Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   24 / 38

69K to 72K   out of 111.1K words

zambalelan hijab. murmushi meenal tai tare da cewa "auty ladidi ina wuni?".



Amma da mamakin meenal sai taga ladidi tace  lafiya lau ba tare da tai mata murmushi ba hasalima fuskar ladidi ba annuri, ba kamar yarda take ba kullum in taga meenal tai ta washe mata baki ba. Meenal ji tai jkin ta yayi sanyi dan haka bata sake cewa komai ba. "hajiya tace in kin gama cin abinci zaki iya saukowa mu tafi". "yanzu kuma?" meenal ta faWa cikin mamaki.



Ladidi bata amsa tai da "eh yanzu tace". meenal cewa tai to kawai tana mamaki, a ganinta abinda yanzu garin bai gama wayewa ba da duku-duku kuma haka.



Ita de tasan kullum sai gari ya Wanyi haske suke tafiya. ladidi daga haka bata sake cewa komai ba ta fuce daga bedroom Win. meenal wayarta ta Wauko ta cireta daga jirgi sannan ta zura jijab Winta. Yesmeen itama mayafinta ta Wauka fuska cike da murmushi tace  aunty meenal bari muje na raka ki .



Har bakin mota yesmeen ta raka meenal tana yi mata bye wai sai sun dawo dan Allah yau kar su daWe, meenal bin da yesmeen tai da to kawai sanan ta shiga cikin motar.



Bayan ta shiga fuska a sake tace  momy ina wana? momy itama fuska babu annuri ta amsawa meenal da "lafiya alau aminatu sannu". Mamaki ya kama meenal a karo na biyu ganin itama momy yau ba sakin fuskar nan ko de dan abinda tai jiya ne tai sakin jiki suyi hira?.



Meenal tana cikin tunanin nan taji driver yaja mota sun fuce daga gidan. shiru ya ratsa wajan ko ta ina, meenal tai jigum ba tare da tace komai ba, dan har ga allah ta tsargu sosai da sosai. tasan da dane suna shigowa mota ko momy bata yi mata magana ba ladidi zata fara janta da hira.



Meenal shiru tai ta su sunkuyar da kai tana addu'a a ranta Allah yasa ba wani laifin tayiwa su momy ba. meenal tana cikin wanan halin taji wayarta da take vibration ta fara ringing. MY ONE AND ONLY sunan da ya bayyana kenan da manyan bai kan scaring Win wayar.



Wato ma'eeshat ce take kira, jiki a sanyaya meenal ta Waga wayar tare da karawa a kunne tana cewa  hello ma'eeshat . Da kyar ma'eeshat ta saita muryarta cikin gunjin kuka tace  wai meenal kun tawo ne? .



Cikin mamaki meenal tace "mun tawo mana, yau da wuri kukazo hospital Win kenan lafiya naji kina kuka mai yake faruwa ne?"

meenal tana faWar hakan taji wayar kit ma'eeshat ta tsinke ta. mamaki ya kama meenal sosai dan haka bin number ma'eeshat tai ta kira, sai da meenal ta kira har sau uku amma ma'eeshat bata Wauka ba.



arshe de meenal haura tai, tai jigum tana tunanin mai ya samu ma'eeshat take kuka, dan daga jin muryarta tana cikin tashin hankali, dan tasan in ba abune yayi abu ba ma'eeshat bata irin kukan nan, ko de faWa su kai da doctor ne, to haka meenal tai ta tunani ita Waya ba mai bata amsa.



Gaba Waya meenal ta tafi wata duniyar, wawalwarta ta rabu sosai, ga lamarin waleed gashi tana so ta tuno mafarkin da tai, kuma gashi taji sahibarta ma'eeshat tana kukan tashin hankali. meenal ta shagala da tafiya duniyar tunani, sai da taji motar ta tsaya cak da tafiya ta dawo hayyacin ta.



Lokacin da meenal ta Wawo mamaki ne ya kamata sosai ganinta a unguwar su maimakon hospital, amma meenal batace komai ba ta buWe murfin mota ta fara oarin fita dan bata kawo komai a ranta ba.



Lokacin da meenal ta fita mamaki ne ya kusan kashe ta ganin ofar gidan su ya cika da maza mail, harma da mata tsuraru suna shiga cikin gidan. Yawancin mutanan da carbi a hanunsu  to inalillahi gobara mu kai a gidan namu ko gine ne ya faWo meenal ta faWi hakan a zuciyarta cikin tashin hankali.



To ni kuwa amina bayero nace mai yake faruwa kuwa? to ku biyo ni a text page dan jin ya zata kaya bye.



Mu haWu a next page



Game buatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link Win channel yayi following.







_page 31





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Haka meenal ta cigaba da takawa cikin tashin hankali tana tunanin allah yasa ba wani abun ne ya samu umman ta ba. afafuwa meenal sun mata nauyi da kyar take iya ci gaba da takawa ladidi da momy suna biye da ita a baya.



Meenal tana zuwa ofar gidan taji baki Waya ta kasa tafiya jikinta duk ya mutu. momy ce ta rie hannun meenal na dama ladidi ta rie na hagu. suka fara jan meenal a hankula, meenal tana biye da su.



Lokacin da suka arasa tsakar gidan meenal ganin mutum tai shimfiWe a tsakar gida an rufe shi da bedsheet. meenal gaba Waya kanta ya Wauke tunanin ta ya Wauke tama rasa waye wance a tsakar gidan. haka ta runga bin wanda yake wance da ido ita de meenal tasan umma bata da wannan tsayin haka. Mutuwar tsaye meenal tai ganin yatsun baban ta sun futo ba'a rufe ba.



 Baba kuma mai ya dawo da baba ko an salla moshi daga hospital ne? meenal ta faWi hakan a zuciyarta dan ita tama manta ana mutuwa a duniya. Dafe kafaWun meenal momy tai tare da cewa " ar ta meenal sai dai kiyi hauri, baban ya rigamu gidan gaskiya".



Tun daga haka meenal bata sake jin komai ba, sai faWuwa asa tayi samamiya. nan da nan mutane suka fara salatin wanda haka yasa har wanda suke cikin Waki suka futo, daga ciki kuwa harda momy da ma'eeshat.



Da kyar aka samu aka cinciSi meenal aka shigar da ita Waki, aka fara yayyafa mata ruwa. Ma'eeshat kuwa sai faman kuka take tana jijiga meenal Win, meenal tana farfaWowa ta saki iwu mai cin rai, haka momy da mami su kai ta lallashin meenal, suna ja mata aya da wa'azi ita kuwa meenal ina bama tasan suna yi ba.



Daga haka rufe gidan akai dady da abba da kuma wani maocin baba aminin sa suka haWu su kai masa wanka gawa suka saka masa ninkafani. suka gama shirya shi tsaff aka fesa mata turare. Bayan sun gama shirya shi, cewa akai umma da meenal harma da an uwan sa na maiduguri da suka bugo sammako suka zo, domin su samu jana'iza da wuri, su futo suyiwa baba addu'a.



Da yar aka lallaSa meenal tai shiru sanan ta iya futowa domin sallama da baba tai masa addu'a. Bayan ta iso tsugunawa tai gefan kan baba ta, hawaye suna gangarowa daga idanuwan ta, wasu nabin wasu.



Itama umma da take dga gefe hawayan take yi, tana yi tana yiwa baba addu'a. Dafe baba meenal tai tana masa addu'a'i kala-kala tun tana sanin wace kalar addu'a take masa har ta rasa wace addu'a take masa kawai tanayu ne, saboda tsabar ruWu.



Hankali meenal bai sake tashi ba sai da 8:00 tayi akace za'a fita da baba domin yi masa sallah akai shi mawancinsa na gaskiya. da yar aka ja meenal ta mie daga kan gawar baba amma tana miewa sai ta sake faWuwa asa sumamiya Amma duk da hakan ba ai sanya wajan kinkimar gawar baba a makara domin futa da ita ba. Itama kanta umma da take gefe sai da ta zube asa sumammiya, saboda tasan tayi babban rashi a rayuwarta.



Allahu Akbar Allah kenan baya barin wani dan wasu suji daWi.



Bayan umma da meenal sun farfaWo kuka suka cigaba da yi musamman ma meenal wanda baki Waya ta fita daga hayyacin ta, bata ji bata gani, duk hauri da rarrashin da ake bata gaba Waya bata sauraran jama'a kukanta take kawai iya son ranta.



Meenal ba ita tai shiru ba sai da aka fara kiraye-kirayan sallah azahar sannan ta tsagaita da kukan nata. Ta mie da yar take tafiya saboda tsabar juwa, arshema meenal kasa tafiya tai sai da ma'eeshat ta rieta tukunna.



Haka de suna tafiya meenal tana tangal tangal kamar wata ar koyo, da yar ma'eeshat ta temakawa meenal tai alwala sanan ta maidota Waki, itama ta Waura tata suka gabatar da sallah.



Gida ya cika sosai da an zaman majoki, dady ya siya kayan abinci yimuli guda domin dafawa an gaisuwa. duk abinda ake biata ya aika an suyo an kawo tun daga kan kayan miya magi ice daWe sauran abubuwan buata.



angaran meenal tuni zazzaSi mai zafi ya rufe ta da ciwan kai mai tsananin gaske, ga tashin hankali mutuwar baba ga kuma hayaniyar mutane, dama ita meenal bata cika san hayaniya ba ko shiga cikin jama'a. Tayi kukan tayi kukan har ta gaji tai shiru, fuskar nan tata ta kumbura suntum ido yayi jajir. Bayan zazzaSi ga ciwan kai da mura da suka rufeta lokaci guda, abun de gwanin ban tausayi.



Duk da ma'eeshat tana cikin tashin hankali hakan bai hanata ganin momy tana mata kama da doctor ba, amma bata kawo komai a ranta ba sai take ganin kawai dan itama tana da hasken fatane.



Kuma haka nan ma'eeshat taji momy tana burgeta sosai da sosai, sai bunta da ido take tana satar kallon ta. arshe de dole ma'eeshat ta yarda matar nan tana kama da doctor ashmal Winta, amma ko kaWan batai tunanin momy tama haWa dangi da doctor ba.



Magriba tana kawo kai momy da ladidi su kai wa su umma da meenal sallama domin tafiya gida. Meenal kuwa da yar ta iya yi musu agai da gida, saboda ciwon da ya rufeta lokaci guda baya barinta tayi ko wawaran motsi.



Misalin arfe goma kowa ya watse gida ya rage daga umma sai meenal da ma'eeshat, sai kuma ragowar an uwan baba da suka zo daga nesa. Meenal haushin su take ji kamarta kashe su, kamar ba gidan mutuwa suka zo ba. Tun dazu sai hira suke da shewa, kuma suna ta bankawa cikin su abinci suna ci suna tusa. arshe de meenal da taji ba zata jure ba tashi tai daga falon ta koma bedroom Win ta, ba jimawa ma'eeshat ta biyo bayan ta.



Meenal tayi jigum ta wanta akan gado hawaye na gangaro mata ta gefan ido. Ma'eeshat da ta shigo, arasowa gefan meenal tai ta zauna, tare da dafata tana cewa "Kiyi hauri mana meenal ki dena kukan nan haka yanzu baba addu'a yake buata daga gare ki ba kuka ba, ko shi yaga kina kuka baze ji daWi ba".



Da yar meenal ta iya samu ta mie zaune tana share hawayen ta ba tare da tacewa ma'eeshat komai ba, tana sake tuna sallamar da su kai da babanta ta arshe a hospital, ashe shi yasan rasuwa zai yi shi yasa ya rie mata hannu yai cikawa.



Wasu zafafan hawaye ne suka sake gangarowa meenal bayan ta tuna da alfarmar da baba ya nema akan waleed a wajan ta. Ai kuwa kamar ma'eeshat ta shiga zuciyar meenal, meenal sai ji tai ma'eeshat tace "meenal wai kin gayawa wlaeed rasuwar baba kuwa?".



Share majina meenal tai tare da girgiza kai alamun a'a. "Gaskiya ya kamata ki sanar da shi bama iya shi kaWai ba ki sanar da sauran awayanki da wanda kuke ma'amalar arziki dasu".



Murya a shage meenal tace "hmmm ma'eeshat a halin yanzu bazan wani iya danna waya ba, bakiji yarda nake ji a zuciyarta ba, ga kuma zazzaSi da ciwan kan nan da suka rufe ni, idona ma dayar nake buWewa, koya na motsa shi zafi nake ji, hasalima ban san inda na jefa wayar tawa ba.



"Eh dazu ni na Wauketa na ajiye miki ita saboda jama'a bari na Wauko ni sai na gayawa waleed Win, sanan na Wora a status, ko dan baba ya sake samun addu'o'i mutane". Ma'eeshat ta faWa tana Waga gefan gadon meenal domin Wauko wayar.



bayan ma'eeshat ta Wauko wayar tana buWe screen Win wayar taga miss call rututu har 20. Dama tasan posword Win dan haka buWewa tai ta shiga call. ma'eeshat tana ganin number da bata asar nan ba, tasan waleed ne. yayi mata kira wajan 12, sauran kuma kiran awayan meenal ne.



Wanda ma'eeshat ta tabbatar labarin mutuwa sukaji suka bugo domin yi musu gaisuwa, dan ita meenal ba mai yawan kule-kulen awaye bace. Ma'eeshat bayan ta kunna data direct WhatsApp Win meenal ta nufa, wanda message suke ta shigowa.



Musamman ma na waleed sun shigo yafi sau 30.  Kai meenal wannan wana kalar so waleed yake miki anya ba haukacewa yayi ba jifa yarda yake turo miki message kamar wanda ku kai shekara ba kuyi magana ba . Meenal tana jin haka hawaye suka cigaba da waranyo mata zuciyarta tana sake bugawa, tana sake jin so da tausayin waleed sun mayeye mata zuciya.



Ma'eeshat kuwa bayan message sun gama shugowa status ta nufa, ta fara rubutu kamar haka! "inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa mahaifina rasuwa jiya da daddare, yau akai jana'iza da safe arfe 8:00 ina mai barar addu'a a gare ku".



Bayan ma'eeshat ta gama rubuta hakan, Worawa tai a status sanan ta kashe data, tana oarin ajiye wayar taji kira ya shig. number da ta kirawo dazu ce mara suna, wanda ma'eeshat take tunanin waleed ne ita ce take kira, dan number ba bata asar 9ja bace.



Ma'eeshat haskawa meenal wayar tai tare da cewa "meenal wanan number waleed ne yake kira da ita Koh?". Meenal da yar ta iya kallon number, ko da ta gani sai da gabanta ya faWi da arfin gaske, kafin ta Wagawa ma'eeshat kai alamun eh.



Bayan ma'eeshat ta Wauka arawa tai a kunne tare da sallama. Ma'eeshat tayi mamakin yarda taji waleed ya sauke ajiyar zuciya kamar wanda akai masa bushara da an bashi auran meenal.



Bayan waleed ya amsa sallamar ma'eeshat Worawa yayi da "ma'eeshat ina mai wayar bata wayar". "A'a yaya waleed taya ka gane nice na Wauki wayar". ma'eeshat ta faWi hakan cike da mamaki, "Haba ma'eeshat in banda a binki ko a mafarki naji muryar meenal dole na gane, nasan wanan ba murya meenal bace, kuma nasan ba wanda zata iya Wagawa meenal waya sama da ke, shi yasa na gane kece".



Jinjina kai ma'eeshat tai tare da cewa "eh hakane, yanzu de ba zaka samu damar waya da meenal ba, Allah yayiwa baban meenal rasuwa jiya da daddare kuma yanzu meenal bama ta cikin hayyacin ta da zaku iya waya".



"Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un amma shine baku sanar dani ba sai yanzu?". "To ya za ai yaya waleed, kasan de yarda mutuwa take, kowa ya shiga cikin jimami shi yasa" "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah ya jian baba da rahma yasa ya huta".



"Ameen yaya Waleed" "yanzu ya jikin meenal Win?" waleed ya tambaya cikin damuwa. "hmmm gata nan de jiki sai godeyar Allah kasan de meenal ba zata taSa dawowa normal ba a hankali yanzu har sai mutuwar baba ta fara sakin ta".



"Hakane ma'eeshat amma dan Allah ki zauna tare da ita ki ringa rarrashin ta, ki bata hauri ki dena barin tana shiga damuwa sosai kinji?" "tom shikenan yaya waleed in sha allah zanyi iya kacin oari na". "Yauwa ma'eeshat nagode kicewa meenal ina yi mata ya hauri, kafin muyi waya kuma na dawo nai mata gaisuwa". "tom shikenan yaya waleed sai an jima". daga haka waleed da ma'eeshat su kai sallama tare da kashe wayar.



Waleed yana ajiye wayar ya sauke ajiyar zuciya, har ga Allah bai ji daWin mutuwar baba ba, amma yayi farin ciki da wanan damar da tazo masa ta auran meenal.



A fili waleed ya Waga hannu tare da cewa "Allah na gode maka, tabbas nasan Allah kana tare da mai gaskiya, Allah kana ganin banji na gani ba baba ya hanani auran meenal yace ina da wasu munanan halaiyar alhalin ni nasan bani da wani Soyayyan hali. Tabbas yau na sake yarda da cewa raban aure ko na haiwuwa yana kisa, may be ma Allah ya Wauki rayuwar baba ne saboda auran mu da meenal tabbatacce ne, duk da ban so ayi auran da haka ba, amma Allah kai ka tsara komai kuma kai ne mai yarda kaso.Tabbas Allah mai tsausayin bawan sane kuma ko wana bawa in ya roi Allah zai cika masa burinsa, Allah na gode maka, Allah ka tabbatar da aure na da meenal nan bada jimawa ba, alhamdulilah bi ni'imatika".............



Mu haWe a next page.







_page 32





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=



Daran ranar dai meeenal juyi ta ringa yi akan bed ta kasa bacci, ma'eeshat kuwa sai faman rarrashin meenal take, karshe de ma'eeshat bacci ne ya kwashe ta ita kuwa meenal yarda taga dare haka taga rana, Sangaran umma ma, itama bata iya bacci ba haka ta kwana tana tunanin baba.



Bayan meenal ta idar da sallah asuba komawa tai ta kwanta kan gado domin tai bacci amma ina ta kasa, gashi tana jin baccin amma bacci yai zuwa, dole haka ta haura ta tashi ta dasa wani saban kukan.



Da sassafe dady da momy suka zo, suma su mami da abba sun zo, dan ana idar da sallah asuba suka tawo domin su samu sadakar 1. Bayan an kammala yiwa baba addu'a da sadaka, dady da Abba gaisawa su kai saboda sun gane juna.



Tun jiya ma dady yake son su Wan keSe da abba domin, yasan ya yake a wajan baban meenal. to amma ruWin mutuwa, gaisawa su kai basu samu damar zantawa ba sai yau.



Bayan sun gama gaisawa dady ne yake tambayar abba ya suke da baba. Abba yacewa dady baba aminin sane ya zama kamar Wan uwan sa na jini ma, haka zalika yaran su ma aminan juna ne, aisha da amina.



Jinjina kai dady yayi tare da cewa  masha allah, Allah yayi masa rahma . dady shima bai Soyewa abba abinda ya faru ba, ya bayyanawa abba gaskiyar zance akan yaron sune anin doctor ya bige shi cikin rashin sani. Abba yayi mamakin hakan sosai, to amma sai ya sake wantarwa da dady hankali, da cewa addara ce kuma da ajali. Haka abba yayi ta wantarwa da dady hankali saboda yaga hankali dady ya tashi sosai, ko ace ma hankali sai yana tashen har lokacin.....



Yau ma gidan mutuwa ya cika sosai da an gaisuwa fiye da

24 / 38