Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   18 / 38

51K to 54K   out of 111.1K words

ku umma meenal ta faWa tana rungume umman". murmushi umma tai sanan ta shafa bayan meenal tana cewa, "mu ma muna son ki meenal, Allah yayi miki albarka, maza ki tashi kije ki huta kafin baban naki ya shigo".



Sakin umma meenal tai sanan tace  to daga haka ta wuce ta Wakin ta, zuciyar ta cike da farin ciki. Bayan meenal ta koma bedroom, waya suka farayi da waleed sosai suke, hirar su har baba ya shigo. Sai wajan ™arfe 10 sannan waleed ya rabu da meenal, shima saboda ita ta bu™aci hakan.



Bayan sunyi sallama da waleed cikin farin ciki meenal ta nufi Wakin su baba da umma. Tsayawa tai kamar yarda ta saba in suna ciki, ta fara sallama. Haka meenal tai ta sallama har sau uku amma shiru kake ji, meenal tunda taji shiru tasan sunyi bacci, dan haka juyawa tai ta koma bedroom Win, ta cigaba da chat ita da waleed.



Washe gari.



Meenal bayan tayi sallah asubayi bacci ta koma saboda bai ishe ta ba, wajan ™arfe 11 ta tashi, sanan tai wanka tai brush, bayan ta futo ta shirya direct kicin ta nufa ta zuba abinci taci. meenal tayi mamakin da bataga umma a tsakar gida ba saboda kullum in ta tashi a tsakar gida ko a kicin take ganin maman ta.



Bayan meenal ta kammala komai bedroom Win su baba ta sake komawa ta fara sallama, kamar yarda suka koya mata. bayan baba ya amsa sallama bata izinin shigowa yayi.



Fuska cike da annuri meenal ta kutsa kai cikin bedroom Win, lokacin umma tana ™wance akan gado kamar mai bacci, amma meenal bata gama tantance, baccin take ba ko kuwa. shi kuma baba yana zaune a kan sallaya yana jan carbi ga dukkan alamu sallar walaha ya kammala.



Meenal bayan ta ™arasa gefan baban tsugunawa tai har ™asa sanan tace "baba ina ™wana fatan ka tashi lafiya". Murmushi baba yayi sanan yace "lafiya ™alau hajiya kema tafan kin tashi lafiya?".



"Alhamdulilah baba ya hanya kuma fatan ka dawo lafiya?".  Hanya alhamdulilah aminatu na dawo cikin ™oshin lafiya". Murmushi meenal tai sanan tace "masha allah baba, fatan de komai ya tafi yarda ake so koh?".



Jim baba yayi kafin yace "meenal ina so na gaya miki ko wana bawa da jarrabawar sa kuma komai sai allah ya nufa akeyin sa, meenal nasan ke me ha™uri ce kuma mai tawakkali, kuma nasan kin sanya kamata koh?".



GyaWa kai meenal tai sanan ta sake sunkuyar da kai ™asa tana cewa "gaskiya ne baba". jinjina kai baba yayi sanan ga gyara zama, bayan yayi shiru na wasu lokuta yace "meenal a matsayina na mahaifin ki, ina umartar ki daga rana mai kamar ta yau na rabaki da waleed babu ke babu shi .



Kuyi ha™uri da wannan page Win yau bai gama cika ba.





Ayi following Win channel na.



kar ku manta da like (reacted) and share.



my number 09162226240.



mu haWe a next page.





_page 22





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=ØòÜ



A gigice meenal ta Wago kai, baki na rawa tace  baba waleed fa kace? . "™warai meenal waleed nace miki, bana so wata ma'amala ta sake shiga tsakanin ki da shi". Cikin gigita meenal tace "inalillahi wa inna'ilaihirraji'un baba mai waleed ya aikata mai yayi dan allah?"



"Nide aminatu, na gaya miki ki fita daga sabgar waleed sanan ki tarkata masa gaba Waya kayan daya baki, ki mai da masa abinsa". Cinkin tsananin kuka meenal tace  baba wai mai waleed yayi maka haka kake ™o™arin raba ni da shi ne? .



 aminatu ni fa baban ki ne bazan taSa aikata abinda zai cutar da ke ba, kuma zan iya sanin abinda ke ba lallai ki sani ba, bai kamata kizo ki titsiye ni akan sai na gaya miki dalilin daya sa na rabaki da waleed ba, amma a ta™aice de kisan waleed ba mutumin KIRKI BANE, ba mijin auran ki bane .



Zaro ido meenal tai cikin tsananin ruWu da kiWimewa tace "baba wlh waleed mutum kirki ne, baba mai waleed ya aikata da zaka hanani auran sa haka? baba wallahi ko wana kalar hali ne da waleed naji na yarda na amince zan rayu da shi a hakan, baba waleed bashi da iyaye bashi da wani farin ciki sai ni baba dan allah kar kai haka waleed mutuwa zaiyi in be same ni ba 



 Ke aminatu dama haka kika koma? yaushe ki kai girman da zakiyi sa in sa dani, ina gaya miki kina gayamin, ke kika haifi kan ki ko mu muka haife

ki, ni mahaifin kine kuma ya zama dole na zaSa miki abinda ya dace dake, wanda ko bayan ran mu ni da mahaifiyar ki zaki samu farin ciki. Ke kaWai muku haifa, ya zama dole mu gina miki rayuwar da zata amfane ki ko bama doran ™asa. dan haka umar ni nake baki ba shawara ba, ki rabu da waleed na har abada . Baba ya ™arasa maganar cikin faWa sosai, duk da kuwa bai taSa yiwa Wiyar tasa faWa ba.



Daga haka a fusace baba ya tashi ya fuce yabar gida. Šora hannu bibbiyu meenal tai a kan ta, ta saki wani gigitaccan kuka murya na rawa tace "na shiga uku inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un baba me kake ™o™arin aikata mana ni da waleed?".



A hankali umma ta sauko daga kan bedroom Win jiki a sanyaye, ta ™araso kusa da meenal Win sanan ta tsuguna tana dafa kafaWun ta bibbiyu, cikin tausayawa umma tace "meenal ki nutsu mana dan Allah ki dena wanan kukan kiyi ha™uri".



 Dan Allah umma ki gayamin dalilin daya sa baba yake ™o™arin rabani da waleed, ki gayamin wana hali waleed yake da shi da baba ya kasa gayamin ko zan samu sukuni?". Jiki a sanyaye umma tace "wallahi meenal ban sani ba nima yarda yayi miki bayani haka jiya yayi min bayan ya dawo, wai waleed ba mijin aure bane. Sam ya™i gayamin dalilin,. shi yasa jiya da kika dawo kika same ni cikin damuwa. tun jiya baban ki yayi ™o™arin gaya miki, da daddare bayan ya dawo, na hana shi hakan saboda kar ki kasa bacci muna jinki kina sallama mu kai shiru. Dan Allah meenal kar kisa komai a zuciyarki, ki zama mai tawakkali dama kina da shi ki Wauki wannan a matsayin kaddarar rayuwarki kawai komai mai wucewa ne watarana sai labari . "wallahi umma bazan iya ba damuwa kuwa na shige ta tun daga yau har ™arshan rayuwata, in baku aura min waleed ba, ina son shi a haka ko wana irin hali ne da shi .



 Haba meenal ke kaWai Allah ya bamu in kika shiga damuwa muma mun shiga dan Allah kar kisa wanan a ranki, in Allah yayi waleed mijin ki ne sai kiga Allah ya dedeta komai" umma ta ™arasa maganar tana kuka.



Itama meenal wani irin ihu da gunji kuka ta saki mai karya zuciyar mai sauraro "inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah in wani laifi nai maka ka jarrabi ni da wanan masifa allah na tuba ka yafe muni .



Cikin kuka mama tace, "auzubillahi meenal, baki da hankali ne wai, kar ki sake kiyi sa™o ko ki faWi abinda zai futar da ke daga musulinci ki sauri ki tuba maza?". Cikin tsananin kuka meenal tace  allah na tuba, Allah ka dubi halin da nake ciki da maraicin waleed ka kawo mana sau™i cikin wanan musibar .



Umma tayiwa meenal rarrashi duniya amma ina meenal ta™i tai shiru, daga ™arshe ma meenal tashi tai ta koma bedroom Win ta, hankali a tashe ta Wauki wayarta ta dannawa ma'eeshat kira. Sai da ta kusan tsinkawa sanan ma'eeshat ta Wauka tare da sallama.



Meenal ko damar amsa sallamar bata samu ba cikin kuka ta fara magana "ma'eeshat kina ina ne?".  Ina gida mana lafiya naji ki kina kuka mai ya faru?" "ma'eeshat wannan maganar bata waya bace dan Allah ki sauri yanzu kizo ina cikin tashin hankali da ban taSa shigar irin sa ba a rayuwa".



"Innalillahi meenal mai yake faruwa ki gayamin mana" ma'eeshat ta faWa cikin tsanani tashin hankali". "Nace miki maganar nan bata waya bace kizo kiji abinda yake damuna kafin zuciyata ta buga na mutu na wuta da ba™in cikin nan". cikin wani saban tashin hankali ma'eeshat tace "inalillahi meenal gani nan zuwa bani 10 minutes" daga haka ma'eeshat ta gimtse wayar, ita kuwa meenal ci gaba da kukan ta tai.



Tana cikin wanan halin taji wayarta ta fara ringing, ido jajiri meenal ta kalli wayar, ai kuwa sake fashewa tai da wani rikitaccan kuka ganin waleed ne yake kiran ta.  Allah sarki waleed bawan allah sai sake kiran meenal yakeyi amma ina meenal ta kasa Wagawa ma.



Meenal tana cikin wanan halin ba'a fi 25 minutes ba ma'eeshat ta rafka sallama hankali tashe ta shigo Wakin meenal Win. Meenal tana ganin ma'eeshat ta sake rafka wani uban kuka mai cin rai". In hankali ma'eeshat yayi dubu ya tashi, dan haka da sauri ta ™arasa wajan meenal Win".



Cikin tashin hankali ta rungume ta tare da cewa "meenal meye haka yake faruwa inalillahi" meenal kuwa tana so tai magana amma ta kasa kuka sai cin ™arfin ta yake. cikin tashin hankali da tausaya ma'eeshat ta sake rungume meenal tare da bibbiga bayanta alamun rarrashi.



Cikin ™wantar da murya ma'eeshat ta fara magana "haba meenal menene haka dan Allah ki kwantar da hankaliki, ki gayamin mai yake faruwa, wanan kukan bashi da wani amfani ki gayamin ko zan iya yi miki magani. Dan Allah kiyi ha™uri ki dena kukan nan wallahi nima hankali na a tashe yake da ™yar nake iya maganar nan yi shiru meenal dan Allah ki dena kukan nan haka". Daga haka ma'eeshat ta saki meenal ta fara goge mata hawaye da hannun ta tana rarrashi.



Har sai da meenal ta samu ta dena kuka, sai ajiyar zuciya take saukewa idon nan nata yayi luwu-luwu kuma yayi jajir abun tausayi. Cikin rarrashi ma'eeshat ta ri™o hanun meenal tana shafa shi murya a sanyaye tace "meenal ki dena kuka ki gayamin abinda yake damun ki ko zuciyata zata samu sukuni . ma'eeshat ta ™arasa magana idon ta yana zubar da zafafan hawaye.



HaWiye wani zazzafan yawu mai tsananin Waci meenal tai, sanan cikin rawar murya tace "ma'eeshat baba yace bazan auri waleed ba ya raba ni da shi har a bada meenal ta ™arasa maganar tana fashewa da wani saban kuka.



Cikin mamaki ma'eeshat tace  waleed kuma inalillahi saboda me, haba meenal kar kice haka nasan baba baze taSa yin haka ba ko wasa yake miki ne, akan wana dalilin ma zai rabaki da Waleed? .



 Wallahi ma'eeshat yarda kika ji hakane ba wani wasa, ai kin san yaje abuja binciken waleed, shine yau da safe yake cewa na rabu da shi, da na tambaye shi dalili yace wai kawai bashi da kyan hali, kuma ba mijin aure bane .



"Innalillahi meenal yaya waleed kuma, gaskiya ban san yaya waleed da wani mummunan hali ba, maman shi fa yayar mami ce, kin san da nasan waleed yana da mummunan hali bazan taSa bari ku fara soyayya ba har maganar aure ta shiga" ma'eeshat ta ™arasa maganar tana zubar da hawaye.



"Wallahi ma'eeshat nima nasan haka, kuma ko za'a ™wana ana cemin waleed bashi da hali bazan yarda ba, in de ba gani nai da ido na ba".



Share waye ma'eeshat tai sanan tace  A'a meenal sanin halin mutum sai Allah ai baba bazewa waleed ™araya ba, tunda ba wanda yasan zahirin halin sa, kuma ba anan yake zaune ba, ba bin sa abujan muke ba .  Haba ma'eeshat in de kika yiwa waleed wanan mummunar fahimta baki kyauta ba, ke fa ´ar uwar sace ta jini, ni da nake bare ma nai masa shedar arziki bare ke".



"Hmmmm inalillahi wallahi meenal akwai damuwa mai tsanani ni bama ta ke nake ba waleed shine abun tausayi ba uwa ba uba gashi a rabaki da shi kin san kuwa tsananin son da yake miki, duk kunyar da waleed yakewa mami wallahi baya ji ta akan soyayyar ki. meenal waleed ya riga da ya mutu akan sanki, kuma gashi kun dace ni naso ace, naga ranar auran ku wanan masifa dame tai kama" ma'eeshat ta ™arasa maganar tana fashewa da kuka.



itama cikin kuka meenal tace "wallahi na sani in bani a rayuwar waleed mutuwa zaiyi, nima bazan iya rayuwa babu shi ba ma'eeshat ina son waleed a rayuwata fiye da komai wallahi in na rasa waleed rayuwata ta ™are har abada wayyo na shiga uku".



Haka meenal da ma'eeshat suka haWu suka ringa rusa uban iwu, kamar an musu mutuwa, sun jima suna kuka kafin umma ta shigo ta rarrashe su da ™yar. Meenal kuwa duk sanda taga waleed ya kira sai ta sake fashewa da wani iwu mai cin rai, daga ™arshe de kawai kashe wayar kawai tai.



Ranar de ma'eeshat wuni tai tana rarrashi meenal kuma ta Wan ™wantar mata hankali akan zata je ta samu su mami da abba ko allah zai sa suyiwa baba magana ya amince, ade zo a sasanta. ™arshe de ma'eeshat da taga meenal ta damu dole cewa tai zata ™wana tare da ita zuwa gobe.



Hirar duniya ma'eeshat takewa meenal saboda ta saki ranta amma ina, ko yaro yaga meenal yasan tana cikin tsananin damuwa a ranar kuwa, meenal bata iya bacci ba, saboda tasan waleed yana can hankalin sa a tashe yau bai ji muryar ta ba.



Washe gari.



Gaba Waya meenal ta kasa samun nutsuwa a rayuwarta, sai kuka take yi ta kasa ci ta kasa sha zancen ta waleed kawai, ma'eeshat har ta gaji da rarrashi dan haka ta yanke shawarar taje ta sanar da su abba abinda yake faruwa dan haka ba Sata lokaci tai wa meenal sallama ta wuce gida.



Hankali a tashe ma'eeshat ta koma gida bayan ta koma ba tai ™asa a guiwa ba ta bawa mami labarin abinda ya faru hankali tashe. Ba shiri mami ta fara salati kafin kace kwabo hankali ta ya tashi.



Mami taso ta bugawa waleed domin tabbatar da hakan amma ma'eeshat tace mami ta dakata, saboda in ta gayawa waleed hakalin sa tashi sai yi abu komai a sannu. Yarda kasan mami tai kuka sam ta kasa gane gaskiya lamarin, kuma tasan baban meenal baze faWi abinda be bincika ba.



Lokacin da abba ya dawo aka bashi labari, baiyi wani dogwan nazari ba ya amince da zancan baba, yace baze yu kuma ai auran meenal da waleed ba saboda shima ya Wauki meenal matsayin ´ar, kamar yarda waleed yake Wansa, dan haka baze shiga lamarin aka ayi aure waleed da meenal ba.



Saboda baze sa baki akan abinda be dace ba, baba yayi dede, amma in ya samu lokaci zai je wajan baban domin yaji menene Soyayyin munanan halin waleed Win. Hmmm zo kaga tashin hankali wajan ma'eeshat, nan da nan ta fara kuka wiwi.



MEENAL



Kamar jiya yau ma bata iya wani cin abinci kirki ba, sai da umma ta takura mata tukunna, tayi wani zuru-zuru kamar mara lafiya, kana ganin meenal kasan tana cikin tsananin tashin hankali. shima baba da umma hankali su ya tashi ganin halin da meenal ta shiga, amma ba yarda suka iya dole sai rarrashin kawai. Yau ma meenal bata iya bacci ba tana can tana tunanin waleed hakan ma dan ta kashe wayar, ™wana tai tana kuka.



Washe gari.



Hankali meenal ya sake tashi sosai bayan da su kai waya da ma'eeshat, ma'eeshat ta sanar da ita abinda abba yace, yana goyan bayan baba. Yau ma wuni tai tana kuka ta kasa komai.



Da magriba meenal tana tsugune a bakin rariya tana Waura alwala domin sallar magriba. Wagowa meenal tai, saboda jin sallamar wani yaro. Amsawa meenal tai tare da cewa "lafiya ko aiko ka akai wajan umma?.  A'a wai wani ne a waje yace wai yana sallama da meenal in ji waleed . gaban meenal ne ya faWi rasss, rasss, rasss, har sau uku dan saboda tsabar tashin hankali kasa cewa komai tai.



Umma kuwa da take nesa cewa tai "kaje kace gatanan zuwa". Bayan yaran ya fita idon meenal cike da hawaye tace  umma ba baba ya hanani kula sa ba sabo da me kika ce haka dama kin bari an gaya masa bazan futo ba kawai".



Meenal ta ™arasa maganar tana zubar da zafafan hawaye, jiki a sanyaye umma tace "eh shi yasa yanzu nake so ki sauri ki futa, kice masa ya dakata da zuwa, nan da wasu ´an lokaci, ki sauri kafin baban ki ya dawo".



Jiki na rawa meenal ta amsa da to, ta shiga Waki da sauri ta Wauko hijab Winta. Bayan tasa hijab Win jiki na rawa, meenal ta fita saboda itama ta matsu tasa idon ta cikin na waleed Win............



Ayi following Win channel na.



kar ku manta da like (reacted) and share.



my number 09162226240.



mu haWe a next page.







_page 23





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=ØòÜ



Jiki a sanyaye meenal ta fita, tun daga nesa ta fara ganin waleed ya faWa duk yabi yayi wani zuru-zuru abin tausayi. tun kafin meenal ta ™arasa waleed yake sakar mata wani tattausan murmushi.



Meenal kuwa idon ta yayi jajir fuskar nan tata ta kumbura, tun daga nesa ™walla ta taru a idon meenal, saboda tsantsar tausayin waleed Win. Ko data ™araso gefan waleed ta tsaya ba tare da tace komai.



"Meenal Wina mai yake faruwa naga gaba Waya kamar bakyajin daWi ko Wan murmushi baki min ba bare sallama, har azo da gai suwa kuma". ˜a™alo murmushin dole meenal tai kamar yarda waleed ya bu™ata.



"Ina wuni?" meenal ta faWa cikin tsananin ™arfin hali,. "Lafiya ™alau babe wai mai yake faruwa ne too days naga gaba Waya bana samun ki a waya ko na kirawo ki a kashe, kuma yanzu nazo naga gaba Waya bakyajin daWi". Meenal bata san sanda wasu zafafan hawaye suka fara bin fuskarta ba. a gigice waleed yace "haba meenal mene haka, kinga yarda kika tada min hankali kuwa mai yake faruwa ko baki da lafiya ne?".



Girgiza kai meenal tai hawaye Waya na bin Waya. "Dan Allah meenal ki dena kukan nan meye haka Please ki kwantar da hankaliki ki gayamin me yake faruwa ko

18 / 38