Doctor Ashmal Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Huguma Category :  Love

Chapter   25 / 38

72K to 75K   out of 111.1K words

jiyama. Mutane ne suke zuwa ko ta ina da yake, baba yana da mutane ba laifi. kuma ga sauran ´an uwa na nesa da ´an makarantar su meenal.



Yau ma meenal wuni tai da ciwan kai tun shekaran jiya rabanta da taci abinci, tun wanda taci a gidan su momy bata sake ci ba, saboda tasan ba zata iya ciba ma yau azumi ta Wauka, ta mayar da shi na ramuwa.



Da magriba ma tayi ansha ruwa, bayan meenal tai sallah kasa cin abinci tai saboda tsananin damuwa, da ™yar mami de ta tursasawa meenal taci abinci, shima ba wani mai yawa ba sannan tasha ruwa.



Sai wajan ™arfe 11:00pm meenal ta samu salama da yake mutane sun ragu sosai kuma an gama share-share da wanke-wanke, sai taji kunnan ta yayi mata sakayau, saboda bata san yawan hayaniyar nan. Meenal ji tai gaba Waya bata jin daWin cikin ta dan yau 2 days raban da tai wanka. Duk da fankar da take kaWawa amma tana Wan jin zafi-zafi, dan haka mi™ewa tai ta Wauki towel ta shiga toilet domin wanka.



Ita kuwa ma'eeshat tana daga gefe tana danna wayar meenal tana ta karSar gaisuwa a online madadin meenal Win. Tana yi tana tunawa da sahibin ta doctor ashmal, da yake yau kimanin 2 days basu yi magana ba,.



tun da aka gaya musu mutuwar baba da zasu tawo ta manta ma da wayarta ta a bedroom Win ta. Amma yau de tacewa ummi ta Wauko mata wayarta gobe in zata zo, saboda ma'eeshat ba zata iya jure rashin jin muryar doctor ba, ko kuma rashin chat, gaba Waya ta shiga damuwa.



Bayan meenal ta futo daga toilet Waure da towel a ™irji direct wardrobe Win kayanta ta nufa, ta ciro wata doguwar riga mara nauyi sosai, bayan ta Wauko rufe dorowar tai, sanan ta buWe Wayar ta Wauko bra da pant sanan ta rufe ™wabar. Sai da meenal ta bawa ma'eeshat baya sanan ta iya saka kayanta, ta yarda bayanta da duwawukanta kawai ma'eeshat zata iya gani.



duk da kuwa ma'eeshat Win hankali ta baya kanta, amma meenal ta cika jin kunya ne. Dan da ma'eeshat ce zata sa kayan to tass, a gaban meenal taza iya sawa ba tare da ta bata baya ba,. Sau nawa ma ma'eeshat tana saka kaya gaban meenal sai dai meenal Win ta Wauke ido, tai tai wa ma'eeshat faWa, tana cewa bata da kunya. itama ma'eeshat Win ta Wauki meenal kamar ´ar uwa, jinta take kamar twins shi yasa zata iya komai gabanta.



In ba gaban mamin ta ba ko meenal Win ba gaban wanda zata iya buWe tsiraicin nata. itama meenal bawai dan bata yarda da ma'eeshat bane take kin cire kaya ko sawa a gabanta a'a kawai tsabar tsananin kunya ce, amma wataran in tana sauri shirin tafiya makaranta, tana iya canza kayan gabanta ma.



Meenal bayan ta gama shiryawa kusa da ma'eeshat ta dawo ta zauna jiki a sanyaye. ma'eeshat tana ™o™arin magana sai ga kira ya shigo, wayar meenal Win da take hannun ma'eeshat. ma'eeshat da take danna wayar Wagowa tai tare da kallon meenal tana cewa  yaya waleed ne yake kira .



Kawar da kai gefe meenal tai tare da cewa "dan Allah ki rabu da shi, ni ba wata waya da zan iya yi da shi". gyaWa kai ma'eeshat tai sannan ta ajiye wayar tana cewa "tom shikenan yarda kika ce ya jikin naki?".



"Lumshe jajayan idanuwa meenal tai, kafin tace da sau™i". ma'eeshat sake tambayar meenal tai da "ko na kawo miki maganin ciwan kai da ruwan ki sha?". meenal tana ™o™arin magana wayarta ta fara saban wani ringing".



Wani siririn tsaki meenal taja, dan tasan ko ba'a gaya mata ba waleed ne. ita kuma ma'eeshat bin meenal da ido tai gaba Waya bata so tai mata dole akan ta Wauki wayar waleed. "wallahi ma'eeshat na gaji da nacin waleed, ko bai san halin da nake ciki ba ne ya barni na huta mana".



Dafa kafaWun meenal ma'eeshat tai kafin tace "kiyi ha™uri ma'eeshat, waleed Win ne gaba Waya ya haukace, wani irin mahaukacin so yake miki wanda baya iya control Win kan sa, dan Allah ki Waga naji muryar ki ko na 20 second ne, may be hankalin sa ya ™wanta".



TaSe baki meenal tai ba tare da tace komai ba har wayar ta katse. Bayan wayar ta katse wani kiran ne ya sake shigowa, again waleed Win ne. hannu ma'eeshat tasa ta Wauki kiran, tana Wauka ta karawa meenal a kunne.



Da ™yar meenal ta iya amsawa waleed sallamar da yayi murya a dashe. wata wawuyar ajiyar zuciya waleed ya saki wanda ta yau ma tafi ta ko wace rana. Murya na rawa yace "meenal Wina ya kike fatan kina lafiya ya ™arin hakurin baba?". Murya a sanyaye meenal ta bawa waleed amsa da "alhamdulilah" "to Allah yaji™an baba yayi masa rahma yasa ya huta, Allah yasa annabi yasan da zuwan baba" "ameen ya rabbi nagode sosai waleed" "meye na godiya meenal, nima ai baba na ne ko".



HaWiye yawu meenal tai kafin tace "haka ne" "tom dan Allah meenal Wina kiyi tawakkali naji muryarki ta nunamin kina cikin tsananin damuwa sosai, Allah ne ya bamu baba kuma ya fimu san sa, shi yasa ya Wauki kayan sa, yanzu tsakanin ki da baba addu'a ce, kiyi ha™uri ki daure duk da mutuwar iyaye tana da zafi to amma dole sai anyi ha™uri".



"Wasu zafafan hawayan tausayin waleed da tsausayin kanta ne zuka zubowa meenal, a zuciyarta tace oh Allah sarki shi waleed bashi da uwa bashi da uba yake bata ha™urin rashin da tai, ai shine abun tausayin ma, kuma gashi ana so a raba ta da shi, ko tace an raba ta da shi ma.



Muryar waleed meenal ta sake tsinka yana cewa, "kinji meenal Wina dan Allah ki dena yawan kuka da damuwa" meenal saisaita muryarta tai yarda waleed ba zai gane tana kuka ba ko maganar da yayi gaya mata ta tsinka mata zuciya ba.



"Tom shikenan waleed nagode sosai da shawararka kuma in sha allah zanyi amfani da ita, yanzu ina so nai bacci ne bye". "tom shikenan meenal Wina bye i love you for ever . daga haka meenal bata sake cewa komai ba ta Wan ture wayar da ma'eeshat ta ri™e ta kara mata a kunne.



Katse wayar ma'eeshat tai, bayan ta katse kallon meenal tai tare da cewa "yauwa ko ke fa na kawo miki maganin ciwan kan kisha koh?". gyaWa kai meenal tai alamun eh, ma'eeshat kuwa mi™ewa tai domin kawowa meenal maganin.



Ma'eeshat magugguna uku ta kawowa meenal, dana ciwan kai sai ciwan jiki, da kuma wanda zai sata tai bacci, tare kuma da ruwan jarka. Bayan ma'eeshat ta buWewa meenal ruwan, mi™a mata tai sannan ta fara Sallo mata magungunan tana bata, ita kuma meenal tana sha.



Bayan meenal ta gama sha, ma'eeshat cewa tai ta tashi daga kan gadon domin ta gyara bedsheet Win saboda duk ya yamutse. Ma'eeshat bayan ta gyara bed Win pillow ta sakawa meenal Win sannan ta kamo hannunta ta ™wantar da ita kan gado ta lulluSa mata blanket.



Bayan haka ta koma ta kashe musu hasken Wakin kamar yarda meenal ta bu™ata, sannan ta kunna futula caji mara haske. daga haka itama ma'eeshat ta ™wanta akan gadon. Shiru ne ya ziyarci wajan kafin meenal tai ™arfin halin cewa  ma'eeshat kinyi ™o™arin naga baki zo da wayarki ba, nasan kina nan kina tunanin doctor Win ki Koh? .



Murmushi ma'eeshat tai sannan tace  uhmm ke de bari meenal to ya za ai mutuwa ba wasa ba, amma saboda tsabar tunanin sa ni gani nake wata mata suna yimin kama, da na Wauka shige suke amma sai kullum nake ganin kamar su tana ™aruwa sosai .



cikin mamaki meenal tace  wata mata" dan ita tama manta da babin momy maman doctor ce. "Wata mai haske haka wanda naji kina ce mata momy, wata mai kirki haka". Cikin dashashiyar murya meenal ta katse ma'eeshat da cewa "sada™allahul azim, yi shirun ki momy ko, ai kam maman doctor ashmal ce in gaya miki ita ta haife shi, shine babban Wanta ma".



Da sauri ma'eeshat ta tashi daga ™wanciyar da tai tare da cewa "kai haba da gaske, ke waye ya gaya miki?" meenal gyara ™wanciya tai tare, da cewa  ina ta zuci-zuci na same ki na baki labari, sai kuma mutuwar baba ta riske mu".



"Allah ya ji™an baba, ma'eeshat ta faWa jikin jimami". "Ameen ma'eeshat, kin san gidan da nake ™wana wajan momy, gidan su ne fa, ni ban taSa sani ba sai daran ™arshe naga doctor ya shigo, wata ™anwar sa yesmeen ta tafi ta rungume shi tana masa oyoyo, to naji ana ta gai da shi, nima bayan na gai da shi kamar ance in Waga kai na kawai naga doctor ki, wai ashe ™anin sa ne ma ya bige baba a mota". cikin ruWu ma'eeshat ta zaro ido tare da dafa ™irji tana cewa "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, dan Allah ™anin doctor ne ya bige baba?".



"Eh ma'eeshat shine amma ya za'ai ™addara ce kawai". shiru ma'eeshat tai murna ta koma ciki da taji abinda ™anin doctor Win ya aikata. jiki a sanyaye ma'eeshat tace  amma shine baki taSa gayamin ba sai yanzu .



"Ai nima nace miki ban san ™anin sa bane sai daran da baba zai rasu, kuma nayi niyar, washe gari in muka haWu na baki labari, sai baba ya rasu, nima dududu ban fi ™wana biyu da sani ba". "jiki a sanyaya ma'eeshat ta ™wanta tare da cewa eh hakane kam".



To daga haka ba jimawa bacci gajiya, wahala, damuwa, ya kwashe meenal, ma'eeshat tayi farin cikin hakan sosai ganin meenal ta samu bacci itama ba jimawa bacci yayi awan gaba da ita......



DOCTOR ASHMAL



Gaba Waya doctor yana cikin tsananin damuwa 2. na farko rasuwar baba, yana tunanin in ma'eeshat ta samu labari ™aninsa ne ya bige baban ™awarta kar tace ta dena son sa, dan yasan halin yarintarta da kuma yarda take matu™ar ji da ™awar nan tata.



Na biyu kuma too days ya dena samun ma'eeshat a waya ga rashin jin muryarta. hakan ba ™aramin tayarwa da doctor hankali yayi ba, doctor bai taSa tunanin haka yake mugun son ma'eeshat ba sai yau. kuma bai taSa ganin tasiri da sha™ura da su kai ba sai a lokacin.



kuma a lokacin doctor ya gane amfanin wayar da yake da ma'eeshat a rayuwarsa. gaba Waya ko hospital yaje baya iya wani aikin kirki yake dawo gida, raban da doctor yaga abinda yake hana shi sukuni ko kuma yake yawan tunanin sa har ya manta a rayuwar sa, kamar yarda yake jin ma'eeshat.



Shi doctor ba wani mutum ne da ya cika sa damuwa da tunanin bane akan sa, tun asalin rayuwarsa ma, kafin a samu abinda yake damun sa za'a jima, amma yau sai gashi ta sanadiyyar so da tunanin ma'eeshat ya kasa aikata komai............



mu haWe a next page.





_page 33





~DOCTOR ASHMAL



~STORY AND WRITING

BY

AMINA BAYERO



~Typing=ØòÜ



Washe gari.



Yau ma anyiwa baba sadakar uku da sassafe, kamar kullum momy tazo ana karSar gaisuwa da ita. sannan momy sun haWu da mami da yake sun samu labarin wajan mazajan su, an gaisa sosai cikin sakin fuska da raha. Momy tayi farin cikin ganin surukar ta ma'eeshat sai wani kaffa-kaffa take da ita, tana nunawa ladidi ita, harma da yesmeen da yake yau da ita kazo, tana cewa tazo taga matar da yayanta zai aura.



Da yake yesmeen tana kusa da meenal saboda sun Wan fi sabawa. yesmeen itama taji daWin ganin ma'eeshat sosai ta gai da ita tana ta sakar mata murmushi. momy ma sosai ta sakarwa ma'eeshat fuska sai kace ba gidan mutuwa ba sai wani jan ta take a jiki.



Duk da ma'eeshat bata wani cika jin kunya ba amma sai da taji kunyar momy sosai. mami taji daWi haWuwa da momy, musamman yarda taga momy nada kirki sosai sai jan ma'eeshat Win take a jiki. A zuciyar mami tana cewa tabbas Wiyar ta ma'eeshat tayi sa'ar suruka.



Ma'eeshat ji tai gaba Waya ta fara jin kunyar momy, kuma gashi ba dama ta Wago kai sai sun haWa ido da momy tana ta faman sakar mata murmushi, ma'eeshat sai mamakin irin mutuncin matar take yi, yarda kasan ta goya ta sai kace kanta aka fara suruka.



Wajan sha biyu ma'eeshat ta ™arbi wayar mami ta bigawa driver kan yazo ya Wauke ta gidan su meenal, ya mayar da ita gida. ma'eeshat ji tai ba zata iya zama ba, sabida mami bata Wauko mata wayar ba wai ta manta, kuma gashi ita ba zata iya jure rashin yin magana doctor ba.



Kuma tana so taje gida ta huta da hayaniya ga kuma kunyar surukarta, momyn doctor da take ji. Bayan ma'eeshat tayi sallah la'asar, lokacin driver yazo Waukan ta, sallama tayiwa meenal, tace mata zuwa azahar zata dawo tana so taje gida.



sai da ma'eeshat taga momy ta tayar da sallah sannan ta yiwa ladidi da yesmeen sallama, tace musu in momy ta idar ko zata neme ta, sai sucewa mata ta tafi gida ba zata jima ba zata dawo, daga haka ma'eeshat ta sulale abinta.



Ma'eeshat tana futa daga gidan su meenal ba Sata lokaci ta shiga mota driver ya tayar suka bar gidan. suna tafe ma'eeshat tana tunanin momy. A zuciyarta tana cewa dama haka ahalin doctor suka da mutunci, ashe duk mutunci doctor ashmal ko ™afar momyn sa bai kama ba.



Ko da yake shi doctor bashi da sakin fuskar kamarta su momy da sa yesmeen, shi in baku saba ba ma kafin kaga murmushin sa ma za ka jima. Itama ma'eeshat sai da suka jima da doctor yake iya yin dariya gabanta, hakan ma ba kullum ba wataran har yazo ya tafi baze mata dariya ba sai de murmushi kawai.



Bayan su ma'eeshat sun ™arasa gifa, driver yana parking ma'eeshat ta futa da sauri. Baki Wauke da sallama ma'eeshat ta shiga babban falon gida. sabuwar ´ar aikin su ce zaune ita da afnan suna kallo a tv.



Afnan tana ganin ma'eeshat ta taso a guje ta rungume ta cikin farin ciki. Itama meenal rungume afnan Win tai tare da Waukar ta, bayan sun gama wasa da dariyar su, ma'eeshat sauke afnan tai sanan ta wuce bedroom Win ta.



Tana shiga bedroom Win ta kayan meenal ta cire daga jikin ta, sannan ta nufi toilet a hanzarce domin wanka. bayan ta futo ™irji Waure da towel riga mara nauyi ta Wauka tasa a jikin ta. bayan tasa kashe AC Win bedroom Win nata tai, sanan ta buWe tagogin saboda ita iskar Allah take son sha ba AC ba.



Daga haka ma'eeshat ™aramar dorowar gefan gado ta buWe ta Wauko wayarta sannan ta kunna ta, ta dawo kan gadon ta zauna. Wayar ma'eeshat tana gama kawowa cireta tai daga security, sanan ta shiga call domin kiran sahibin ta doctor& & &



Gaba Waya yau ya kasa komai a hospital, jiya ya Wanyi ™arfin halin duba wasu marasa lafiya, amma yau ya kasa, dan haka bayan yayi sallah azahar office ya koma ya Wauki laptop Win sa da wayoyin sa, sanman ya fice daga hospital Win.



Doctor yana shiga mota ya ajiye wayoyin sa da laptop Win sa a kan kujerar gaba, sannan ya Wan ™wantar da kujerar motar domin ya samu ya ™wanta dan gani yake baze iya driver yanzu ba saboda damuwa.



Lumshe idanuwan sa yayi, kamar mai bacci yana tunanin ma'eeshat, saboda me wayarta take a kashe, kuma babban tashin hankali doctor ma'eeshat bata neman sa ko ta wace wayar dan yasan ta haddace number sa.



Doctor ya Wauki kimanin 30 minutes a haka dan har bacci ya fara Waukar sa sama-sama, kawai yaji wayarsa ta fara ringing. Ji yayi kamar kar ya buWe idanuwan sa, har wayar ta kusan katsewa ya Wan buWe idanuwan sa, sannan ya juyar da kan sa gefe daga ™wance dan yaga me kiran.



Tuni idanuwan doctor suka washe damuwa bacci suka fuce a lokacin, saka ma™wan ganin ma'eeshat tana kiran sa. da sauri doctor ya kai hannu, amma kafin ma ya Wauki wayar kiran ya katse. doctor yana Waukar wayar ya fara ™o™arin bin ma'eeshat Win.



Amma kafin ma doctor ashmal ya kai da bin ma'eeshat Win, itama ta sake kiran shi. sai da doctor ya Wan ja aji kaWan kafin ya Wauki kiran, duk da kuwa damuwa da ma'eeshat Win da yayi amma abin a jinin sa yake, komai a nitse yake.



Doctor bai kara wayar a kunne ba a handsfree ya saka ta sanan ya rufe ido kamar dazu, kafin ya rangaWawa ma'eeshat sallama cikin dadaWar muryarsa.



Bayan ma'eeshat ta amsa sallamar ™arawa tai da cewa "ai nayi tunanin ba zaka Wauki wayar tawa ba". "no me zai hana na Wauki wayarki kuwa?". gyara zama ma'eeshat tai kafin tace "aiki mana, nasan ko aiki yayi ma yawa".



Murmushi doctor yayi a zuciyarsa cewa yayi  hmmm lallai baki san halin da na shiga bane rashin ki amma a fili cewa yayi "a'a ko ina aiki in de naga kiran ki zan Wauka mana sai nace miki aiki nake a lokacin, bayan na gama kuma sai muyi wayar".



"Tom yanzu de fatan ba aikin na katse maka ba Koh?" "a'a kin kirawo a dede bana aikin komai sai aikin tunanin ki". "hmmm banga alama ba ai nayi tunanin baka damu dani ba".



Murmushi ya™e doctor yayi, saboda shi ba mutum bane wanda zai iya tsayawa yana faWar adadin damuwar da ya shiga akan abu, a ganin shi hakan ba tsari bane, amma da zai iya gayawa ma'eeshat damuwa da ya shiga akan ta, daya bata labari.



Amma a fili cewa yayi "hmmm rigima ko na damu dake mana sosai eshata, ina kika shiga kika manta da ni haka ko laifi nai miki". "Kai ma kasan bazan manta da kai ba, baban meenal aminiya ce ya rasu kaga kuma kamar babana ne dole na shiga damuwa".



Dama doctor yasan abinda zata faWa kenan kawai ya tambaye ne "innalillahi Allah ya ji™ansa da rahma yasa ya huta, zan zo nai miki gaisuwa har gida". "Ameen kai kenan baka sani ba sai yanzu, ai nayi tunanin zaka sani tunda ance ™anin kane ya bige shi har ya ™wanta gadon hospital kafin ya rasu".



"Eh na sani, kuma

25 / 38