Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   23 / 38

66K to 69K   out of 111.1K words

ya kashe wayar saboda zazzafar sha'awar da ma'eeshat ta tayar masa. soyayyar ma'eeshat ta kama doctor yarda bai taSa zata ba shi gani yake lokacin auran da aka sa musu yayi tsawo kamar ma tafiya......



Meenal



Kiran sallah asubar fari momy ta shigo bedroom Win yesmeen ta tashi meenal da yesmeen suka shiga toilet suka Waura alwala, bayan sun futo suka gabatar da sallah,. bayan sun idar da sallah yesmeen komawa baccinta tai.



Ita kuwa meenal toilet ta nufa tai wanka, kamar jiya kafin ma ta futo har momy ta sake Wauko mata kayan yesmeen, dan haka meenal tana futowa kwasar kayan tai ta koma toilet tasa kayanta. dan meenal gani take ba zata iya sa kayan ba in bata shiga toilet ba, kamar wani zai shigo ya ganta.



Bayan meenal ta gama breakfast Winta tass, ladidi ce ta shigo suka fara hira kafin momy ta gama shiryawa. Bayan momy ta gama shiryawa, ladidi har wajan mota ta raka su meenal saboda yau bada ladidi za'a ba. momy da meenal suna shiga ba Sata lokaci driver ya fuce daga gidan domin zuwa hospital.



Lokacin da su meenal suka isa hospital baba ya farka kuma cikin ikon Allah ya fara magana harshen sa ya dawo. Lokacin da baba yaga meenal yayi murna sosai da sosai ya ri™e ta gam ya rungume ta daga zaune kamar wanda za'a ™wace masa ita.



Itama meenal tayi murna sosai, bama ita kaWai ba har momy taji daWin hakan, kuma baba da meenal sunyi mugun burgeta ganin yarda suke farin ciki da ganin junan su. Meenal ta sake farin ciki sosai ganin baba da kan sa ya rike cup Win tea yayi breakfast.



Wajan ™arfe 11:00 na safe baba ya koma bacci bayan yasha magungunan sa. Itama momy da taga jikin baba yayi kyau cewa tai bari ta wuce gida domin dafa abincin rana amma anjima zata dawo, daga nan kamar jiya suka Wauki umma domin su sauke umma a gida, ta huta ta Wanyi bacci.



Meenal ita Waya aka bari wajan baba, kuma bayan haka likitoci suka ce mata ta fita ta bawa baba waje domin ya huta kuma babban likita ya kusan ™arasowa.



Meenal da taji haka fucewa tai daga sashin baki Waya ta koma wajan wasu flowers masu kyau a hospital Win suka fara shan chat Win soyayya ita da waleed, saboda meenal yau ta nutsu ganin baban nata ya dawo normal.



Har doctor ashmal ya shugo hospital Win meenal bata sani ba, ita de taji daga nesa-nesa wai ana cewa babban likita zai shigo. Bayan doctor ya shigo sai da aka tashi baba ya duba shi sosai su kai yi maganganu ya tambayi baba yanzu ya yake jin jikin nasa.



Doctor ashmal ya jima kan baba saboda tun jiya dady yake masa magana akan dole yazo ya duba jikin baba ya gani ko akwai wata matsalar. Amma doctor ashmal bayan ya duba baba yaga jikin sa da sau™i ba wata matsalar.



Ya bawa likitocin shawara da dama yarda zasu kula da baba, sannan ya ja musu kunne akan su kula da jikin baba sosai kar suyi wasa, saboda shima kamar baba yake wajansa. Likitocin sun amsa umarni da doctor ya basu, kuma sun ce in sha Allah zasu kula.



Doctor ashmal yayi hakan ne saboda yarda yaga momy da dady sun damu sosai akan jikin baba, kuma gashi twins ma hankali su ya tashi, musamman ma fadeel da ya aikata lefin. Daga haka doctor ya bar hospital Win bai sake duba kowa ba saboda yana da marasa lafiya sosai da suke san ganin sa.



Sai wajan la'ar meenal ta mi™e ta Waura alwala sanan ta koma cikin hospital Win ta gabatar da sallah. meenal bata wani jima da idar da sallah ba momy ta aiko ladidi ita da driver domin ta kawo abinci rana. ladidi tace momy bata Wan jin daWi amma zuwa anjima zata dawo.



Sai wajan ™arfe uku sanan meenal da ladidi suka zuba abinci suka fara ci, suna ci suna hira. Bayan sun kammala ci baba ya tashi meenal zuba masa tai shima sanan ta kai masa ya faraci. daga nan kuma meenal da ladidin sukayi sallah la'asar.



Masalin ™arfe 5:30 na yamma baba yana ™wance akan gado hospital ita kuma meenal tana dage gefe tana danna wayarta. "Aminatu" meenal har tsakiyar kanta taji baba ya faWi sunan ta.



Ajiye wayar meenal tai a cinyar ta sanan ta koma gefan kan baba ta zauna tare da cewa "baba lafiya ko wani abun kake so?" "a'a bana bu™atar komai meenal Allah yayi miki albarka" "ameen baba na" "amma ina so muyi wata magana da ke ne?"



"Tom baba ina jin ka" meenal ta faWa tana tsare baba da ido.  meenal kinga kece kaWai wanda Allah ya bani na haifa a matsayin ´a a duniya, kuma ina sonki har cikin rai na duk duniya bani da kamar ki ke da mahaifiyar ki dan haka ina so......... shiru baba yayi da maganar sakamakon jin sallama.



Meenal tana Wago ido taga dady ne ya shigo fuska nan tasa Wauke da fara'a. Har ™asa meenal ta tsuguna ta gai da baba. "lafiya ™alau sannu ki tashi ya mai jiki?". dady ya tambayi meenal. kafin ma meenal tai magana baba yace "jiki alhamdulilah" duk da kuwa bai san wane ba.



Meenal a ta™aice tayiwa baba bayanin wanene dady,. Nan da nan dady ya hau bawa baba ha™uri bisa abinda ya faru, shi kuwa baba yace ba komai ya yafewa fadeel duniya da lahira ai ™addara ce. dady yaji daWin hakan kuma ba laifi sun Wanyi hira da dadyn.



Da baba yaga dady kamar ba yanzu zai tafi ba kuma baba yana son yin magana da meenal, cigaba da magana baba yayi da cewa "aminatu kina jina koh?". Jinjina kai meenal tai tare da cewa"eh baba ina sauraran ka".



 Meenal tunda na haife ki duk abinda kike so ina ™o™arin yi miki, ina so na faranta miki kuma burinki shine nawa, duk abinda kike so ina maraba da shi banda ´an ™wanakin nan da muka samu matsala hakane ko?".



Sunkuyar da kai meenal tai sanan ta bawa baba amsa da cewa "eh hakane baba". gyara kwanciya baba yayi sanan ya ru™o hanun meenal yana cewa "meenal dan Allah dan annabi kimin wanan alfarmar akan waleed".



Shiru meenal tai ba tare da tace komai ba sai ma wani yawu da ta haWiye mai kauri. baba kuwa cigaba da magana yayi kamar haka "nasan kina son waleed kuma ni bazan so na rabaki da abinda kike so ba ko a mafarki ba, amma meenal bani da yarda zanyi, waleed bashi da kyan hali meenal, naso na zaSa miki mijin da ya dace dake nan kusa-kusa amma gashi rashin lafiya ta kamani, dan Allah meenal ki rabu da waleed, waleed ba mijin aure bane ko kin aure shi ba zaki taSa samun kwanciyar hankali ba .



 bana so ko bayan idona ki cigaba da ma'amala da shi. Bana son ki auri waleed meenal wanan shine alfarmar da nake so kimin, waleed ba mutumin kirki bane, kuma ke nasan me daraja ce bana so na bawa waleed ke a matsayin miji ba mutum na gari bane kuma be cancanta da ke ba".



Wani gigitaccan kuka meenal ta fashe da shi tare da cewa "baba ina son waleed sosai shima yana sona, baba in na rabu da waleed zai shiga wani hali dan Allah dan annabi baba ina ro™anka da ka gayamin mene halin waleed kafin na rabu da shi Win, in sha allah in ka gayamin halin nasa in de naji yayi muni zanyi maka biyayya na rabu da shi" meenal ta ™arasa maganar tana fashewa da kuka mai cin rai, wanda duk wani Wan adam in yaji tabbas zai sosa masa rai.............



mu haWe a next page.





_page 30





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=ØòÜ



"Shikenan meenal ki dena kuka in kina kuka zaki Wagamin hankali zan gayamiki dalilin da yasa na rabaki da waleed duk da kuwa banyi niyar faWa miki ba amma naga kin takura kuma kin Waga hankalin ki". Baba ya ™arasa maganar tari yana sar™e masa, da sauri dady da yake gefe ya mi™e tare da cewa "kuyi ha™uri zan sa muku baki akan maganar ku duk da bada ni kuke ba".



"Haba aminatu ke da nake ganin kamar kina da hankali kar ki bani kunya mana, idan so hauka ne ha™uri magani ne ai, duk abinda iyaye suka hana ´ayan su wallahi abun ba shi da kyau, kuma abinda babba ya hango yaro baze hango ba, kuma bugu da ™ari iyaye biyayyah dole ce gare su,.Yarda kike da tarbiya kuma babanki yake yaban ki ai be kamata ki matsa masa akan dalilin sa na yanke wukunci akan ki ba, please amina kiyi ha™uri kiyiwa mahaifinki uzuri baki ga halin da yake ciki bane ko bakya tausaya masa?.



Fuska cike da hawaye meenal tace "ina tausaya masa dan Allah baba kayi ha™uri bazan sake ba". Baba da yake ™wance wanda ya gama tari girgiza kai yayi tare da sake matsa hannun meenal da yake cikin hanun sa yana cewa!



"Ba komai amina baki yimin komai ba, nide fatana kimin biyayyah Allah yayi miki albarka, ya albarkaci rayuwar ki ya baki miji na gari tare da zuri'a Wayyiba wanda ko ranar gobe ™iyama za muyi alfahari da su".



"Ameen babana nagode" Meenal cikin shashe™ar kuka ta faWi hakan, hannu baba yasa ya fara ™o™arin sharewa meenal hawaye tare da cewa "ki dena kuma amina bana son gani kina zubar da hawayan ki, dan Allah ki dena kuka".



Tom shikenan baba na dena meenal ta ™arasa maganar tana goge hawayan fuskarta da mayafi. "Nagode sosai bawan allah da kake Wora Wiyata turba ta gari". baba ya faWa yana kallon dady da yake gefan su tsaye.



"Ba komai ai nima amina kamar Wiya take a waje na, amina maza kije wajan ladidi ki zauna kinji kibar baba ya hutu". Ba yarda meenal ta iya haka ta mi™e tsaye domin ta fiya kamar yarda dady ya bu™ata, kallon baba meenal tai sakamakon yarda ya rike mata hannu gam ya™i saki.



"Meenal tsayawa tai na kimanin 5 minutes saboda baba ya ri™e hanunta, kuma ita ba zata iya cewa ya saki ba yana binta da wani kallo wanda ita kanta bata san na menene ba. ™arshe de baba sakin hanun meenal yayi ita kuma meenal ta fara tafiya jiki a sanyaye haka baba yayi ta bin meenal da ido har ta fuce daga cikin Wakin.



Bayan meenal ta fita, baba da dady hira suka farayi sama-sama har aka kirawo sallah magriba dady ya fita yaje yayi sallah magriba sannan ya dawo. jinin baba da dady ya haWu sosai dan haka sun sha hira baba ya gaya masa magaggauna sosai wanda har su ka kai ™arfe 9:00 dare suna hira.



Lokacin momy da umma sun jima da dawowa hospital Win ma, har lokacin dady da baba suna nan suna hira, kai har sai da likitoci suka shigo suka bawa baba magani sanan suka masa allura bacci yayi awan gaba da shi. Bayan dady sunyi sallama da baba ko minti Waya bai ™arasa yabar hospital Win yana ta tunanin zantutukan da su kai da baban meenal.



lokacin da momy tacewa meenal tazo su tafi gida kamar yarda suka saba sai da meenal ta koma wajan baba, amma sai taga har ya koma bacci dan haka ba yarda ta iya haka tabi momy da ladidi suka tafi zuciyarta cike fall da ba™in ciki.



Haka suka ™arasa gidan jikin meenal a saluSe, yau de momy tace ta zauna a falo su Wanyi hira ita da yesmeen harma da ladidi. haka aka kawowa meenal abinci kala-kala suna ta janta da hira, itade meenal daga eh sai a'a kawai take cewa saboda damuwar da take ciki.



Har tsakiyar kanta meenal taji anyi sallama amma ta kasa Wagowa saboda ta tafi duniyar tunanin sahibinta waleed. Ji tai su momy sun fara amsa sallamar, ita kuma yesmeen da take gefan ta a zaune a guje ta ta mi™e ta nufi yayan nata tana masa oyoyo.



Bayan ya ™araso yana gai da momy, meenal taso gai da shi amma ta kasa Wagowa, saboda taji ladidi tana gai da shi. da kyar meenal ta iya Wagowa tare da cewa "ina wuni" ta faWa tana kallon sa. Lokacin da yaji ba™uwar murya tana gai da shi Wagowa yayi dan shi tunda ya shigo bai kula da ita ba bare ma yasan da zamanta. doctor yana Wagowa yayi sukai 4 eyes shi da meenal.



kallo Waya su kai suka janye idanuwan su, saboda kowa ya sheda kowa. bayan doctor ashmal ya amsa mi™ewa yayi ya tafi yana tunanin mai ya kawo wanan yarinyar gidan su kar fa aje itace fadeel ya bige mahaifinta, ya janyo masa ba™in jini wajan ma'eeshat, dan yasan ma'eeshat tana ji da wannan yarinyar.



Abinda yasa doctor kallo Waya yayi ya sheda meenal saboda yawanci, ma'eeshat tana yawan Wora status Win ta shi wataran yana buWewa ma yana fara ganin hoton meenal yake dena fita daga status Win, yanzu yayi kimanin 2 moths ma baya buWe status Win ma'eeshat saboda meenal.



Kuma bugu da ™ara doctor yana da memory mai kyau ko da ace ma'eeshat bata yawan Wora meenal a status, lokacin da suka haWu da meenal da ya kalle ta sosai ba abinda zai hana ya gane ta, sai de ya shiga tattamar ina ya santa.



 Kai subhanallahi kar de ace doctor ne ya kaWemin babana? meenal ta raya hakan a zuciyarta. can kuma wata zuciyar tace mata  a'a shi ai wanca kamar fadeel taji ana cewa shi kuma wannan sunan shi ashmal. Yanzu a ta™aice de Wan gidan su doctor ne ya bigemin babana a mota. haba no wonder shi yasa nake ta ganin yesmeen kamar na santa, ashe da doctor take kama duk a cikin zuciyarta meenal take raya wanan abun.



Itama meenal ta gane doctor ne ba wai dan kallon da ta taSa yi masa a zahiri bane yasa ta gane shi, a'a kawai saboda tana yawan ganin picturs Win sa wayar ma'eeshat, sometimes ma ma'eeshat ce take saka meenal a gaba wai sai taga hoton doctor, duk da ba shi yake turo mata ba, in yazo zance sai ma'eeshat tai tai masa picturs da video tun yana gajiya har ya zuba mata ido.



Firgigit meenal ta dawo daga dogwan tunanin data tafi, sakama™wan ladidi ta zungureta da hannu. Momy murmushi tai tare da cewa "yau de meenal naga kamar bata son magana tun da muka tawo a hanya naga tana wanan tunanin maza yesmeen tashi ki kai ta Waki ta wuta ta ™wanta".



Murmushi dole meenal tai tare da sunkuyar da kai ™asa kawai. "Gaskiya de kam hajiya meenal yau da yamman nan naga bata son magana" ladidi ta faWa tana washe baki. yesmeen hannun meenal taja tare da cewa taso mu tafi aunty na, ba yarda meenal ta iya haka tabi bayan yesmeen suka wuce ciki.



Bayan sun shiga bedroom Win meenal hijab Winta ta cire ta ajiye shi sanan ta zauna a gefan gado. Hawa online meenal tai, tacewa ma'eeshat  dan Allah gobe tazo hospital dan da akwai labari meenal tana son gobe ta bawa ma'eeshat labarin ashe wai gidan su doctor ashmal Win ta tazo take ™wana.



Bayan ta gama turawa ma'eeshat message dawowa kan waleed tai wanda ya zubo mata message rututu, ko tsayawa karantawa ma ba tai ba, tace masa bata jin daWi zata ™wanta, saboda tasan yanzu in bata masa reply ba ko bai ganta a online hankalin sa tashe zai yi.



daga haka meenal tasa wayarta ta a jirgi sanan ta ajiye ta a gefan gado. Yau meenal saboda damuwa bata ma tsaya yesmeen tai mata tayin kwanciya ba hayewa kan bed tai sanan ta shige cikin blanket tana ta tunanin taya zata fara rabuwa da waleed a rayuwarta.



Itama yesmeen da taga meenal ta ™wanta kuma yau de da gaskiya bata cikin mood Win da zasuyi hira, mi™ewa tai ta kashe globes sanan ta kunna mara hasken ta dawo itama tabi lafiyar gado ta ™wanta abinta, ba jimawa bacci ya kwashe ta ita da meenal Win.



Washe gari.



Asubar fari meenal ta farka daga baccin a firgican gaske. sakamako mafarkin da tai, ita de meenal tasan tayi wani mummunar mafarki mai cike da tashin hankali amma ta rasa mafarkin menene dan harma ta manta, duk da kuwa tana cikin mafarkin ta farka.



Irin mafarkin nan ne da kake amma kana tashi ko kafin ka tashi harka manta. duk da a.c da take bedroom Win hakan bai hana meenal yin gumi ba. Jigum meenal tai tana tunani wana mafarki tai. Meenal yin duniya ta kasa tuno mafarkin da tai, dan haka mi™ewa tai ta wuce toilet domin alwala.



Meenal bayan ta Wauro alwala dawowa tai ta tashi yesmeen, domin itama tai sallah. Bayan yesmeen ta shiga toilet ita kuma meenal dadduma ta shimfiWa sannan ta zumbula hijab Winta ta fara gabatar da sallah.



Bayan ta idar komawa tai kan kujera ta fara karanta azkhar Winta. ita kuma yesmeen ta hau kan daddumar ta fara gabatar da sallah. Bayan yesmeen ta idar da sallah ™wabar kayanta ta buWe tare da Webowa meenal kayan da zata sa.



Kamar kullum abayar ce de wanda ta Wanyiwa yesmeen yawa, itama sabuwar ce bata taSa sata ba, dan yesmeen tana da kaya da yawa wanda bata taSa sakawa ba na maji gaba. da yake mutan gidan suna ji da ita, kuma gata ita kaWaice mace tilo.



Bayan yesmeen ta Wauki kayan meenal ta kaiwa har inda take zaune. hannu biyu meenal tasa ta ™arSa fuskar meenal cike da murmushin dole tace  nagode sosai yesmeen daga haka meenal ta wuce toilet da kayan.



Kafin meenal ta futo daga wanka har an kawo mata breakfast. bayan ta fito zama tai ita da yesmeen suka faraci, saboda yesmeen tana so tace abinci ita da mutum bata son ci ita Waya. yesmeen sai janta take da hira, itade meenal tana biye masa bisa dole.



Meenal bata ci wani abincin kirkiba ta mi™e saboda gaba Waya bata son cin abinci. Meenal tana mi™ewa taji an murWa handel Win ™ofar. juyawa tai dan mai shugowa duk da kuwa tana tunanin momy ce zata shigo. Amma ga mamakin meenal sai taga ladidi ce ta shigo cikin

23 / 38