Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   8 / 38

21K to 24K   out of 111.1K words

in na hau online sai tace na koya mata haka nake koya mata. to shine fa na gayawa muhseen har yanzu muna tare da ita ina koya mata karatu.



Tun daga nan ya fara bibiyarta to bata sakar mai fuska saboda abinda yayi mata a baya. shine kuma wai ya dawo waje na yace min na bata hauri akan abinda yayi mata, ni kuma nace ba ruwana, karatu ne a tsakanin mu nake koya mata. to shine yake tajin haushi na wai soyayyah muke da ita, kuma shi gashi yayi nadama ya fara son ta.



yanzu da safan nan ina fotowa daga toilet naga wayata a hanunsa wai ita ta kirawo, banma fa san mai tace mai ba shine ya kamani da dambe wai mayaudari na raba shi da masoyiyar sa .



Momy da yasmeen sake fashewa su kai da wata dariyar shi kuwa doctor ashmal shanye dariyar tasa yayi sosai tare da watsawa fadeel wani kallo yana cewa, "dama nasan kai ne da neman rigima sam baka san zaman lafiya, tunda kai kai koya mata karatun ba sai kabar wanda zai koya mata ya koya mata ba, mene nayi musu binbini .



 Wallahi Doctor arya yake maka, soyayya ce a tsakanin su ba wani karatu, da na Waga wayar fa ji nai tace, hello dear zaka shigo ne yau .



Jinjina kai doctor ashmal yayi zuciya cike da dariya yace  shikenan kuje kuyi, wato har tunanin soyayya kuke yanzu ko makaranta baku gama ba ko?. to ku shiga hankalin ku gaba Waya ku tafi ku bamu waje saura na sake jin kunyi faWa zaku ga yarda zanyi da ku . sumi-sumi fadeel da muhseen suka wuce suka bar wajan suna harara junan su ta gefan ido. duk da kuwa muhseen ne da gaskiya dan duk yanda ya faWa haka zancan yake. bayan sun wuce doctor ashmal murmushi yayi tare da cewa  kai momy Allah ya shirya mana twins Win nan naki basa jin magana .



Yesmeen sake fashewa da dariya tai tare da cewa  wallahi yah, fadeel ne bashi da gaskiya duk abinda muhseen ya faWa hakane sabida nima inaji suna faWan akan haka tun ba yau ba . Kumatun yesmeen doctor ashmal yaja, tare da cewa  oh, ni de babe ba ruwana in suka jiki, kiyi shiru kar suzo su takura min ke su ringa oarin hucewa akan ki .



Dariya yesmeen tai sanan tace  tom yah, amma yaushe za kazo ka kai ni musha ice cream tare, jiya ma sai da su muhseen suka ce nazo su kai ni, nace a'a ni kai nake so, ka kai ni .



Zaro ido Doctor Ashmal yayi tare da cewa  no babe kar ki yarda, wanan yaran masu rawar kai ne zasu kai ki tabb Wi jam, wallahi kibi a sannu duk sanda suka Wauke ki a mota kafin kuje inda zaku sun gama Waga miki hankali, sun saki kinyi kuka da idanuwan ki, gudu za suyi tayi dake akab titi, wato har daWi suke ji dan sun arbo certificate Win su na driven school, shine suke cewa kizo su Wanaki ko, to kar ki yarda babe na, ki bari ni da kai na, zan kai ki in na samu lokaci .



Jinjina kai yesmeen tai tare da cewa  tom shikenan yah ina son ka wallahi .  hmmm nima ina sonki yesmeen tawa maza kije ki shirya ki tafi tahafiz kar ki makara a dake ki, kin san bana son a dakar min ke .



 Tom shikenan yah bye daga haka yesmeen ta saki hanun doctor ta wuce bedroom domin shiryawa.



Yesmeen yarinya ce kyakyawa mai diri, bata fi shekara 14yers ba, amma tana da girman jiki sosai dan in ka ganta sai kai tunanin za tai 16, amma ko na 1 hour ka zauna da ita zaka tabbatar yarinya ce shakaff, sabida kalamanta da rashin wayo.



juyawa doctor ashmal yayi shima ya koma bedroom Win sa, ya kashe wayoyin sa baki Waya sanan ya koma wani saban baccin.



Bashi ya tashi ba sai misalin arfe 12:00 da rabi na rana, yana tashi ya shiga toilet yayi wanka, sanan ya futo ya taje sumar kan sa ya shafe jikin sa da maya mayan sa, sanan yasa wanda 3 qauter da baar t sheets ya fita fallo.



Lokacin da ya fita ba kowa a fallon, amma ga abinci nan an shirya kala-kala, zama yayi a kan kujerar daining Win, sanan ya fara saving Win kan sa. Haka ya zauna ya ringa cin abinci yanaci tunanin ma'eeshat yana sake bijiro mai a zuciya.



Bayan ya gama ci, bedroom Winsa ya koma ya Wauro alwala sanan ya wuce masallaci domin sallah. Bayan ya dawo daga masallaci ji yayi gaba Waya jikinsa ya mutu, da yayi niyar fita ya shiga hospital ko guda Waya ne amma ya kasa, gaba Waya yana cikin damuwa, zuciyarsa ta azaftu da son ma'eeshat. Gashi kuma shi sai dambe yake da zuciyar tasa akan ta manta da ita ma'eeshat Win amma, ina abu kamar ara shi ake. Haka doctor ya kwanta yayi lamo kamar mara lafiya, yana ta tunanin mafita amma ya kasa gaba Waya komai ya tsaya masa cakk.



To yau dai doctor ashmal wuni yayi a bedroom yana tunanin ma'eeshat, raban da ya zauna a bedroom ya daWe har ya manta, sabida ko bashi da aiki in ya gama hutawa yana fita wani wajan, ko ya lea hospital.



Amma sai gashi yau shine a bedroom ya kasa sukuni har wajan arfe 7:30 na yamma dan har an fara kiraye-kirayan magriba. Ala dole Doctor Ashmal ya mie ya Waura alwala sanan ya fita ya gabatar da sallah isha'i.



Yana dawowa yesmeen ta tare shi wai sai yazo sun je sunci abinci sunyi hira. Dr ashmal bashi da yarda zaiyi da yesmen, yasan ba zata yarda yace mata aa ba, dole haka ya biye mata, suka tafi suna cin abinci suna hira ko ta Webe mai kewa.



Doctor ashmal yana matuar son anwarsa yesmeen, sabida itace last bron Win su, kuma gashi tazo a mace, sanan ita kaWai ce mace a cikin gidan nasu.

Dama doctor ashmal yana son mace, mace tana burge shi ko saboda annan sa duk ba mata bane, shi yasa yake bawa yesmeen kulawa duk abinda take so yana yi mata shi ko mene kuwa, kuma sam bayi yi mata faWa ko tayi abun faWan sai de ya lallashe ta yayi mata nasiha.



Sai wajan arfe 9:00 Doctor ashmal ya dawo bedroom Winsa, yana dawowa ya shiga toilet yayi wanka, bayan ya futo gajeran wando kawai yasa ko arziki sa rigar bai samu ba yayi wanciyar sa akan bed, sanan ya kunna wayoyin sa.



Bayan wayoyin sun gama kamawa, babbar wayar ya fara Wauka yana Wauka yaga message ya shigo, dan haka direct wajan message Win ya nufa ya buWe. Different message aka turomai wajan kala goma, dan haka kallon su ya fara yi yana tunanin wanne zai fara buWewa sabodaa duk yasan de gama da aiki ne, suna da mahimmanci. Kamar ance doctor ya tafi asan message haka ya yasa hanunsa ya gara messages Win wayar, ai kuwa cak wayar ta tsaya akan tsofaffin message.



Wata duguwar ajiyar zuciya doctor ashmal ya saki lokacin da idon sa yayi masa tozali da number da ma'eeshat ta turomai gajeran sao lokacin da wayarsa ta Wauke, da yaje gidan su.  Dama can ina da hanyar da zan haWu da ita cikin saui amma na manta kai doctor ashmal ya faWi hakan a zuciya sa yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Har ga Allah doctor ashmal ya manta da sunyi wani communication Win number shi da ma'eeshat, sai yanzu daya gani sanan ya tuna.



Da sauri doctor ashmal yayi save Win number da litter m kawai, yama rasa ta ina zai fara kiran number, dan haka kawai tusa number a gaba da ido yayi yana kallonta kamar mai haddar number, shi kansa ya rasa ta ina zai fara kiran number..........



MA'EESHAT



Sai wajan arfe 5 na yamma ma eeshat ta dawo gida, sabida tun wajan arfe goma ta tafi gidan su meenal, sai da yamma driver yazo ya Wauke ta ya dawo da ita gida.



Tana dawowa gida wayarta ta saSa ta hau online tana duduba messages Winta. gaba Waya ma'eeshat bataji daWi ba saboda taga abbas bai mata reply ba, yau kimanin 3 days tana jiran sa, amma shiru. baya hawa online kuma in ta kira wayarsa a kashe.



Ma'eeshat ta damu da abbas ne, sabida shi ko da yaush in ta hau online suna magana, 247 suna chat, shi yasa too days da baya hawa online ta damu tana ta tunanin ko lafiya, haka ma'eeshat tai ta danna wayar ta tana jiran kiran abbas.



Sai da aka kirawo isha'i ta iya miewa dama batayin sallah, dan haka asa ta sauka, ta wuce kicin za zubo abinci, taci, sai da ta gama cin abinci sanan ta dawo sama, tai wanka tasa kayan bacci.



Haka ta cigaba da kallon ta a waya hankali wance, wajan arfe tara da rabi ma'eeshat taji ta fara jin bacci, duk da gobe babu school, ji tai ba zata iya ba gwara tai baccin ta kawai, dan haka kashe wifi Win wayarta tai, tana oarin kashe wayar, taga wata bauwar number an kira ta da ita, wayar sai faman ringing take.........



Gaskiya kuna yimin auran like fisabillahi, sai na gama shan wahala na mu ku typing, amma like ya gagara, to kuwa zan tafi yaji, iya masu yimin like zan ringa turawa ta privet.



kuma kar ku manta da fallowing Win channel Wina.



mu haWe a next page.







_page 10





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Da ido ma'eeshat ta bi number tana tunanin wanene? dan ita ba wani kasafai ta fiya Waukar number da ba suna ba. dan haka ji tai ba zata iya Waga wayar ba, zuba mata ido tai har tai ringing Winta ta katse. Ma'eeshat tana oarin kashe wayarta ta tuna da Abbas, a fili tace  subhanahi ko to de shi ne yake kirana ma da wanan number? .



 Ai kuwa zai aikata in de abbas ne may be shine ma kika i Wauka zuciyar ma'eeshat ta gaya mata haka. A fili ma'eeshat tace  tom bari na jira naga ko zai sake kira .



Sai da ma'eeshat tai 10 minutes tana jira a sake kira amma shiru, kawai ta yanke shawarar ta kira da kanta , dan tasan halin abbas in ya kirawo bata kusa, baya sake kira sai de in ta bushi iska wataran ta sake kira.



 Kai gaskiya ban san ko lafiya ba yayi offline, yanzu in shine ya bugomin da wanan number ban sani ba fa, kai gaskiya gwara nabi shi ma'eeshat ta arasa zance tana Waukar wayar ta tah.



Direct call ma'eeshat ta shiga sanan ta dannawa bauwar number kira tana gyara kwanciyar ta. ringing 4 ma'eeshat taji an Wauki wayar. Shiru ma'eeshat tai tana sauraran number. abin mamaki shiru ma'eeshat itama taji anyi ba'ace komai ba kuma, bayan tana iya jin sautin numfashi mai wayar.



Dan haka daurewa tai ta furta  hello ina ji? . amma still shiru ma'eeshat ta sake ji ba magana, mamaki ya kama ta sosai ganin yarda taji an kira ta ani magana ita kuma tayi magana an mata shiru, kuma bayan tasan me wayar yana jin ta saboda tana jin alamun hakan.



 Dan Allah waye haka ina ji ko wacece, koma wane yayi magana ina da abunyi fa ma'eeshat ta faWi hakan a Wan tsawace. amma mai makwan magana sai jin sautin ajiyar zuciya taji kawaii.



Cikin mamaki ma'eeshat tace  lallai ma, to ko wane ya bari duk sanda ya shirya ya kirani, in mutum yasan ba magana zaiyi ba to kada ya sake kira na dan gaskiya bazan Wauki wanan rainin wayon ba, a kira mutum ai mai shiru, mutum yasan bashi da abin cewa ya kirawo ni, to ya bari in ya tanadi abin cewa sai ya kira ni, daga haka ma'eeshat ta katse wayarta tare da jan wani dogwan tsaki.



Kashe wayar tayi gaba Waya, ta ajiye ta a gefe sanan ta shige cikin blanket ta kwanta tana jin takaicin kiran da akai mata ba magana, sabida ita ma'eeshat tana da zafi da saurin jin haushi sam bata son raini. Haka de ba jimawa bacci yayi awan gaba da ita......



" " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " " "



angaran doctor ashmal kuwa ma'eeshat tana kashe wayar ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tare da sakin wani siririn murmushi, sabida har ga Allah yayi matuar jin daWi da yaji muryarta. Ji yayi zuciyarsa tai mai sanyi sosai, duk damuwar nan ta ragu sosai ba kamar da ba.



Doctor ashmal ara danna call yayi domin ya kira ta amma yaji wayar a kashe,. Gyara kwanciya yayi yana ta tunanin sabida me ya kasa yi mata magana dan lokaci data Wauki wayar ji yayi kamar an rue masa baki. Gashi kuma sai wani burge shi take da take zazzaga masa faWan nan, duk da kuwa yasan shi ya jawowa kan sa.



To doctor sai da ya kai arfe 12:30 na dare yana tunanin ma'eeshat kafin yayi bacci, zuciya fari all yake baccin sa, ba damuwa kamar jiya, yana farin cikin jin muryar ma'eeshat Win.



Washe gari.



Doctor ashmal da wani tsananin son ma'eeshat ya farka, ji yake duk duniya ita yake son gani. dole haka yayi arfin halin shiga toilet yayi wanka ya futo ya shirya a hanzarce.



Be so fita hospital ba, amma jiya an mai message akan wani mara lafiya sosai, wanda aka kasa gane mai yake damun sa, dole sai yaje hospital ya duba shi.



kaWan daga baiwar da Allah yayiwa doctor ashmal kenan, duk rashin lafiyar mutum in aka kasa gane mai yake damun shi, doctor ashmal yana zuwa yake gane me yake damun sa, in de ba aikin asiri bane ko na aljanu, in sha allah yana ganin patien zai san mai yake damun sa.



Haka doctor ashmal ya fita a hanzarce zuciyar sa cike fall da soyayyah da tunanin ma'eeshat.



MEENAL



 Meenal kwana biyu gaba Waya naga kin canza, kina yawan waya da mutane, sai ki shige Waki kita yin waya, kuma bayan da ba haka kike ba umma da suke aikin tsinke zogale ita da meenal, ta watsawa meenal tambayar.



Sunkuyar da kai asa meenal tai tare da cewa  eh wanan Wan uwan su ma'eeshat Win nan ne dana baki labari kwanaki, shine ma'eeshat tace dan Allah na ringa daga wayarsa in ya kirawo baya jin dadi, to bana son ma'eeshat ta roi alfarma ban mata ba shi yasa .



 A'a ai ba wani abun bane ba ma, in kuna magana tunda yanzu ai kin girma, matsala de shine yanayin tarbiyarsa, sannan kuma duk mutumin da yake san ki tsakani da allah ai ya kamata ace yazo ya samu iyayan ki kafin ku fara ma'amala Koh? .



Jin jina kai meenal tai tare da cewa "hakane umma, amma ni ina tunanin waleed zai kasance mutumin kirki tunda kinga ai nasan ma'eeshat ba zata haWa ni da mutum da be dace ba, yayan ta ne, sannan mami ma da tasan bashi da hali ba zata bari yace yana so nah ba. sanan kinga baya garin nan a abuja yake aiki sai yayi wata biyar ma bai dawo ba, amma in sha allah yana dawowa zan gaya mai yazo ya samu baba .



 Gaskiya ne aminatuwa ya kamata kuwa, in mutumin kirki ne sai ayi a wuce gurin kin san de kyan 'yar mace Wakin mijin ta, dan ni bana son wanan karatun .  Kai umma aure kuma yanzu, a'a ni gaskiya bana so, ma'eeshat ce de mai wanan ra'ayin, ni karatu nake so .



 A'a ni kyma bana son wanan karatun me tsayi ko kinyi auran bana so, ki zauna a gidan mijin ki kawai ki mai biyayya, shifa karatun nan bashi da wani amfani in de ka samu miji na gari shikenan, karatun da ba zai taimake ki ba ranar iyama, ai da na muhammadiya ne bazan damu ba, ko zaki mutu kina yi daWi zanji, amma wanan karatun yanzu ai turawa ake bautawa kawai, abinda ba allah ne ya aiko mu muyi shi ba, iya karatun kore jahilci ai kin yi shi meenal .



 A'a umma yanzu karatu shine mutum wallahi, yanzu in nayi ilimi ai bazan dogara da mijina ba zan ringa taimaka muku, kuma misali ko mutuwa mijin yayi ai zan taimaki aa nah . Umma tana shirin yin wata maganar wayar meenal ta fara ringing.  to gashi ana kiran ki shine ko? .



GyaWa kai meenal tai tare da cewa  shine mana, matsala ta da shi yawan kira wallahi, amma mu cigaba anjima mayi wayar .



Girgiza kai umma tai tare da cewa  a'a gaskiya ya kamata ki Wauka in mutum yana son ka ai ba'a wulakanta shi, yafi wanda yace baya yi da kai ai, maza ki tashi kije kuyi wayar, ni zan arasa dama ai mun kusan gamawa . miewa meenal tai tare da cewa "tom bari na Wauka" dama tunda can meenal taiwa umma kara ne, amma tana son Waga wayar waleed Win dan yanzu har ta saba da nacin sa na kira, in bai kirata ma ba gaba Waya bata jin daWi.



Kafin meenal ta kai da Waukar wayar kiran har ya katse, amma yana katsewa wani ya shigo, sai data arasa Wakin ta zauna a kan gado sanan ta Wauka tare da kafawa a kunne tana cewa  Assalama'alaika .



 Wa'alaikissalam babe nah, shine ina ta kiran ki baki dauka ba, so kike nai kuka ina kika shiga ne wai?.  hmmmm yanzu kai in ka kira ni ban Wauka ba ai kasan uziri nake, haba yaya waleed sai kace zan gudu .



Dariya waleed yayi tare da cewa  to na sani ko guduwa zakiyi ki bar Wan marayan allah? .  Hmmm tom na gudu naje ina kai ma waleed ka cika rigima .



 Hmmm gimbiyata ba zaki gane bane, nifa in nayi one hour banji muryarki ba ji nake kamar

8 / 38