Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   29 / 38

84K to 87K   out of 111.1K words

cewa "kuma meenal naga hakan ai ba laifi bane, sannin kan ki ne baba baya son auran ki da waleed har ya kwanta asa, yanzu kinga ai ba hali ki aure shi, tunda ke yanzu kin san ba maganar auran ki da waleed to me zai hana ki bawa anin doctor dama".



Ido jajiir meenal ta Wago ta kalli ma'eeshat cikin mamaki tace "Haba ma'eeshat ke da kan ki kike cewa haka ban taSa tunanin zaki goyawa abinda bana so baya ba, wallahi ma'eeshat bana son wannan haWin na tsani a rayuwa a haWa mutum da wanda ba shi ya gan shi yace yana sona ba, Ke ni na haura da auran waleed Win amma wallahi bana son na auri brother Win doctor" meenal ta arasa maganar a raunane tana fashewa da kuwa".



Cikin nauyin zuciya ma'eeshat ta Wago tare da jan gauran nunfashi tana rie hannun ma'eeshat Win. Murya a sanyaye ma'eeshat tace "tom meenal naji amma dan Allah wana dalili ne yasa ba zaki auri anin doctor Win ba? baki yarda da tarbiyar gidan su ba ko kuma nasabar sa ce bata yi miki ba, ko kuwa shi kan sa yaron ne bai miki ba?".



Share hawaye meenal tai da hannayan ta baki na rawa tace "ma'eeshat ni ban ma taSa ganin yaron ba and kuma sanin kan ki ne su momy su suke da nasaba ko da ban san wanda take min tayi ba, bani da shakka yana da tarbiya amma ma'eeshat, ni bana son na auri mijin da bashi ya ganni yace yana so ba, bana so a haWa ni da miji wlh gwara mutum ya ganka yace yana sona sabida gudun gori ma".



"Gaskiya kika faWa meenal amma, in sha allah nasan jinin momy baze taSa miki gori ba, wannan ba halin su doctor bane suna da sauin kai sosai duk da kuwa wani yaron zaka haife shi baka haifi halin sa ba, amma ina kyautatawa yaran momy zato, kuma ai babban abin tsoran shine ke kiga namiji kice kana so, Duk da kuwa ba haramun bane, nana khadija ma ita ta fara ganin annabi muhammad s.a.w tace tana so, amma yanzu zamanin ya lalace bama zaki taSa haWa samarin yanzu da koyi da halin manzan Allah ba saboda shi na daman ne, kuma samarin yanzu yawan cin su basu da kirki sai sun goranta maka. Tom shi yasa matan yanzu suke gudun suga namiji suce suna so, wannan zub da mutuncin da ake cewa shine! namiji yazo yana goranta miki yana ci miki mutunci shine abinda ake gudar miki, kuma ya kasance kece sanadin cin mutuncin.



Amma tunda bake kika ce kina son shi ba shikenan, maman shi ce ta kawo miki tayin sa, kuma mutuncin su momy zaki duba da karamcin su, bawai dan wani abun ba please meenal ki amince".



Ido shaSe-shaSe da kuka meenal tace  wallahi ma'eeshat ba zaki gane abinda nake ji a zuciya ta ba bana ji zan iya amincewa". Cikin muryar lallashi ma'eeshat tace "sorry meenal kar kice haka dan Allah ki amince da wannan zancan zanfi kowa jin daWin zancan nan kinga zumuncin mu ma zai aru ace yau ni da ke mun auri miji yaya da ani".



To haka de ma'eeshat tai ta rarrashin meenal da kalamai masu kwantar da hankali har zuciyar meenal tai sanyi kuma ta fara jin zata iya amincewa ko dan ta farantawa mahaifiyarta, tunda taga itama tana son abin, kuma ta farantawa awarta ma'eeshat da momy.



Cikin muryar rarashi ma'eeshat ta sake ruo hannun meenal duka biyun tare da cewa "to yanzu ya kenan kin amince?" Cikin dashashiyar murya meenal tace  yanzu bama wannan ba, gaba Waga hankali na ya tashi saboda Wazu da umma ta sanar da ni zancen momyn, ba kiga yarda nai mata ba wallahi".



Meenal ta arasa maganar tana zubar da hawaye. "subhanallahi mai kikai mata?" "nayi mata abinda ban taSa yi ba lokacin da ta sanar da ni, kuma naga kamar tana son abin, tana faWa ina faWa sannan arshe na tashi na barta a wajan ba tare da mun gama maganar ba" meenal ta arasa maganar kuka yana wace mata.



rungumota meenal ma'eeshat tai jikin ta tare da cewa "is okay cool down meenal, ki dena kukan nan haka komai ya wuce, dama Wan adam watarana yana yin ba dede ba yanzu za kije ki tsuguna har asa ki bawa umma hauri sannan ki sanar da ita kin amince hakan zai sa taji sanyi sosai kuma ta manta da abinda ki kai mata".



Kallon ma'eeshat meenal tai almun tana nazarin shawarar data bata. "Meenal, don't think too long and just agree". "Tom ma'eeshat bari naje" meenal ta tashi jiki a sanyaye, duk da kuwa ta amince ne amma ba har zuciyarta ba.



Zauna meenal taga umma ta rafka tagumi a gefan gado. jiki a sanyaye na rawa meenal ta arasa wajan umman ta tare da zubewa kan guiwowin ta biyu baki na rawa tace "umma dan Allah kiyi hauri akan abinda nai miki dazun, nasan nayi kuskure sharrin sheWan ne kuma na amince da maganar momy zan auri yaran nata".



Meenal ta arasa maganar baki na rawa tana fashewa da matsanancin kuka mai cin rai. Bibiga bayan meenal umma tai farayi alamun rarrashi, ko ba'a gayawa umma ba, umma tasan wannan aikin ma'eeshat ce, saboda meenal tana jin shawarar ma'eeshat, Ma'eeshat tana juyawa meenal ra'a yi sosai a lokaci guda,. Kuma umma taji daWin hakan sosai da ma'eeshat ta shawo mata kan meenal har ta amince. Meenal taji shiru sai uwar ajiyar zuciya take saukewa.



Umma magana ta farayi cikin sassauta murya take cewa "ba komai meenal komai ya wuce Allah uban giji yayi miki albarka kinji meenal, naji daWi da kika amince nagode, in sha allah sai kin samu farin cikin da baki taSa tunani ba a gidan auran ki".......



To ma'eeshat sai da ta tabbatar meenal ta samu nutsuwa sosai, dan har sai da tasa ta saki jiki su kai hira sosai sannan hankalin ma'eeshat ya kwanta. ko da doctor ya bugowa ma'eeshat, ma'eeshat taso tambayar shi zancan meenal da muhseen amma sai tai tunani doctor bai cika son mutum ya shiga maganar da bata shafe shi ba, dan haka shiru tai da bakin ta.



Tom meenal sai bayan sallah magriba ta fara oarin tafiya gida. da driver yazo Waukar ma'eeshat meenal har bakin ofa ta rakata, ma'eeshat ta dage meenal ta bita gidan su amma meenal tai amincewa tom dole haka ma'eeshat ta haura ta tafi.



After one week.



Tom komai na makarantar ma'eeshat ya gama kammala, yau ya rage saura one week ta fara zuwa makarantar. Ma'eeshat har ga Allah bata son zuwa school Win nan kawai dan abban ya matsa mata ne, doctor kuma sai rarrashin abarsa yake yana sake arfafa mata guiwa shi yasa za taje.



Ma'eeshat tana kammala sallah la'asar kishingiWa tai a kan dadduma dumin duba wasu littattafai, dan yanzu ma'eeshat ta fara karatu sosai saboda school Win da zata koma ba wasa za tai ba karatu za tai, bata so taji kunya wajan mijinta doctor. Ringing wayarta da take kan bed ta fara, ma'eeshat gyara zama tai dan bata da niyar Waukar wayar sabida tasan ba mai mahimmanci bane doctor baya kiranta war haka in de ba weekend ba.



Amma daga arshe sai tai tunani meenal ce dan haka da sauri ta arasa, tana zuwa ga mamakin ta taga doctor ne, wayar tana gab da tsinkewa ma'eeshat tai sauri tasa hannu ta Wauka, tare da sata a handsfree sannan ta zauna akan bed Win tana cewa "hello".



"Assalama'alaikum" doctor ya faWa daga can Sangaran" "wa'alaikassalam dee yau an tuna dani kenan naga kiranka war haka". murmushi mai sauti doctor ya sauke tare da cewa "eeshat ta kin cika rigima ni ai kullum cikin tunanin ki nake, wai dan bana kiran ki a lokacin bashi ne yake nuna bana tunawa da ke ba, aiki nake".



"Tom dee naji daWi kiran nan da kai min, ya aiki?". lafiya alhamdulilahi, yau na futo da wuri ne sabida ina buatar hutu zani gida, shine nace bari na kiraki naji muryarki ko na samu warin jikin komawa gida".



"Hmmm dee nah ina son ka sosai na rantse maka". "hmmm eeshata nima ina son ki, ke ta musamman ce a wajena, kina bani farin ciki na musamman kuma ina ji dake eeshata fatan de kina karatu sosai kamar yarda nake tuna miki kullum". Cikin shagwaSa ma'eeshat tace "eh ina yi mana sosai, yanzu ma gashi ina tayi, gaba Waya naji brain Win tawa ma ta toshe yanzu bana ji zan ci gaba da iya karatun nan fa yanzu gaskiya sai zuwa gobe".



Cikin rarrashi doctor ya cewa ma'eeshat "sorry dear na, ki huta kar ki takura kan ki, ko nazo ne na ganki ko zaki samu nutsuwa?". Cikin farin ciki ma'eeshat tace "eh please kazo dan Allah ina son ganin ka maybe in na gan ka ma naji na dawo normal".



"hmmm nima kamar yarda zan dawo normal na ganki ba, amma bari naje gida na shirya zuwa anjima kafin magrib zan zo, kin san bana son zuwan dare, gwara nazo da haske na ganki sosai" cikin shagawaSa ma'eeshat tace  to ko kazo ai ba kallon na kake ba sosai Win".



Wata siririyar dariya doctor ya saki sannan yace "ina kallon ki sosai mana". "uhmmm to ai ni bana gani" ma'eeshat ta faWa tana turo baki kamar tana kallon sa. "zaki gani ne tom" "yaushe zan gani?" ma'eeshat ta tambayi doctor tana sakin murmushi. "Yau in nazo har sai kin tsargu zan ta kallan ki ba kiftawa. "Tom shikenan allah ya kawo ka lafiya my Love" "ameen tawan" daga haka doctor da ma'eeshat su kai sallama.



Suna sallama doctor ya tayar da motar ya fita daga babban hospital Win. Doctor yana tafe yana tunanin rigima irin ta ma'eeshat wato ita so take ya ringa kallon ta, shima yana son hakan amma in de doctor ya cika kallan mace sosai, yana da matsala ciwan sa tashi zai yi.



Bayan doctor yaje gida ko hutawa bai yi ba yayi wanka, sannan ya ci abinci, bayan yaci abinci shiryawa yayi cikin milk Win shadda, kana kallan sa dole ka ara yayi matuar kyau sosai.



Bayan doctor ya gama shiryawa ya fesa turare yasa hula da agogo, wayarsa ya Wauka ya turawa ma'eeshat message kamar haka "eeshata na gama shiryawa yanzu zan futo daga gida na taho". daga haka ya zura wayoyin sa a aljihu sannan ya Wauki key Win motar sa yayi gaba abinsa.



Ma'eeshat tana ganin message Win doctor jiki na rawa ta shiga toile tai wanda sannan ta fara shiryawa a hanzarce. Tayi matuar kyau sosai, abaya tasa baa sannan ta yafa mayafinta, ta kame akan bed tana jiran doctor har takalmi tasa....



Ma'eeshat tayi kimanin 1 minutes tana kallon doctor wanda bai ma san da zuwanta ba hankali sa ya karkata kan laptop Win da take gaban sa a kan ciyarsa. da yake yau mota mai farin glass doctor ya Wauko ba mai bai ba.



Kamar ance doctor ya Wago, yana Wagowa ya hangi kamar an tsaya bakin motar daga gefe. a hankali doctor ya juya gefe bayan ya Wago, ai kuwa ma'eeshat ya gani tsaye tana sakar mata kyakyawan murmushi. Shima nasa murmushin ya sake sannan ya buWe mata ofar motar a hanzarce.



Ma'eeshat bayan ta shigo gyara zama tai sosai sannan ta rufo murfin motar tare da cewa "wai kai saboda me baka son shigowa cikin gida ne?". Ma'eeshat jin shirun doctor ba amsa hakan ne yasa ta Wago domin ganin me yake yi bai bata amsar tambayar da tai masa.



Sai da gaban ma'eeshat ya Wan fadi rass saka makwan ganin doctor ya zuba mata ido yana kallo ko iftawa babu, abinda bai taSa yi mata kenan ba. Kawar da kai ma'eeshat tai sannan tace "wannan kallon bai yi yawa ba kuwa".



Doctor ba tare da ya dena kallon ma'eeshat ba ya bata amsa da "ke kika buata kuma, hakan yana da fa'ida ashe gaskiya ke me kyauce sosai". Wagowa ma'eeshat tai tana cewa "ai ban kai ka kyau ba ko" "dama maza suna da kyau ne" doctor ya tambaya yana sake tsare ma'eeshat da ido.



Lokaci kuda ma'eeshat ta dabarbarce saboda kallon da doctor yake mata ya ishe ta haka gani tai yana mata kwarjini sosai, baki na rawa tace "pls doctor ka dena min kallon nan haka ya isa na gode". "hmmm me akai ai kallon ki yanzu na fara eeshat" cikin ruWu ma'eeshat tace  to ni gaskiya ka buWe min ofa na koma gida". "hmmm da kin san ba zaki iya jure kallon ba kike cewa bana yi ai yau zan sha kallo har sai idona ya bushe tukkuna".



Lokaci guda ma'eeshat ta haWe rai sannan ta fara cije leSe. Doctor kawar da ido gefe yayi tare da cewa  I'm sorry na dena". dama can fuskarta kawai yake kallo ba wani abun ba. murmushin ma'eeshat tai tare da cewa "yauwa ko kai fa".



"hmmmm ai yau nasha yarinta eeshat kin cika rigima fa". to doctor da ma'eeshat sun sha soyayya sosai da sosai, kamar kar su rabu,. sai da aka fara kiran sallah sannan su kai sallama cike da aunar juna doctor ya wuce masallaci.



Washe gari.



MEENAL



Yau ta kasance Waya daga cikin ranar bain ciki a rayuwar meenal wanda ba zata taSa mantawa da ita ba a cikin jerin baayan ranakun da suka zo mata, na tashin hankali. daga mutuwar baba sai rabuwar ta da waleed sai kuma wannan rana.



Saka mawan yau aka kawo kuWin zance meenal akai mata engagement ita da muhseen Wan gidan momy. kuma an sa mata 3 moths ne ba wani dogon lokacin ba. Abban ma'eeshat ne ya arbi kuWin auran meenal sabida yace shi yake da alhakin aurar da ita koda baba yana da rai..............



mu haWe a next page



_page 39



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Kwana biyu gaba Waya meenal ta shiga matsanancin tashin hankali, gaba Waya ta faWa kana ganinta za kasan tana cikin matsananciyar damuwa. ga mutuwar baba bata sake ta ba, ga rabuwa da waleed sannan gashi an mata engagement da dan gidan mommy wanda bata san shi ba bata taSa ganinsa ba ma.



Abun haushin ma da Waga hankalin bama shi yace yana son ta ba, auran haWi za a musu, kuma har ga allah ita meenal bata so saboda a halin yanzu ma wata muguwar kaunar waleed ce take damun meenal daran duniya bata iya bacci.



Tun meenal tana iya hakuri ta dena chat da waleed tai blocking Win shi harta hakuri taci gaba da kula shi a Soye ba tare da sanin umma ba. Yanzu meenal ta lura da cewa in ta rabu da waleed matsala za ta shiga ga ciwon zuciya yana oarin ya kamata dan haka tuni ta sake sakarwa waleed jiki a karo na biyu suna ta shan soyayya su.



Amma bata nuna masa anyi engagement Win ta ba saboda meenal tasan waleed zai shiga mawuyacin hali, kawai tana nuna masa, su cigaba da addu'a kuma zata shawo kan umman ta akan auran su, in sha allah umma zata amince, suyi auren su.



Waleed yaji dain hakan sosai saboda, lokacin da meenal ta juya masa baya har rashi lafiya yayi duk yabi ya haukace ya furgice, kamar mara hankali. Yanzu waleed ya gama gane in ba meenal a tare da shi tsaff zai iya mutuwa sabuda mugun son da yake mata sosai.



Allah sarki waleed bawan allah ga maraici ga soyayya, gashi ba shi da wanda zai kai wa kukan sa ya share mai sai de allah, ba uwa ba uba ba Wan uwu ko ar uwa wanda suke uwa Waya uba Waya. hakan ne yasa meenal take mugun tausaya masa.



angaran umma kuwa itama abun yana bata mamaki ace wai za'a haWa auran meenal da Wan gidan mommy amma baya zuwa ya ganta, duk da de mommy ta kawo uzirin baya asar, amma ya kamata ai ace yana bugo mata.



Umma ta fara jin tsoron kar aje yaron mommy baya son haWin nan kuma bayan aure azo a samu matsala, kuma gashi itama meenal Win bata son abun. haka umma take ta irin wannan tunanin, amma daga arshe dai sai ta kwantar da hankali ta kuma ta cigaba da addu'a akan lamarin.



kullum sai umma ta tashi tai addu'a da daddare akan in wannan auran meenal Win da za ai ba alkhairi bane allah kar ka tabbatar in kuma alkhairi ne allah ya tabbatar,.



itama Sangaran meenal Win haka, in umma ta tashe ta sallah dare addu'a take akan allah ya mallaka mata waleed ko wana hali ne da shi zata iya zama, duk da tasan da wuya waleed Win ta yana da wani Soyayyan hali mara kyau,.



Ma'eeshat.



angaran ma'eeshat kuwa ta fara zuwa school masha Allah, duk da de ba wani mai da hankali take a school Win ba saboda hankalinta yana kan doctor soyayya doctor kawai tasa a gaba, duk da kuwa shi doctor Win yana iya bakin oarinsa wajan ganin ma'eeshat tana mai da hankali a karatun.



saboda yanzu doctor ya rage bugowa ma'eeshat wayar dare, sai ya tabbatar daran da za suyi waya washe gari basu da lactures,. kuma ba waya suke kamar da sosai ba in sun daWe suna waya suyi 30 to 40 minutes suna waya, saSanin da da sai suyi 2 to 3 hours suna waya.



ma'eeshat har allah-allah take meenal ta gama warewa su fara zuwa school Win nan tare saboda bata jin daWin karatun ko kaWan, tasan da meenal tana nan ita zata ringa takura mata kan ta mayar da hankali wajan karatu. tunda yanzu doctor yasa ma'eeshat ta canza course ta koma medicine kamar yarda meenal take so, dan haka koda meenal ta fara course Waya zasu karanta.



Yau ta kasance ranar weekend ma'eeshat basu da school dan haka bayan ta gama baccin ta sosai ta huta, tana tashi taci abinci ta oshi, sannan tai wanka ta shirya, daga haka tayiwa mami sallama tace mata ta tafi gidan su meenal. tana futa driver ya Wauke ta ya wuce da ita gidan su meenal.



Bayan ma'eeshat ta wanwasa umma ce ta buWe mata sai da suka gama gaisawa ma'eeshat take tambayar umma meenal, umma tace meenal tana ciki tana bacci,. Daga haka ma'eeshat ta shiga ciki kamar

29 / 38