Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   6 / 38

15K to 18K   out of 111.1K words

ga kyau har wani ja suke wallahi ma'eeshat ta faWi hakan a zuciyar ta. in de akazo hoton doctor ashmal da anwar sa yesmeen sunyi a tare, sai ma'eeshat taji wani yarrr a zuciyarta duk da kuwa yar uwarsa ce, kuma ba wata babba bace.



DOCTOR ASHMAL



Bayan doctor ashmal ya katse wayar wani dogwan tunani ya tafi dan shi har ga Allah bai gane dawa su kai waya ba. Kuma shi yasan sunan ma'eeshat aisha shi yasa baiyi saurin gane ta ba.

jin arar shigowa message wayar sane ya dawo da shi daga tunanin daya tafi. Lokacin da doctor ashmal ya karanta address Win da ma'eeshat ta tura masa gani yayi hanyar tafiya gudan sune WoWar dau d kuwa da Wan nisa da gidan su, kuma yau kafin magriba ma ya koma gida, dan haka bari yayi kawai in zai koma gida ya tsaya ya karSa.



miewa doctor ashmal yayi, ya Wauki i phone 17 pro max Win sa ya zira a aljiwu, sanan ya Wauki lapcout Win sa, da jakar laptop Winsa ya fuce daga office Win sabida yau gaba Waya bashi da aiki a hospital Win nan wasu takadduma yazo Wauka daga nan ya fara duba wani abu a laptop shi yasa su ma'eeshat da su kazo suka same shi, lokacin da suka shigoma yayi mamaki sosai sabida yasan shi ranar bashi da wani booking din patients..........



MA'EESHAT



Sangaran ma'eeshat kuwa kallonta tasha sosai a wayar doctor ashmal har sai da taga wayar tayi low sanan ta ajiye ta, kuma gashi wearing Win gidan nasu ya Wauke bare tasa mai a caji.



asa ta sauka ta zuba abinci taci ta oshi sanan ta dawo sama ta fara dailing Win number meenal. Meenal tana Wagawa ko gaisawa basu gama yi ba, tace "meenal wai ba zaki zo bane? .



 zan zo mana ma'eeshat ki bari sai anjima mana .  a'a wallahi ni ban yarda ba yanzu ki tawo kin san yau ina so ki ciremin aiki hoto zaki yimin mai kyau, wallahi Abbas ya takuramin wai sai na turo mai saban hoto na .



 tom shikenan ma'eeshat bari na gama wanke-wanke nai wanka sai na tawo, kin san nima ina so muyi magana dake akan waleed  hmmmm ai na sani wallahi 'yar nan ai meenal tunda kika fara bawa waleed lokaci dole ko fara son shi nan kusa ma'eeshat ta arasa maganar tana sakin dariya.



itama dariya maeenal Win tai sanan tace  kai ma'eeshat bana son haka sai nazo kawai .  tom shikenan sai kinzo, ke ban baki labari ba, wai yau da safe aka bugowa abba daga school wai naje makaranta exams Win wasu Waliban ta Sata ta english kuma har da tawa wai nazo na sake wata .



 innalillahi garin yaya? meenal ta tambaya cike da mamaki.



dariya ma'eeshat tai sanan tace "hmm ke ai daga arshe ance an ganta harfa na shirya dady zai kai ni na gaya miki ciki na yaja ruwa dan kin san duk karatun da nai na manta kuwa Hmm.



dariyar itama meenal tai mai isarta, sanan tace  kai ma'eeshat kiji tsoran Allah naga alama bakya son karatu, yanzu karatun da ki kai a exams har ya zube ai da wani video kika gani a ig ko a social media baza ki manta ba .



 hmmm kede bari wallahi ina zan manta maeenal ai ni na gaya miki aure nake so ba karatu ba ke kike Waukar zancan wasa .



 Au haka zaki ce ma, bari nazo zan gayawa mami wallahi .



 Au tun yaushe nake gayawa mami ai mamin ma ta sani ke de kiyi sauri kizo dan Allah .  Tom shikenan ma'eeshat gani nan sai nazo daga haka ma'eeshat da meenal su kai sallama.



ma'eeshat haWa wayarta tai da ta doctor ashmal ta ajiye a arashin folanta sabida afnan. ba jimawa bacci yayi awan gaba da ita........



kar ku manta da fallowing Win channel Wina, saboda sai na fara posting a channel Wina, mutanan arziki kuje kuyi following.



kar ku manta da sharing to another groups.



kar ku manta da like (reaction)



mu haWe a next page.



https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d



Game buatar comments ga link Win group Wina yayi joining







_page 7





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Ma'eeshat ba ita ta tashi daga bacci ba sai wajan arfe 3 na yamma, a lokacin ma maeenal ta daWe da zuwa tana jiran ta.



 Kai meenal shine kika zo ko ki tashe ni? meenal da take kwance akan sofa murmushi tai sanan tace "kin tashi kenan to sannu, haba daga zuwa kuma sai na tashe ki kina bacci, barin ki nai ki wuta kawai kuma gashi baki da lafiya".



mutseke ido ma'eeshat tai tare da yin mia sanan ta Waga arashin fulo ta zaro wayoyin data ajiye, tare da cewa  meenal zo kiga guy Win da nake baki labari jiya nace miki ya haWu ma'eeshat ta arasa maganar tana shiga cikin gallery a wayar doctor ashmal.



Meewa meenal tai tare da cewa "ah masha allah kice har kun haWe kenan .



taSe baki ma'eeshat tai tare da cewa  wana kalar mun haWe, baki ga wayoyin biyu bane ba, wanan ai wayar sa ce ba tawa ba .



zama meenal tai a gefan ma'eeshat Win tare da cewa  to garin yaya wayar tazo hanun ki kuma? . washe baki ma'eeshat tai tare da miawa meenal wayar tana cewa. "dan Allah meenal ya kika ga guy Win nan, kamar ba bahaushe ba ko? .



karSar wayar maeenal tai tare da zuba mata ido. meenal tana kallon hoton ta taSe baki sanan tace "eh masha allah yana da kyansa, amma ma'eeshat akan namiji kike rawar jikin nan to wai ina ma kika samo wayar tasa, wanene shi wai? .



 Doctor Ashmal sunan shi, shine fa wanan babban likitan da nake ce miki wai sai anyi min booking Win ganin sa, to yau da safe muka koma karSo gwajin da akan min nida abba da afnan, shine afnan ta Wauko wayar, ni kuma ban lura ba har sai da muka dawo gida sanan na gane ba tawa bace .



 Ah kai afnan da abin dariya, yanzu to ya za ai a mayar mai da wayar? meenal ta tambaya tana kafe ma'eeshat da kyawawan idanunwan ta.  Hmmm ai ya bugo, har na tura mai address yace zai aiko a arSa masa, kuma gashi wearing Win gida ya lalace bare nasa masa waya duk fa ni na arar da caji da akwai wajan 60 percentage fa, amma yanzu dubi befi saura 12 percentage ba .



 Kai ma'eeshat kiji tsoran Allah shine kika fara yiwa bawan Allah bincike a wayar sa? .



dariya ma'eeshat tai tare da cewa  ke kuwa ba dole ba naga jinin larabawa ke kinga 'yan gidan nasu ma suma kyawawa kai wallahi mutumin nan ya haWu ma'eeshat ta arasa maganar tana lumshe ido tare da kara hoton nasa a irji.



Fuzge wayar meenal tai tare da cewa cillata gefe tana cewa "ke de wallahi ma'eeshat ba de san maza ba, daga ganin bawan Allah kin bi kin ruWe mutsuuuu .



 kai meenal wallahi ba zaki gane ba ke kawai dan baki Wauki rayuwar ki da zafi bane shi yasa maza, basa burge ki. ke wai ya maganar waleed kuwa wana biyu naga ya dena yimin magana amma da kullum roona yake akan na shawo mai kan ki .



meenal bata san sanda wani siririn murmushi ya wace mata ba. ma'eeshat wani uban iwu ta wada tare da dukan meenal Win tana cewa "shegiyar gari wato kina sumu-sumu da kai kice kun fara shan soyayyah ".



maeenal bata ce komai ba kawai ta sake sakin wata dariyar.



 Ke bana son iskanci dan Allah ki gayamin me yake faruwa? . gyara zama meenal tai tare cewa  ke nifa ba abinda kike tunani bane ba wata soyayya da muke sha, kawai kwana biyu na bashi lokaci ne muna shan hirar mu da shi sosai, amma gaskiya yana da kirki sosai jiya fa da daddare ya turomin kati waya airtime na 20k data kuma 50GB.



Zaro ido ma'eeshat tai tare da cewa "kai! kai! kai! kai! meenal irin wanan abun arziki haka, dama wallahi waleed bada ga nan ba, bashi da rowa, abinki da me shi yana da kuWin sa babu laifi kuwa, da tunda kin bashi lokaci kun fara soyayyah ai da yanzu Allah ne yasa mai zai ringa kashe miki .



Girgiza kai meenal tai tare da cewa "a'a nifa ba ruwana, rufamin asiri da cin kuWin maza nifa wallahi dama yayi shawara dani da bai turamin ba .  Kai meenal ke dai ar Sarar da samu ce, ni kinga turamin ko katin 5K ne na rage zafi .



Miawa ma'eeshat wayarta meenal tai tare da cewa arSi ki tura na 10k ma kinsan de ni bana yawan kiran mutane, kece kawaii muke waya ko kin bar katin ma ba amfani zanyi da shi ba .



Hannu ma'eeshat tasa ta arSi wayar meenal tare da cewa  ah kawo wallahi na tura ni kuwa nake waya, meenal tawa, dan Allah ki cigaba da sakar mai fuska yana sakar mana abun duniya.



dan baki san yarda yaya waleed yake son ki bane, duk abinda kike so yayi miki yi miki zai yi, ke ko yanzu kika buWe baki kika cewa yaya walee ya baki 500k wallahi sai ya baki, kinji ma na rantse .



Zaro ido meenal tai tare da dafa irji tace "dubi Wari biyar kuma ma'eeshat? ah rufamin asirin nayi me da su, ke nifa bazan taSa iya rowan namiji kuWin sa ba, ko ya bani ma bazan arSa ba, dan kiji in gaya miki .



Tsaki ma'eeshat taja tare da cewa "sai kije kiyiwa kan ki in ya baki karki arba, ke baki san ihsanin masoya ba, wallahi ko million 5 yaya waleed zai fitar nasan ko ajin sa sabida shi baya jin fitar kuWi Allah ya bashi in kinji ana yaro da kuWi shine .



Girgiza kai meenal tai tare da cewa  kai ma'eeshat Allah ya shirye ki da son kuWi, Allah ya baki miji na gari mai arziki, arzikin mai amfani  yauwa ameen meenal mai kuWi kuma mai kyau .



 Kai ma'eeshat Allah ya iya miki meenal ta arasa maganar tana girgiza kai.



To haka ma'eeshat da meenal su kai ta hira har sai da aka fara kiraye kirayan sallah la'ara sanan suka mie su kai sallah.



Bayan sun idar ma'eeshat toilet ta shiga tai wanka, bayan ta futo zama tai ta fara shafa kayan kwalliyar ta. ta Wan yi de kwalliya ba mai yawa ba, sanan ta Wauko abayar ta baa ta saka, tai yafa Sakin mayafin abaya.



Ma'eeshat ma'abociyar son abaya ce sosai, duk rabin kayanta abaya ce, kuma gashi in tasa tana matuar yi mata kyau abinka dame jiki.



Bayan ma'eeshat ta shirya tsaff wayoyin su ta Wauka harda ta doctor ashmal sabida kar a kirawo in ya aiko a arSar mai wayar kuma bata kusa da ita. daga haka ma'eeshat da meenal suka wace garden domin yin hoto.



haka meenal da ma'eeshat su kai ta shan hotunan su kala-kala, waccan tayiwa wanan, wannan ta yiwa wanan, basu suka gama pictures Win ba sai wajan arfe 5:30.



Suna gamawa suka fara editing Win abin su hankali kwance gaba Waya hotunan a wayar meenal akayi su.  Kai meenal ji yarda kika yi kyau a hotanan dole na turawa waleed ko nima yayimin kyauta .



ringing Win wayar daya fara tashi ne ya dakatar da meenal daga maganar da zata yi.



Wayar doctor ashmal ce ta da take gefe a ajiya ta fara ringing.

da sauri ma'eeshat ta kai hannu, ai kuwa gaban tane ya faWi rass ganin ansa my number. baki na rawa tace "Kinga meenal shine yake kira wallahi, may be ya aiko a arSar mai fa .



meenal kuwa ci gaba tai da editing Win hoton tare da cewa  to ki Waga mana kiji ko ya aiko . Hannu na rawa ma'eeshat ta Waga wayar tare da karawa a kunne tana cewa "hello".  Gani nan nazo dede address Win da kika bani, ki aiko a kawo min wayar tawa .



Rass gaban ma'eeshat ya sake faWuwa jin muryar doctor ashmal, amma dakewa tai tace "Please in ba damuwa ka shigo cikin layi sai ka mie, gida na arshan layin daga hannun hagu ka tsaya ganin nan futowa sai na baka wayar, sabida yanzu ba wanda zan aiko kuma bazan iya futowa har titin nan ba yayi nisa .



Ma'eeshat tana arasa faWin haka Doctor Ashmal ya katse wayar.



Wani gumi ne ya fara getowa ma'eeshat, Kallon meenal tai wanda ta duufa tana editing Win hototunam. ckin sanyayiyar muryar ma'eeshat tace "meenal kizo ki raka ni mana na kai mai kinga ya katse wayar Allah yasa ba haushi yaji ba, da kansa ma yazo .



Girgiza kai meenal tai tare da cewa  a'a kinga ki bari ba sai munje ba ki bawa baba mai gadi kawai ya mia masa wayar tunda su aryan basa nan. Wani kallon galala ma'eeshat ta watsawa meenal tare da cewa  tab Allah ya kiyaye yanzu so kike nai asarar ganin kyakyawan nan da kan sa fa yazo ba aikowa akai ba, ni kuma sai nai fita gaskiya bazan iya ba kawai ki tashi muje malama .



Meenal tana oarin yin magana wayar doctor Ashmal Win ta fara ringing, a karo na biyu.



Da sauri ma'eeshat ta Waga tare da cewa "hello". Amma ma'eeshat shiru taji ba amsa, da ma'eeshat taji shiru sake cewa tai  hello kana ji? . amma de again shiru, sai ma arar cajin wayar taji alamun wayar za tai short down.



Da sauri ta katse kiran tare da cewa kinga meenal ba network kuma gashi wayar saura one percentage yanzu zata mutu wallahi kuma ban san ya zanyi ba. maeenal hankali kwance tace  to ki sauri ki kwafi number mana ko wayar ta mutu sai ku cigaba da communication da wayar ki .



 Eh kin kawo shawara ma'eeshat ta faWa tana shiga call, Tana shiga ta buWe number tara da miawa meenal tana cewa yi sauri ki karanto min dan Allah kafin wayar ta Wauke .



Kamar yarda ma'eeshat ta buata haka meenal ta fara karanto mata number da sauri ita kuma tana sawa, ai kuwa suna cikin wafa wayar ta mutu.  Wayyo ma'eeshat wayar ta mutu, amma 4777 ne a arshan number maza kisa, number special ce .



Yauwa maeenal ma'eeshat ta faWa tana oarin sawa, tana gama sawa ta danna call tare da karawa a kunne. Amma abin mamakin shine har wayar ta tsinke Doctor Ashmal bai Wauka ba. Wani dogwan tsaki ma'eeshat taja tare da cewa  dama nasan zaka aikata sai girman kan tsiya wato bama zaka Wauki number da baka sani ba ma'eeshat ta arasa maganar tana sake kiran doctor ashmal Win.



A taaice de sai da ma'eeshat tai wa Doctor Ashmal kira uku be Wauka ba.



Tsaki ta sake ja sanan ta tura masa gajeren message kamar haka, "Wayar taka caji ya Wauke shine nake kiran ka da wanan layin, in kazo zaka iya bugomin ta wanan layin". Ba a Wauki 2 minutes ba Doctor Ashmal yayiwa ma'eeshat reply da " ina kofar gidan da kika ce".



Ma'eeshat tana gama karantawa ta saki ajiyar zuciya tare da cewa  yauwa meenal yazo, taso ki rakani na kai ma, kinga kema kya ganshi a zahiri . girgiza kai meenal tai, sanan tace " a'a gaskiya ni ba zani ba wallahi tabb . Tsaki ma'eeshat taja sanan ta Wauki wayar ta da ta Doctor Ashmal Win tace  to ni bari naje kar kije Win daga haka ma'eeshat ta wace fuuuuuuuuuuu.



Ko da ta fita ofar gidan nasu wata mota ta gani mai rai da nunfashi gaba kaWan da gidan nasu. A cikin ranta ko ba'a gaya mata ba tace " wanan shine".



angaren Doctor Ashmal kuwa zaune yake a cikin mota yana danna wayarsa kamar ance ya Wago yana dagowa ya hange ta, a baya ta cikin mudubin motar. Sosai ya tsura mata ido yana kallon yarda take tafiya, duk da ba sauri take ba amma jikin ta yana Wan rawa, sabida tana da jiki ba lefi.



tunani Doctor Ashmal ya farayi, taya wayarsa taje hanun ta ita da ko arasowa table Win ba tai ba bare ta zauna. sai yanzu yaji sunan ma'eeshat ya dawo mai lokacin da tace mai ma'eeshat ce, kuma ya tuna afnan tana ta cewa macica amma de ya kasa gane mai take nufi sai yanzu. Duk da doctor ashmal bai fiya kallon mutane ba amma haka nan yaji ya kasa janye idanunsa daga kallon ta harta kusa arasowa, sai da yaga da gaske-gaske tana gabb da arasowa ya sunkuyar da kansa ya cigaba da danna wayarsa.



Ko da tazo galass Win motar a kulla yake kuma gashi bai ne baka ganin wanda yake ciki. Wani dogwan tsaki taja, tare da Waga wayarta domin kiran sa.



Doctor ashmal kuwa yana kallon ta sarai tass, lokacin dayaga taja tsaki, burge shi tai sosai musamman ma dayaga lokaci guda tasha kunu. kiranta yana shigowa bai Wauka ba, katsewa yayi sanan yasa hannu ya buWe murfin motar.



Ma'eeshat kuwa tana ganin ya buWe murfin motar taja baya a zuciyarta tace  wallahi in be futo ba, ba zata bashi ba, sabida tsabar rainin hankali ko murfin motar ma bai gama buWewa ba, ni yake so na arasa buWe mai kenan, to ai wanan ba office Win sa bane da zai zo yana shawa mutane amshi duk ma'eeshat a cikin zuciyarta take faWin hakan.



Doctor ashmal sai da yayi kimanin 5 minutes bai futo ba yana kallo yarda ma'eeshat take cika take wani batsewa shi kuwa sai murmushi yake ta saki shi kaWai, dan abun ma dariya yake bashi.



Doctor Ashmal ji yayi gaba Waya bai kyauta ba, da yake shi yasan darajar mutane Kuma yasan ya kamata shi har ga Allah ba da niya yai futowa ba kwai yana so yaga ma'eeshat tayi faWa ne in ya fita. Dan haka a hanzarce doctor ashmal Win ya cire bell Win motar sanan

6 / 38