Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   13 / 38

36K to 39K   out of 111.1K words

arshe ma sai da ya raka ta har ofar soran gidan su, nan ma bayan ya rako ta bai rabu da ita ba har sai da baba ya leo kiran ta sanan ya tafi, zuciyarsa cike fall da kewa da soyayyar meenal.



DOCTOR



To soyayyah gaggaruma ta shiga tsakanin doctor ashmal da ma'eeshat. Kullun doctor in bai ji muryar ma'eeshat ba baya samun sukuni, itama in bata ji tasa ba batajin daWi.



Yanzu ma'eeshat da wuri take bacci tana sallah magriba, shi kuma doctor in ya dawo gida wajan 12:00 sai ya bugo mata waya. To in doctor ya tashi ma'eeshat da yake ta dan yi bacci sai susha wayar su, har sai su kai 1 dare suna waya.



sam doctor baya son wayar daran nan, sai yaji kamar hakan da yake bai dace ba, amma ba yarda zai iya hakan ya zamar masa jiki in ba suyi wayar ba baya iya bacci, shi yasa ma suka yanke shawarar ta ringa bacci da wuri kafin suyi wayar 12:00am saboda school.



Shauwa sosai doctor da ma'eeshat su kai, duk da de gaSuwa ce ma'eeshat bata da wayo tana yawan yiwa doctor yarinta da kuma waSa mai maga haka doctor yake haura ya lallaSa ta.



Yanzu shima doctor ya gane ma'eeshat ta fara son sa, dan haka yayi farin ciki sosai kuma yana nan yana shirin zuwa wajan dadyn ma'eeshat on expected ba tare da ma'eeshat Win ta sani ba, shi yasa doctor yayiwa ma'eeshat dabara har ta bashi number abba....



Yau weekend ta kasan ce doctor ba zai fita ko ina ba, gaba Waya yaran gidan basa nan twins tun tafi driving school ita kuma yesmeen ta tafi tafiz daga dady sai momy sai kuma doctor ashmal Win. Bayan doctor ya gama wanka ya shirya direct falo ya futa domin samu yayi breakfast. Lokacin da doctor ashmal ya fita daga bedroom Win sa yana shiga falon ya hangi dady shi kaWai yana breakfast.



Fuska a sake doctor ashmal ya arasa inda dady yake tare da durusawa har asa yana cewa  dady ina wana? . murmushi dady yayi tare da cewa  lpy alau alhamdulilahi fatan ka tashi lafiya kai ma, ya gajiya asibiti kuma? .



Miewa doctor yayi sanan yace  gajiya tabi jiki alhamdulilahi dady ya arasa maganar yana jan kujerar draining Win yana zama.  Masha allah haka ake so a cigaba da tai mawan jama'a . Murmushi doctor ashmal yayi sanan yace in sha allah Dady.



Bayan doctor yayi saving Win kan sa, a hankula ya fara ci a nitse yana ci yana tunanin ma'eeshat. doctor yana tsaka da tunani yaji dady yace masa "yauwa dama ina taso muyi magana amma naga alama 2 days baka samun wani free sosai ko dawowa da wuri bakayi, shine nace bari na bari sai weekend mayi magan".



Jinjina kai doctor yayi tare da ajiye spoon Win da yake hanun sa yana kallon Dady, cikin girmamawa yace  Tom shikenan dady ina jin ka .



Shima dady ajiye spoon Win hanun sa yayi sanan yayi gyaran murya kafin ya fara cewa "Doctor gaskiya zaman nan naka haka yayi yawa na gaji da ganin ka haka, wanan maganar tawa itace ta arshe gare ka daga haka zan Wauki mataki da kai na ni da momy gaskiya". cikin mamaki doctor yace "dady lafiya fatan ba wani laifi nayi ba".



 Laifi mana kayi doctor yanzu ace har ka kai 32 to 33 years ba kai aure ba, kullum mu sai muyi ta zuba maka ido kenan, in munyima magana kace komai lokaci ne, tabas komai lokaci ne amma ai mutum in ya daura niya sai allah ya temake shi. Kai baka so kaga yaranka kenan, su taso kaga girman su, yanzu fa doctor kayi girma sosai dan da kayi auran wuri da tuni ka ajiye mana jikoki fiye da biyu ma, gaskiya mun gaji momyn ka kullum cikin damuwa take akan kai aure, in ma ka kasa zabar matar da kan ka mu zamu zaSa maka wanda ta dace, mutum sai kace wnda aljana ta aura .



Murmushi doctor yayi tare da cewa "a'a dady aljana kuma"?.  warai kuwa doctor to me kake nufi in ba aure akai maka da aljana ba? . Dariya doctor yayi sanan yace  a'a dady bana nufin komai sai alkhairi, kamar de kullum komai lokaci ne, in lokaci na yazo zanyi .



 Wallahi doctor baka isa ba, gobe zan sa momy ta binciko ma can wata yarinya a auye ka aura . Zaro ido doctor yayi tare da girgiza kai yana cewa  a'a dady kasan an auyan nan basu wani cika wayewa ba bare su san ya kama ta .  Eh in tazo gidan naka, sai ka koya mata ya kamatan ai tunda taimawan ka ma za tai ta aura, kai fa yanzu na dena mamaki, dan naga alama aljanar ce ma ta aure ka .



Ajiyar zuciya doctor ya sauke sanan yace "a'a dady bama sai anyi haka ba, dama da akwai yarinyar da nake nema yanzu ina so ita zan aura, to bana so na gaya muku da wuri so nake sai mun gama dedetawa na samu baban ta munyi magana sai na gaya muku .



Nan da nan dady ya saki wani murmushin farin ciki saSanin da daya haWewa doctor rai, cikin farin ciki dady yace "ah to to haka nake son ji, ashe haka abun alkhairi ya faru ah masha allah". shima doctor Wan murmusawa yayi, saboda tunawa da mosoyiyar sa ma'eeshat da yayi, sanan yace  in sha allah dady ade taya ni da addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi .



 Gaskiya doctor ka bani mamaki sosai da badan nasan baka yimin arya ba sai nace ban yarda ba, yau da bakin ka kace kana neman wata a matsayin mata aure kai Allah uban giji yayi maka albarka ya baka ita a matsayin matar aure .



 Ameen dady ina so ku taya ni addu'a kai da momy, kasanar da ita .  tom shikenan doctor ai ko baka ce na gayawa momy zancan farin cikin nan ba zan gaya mata. amma dan Allah banda wasa na baka nan da 3 moths ka gama shirya komai ku fahimci juna dan bana so wata shekarar ta zagayo ba kayi aure ba .



 Tom dady in sha allah komai zai tafi yarda ake so . Jinjina kai dady yayi sanan yace,  nasan kana da hankali sosai kuma kai babba ne, amma ina so na sake jan hankalika akan kasan yar gidan da zaka aura kake nema, ina son mace ar gidan manya mai tarbiya mai ilimin addini sosai .



Jinjina kai doctor yayi sanan yace  hmmm dady kar ka damu in sha allah itama tana da tarbiya sosai, dan gaskiya ba wata babba bace ma dan ko canday ba tai ba, nan da wata Waya zata yi candy, to so nake sai munyi aure in tana so sai ta cigaba da karatun nata .



Jinjina kai dady yayi sanan yace  ba komai ai wanan ba matsala bace, daka auri babba mara hankali mai halin banza gwara ka auri yarinyar, sai kama fi iya control Win ta, ni de fatana ta zama mai tarbiya .



To haka de doctor da dady suka cigaba da cin abinci suna hirar su hankali wance. dady kuwa ya saki jikinsa sosai saboda yayi farin ciki da jin doctor ya samu wanda yake so......



Bayan doctor ya koma bedroom number abban ma'eeshat ya duba, ya tura masa matsakaicin sao mai Wauke da sallama, gaisuwa, da kuma neman izinin ranar da ze zo suyi magana. Doctor bai fi 20 minutes da turawa abba message din ba, abba yayi masa reply da, ba damuwa zuwa anjima in yana da lokaci ma zai iya zuwa da yamma su gana.



Doctor bai nunawa abban ma'eeshat son ta yake ba, kawai ya nuna masa shi doctor Win daya taSa dubata wanaki ne, kuma yana so su haWu da dady dan suyi wata magana mai mahimmanci.



Allah sarki abba harda turawa doctor address Win gidan, dan shi ya bada akan rashin lafiyar ma'eeshat za suyi magana. Doctor kuwa lokacin da yaga message Win yayi farin ciki sosai da ganin abban ma'eeshat Win ya amince yazo, kuma yana sake addu'a akan Allah ya bashi sa'a. Doctor ko sanar da ma'eeshat zuwansa baiyi ba, kuma sun daWe suna chat, suna ta shan soyayyah su.



Doctor misalin arfe 5 na yamma ya gama shiryawa tsaff cikin ash color Win shadda bakajin komai sai tashin amshin turare. Shaddar tayi matuar arbar jikin sa, abinka da farar fata, ga hular nan tasa itama ash sai yalli take.



Zuciyar doctor cike da zullumi ya shiga motar sa, sanan ya fuce daga gidan nasu. Kafin doctor ya arasa shiga layin su ma'eeshat parking Win motar sa yayi sanan ya fita ya shiga masallaci mafi kusa da shi da yake yana da alwala kuma lokacin an fara kiran sallah. Bayan doctor ya idar da sallah futowa yayi ya koma motar sa sanan ya shiga layin su ma'eeshat sai gashi a ofar gidan nasu. Wayar sa doctor ya Wauka sanan ya fara kiran layin abba zuciyarsa cike da zullumi.



Bayan wayar tayi ringing 4 abba Wauka yayi baki Wauke da sallama. cikin girmamawa doctor ya amsa sanan ya sanar da abba ya araso. Abba cewa yayi  tom bari ya aiko yaro yayi masa iso .



Sai da doctor ya Wauki kimanin 10 minutes, yana zaune a mota yana chat da ma'eeshat. ita kam ma'eeshat bata san wainar da ake toya ba tana can harWe a bedroom Win ta. sanan doctor ya hango wani yaro mai shigen kama da ma'eeshat Win ya futo wanda baze gaza 12 years ba.



Har mota ya araso cikin giramamwa ya gai da doctor sanan ya sanar da shi abba yace ya rako shi ciki. ba musu doctor ya futo ya rufe motar ta, sanan suka fara jerawa shida yaron.



Bayan sun shiga, sai da suka Wanyi tafiya sosai da yake gidan da girma ba laifi sanan suka isa ofar wani katafaran sitroom. Tun daga nan yaron ya dakata sannan ya cewa doctor ya shiga abban nasu yana ciki. Doctor kuwa ba musu ya shiga baki Wauke da sallama. A zaune ya hangi dady akan kujera afnan tana daga gefan sa tana danna wayar abba.



Amma afnan tana Wagowa ta hangi doctor da sauri ta ajiyewa abba wayar tasa sanan ta sauka daga kan kujera a guje ta nufi doctor ashmal tana masa oyoyo...............



Kuna tunanin abba zai amince da doctor ashmal ya basa auran ma'eeshat ko kuwa de?.



kar ku manta da like (reacted) and share.



Ayi following Win channel Wina saboda ina samu posting da zarar na dora.



mu haWe a next page.







_page 16





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Lokacin da afnan ta arasa wajan doctor a guje tana masa oyoyo, ko aurin sa bata arasa ba sai afafuwan sa ta samu ta rungume. Fuska a sake doctor ya rie hanun afnan tare da cewa  oyoyo afnan sanun ki .



Sanan ya durusa har asa yace  abba ina wuni hanun sa rie dana afnan. Abba kuwa kana ganin fuskar sa kasan yayi farin ciki da zuwan doctor sosai, cikin sakin fuska yace  lafiya alau doctor, sannu da zuwa ya hanya, ah tashi-tsahi haka, ga kujera nan ka zauna, mana .



Miewa doctor yayi kamar yarda abba ya umarce shi ya nufi lafiyayyiyar kujera mai face Win wanda abba yake zaune ya zauna. itama afnan mia masa hannu tai tare da cewa  nima kaga doctor Worani na zauna kusa da kai . Murmushi doctor yayi tare da Waukan afnan yana zaunar da ita akan kujerar kusa da ita. Abba kuwa cikin jin daWin yace  ah afnan kenan wato baki manta doctor ba ko, har kin gane shi .



Dariyar su ta yara afnan tai, sanan tace  eh na san shi mana abokina ne, ko doctor? Afnan ta tambaye tana tsare doctor da Ido. Murmushi doctor yayi wanda har sai da fararran kyawawan haoran sa suka futo, sanan ya gyaWa kai yana cewa  sosai ma afnan ni abokin ki ne ni .



Dariya abba yayi tare da cewa "eh lallai afnan an girma yanzu doctor ne abokin naki kenan . gyaWa kai afnan tai, sanan tace kuma gashi har sweet ma yake bani in naje wajan sa, nima zan bashi nawa alawar .



Murmushi doctor yayi sanan yace  tom afnan harda kyauta haka nagode sosai afnan saukowa tai da sauri ta mie tare da cewa  na tafi naje na kawo maka daga haka afnan ta mie ta fuce ta cikin wata asaitacciyar kofar daga cikin sitroom Win.



Daga abban har doctor ashmal murmushi su ke, saboda afnan ta basu nishadi ba laifi. Bayan afnan ta fita doctor da abba sake gaisawa su kai yi sosai, cikin ladabi da biyayyah. Bayan sun gama gaisawa sun Wanyi hira akan marasa lafiya hospital, abba cewa yayi  doctor zai iya faWan abunda yake tafe da shi kai tsaye . Gyaran murya doctor yayi tare da gyara zama.



Cikin nutsuwa ya fara yiwa abba bayani kamar haka "dama zuwa nayi in ba damuwa na roe ka alfarma abba akan ayusha . Jinjina kai abba yayi alamun yana sauraron sa., doctor ashmal kuwa cigaba da magana yayi cikin nutsuwa.



 Nayi tunanin kafin komai yayi nisa nazo na same ka na gaya maka saboda ka bani izini, ina so ka bani izini mu dedeta da ayushat kafin a nema min auran ta, naganta na yaba da tarbiyar ta da kuma hankali ta, tayi dede da irin matar da nake so. Tom shine nace bari nazo na sameka abba kafin na fara zuwa sai na nemi izini . Jinjina kai abba yayi, sanan yace



"warai kuwa doctor kayi yan kai sosai, kuma nima na yaba da yawawan halinka, duk da dama ana ganin ka anga babba mai nutsuwa da hankali. saboda yanzu gaskiya a zamanin nan ba ko wana saurayi ne zai fara zuwa wajan iyayan yarinya ba kafin ya fara neman ta, naji daWi hakan sosai, kana da aure ne? . abba ya watasawa doctor ashmal tambayar?.



Murmushi doctor yayi tare da girgiza kai cikin ladabi da biyayyah yace " a'a abba bani da aure kuma ban taSa yin aure ba yanzu ne de nake sa ran hakan, tunda komai lokaci ne".



 Gaskiya ne doctor komai lokaci ne, dama na daWe ina tunani, bazan bawa ma'eeshat yaro ta aura ba sai mai mata, saboda ta cika rawar kai da gaSintar fari. kuma kasan yaran zamani basu da kirki, yanzu sai aita samu saSani, in ta haWu da mara hauri, amma yanzu kai naga ka dace da irin mijin da nake so, sobada kai babba ne kuma na yaba da tarbiyyar ka.



Sai de wani hanzar ba guda ba, kasan ni uba ne a wajan ma'eeshat kuma ba tare nake zama da ita kullum ba. baze yu na gane ra'a yin ta ba, amma zan tambayi mahaifiyarta ta tambaye ta in de har tana son aure bayan tayi canday to sai ka fara zuwa ko dedeta har Allah yasa ku fahimci juna .



Jinjina kai doctor yayi tare da cewa "gaskiya ne abba duk abunda kace haka ya kamata ayi, amma ni bani da ra'ayin fara zuwa wajan ta hira har sai tayi canday saboda kaga kar na janye mata hankali, kuma gashi za tai jarabawar arshe .



 Gaskiya ne doctor kayi gaskiya kam, shi yasa ake son masu hankali irin ku, dama ina tunanin sauran wata Waya ta kammala jarabawar dan inaga zuwa jibi zama su fara jarabawar. Bayan kuma nan sai canday. Amma yanzu bari de na bugawa ma'eeshat Win ta sauko ku gaisa, daga nan ko exchange Win number wayi ku fara gaisawa kafin aga abunda Allah zaiyi .



Kafin doctor ma ya kai da magana abba ya Wauki wayarsa ya fara lalubo number ma'eeshat Win. angaran doctor kuwa ba aramin daWin hakan yaji ba, saboda shi dama har ga Allah yana son ganin ma'eeshat amma ba hali kuma ko da wasa bai yi tunanin abba zai sakar mai fuska kamar haka ba har ya bashi damar ganawa da ma'eeshat Win.



Doctor jin muryar abba yayi yace  hello daughter? . Bayan Abba yayi jim kaWan arawa yayi da " ki sauko ki same ni a sitroom Win kasa, nayi bao zaku gaisa daga nan ki tawo masa da abun sanyi daga haka abba ok yace kawai sanan ya katse wayar.



Cikin sakin fuska abba yace  yauwa doctor gata nan zuwa . murmushi doctor yayi cikin jin daWi yace  okay shikenan abba ba damuwa angode . Daga haka abba da doctor ashmal hira suka cigaba da yi har tsawan 15 minutes amma shiru kake jin ma'eeshat.



Abba cikin mamaki ya kalli agogo tare da cewa  kai subhanallahi, kaga har 18 minutes amma ma'eeshat shiru, hmmm dama haka an fari suke da shiririta, sai hauri bari na sake kiran ta . Girgiza kai doctor yayi tare da cewa  no abba ba komai .



Abba yana kiran wayar ma'eeshat ringing uku tai suka ji ma'eeshat ta waWa sallama, ta futo ta Wayar ofar da afnan ta fuce. Katse wayar abba yayi tare da amsa sallama, shima haka doctor ya amsa sallamar asa-asa zuciyar sa cike fall da son ganin ta.



Bain skirt ne a jikin ta na engalish wst, sai riga fara t shert mai dogwan hannu wanda taluluSeta da babban mayafi dan bama a ganin rigar sai hanun ta, saboda mayafin ma na mami ne. A hankali ta shigo tana tafiya, hannun ta rike da tire mai Wauke da leman wali da kuma ruwa sai class cup guda biyu.



Abba kallan ta yayi tare da cewa  ma'eeshat kenan ina kika tsaya, kina can kina danna waya ko . murmushi ma'eeshat tai hannu rike da flat tace  kai abba amma a haka sai naga kamar ma nayi saurin zuwa .



Ma'eesha ta arasa maganar tana tsugunawa asa gefan afar doctor ashmal ta ajiye tire Win tare da cewa  ina wana ta faWa tana Wagowa domin ganin wana abokin abba ne, saboda tunda ta shigo ko kallan sa ba tai ba, sai faman amshin turare da yake tashi.



Gaban ma'eeshat

13 / 38