Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   15 / 38

42K to 45K   out of 111.1K words

kai .  It's okay my eeshat kar kiyi fushi dani, zan gaya miki in zan sake zuwa next . Murmushi ma'eeshat tai sanan tace  yauwa ko kai fa .  Hmmm kema ko ke fa an matana kin cika rigama sosai kamar yar baby .



 To ni ba baby bace a wajan ka? . murmushi doctor yayi sanan yace  eh haka ne kinma fi baby, a wajan doctor  Yauwa haka nake son ji .

 Tom babe gaskiya yau naji daWin ganin ka sosai dama haka kike da kyau?



Murmushi ma'eeshat tai sanan tace  duk kyau na ai ban kai ka ba . Cije lips doctor yayi sanan yace  ke daWi na da ke kin cika yarinta, dama maza suna da wani kyau ne? .  Eh suna da shi mana sosai . Cikin mamki doctor yace to, in ban taSa sani ba kuwa sai yau .  Tab to in kai baka gani kyanka, ni ina gani kyan ka sosai da sosai .



 Hmmmm eeshat kenan Allah ya shiryamin ke? .  Ameen doctor to ka bani labari .  Hmmm my love labari sai ke maza ki bani nasha . cikin jin daWi ma'eeshat tace  tom shikenan zan baka labarin da zaka ji daWin sa . Tom haka ma'eeshat da doctor su ka sha hirar su sosai, sai da su ka kai kimanin 12 dare sanan doctor yace suje su wanta haka. amma iriiri ma'eeshat tace a'a ita bata gaji da shi ba ta ringa zabga masa shagwaSa.



Wanda hakan ba aramin tayarwa da doctor hankali yayi ba, sai da tasa ciwan sa ya tashi, ba shiri. amma haka de ya lallaSa ta da kyar ta yarda su kai sallama cike da aunar junan su........



To jarabawar su ma'eeshat ta kankama sosai, dan meenal da ma'eeshat sun fara jarabawa. Gaba Waya ma'eeshat ta watasar da doctor saboda jarabawa, shima doctor ya Wan Waga mata afa saboda kar ya Wauke mata hankali ta faWi jarabawa.



Sai bayan too day's yake kiranta shima ba wani jimawa suke ba, 30 minutes suke ko 1 hour. Ma'eeshat ta mai da hankali sosai tana karatu, ga addu'a da take ga sallah dare, ahakan Allah ya basu sa a suji jarabawa ita da awarta meenal.



Itama Sangaran meenal Win, tayi baya-baya da waleed duk da kuwa shi bai san haka ba, baya Waga mata afa kullum sai sunyi waya. haka dole meenal take bashi lokaci, da yake duk karatun jarabarwar ma ta gama yi, sai de wanda ba za'a rasa ba.



A rana sau Waya take Waga wayarsa, shi kuwa waleed sai ya kai 2 hours yana waya da meenal sam ya kasa Waga mata afa, shi in bai ji muryar ta ba sosai sam baya jin daWi ji yake kamar bashi da lafiya.



To kwance tashi ba wuya wajan Allah, meenal da ma'eeshat sun kammala jarabawar su baki Waya bayan an Wauki 2 moths. sunyi jab, waec,neco. yanzu saka maka makwan su kawai zasu duba su gani.



Zaman gida ya kama su, suna nan suna shirye-shirye shan canday nan da sati 1.



Soyayah tsakanin doctor da ma'eeshat ta sake dawowa sabuwa, kuma doctor yayi mata alawarin, ranar da sukai celebrate Win candy in sha Allah zai zo zance wajan ta.



Ma'eeshat kuwa taji daWi sosai, dan haka sai Allah-Allah take suyi, celebrate Win candy Win. wana biyu basa zama, ita da meenal kasuwa suke zuwa da shopp saboda su, suyi siyayyar abubuwa da suke buata da kuma kayan da zasu sa ai musu picturs Win graduation. Musamman ma ma'eeshat Win tama fi meenal zagewa, dan ko meenal bata je ba, ita da kanta zata sa driver ya fita da ita ta suyo musu wani abubuwan.



angaran waleed shima yana nan yana shirye-shiryen dawowa kano, saboda canday Win meenal. sanan yayiwa meenal alwari yana dawowa in sha Allah baze koma ba sai an sa musu ranar aure..........



Yau de gaskiya busy yayi min yawa shi yasa ban muku typing sosai ba, dan typing Win yau bai gama cika page ba, kuyi hauri da wanan.



Ayi following Win channel na.



kar ku manta da like (reacted) and share.



my number 09162226240.



mu haWe a next page.







_page 18





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Yau ta kasance ranar canday Win su ma'eeshat. Zuciyar ma'eeshat cike fall take da farin ciki saboda tasan ko ba komai, doctor zai fara zuwa wajan ta zance.



Itama meenal zuciyar cike fall take da farin cikin, saboda yau waleed zai biyo jirgin dare ya dawo, kuma tasan tabbas an kusan kawo kuWin auran nata, saboda yace yana zuwa zai aiko manya ai maganar auran su.



Makarantar su ma'eeshat ta cika sosai da iyaye malamai da kuma sauran Walibai. Ma'eeshat tasha yabo sosai wajan malamanta biyu. Ita kuwa meenal ba'a magana gaba Waya malaman school Win kowa sai da ya yebe ta ga san barka.



Sanan har kyauta akai mata, ta gaba Waya makarantar tafi kowa hankali da nutsuwa a zangwan shekarar arshe. kuma gashi taci kyauta zuwa first class a ajin su tunda aka sa meenal a school Win first class take zuwa, ba taSa Waukar ta 2 ba kullum itace first class.



Ita kuwa ma'eeshat kyauta Waya ta samu ta lashe, wato tazo ta uku. Shine kawai kyautar da ta lashe, saboda bata da hauri kuma ka shegen surutu a class kamar taci aku. Masha allah, yan uwa da abokan arziki sun hallaci candy Win su ma'eeshat sosai. Su ma'eeshat da meenal sun sha celebrate Win canday su da class mate Win su. Ansha picturs sosai da sosai.



Sanan kuma an zane riguna da makoki kala-kala harda hijab, kowa yana yima Wan uwan sa, sa hannun sa a kaya. Su meenal wuni Waya su kai suna abu guda, suna farin ciki sosai da wanan rana, masu kukan rabuwa da awaye suna yi.



Anci an sha, anyi picturs, anyi wasa, anyi tsalle tsalle, an zane bangwan school da rubutu, kai abubuwa da dama de akai, ranar sai da student maza da mata suka rikita school Win nan ta ko ina.



Sai misalin arfe biyar da rabi driver su ma'eeshat ya araso domin Waukar su. Haka suka rabu da awayan su cike da kewa da aunar juna.



Direct driver gidan su ma'eeshat ya wuce da su. A gajiye suka shiga cikin gidan, bayan sun shiga ciki, mami tai musu san barka. bedroom Win ma'eeshat suka wuce., suna shiga meenal ta cire kayanta tai ta Wauko towel ta Waura sanan ta shige cikin toilet domin yin wanka.



Bayan ta futo itama ma'eeshat shiga tai domin wankan. A nitse meenal ta arasa wardrobe Win ma'eeshat ta buWe sanan ta fara lalubo kayan da za tasa. Wata blue Win abaya ta Wauka mara nauyi bayan tasa, ta Wauke kan ta da blue Win mayafin abayar sanan ta koma kan bed ta zauna.



Bayan meenal ta duba wayarta dogwan message ta gani ya shiga mata na waleed. Ajiyar zuciya tai tana tunanin mene haka a cikin message Win. Dan haka karantawa ta farayi cikin nutsuwa.



Koda meenal ta kammala karanta dogwan message Win murmushi ta saki saboda taji daWin message Win Waleed. Congratulations yake mata kan canday Win da tai, sanan yana mata fatan suyi aure very soon, harda tsara musu rayuwar da za suyi.



Godiya meenal tai mai sosai ta turamai, zuciya cike fall da kauna. Kafin meenal ta ajiye wayar kiran waleed ya shigo, tayi farin ciki sosai da ganin kiran nasa, dan haka kwanciya tai akan gado sanan ta Wauki wayar baki dauke da sallama.



Bayan ma'eeshat ta futo, itama wardrobe ta nufa ta Wauko rigar tasa, sanan ta haukan gado tana bin meenal da ido wanda shaui da soyayah ya gama tafiya da ita, sai wani lumshe ido take kamar mai jin baccci tana magana a hankula.



Murmushi ma'eeshat tai tana mamaki yarda meenal ta faWa soyayya waleed cikin lokaci anani, ita da ada ko burgeta soyayya bata yi.



Lokacin da meenal ta ankare da ma'eeshat a wajan da sauri ta rufe fuska alamun jin kunya saboda tayi mugun tsarguwa da kallon da ma'eeshat take mata. Meenal ko sallama batayiwa waleed ba ta kashe wayar sanan ta sata a jirgi, saboda karma ya sake kira.  Ah kiji ar iska, shi yaya waleed Win da kike kashe mai murya kuna shan kalamai baki ji kunyarsa ba sai ni? Ma'eeshat ta faWi hakan tana gallawa meenal hararar wasa.



Wani siririn murmushi meenal tai sanan tace "hmmm ai kece kin cika sa ido wallahi duk kin sa na wani tsargu da yawa". Murmushi ma'eeshat tai sannan tace "hmm ai meenal mamaki kika bani wai yau kece kike soyayya koh".



Itama meenal murmushi sai sanan tace "hmmm ma'eeshat kenan ki dena mamaki kin san komai na allah ne, ai bama yanzu zaki mamaki ba sai allah ya kai mu lokacin bikin namu" meenal ta arasa maganar tana sunkuyar da kai.



an duka ma'eeshat ta kai wa meenal "iye lallai meenal matar waleed, yau da kan ki kike faWar hakan, to Allah ya kai mu lokacin". Sunkuyar da kai meenal tai sanan tace  ameen a hankali.



Wayarta ma'eeshat ta janyo, bayan ta gama duba whatsApp gani tai gaba Waya ba message Win doctor, kuma gashi ko Wan congratulations bai mata ba, yau gaba Waya bai mata magana ba bare ya kira ta, tunda safe, kuma bayan yasan yau ne candy Win nata. Wani siririn tsaki taja, sanan ta fara lalubo number doctor Win. bayan ma'eeshat ta gama lalubo number doctor Win, biga masa ta farayi zuciya a zafafe.



Amma abun mamaki ba amsa, sai da ma'eeshat tai wa doctor kira har sau uku ta duka layin sa amma ina ba amasa. Gaba Waya jikin ma'eeshat yayi sanyi kuma farin cikin ta ya fara komawa ciki. Bayan ma'eeshat tai dogwan tunani, sai ta bada doctor aiki yayi masa yawa ne shi yasa, dan haka nan da nan hankali ta ya kwanta.



"Hmmm ma'eeshat kin ga nifa gida zan wuce yanzu nan" meenal ta faWa tana hamma. Cikin mamaki ma'eeshat tace  gida kuma meenal? kinga fa ana oarin kiran sallah magriba, kuma gashi mun waso gajiya sosai kamar ma bacci kike ji? .



"Wallahi kuwa ma'eeshat na gaji da yawa bacci nake ji shi yasa nake so na tafi gida, tun kafin ma dare yayi".  Ah haba gaskiya ba in da zaki kina nan, to wai nan ma ba gidan ku bane, ki zauna mana kin san yaufa zamuyi hira dole mun mai da yarda akai .



"Ah haba ma'eeshat karfa kice na wana gaskiya a'a" meenal ta faWa tana girgiza kai.  A'a gaskiya meenal ba inda zaki wallahi yau a nan zaki wana to menene, gobe ba sai ki tafi ba .  A'a ma'eeshat yanzu nasan umma da baba suna nan suna jira na, kar suji shiru ban dawo ba . Ki kwantar da hankalin ki, ki bari ni da kai na zan kirawo su na gaya musu .



To haka meenal da ma'eeshat su kai ta musu daga arshe de dole sai haura meenal tai da tafiya gidan nasu, saboda ma'eeshat tafi meenal naci da ban baki, harma da kafiya, dan haka ba yarda ta iya.



Daga haka kuma, kiran sallam magriba aka farayi, a tare meenal da ma'eeshat suke mie tsaye suka wuce toilet domin alwala. bayan sun gama Waura alwala sun fito, sallaya meenal ta shimfiWa musu, sanan suka saka hijabai domin gabatar da sallah. Bayan sun idar asa suka sauka domin cin abinci. suna cin abinci suna hira jefi-jefi, amma gaba Waya hankali ma'eeshat baya jikin ta, tunanin doctor ashmal kawai take yi.



Bayan sun gama cin abinci komawa bedroom su kai, meenal sai jan ma'eeshat take da hira ita kuma ma'eeshat tai jigum, ana cikin haka wayar ma'eeshat ta fara ringing, da sauri ma'eeshat ta Wauki wayar tare da duba sunan mai kira.



Lokacin da ma'eeshat taga sunan doctor, sauke ajiye zuciya tai, lokaci guda farin ciki ya cika mata zuciya. amma da yake ma'eeshat tana Wan fushi da doctor ajiye wayar tai a gefe, saboda ta rama abinda yai mata.



Bayan wayar ta tsinke wani kiran ne ya sake shigowa. lokacin da ma'eeshat taga doctor ne yake sake kiran ta, tayi mamaki sosai saboda tasan doctor baya sake kiranta in bata Wauka ba, sai bayan 30 minutes haka ko 20.



Tunda ma'eeshat taga haka, tasan da akwai abu mai mahimmanci kuwa, dan haka Waukar wayar tai ta kara a kunne ba tare da tace komai ba. Daga can Sangaran kuwa doctor ashmal sallama yayiwa ma'eeshat bayan yaji shirin yayi yawa.



A daile ma'eeshat ta amsa sallamar kamar wanda akai wa dole, wai ita alallai fushi take da shi. Ma'eeshat jin sautin murmushi doctor tai yi, bayan ya Wanyi jim, yace  hmmm eeshat wana laifi yau doctor yayi? . TaSe baki ma'eeshat tai kamar doctor yana kallan ta sanan tace "yafi kowa sanin abunda yayi ai".  Ah! Ah! Ah! kin taSa jin inda mutum yasan abinda ba'a gaya masa ba .



 Eh sosai ma kuwa yana sani, musamman in shi yana da zurfin tunani da basira .  To eeshat kin cika rigima, amma de yanzu kin san menene? . Girgiza kai ma'eeshat tai sanan tace "a'a sai ka faWa .  gani a ofar gidan ku nazo zance wajan 'yan matana eeshat . Zabura ma'eeshat tai tare da zaro ido tana dafe irji, cikin tsananin mamaki tace  da gaske? . Murmusawa doctor ya sake yi sanan yace  da gaske mana ko kina tantama ne? .



Cikin mamaki ma'eeshat tace "gaskiya kam ina kowanto, nafi tuanin wasa kake min kawai".  Ok shikenan tunda kowanto kike na koma ko zaki futo ki tabbatar da haka .  Wayyo Allah na doctor wai da gaske kake? shiru doctor yayi bai ce komai ba yana sauraran ma'eeshat.  Hmm tom shikenan ganinan futowa, give me 10 minutes only .  Ok no problem doctor yana gama faWar hakan ya katse wayar.



Ita kuwa ma'eeshat wani tsalle ta tafka tare da fara iwun daWi. Meenal da tun dazu take kallan ta tana jira ta kammala wayar ta tambaye ta, cewa tai "kai ma'eeshat meye haka mai ya faru kuma?".



A guje ma'eeshat ta rungume meenal tare da cewa "meenal ki taya ni farin ciki wai doctor ne yazo yace yanzu yana ofar gidan nan".  Ah da gaske masha allah inaga surprise Win ki kawai zai yi .  Wallahi meenal surprise Wina doctor yayi .



 Okay to kar yayi ta jiran ki maza ki tashi ki shirya mai kike jira? . Sakin meenal ma'eeshat tai tare da cewa "yanzu ma kuwa meenal wayyo farin ciki zai kashe ni". Daga haka ma'eeshat ta nufi wardrobe ta fara binciko kaya jikin ta sai rawa yake.



Dariyar meenal tai, sanan ta mie ta nufi wardrobe kusa da ma'eeshat, wanda har yanzu ta kasa zaro riga Waya a ciki.  Kai ma'eeshat ke da zakiyi sauri, kinga jeki ki Wan gyara fuskar ki ko lipstick kisa da hoda, bari na duba miki kayan da zaki sa, dan kiyi sauri .



Jiki na rawa ma'eeshat tace  tom meenal na gode sanan ta nufi merro domin yin kwalliya. A hanzarce ma'eeshat ta kammala gyara fuskarta ta, sanan ta fara shafa jel. Lokacin dta kammala, gani tai meenal har ta Wauko mata kayan da zata sa.



Doguwar rigar atamface, read Win atamfa mai ratsin bai da fari da kuma zanan ganye kore, an mata Winki doguwar riga rafa, wanda tasha stone ko ta ina sai wani walwali take.  Kai meenal nifa kin san nafi son sa abaya wallahi nafi jin daWi .



Wani kallo galala meenal ta watsawa ma'eeshat tare da cewa "kullum ke sai ki tasa wata abaya har ta dena yi miki kyau, to wallahi sai kin sa wanan atamfar yarda kike da hasken fata kyau za tai miki, ke bakya so ki sace zuciyar doctor ne? .



Murmushi ma'eeshat tai tare da cewa "ina so mana, amma takuramin rigar za tai".  A'a ba wani takura, kisa mana, za tai miki kyau sosai bari ma na nemo miki mayafi black".  Tom shikenan ma'eeshat ta faWa tana Waukar rigar domin sawa.



A hanzarce meenal ta nemowa ma'eeshat mayafin da zata sa, harma da takalmi. Meenal tana juyowa ta saki baki galala, ganin yarda rigar tai mugun karSar jikin ma'eeshat Win, kamar drowning.  Wow dubi kiga yarda ki kai kyau ma'eeshat meenal ta faWa tana arasowa.



Murmushi ma'eeshat tai sanan tace, "kinga maza kizo ki Wauramin Waukwalin nan kin san de ba iyawa nai ba". KarSar Wankwalin tai meenal sanan ta buWa shi ta fara ninkawa. Ita kuma ma'eeshat ta zauna akan kujerar merro, meenal ta fara Waura mata.



Cikin ananin lokaci meenal ta kammala yiwa ma'eeshat Wauri mai v wanda yayi matuar yi mata kyau sosai da sosai. Da sauri ma'eeshat tasa sara da Wan kunne, bayan ta gama ta yafa Wan mayafin ta.



Tabarakallah masha allah, ko Wan bain ciki ya kalli ma'eeshat sai ya ara kuma dole yace tayi kyau. itama kan ta ma'eeshat ta tabbata tayi kyau sosai da sosai, wanda raban da tayi irin sa har ta manta.



Har ta kama hanya zata fita meenal ta biyo ta da turare, tana cewa " ki tsaya kin manta baki fesa turaran ba . murmushi ma'eeshat tai sannan ta tsaya meenal ta fesa mata turaran sama-sama, daga haka ta fuce da sauri.



Da sauri ma'eeshat take tafiya, tana gab da futa suka ci karo da Mami. cikin mamaki mami tace "kai ma'eeshat ina zakije haka kike sauri harda bige ni gashi kinci kwalliya .



Murmushi ma'eeshat tai, sanan tace  ya hauri mami sauri nake ban kula dake ba doctor ne yazo . Cikin mamaki mamki tace "doctor ne yazo shine baki gayamin ba kike oarin fita ma'eeshat? .



 Wallahi mami nima yanzu ya bugomin yace yana ofar gidan ban san da zuwan sa ba . Jinjina kai mami tai, sanan tace  shikenan kije ki shigo da shi sitroom, sai kuyi magana, kin san ni bana son zancan waje .  Tom mami daga haka ma'eeshat bata sake cewa komai ba, ta wuce tabar mami tsaye da mamaki. da ido mami tabi ma'eeshat tana mamakin rawar kai irin tata, a fili tace "kai ma'eeshat Allah ya

15 / 38