamar yarda akasa bamu Waga ba abba jinjina kai yayi cikin gamsuwa alamun yana fahimtar zancan. Dady kuwa cigaba da magana yayi da cewa  hakan ne yasa mai Wakina taje ta samu mahaifiyar yarinyar!



Kuma ta sanar da ita, akan shawarar da muka yanke, sannan kuma ta tambayeta akan ra ayinta, kuma ba Sata lokaci mahaifiyar yarinyar ta amince da hakan, amma tace kafin a aiwatar da komai, ni da kai mu zauna, mu sake tattaunawa akan maganar, tunda a yanzu kai ne a matsayin uba kuma wakili a wajan yarinyar .



Daga haka dady yayi jim, kafin ya cigaba da maganar abba yace  ah masha Allah, alhamdulillahi hakan yayi kyau sosai, kuma ina farin ciki da wannan abu, amma kuma baka ganin kamar ansa lokacin auran da wuri haka, saboda su mata kasan su da shagali, ga taro kala-kala dan haka ya kamata a zauna a tsara komai .



 Eh hakane, amma ai a halin yanzu Waura auran kawai za ai daga baya in zasu tare, duk shagalin da yakamata sai ayi in sha Allah . Cikin mamaki abba yace  okay dama ba tarewa za tai ba, in an Waura auran sai nan da yaushe kenan? .



Jinjina kai dady yayi tare da cewa  hakane ba ana Waura auran, zasu tare ba, sabida mijin nata ma nan da one week zai koma saudiya ya ™arasa karatunsa, sai nan da one years zasu dawo in sha allah sai su tare .



Abba gyara zama yayi tare da cewa  hakan yayi kyau ranka ya daWe, amma wani hanzarri ba gudu ba sai nake ganin kamar, hakan za a ™wari yaran namu, ayi aure ba a tare ba kuma, ko za a bari sai ya ™arasa karatu sai ayi bikin gaba Waya su tare, musamman ita amina sai tai ta zama da aure kuma a gidan su hakan kamar ba daWi .



Jinjina kai dady yayi tare da cewa  gaskiya ne zancanka, kuma duba da hakan ne ma yasa, me Wakina tace, in anyi auran za a kawo mata amina wajanta, su cigaba da zama da ita tana cigaba da karatun nata, har lokaci yayi .



Jinjina kai abba yayi tare da cewa  gaskiya ne inaga haka sai yafi, in de kana ganin ba wata matsala, amina zata zauna lafiya kuma ta sake a can shikenan ba damuwa cikin sakin fuska dady yace  in sha Allah hakan ba matsala, saboda ma, mahaifiyar yaran, tana ™aunar amina hakan ne yasa ma tace zasu zauna tare .



Abba ya gamsu da zance dady amma da aso samun sane, ana auran a tare sai yafi. Dady kuwa kamar ya shiga zuciyar abba yace  amma dalilin da yasa kaga muna so ayi auran nan kusa, kamar mun dage shine  akan wannan yaron ne waleed wanda mahaifin yarinyar baya so ta aura!



Kasan yaran yanzu, in suna soyayya basa so su rabu, in zasu rabu ko aka raba su, ba abinda baza su iya aikatawa ba, shi yasa muke so, ayiwa tufkar hanci, tunda har mahaifin amina yabada wasiya akan, ko bayan ransa kar a aurawa amina yaro, to kaga yanzu in aka bar yarinya haka, zaune ba aure zasu cigaba da soyaya ne!



Kuma allah ne kaWai yasan abinda zai iya faruwa, amma yanzu in aka Waura mata aure nasan a matsayinta na mai nutsuwa da ilimin addini dole zata nisanta kanta da shi, kuma ta manta da shi . Cikin gamsuwa da jin daWin jawabin dady, abba yace!.



 Gaskiya ne ranka ya daWe kunyi tunani me kyau, allah ya temaka ya bada zaman lafiya, allah yasa anyi a sa a, kuma yasa hakan ne yafi alkhairi . Duk da abba yasan waleed kamar Wa yake a wajansa, Wan uwan ma eeshat ne kuma Wan matar sa mami ne, tunda dan yayar mami ne,



amma in de ta tabbata bashi da ™yan hali baze so haWa su aure da meenal ba. sabuda meenal yana sonta kamar yarda yake son ma eeshat. Maganar dady ce ta dawo da abba daga gajeran tunanin daya tafi in da yake cewa



 Sai kuma maganar Wanka kuma surikinka doctor, yana so akan nazo na sameka tun ™wanakin baya, akan a rage kwanakin auran su da aisha, kuma gashi bamu haWu ba, sai yanzu yau, dady ya ™arasa maganar yana dariyar su ta manya& & & & &



Please mutanan amana ku ringa sharing, kuma ku ringa react, kwana biyu, bakwa gigitani da like gaskiya, musamman mutanan arzikina ´an channel

35 / 38