Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   28 / 38

81K to 84K   out of 111.1K words

tare da kashe ta baki Waya cikin birkicewa da rashin gaskiya meenal tace "umma yaushe kika shigo".



Fuskar umma ta canza ba walwala, zama tai kusa da meenal cikin rashin sakin fuska tace "dama ina zaki san na shigo tunda kina waya da masoyin ki". meenal ba tace komai ba ta sunkuyar da kai ta fara wasa da wayarta.



Kallan meenal umma tai kafin tace "meenal gaba Waya kin canza min, kin koma wata meenal Win ta daban ba wanda na sani ba, ada ko yaya muka gaya miki magana kin kiyayeta har abada amma ban da yanzu, meenal karfa ki manta mahaifinki ya rabaki da yaran nan amma kin i? Yanzu mahaifin ki yana arashin asa, ko baki masa biyayya yana raye ba, ya kamata ki masa biyayya yanzu tunda ya rasu".



lokaci guda hawaye suka fara shararowa meenal, saboda tasan gaskiya umma take gaya mata kuma ga wasiyar da mahaifinta ya bar mata game da waleed tana faWo mata. Ita har ga Allah ma ta sha'afa sabida son waleed ya rufe mata ido. hannun meenal umma ta rie tare da cewa



"kiyi hauri meenal, kiyiwa mahaifin biyayya, baki san mai ya gani dan gane da waleed Win nan ba in sha allah, allah zai kawo miki miji na gari wanda ya fishi komai. Wallahi meenal da ina da halin da zan baki auran waleed da na baki sabida kiyi farin ciki, bazan iya hanaki abinda kike so ba, to amma bani da hali kuma mahaifin ki sai da ya roe ni akan ko bayan ran sa kar na bari ki auri waleed, kuma ya gaya min dalilin da yasa ya hanaki auran waleed, tabbas kuma dalilin babba ne ya cancanci a hanaki auran sa.



Da sauri meenal ta Wago ido sharSe da hawaye ta cewa umma "dan Allah umma ki gayamin dalilin da yasa kuka hanani auran waleed kuka rabani da shi, na amince zan rabu da shi na har abada amma dan Allah ki gaya min dalilin".



Meenal tana rufe baki, suka ji ana buga ofar gida, alamun anyi bai. kallon meenal umma tai tare da cewa "kiyi hauri ki dena kukan nan zamu zauna muyi magana, dan Allah kar kisa damuwa a ranki aminatu, bari naje na duba waye yake bugawa, ila ma'eeshat ce maza kije ki wanke fuskar ki".



Daga haka umma bata sake cewa komai ba ta wuce tai hanyar fita,. kamar yarda umma tacewa meenal, haka meenal ta mie ta nufi toilet ta wanke fuskar sosai sannan ta dawo ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.



an garan umma kuwa, tana buWe ofa ta tarar da momy tsaye bakin ofa. fuska cike da farin cikin umma tace  ah maraba lalele hajiya ashe kece tafe shigo mana . murmushi momy tai tare da cewa  eh wallahi tare muke da dady zamu iya shigowa .



 Ah sosai ma, kije ki masa iso sai ku shigo hajiya . fuska cike da fara'a hajiya tace to sannan ta koma domin kiran dady, umma kuwa tana tsaye tana jiran su da yake dama tasa hijab a jikin ta kafin ta futo.............



Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa Waya daga cikin members Win gidan nan rasuwa, tana bibiyar litattafan mu kuma Waya daga cikin admin din group Win mu na doctor ashmal, dan Allah dan annabi muna barar addu'a a gare ku Allah ya jian Hafsah (oum farhan) da rahma, ya kyautata mawanci yasa ta huta, wallahi munyi babban rashi.=-=-=-=-=-=-



Mu haWe a next page.







_page 37





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Bayan su dady sun araso fuska sake umma ta musu jagora suka shiga cikin sitroom. Cikin giramawa momy da dady suka fara gaisawa da umma. Fuska sake dady yace "wai ina Wiyata ne?" momy itama cafe zancen tai da cewa "nima tun dazu nake son tambaya amma ka rigani. "ah bari na kira muku ita ku gaisa" umma ta arasa maganar tana miewa.



Daga haka umma ta fuce daga sitroom Win ta koma bedroom Win meenal. umma zauna taga meenal gefan gado tayi jigum abinta, kamar mai tunani. arasawa umma tai gab da ita ba tare da ta zauna ba ta fara mata magana "meenal".



agowa meenal tai tare da cewa "na am"  ki taso muje momy da mijinta ne suka zo, suna cigiyarki kije ki gaida su . Haka nan meenal taji gabanta ya faWi rass, amma sai tai arfin halin cewa "tom" sannan ta mie abinta. Hijab Win ta na sallah meenal ta zumbula har asa sannan ta nufi bayan umma, tana tafe salo-salo kamar wanda bata son tafiyar. Baki Wauke da sallama meenal ta shiga cikin sitroom Win.



Har asa ta tsuguna ta gai da momy da dady. Fuska a sake momy da dady suka amsa, musamman momy ma sai washe mata baki take yi tana cewa tazo ta zauna kusa da ita. Meenal kuwa bata ce komai ba murmushi kawai ta saki abinta tare da sunkuya da kai. " meenal kenan sarkin kunya, kin mai damu surukan ki na arfi da yaji, ji wani yarda kike sunkuyar da kai".



Momy ta faWa tana sakin dariya, itama meenal siririyar dariya ta saki. "Tom yaushe zaki zo gidana ki sake wana yesmeen sai cigiyarki take, da, da itama zamu zo amma tana school".



Murya asa-asa meenal tace "momy zan zo ne" "ah ni ban yarda da zuwan ki ba, kawai kizo mu koma tare yau". meenal bata ce komai ba sai sakin murmushi kawai, murmushin da yake sa dimple Win kumatun ta rige-rigen motsawa.



Bayan momy ta gama zaulayar meenal da wasa, Worawa tai da cewa "tom shikenan de meenal tunda kin i magana, maza kije ki haWa kayan naki, ki bamu waje muyi magana da umma, in na gama zan miki magana kizo mu tafi kawai".



Momy ta faWa cikin sigar zaulaya, murmushi meenal tai tare da miewa, a dede lokacin umma ta shigo hannu rie da plate mai Wauke da ruwan jarka da lemuka, sannan ta araso ta ajiye a gaban su momy.



"Sannu da oari mun gode" dady ne ya faWi hakan yana gyara zama. momy kuwa ruwan ta Wauko ta buWe ta fara tsiyayawa a cup duk da bata jin ishi amma haka nan take son shan ruwan saboda bata so umma ta wahala, kuma basu sha ba".



Momy bayan ta Wan sha ruwan kaWan ajiye cup tai sannan tace,  yauwa maman amina in ba damuwa muna son magana dake". umma da take zauna jinjina kai tai tare da mai da hankali tace "tom ina sauraran ku hajiya".



Kallon dady momy tai tare da cewa "za kai mata bayanin ko ni zan fara?". "a'a ba damuwa ki farayi mata bayanin kawai". momy baya ni ta farayi kamar haka "Dama maman meenal wata magana ce take tafe damu game da aminatu".



GyaWa kai umma tai alamaun tana sauraro.  Kafin baban amina ya rasu, sunyi magana da dady sosai, sannan dady ya fahimci mahaifin meenal baya son saurayin da suke tare, sabida dady ya shedamin cewa a gaban sa yake cewa amina ko bayan ran sa kar ta auri saurayin da suke tare, kuma bayan haka ma baban amina ya sake jaddadawa dady hakan momy ta arasa maganar tana tsare umma da ido.



Jinjina kai umma tai kafin tace "warai hakane hajiya, nima ya barmin wassiya da ko bayan ran sa baya son meenal ta auri waleed kuma gashi ita yarinyar tana son yaran sosai, gaba Waya ta kasa rabuwa da shi, duk ta shiga damuwa sosai".



"Subhanallahi wai menene dalilin baba na hana amina auran yaran nan, inaga in dalilin bai wucewa shari'ar muslinci ba, za'a duba kawai sai a gyara ko menene ayi auran in kuma, ya wuce dole ta hakura, tunda kince ta shiga damuwa sosai".



Dady ne ya faWi hakan cikin jimami. umma gyara zama tai da cewa "to ana gab da turo kuWin auran su ne shine baban meenal yaje bincike nan ne ya gano wai bashi da tarbiyya shaye-shaye yake da kuma bin mata, a can abujan in da yake aiki, shine dalilin da yasa baban meenal ya dakatar da auran, saboda yace meenal ita kaWai allah ya bashi baze so yaga ya aura mata mutum mara tarbiya kamar waleed ba, saboda yana so ya bata miji na gari wanda zata samu kwanciyar hankali ta haifi aaye masu tarbiyya.



Jinjina kai dady yayi kafin yace "eh gaskiya ne malam yayi gaskiya dole haka zata haura da shi gaskiya wannan ba mutumun aure bane". "Hakane amma ni da dady mun yanke shawarar zamu haWa amina aure da Wan wajan mu muhseen in ba damuwa".



"Eh mun jima da yanke shawarar amma sai muka ce bari a share zaman makoki, sai muzo mu same ki da zance" dady ya faWa yana gyara zama. momy Worawa tai da "amina ta shiga rai na sosai sabida yarinya ce mai hankali, bana so tai maraici sosai, kuma ina tunanin in anyi mata auran hankalin ta zai kwanta, kuma zata dena tunanin wancan saurayin nata".



A zahirin gaske umma tayi mamaki da jin maganar su momy da dady sosai, dan batai tunanin ko da wasa za suyiwa meenal tayin auran Wan su ba. momy da taga umma tayi shiru cigaba da magana tai kamar haka



"Amma fa ba zamu matsa miki ko mu matsawa amina a kan haka ba, kawai shawara ce sai kin amince hakan zai faru, in baki amince ba shikenan, zamu cigaba da zumunci mu kawai momy ta arasa maganar tana sakin murmushi.



Itama umma murmushi ta waulo sannan tace "a'a hajiya rashin maganar tawa, bashi yake nuna rashin amincewa ta ba, nayi mamaki ne sosai ta yarda kuka yiwa meenal tayin auran yaran ku, ba tare da shakkar wani abun ba". "Cikin mamaki momy tace "shakka kuma haba umman amina ki dena faWar haka, ai na yarda da tarbiyar gidan nan 100% kuma amina mace ce da ko wana iyaye za su so Wan su ya aure ta".



"Hakane hajiya naji daWi sosai kuma nayi farin ciki da jin wannan, saboda nima nasan duk yaran da ya futo daga gidan ku, ya futo ne daga babban gidan mutunci, tarbiya, da kuma sanin yakamata, ni de ta bangarena, na amince sai dai kuma ita amina, amma in sha Allah itama zata amince".



"Alhamdulilahi kar ki damu ai ni bana jin ata amina zata amince in sha allah, komai zai zo dede". momy taso ta sanar da umma in anyi aure meenal a wajanta zata zauna ta cigaba da karatu kafin suma su muhseen Win su kammala nasu, amma sai taga hakan bai dace ba, umma zata fahimci lamarin a bai-bai gwara in lokaci yayi a sanar da umma".



Daga haka momy da dady miewa su kai domin shirin tafiya, dady ne ya fara fita ita kuma momy tace sai tayi sallama da meenal dan haka har bedroom Win meenal momy taje.



Ko da momy taje kwance ta samu meenal tana bacci dan haka bama ta tashe ta ba, kuma ta hana umma tashin ta. Daga haka umma har ofar gida ta raka momy, momy kuma ta sake jajjadawa umma duk abinda suke buata dan Allah ta tuntuSe ta a waya ta sanar da ita.



Su momy suna tafiya umma ta kullo ofa sannan ta nufi kicin ta fara oarin Wora musu abinci. umma aiki girki take amma gaba Waya hankali ta baya kan girkin yana kan maganar da su momy suka zo mata da shi......



Sai da aka fara kiran sallah la'asar meenal ta farka daga baccin da ta tafi. tana miewa ta Waura alwala sannan ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar kicin ta shiga ta zubo abinci, sannan ta zauna ta fara cin abinci, ci take amma ita kaWai tasan damuwa da take ciki na rabata da waleed da akayi, har ga allah tana yiwa waleed son da ita kanta bata son adadinsa ba.



Umma kallon meenal tai, ta fahimci cin abincin take kawai amma hankalinta yana can wata duniyar. "meenal in kin gama ina so muyi magana dake". Sai da gaban meenal ya faWi rass, da taji umma tace haka, amma sai ta dake tace"tom umma". Nan da nan meenal ta mai da hankali ta cigaba da cin abincin dan a iya tunanin ta maganar waleed umma za tai mata, maganar da suka farayi Wazu ita zasu arasa.



Bayan meenal ta kammala cin abinci mikewa tai ta kai plate Win kicin sannan ta dawo ko ruwa bata sha ba ta zauna kusa da umma tana cewa "umma na gama ina jin ki".



"Eh na gani amma ya kamata ki sha ruwa kafin mu fara maganar, kyaci abinci baki sha ruwa ba kuma". Daga haka meenal bata sake cewa komai ba ta nufi bakin randa ta Webo ruwa tasha sai da ta oshi sannan ta ajiye cup Win ta dawo wajan umma.



Bayan ta zauna, itama umma gyara zama tai kafin ta fara cewa "meenal nasan za kiji maganar da baki zaSa zata ba bare tunani, dazu momy da alhaji akan maganar ki su kazo gidan nan". Da sauri meenal ta Wago cikin mamaki tace "maganata kuma umma?" "eh ki godewa Allah da yasa kike da farin jinin da kika shiga ran su lokaci guda har suke bibiyar lamarin ki".



"Umma ban gane abinda kike nufi ba wallahi". "Eh zaki gane ai bayani zan miki yarda zaki gane, meenal momy da alhaji suna so su aura miki Wan su, shi yasa suka zo suka sanar dani, sannan suka ce a sanar da ke kema in mun amince amma".



Meenal jin maganar tai ta dakar mata kwakwalwa on expect, cikin mamaki tace "umma Wan su kuma wana Wan nasu, haba umma sai kace an ce musu bani da masoya ne, da zasu fara oarin haWa ni da Wan wajan su". Umma tayi mamaki sosai da jin maganar meenal haka gatsau sabida meenal bata cika, fadar magana a tsaitsaye ba, musamman ma in maganar daga bakin manya ta fito.



Girgiza kai umma tai kafin tace "a'a meenal bace musu akai baki da masu san ki ba, kawai gani su kai ya kamata tunda mahaifin ki yacewa alhaji ko bayan ran sa kar ki auri waleed shine su kai miki miji".



"hmmmmm umma ni zan rabu da waleed ko nace nama rabu da shi amma, bana son Wan su bazan iya auran saba ko wanene gaskiya, duk da kuwa suna da kirki da mutunci ga sanin darajar Wan adam, amma ni gaskiya bama naso ba sai an kai maganar nan da nisa ba".



Cikin mamaki umma tace "meenal ni kik cewa haka, meenal hankali ki Waya kuwa, meenal nima farko ban amince da zancan ba, amma daga arshe sai naga in mu kai musu hakan ba zasu ji daWi ba, kuma ya kamata tun wuri a aurar dake meenal, sabida ke ba irin matan da suke karatu me tsayi bane, ba tare da aure ba, ni na fahimci ke mace ce mai san aure tun ba yanzu ba, meenal baki da wani zaSin daya wuce ki amince ki auri yaran su momy".



Murya na rawa meenal tace "haba umma ni wallahi gaba Waya aure bai taSa birge ni nan kusa ba, umma dan Allah kar kimin dole wallahi bana so meenal ta faWa hawaye na wararo mata.



"Meenal ai mace bada baki take faWa taka son aure ba, Wabi'un ta ne suke nuna hakan, kuma gashi ke macace mai gaba-gaban jiki komai naki masha allah bai ci ace kin cigaba da karatu babu aure ba, ko wana kalar maza hari za su ta kawo miki, na gari da na banza". Kuka sosai meenal ta fashe da shi sannan ta tashi ta shige Waki. sai da jikin umma yayi sanyi sosai ganin halin da meenal ta shiga sabida ita tunda ta haifi meenal bata taSa tashi ta bata waje ba in suna magana sai yau.



Umma tana kai haka da tunanin taji arar bugu, ana buga gidan. Jiki a sanyaye umma ta mie ta Wauki hijab Win ta da yake gefe ta saka, sannan ta tafi buWe gidan zuciyar ta cike da tunani kala-kala.



Umma tana buWewa ma'eeshat ta gani tsaye bakin ofa, aalo murmushi dole umma tai kafin tace "ah ma'eeshat kece tafe kenan sannu da zuwa". "eh wallahi umma ina wuni, kinga ni da driver nazo dady ne ya aiko shi, shine nace muzo tare saboda ina son zuwa".



"lafiya alau ma'eeshat Allah sarki to kice ya shigo, umma tana rufe bakin ta taga driver ya fara sauke kayan abinci a ofar gida. Ita kuma ma'eeshat ce masa tai in ya gama futo da su daga boot ya shigo da su ciki, daga haka ta shige ciki wajan meenal.



Sosai hankali ma'eeshat ya tashi ganin yarda meenal take ta sharara hawaye, hankali tashe ma'eeshat ta arasa kusa da ita tare da rie hannun ta tace "rabin rai kukan me kike yi ne haka, wallahi jiki na ya bani kina cikin damuwa tun daga yanayin yarda kike min reply a chat da kuma in na bugo nasan kina damuwa, haba rabin rai ki gayamin me yake damun ki ya isa kibar kukan nan haka please".daga haka ma'eeshat ta fara sharewa meenal hawaye da hannun ta. bayan ta gama tsare ta tai da ido tare da cewa  maza ki gayamin mai yake damun ki kar nima kisa nayi kukan .



Shaar hanci meenal tai sannan ta fara magana murya a dashe "ma'eeshat kema kan ki kin san ina matuar son waleed sosai koh?" gyaWa kai ma'eeshat tai alamun eh.  An rabani da waleed ina cikin damuwa madadin damuwar ta ragu kullum aruwa take, sannan yanzu ana so a bani wani wanda bana so".



Cikin mamaki ma'eeshat tace "kai wa za a baki kuma meenal kimin bayani yarda zan gane mana". Nan da nan meenal ta zayyane labarin da umma ta bata na zuwan su momy da abinda suka ce, ta bawa ma'eeshat labarin komai........



Mu haWe a next page.







_page 38





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Ajiyar zuciya ma'eeshat ta sauke sanan ta gyara zama tare da dafa meenal tana cewa "meenal abinda nakeso na fada miki ko wana bawa akwai kaddarar sa a rayuwa, kuma dole ya dage domin yaga ya cinye ta".



Cigaba da magana ma'eeshat tai da

28 / 38